Showing 123001 words to 126000 words out of 300844 words
ana monitoring warkewar gurin da aka yi masa aiki internal da external. It has not been easy on him duk da cewa Hassan yana tare dashi kuma likitocin suna kulawa dashi sosai, magana mai dadi, karfafa guiwa, da tabbatar da cewa he is comfortable. Shi kansa yasan ya rame, tun kafin ayi aikin kuma ya rane din dan Fatima tasha yi masa mita a waya cewa ya rame, tun yana kakkaucewa har dai ya daina kiran ta video call itama kuma inta kira baya dauka sai yace mata phone dinsa ta samu matsala.
A haka har ya fara jin dadin jikinsa, su kansu doctors din suna yabawa da yadda jikin nasa yayi kyau, ya rage yin amai sosai wanda yana daga cikin side effect na chemotherapy kuma shi yake saka rama, saboda jikinsa ya fara sabawa da magungunan da ake bashi. Sai kuma ya dage da cin abinci, ya kuma cire damuwa a ransa nan da nan ya kara murmure wa. An gama radiation therapy din, magunguna ne kawai yake sha dan haka ya fara maganar yana son ya tafi gida. Da farko doctor din yaki yarda, ya fi son ya kara kwanaki ciwonsa ya kara warkewa duk da cewa ba zasu tabbatar da cewa surgery din is a success ba sai bayan wata uku sannan zasu sake dubawa su gani idan cancer din bata dawo ba, still daga nan ma ba za'a saki kiji ba za'a cigaba da dubawa bayan wata uku uku har sai an tabbatar ta tafi.
Sai daya tabbatar jikinsa yayi kyau sannan ya kira Fatima video call, suka yi hirar su ya tabbatar mata nan da kwana biyu zasu dawo, dan shi kam ya gaji ko ba'a sallame shi ba guduwa zaiyi.
*Nigeria*
Tun bayan tafiyar su Hassan sai Ruqayyah ta samu sake, a lokacin ne ta samu damar zuwa ta ga dakin Minal. Gidan ta mai kyau kuma mai girma part dinta daban na uwargidan ta daban, shi kuma mijin ya raba kayan sa a tsakanin su tunda akwai dakin sa a kowanne part. Minal ta baje sosai abinta ta na zuba wa uwargida rashin kunya son ranta yayin da shi kuma mijin ya ja bakinsa yayi shiru, yan uwan miji ma sun fara dawowa gurin Minal musamman uwar mijin da shekarun ta suka riga suka ja kuma bata da buri irin taga jikokin ta daga ɓangaren Alhaji Kabiru kuma a yanzu dukkan hopes dinsu yana kan Minal tunda suna ganin cewa rashin haihuwar daga matar ne ba daga mijin ba. Wannan yasa uwargidan mai suna Hajiya Baraka ta ja kofar part dinta ta rufe, bata gani ba ballantana ranta ya baci, babu mai shigar mata sai nata bakin idan sunzo, sai kuma mijinta idan ranar kwanan ta ce.
Ranar wuni suka yi suna hira, farko Minal ta nuna fushin ta akan kin zuwa bikinta da Ruqayyah tayi, daga baya kuma sai ta sauko ta nuna dama ai tasan wannan matsolon mijin na Ruqayyah ne zai hana ta zuwa dan kar ya kashe kudi. "Ni dai Ruqayyah da Allah ya bani miji irin naki gwara in yi ta xama a gida, ya za'a yi ina kallon dukiya kuma ace ba zanyi abinda nake so da ita ba? Kema walllahi da laifin ki, ai wallahi idan ni ce ba ka isa ba, a matsayin na na matar ka sai nasan yadda nayi na lankwasa ka kabi ra'ayi na wallahi" Ruqayyah ta tabe baki tace "kema dai kya fada Minal, ke ni fa duk kwanan nan abubuwa sun cushe min wallahi, ji nake yi ma kamar ba ya sona yanzu. Irin soyayyar da nake gani a idonsa yanzu duk sai inga kamar babu" Minal tace "haba dai! Kuna nufin ki ce min babban makamin naki ya ragu? Soyayyar da yake miki ce fa take rike dake a gidan, wallahi kar ki bari ta tafi, chafdi, ki zo mu koma gurin Malam a juyo miki da hankalin sa kachokan ya dawo kanki. Ke ba ki ga yadda mai gidan nan da yan uwansa suke rawar kafa a kaina ba? Ai ba haka na barsu ba fa".
Ruqayyah ta dauke kai gefe tace "ke raba ni da wannan malamin duban, ki barni kawai zan samar wa kaina mafita dan ni tsoron malaman nan nake yi wallahi, na tabajin ance aikin su gaba yake ci sannan ya dawo ya ci baya, ku barni in lallaba kawai" Minal tace "sai kiyi ta lallabawar ai. Ni kam babu wata lallabawa da zanyi a rayuwa" sai kuma tace "ni bamu yi maganar wannan maganar da Malam yayi a kanki ranar nan ba, na cewa zakiyi kudi. Kinga fa maganar sa ta fara tabbata tunda gashi kin haifi yara biyu kamar yadda yayi alƙawari" Ruqayyah tayi murmushi tace "maganar da nake miki kenan ta lallaba war ai, na sani duk wani kudi da zan saka ran yi to ta hanyar Hassan zai taho, dan haka nake lallaba abuna har zuwa lokacin da zamu ga abinda rayuwa zata zo mana dashi kuma" Minal tayi dariya tana dan dukan Ruqayyah tace "munafuka, ashe dai kim yarda da Malam din tunda kin yarda da maganar sa. Ina tabbatar miki da cewa abinda ya fada zai faru din. Ni dai fatana daya shine Ruqayyah kar ki samu duniya kuma ki manta dani, ko me kika samu ina so na zama a hannun daman ki" Ruqayyah tace "a'a ban yi miki wannan alkawarin ba Minal, za dai ki zauna a hanun hagu na amma Sumayya ita ce a hannun dama na" Minal ta bata rai, "shikenan tunda wariya za'a nuna min, hannun hagun ma ban raina ba".
Sai dare Ruqayyan ta koma gida, bata shiga gurin Aunty ba dan kar tayi mata fadan ina taje ymtayi dare haka sai ta wuce part dinta ta hau sama direct tunda ta riga taci abincin ta a can gidan. Tayi wa yaranta wanka tana ta yi musu wasa suna dariya gabaki daya, tana jin son si sosai a zuciyarta irin son da bata taba yi wa kowa irinsa a duniya ba. Sai dai kuma a ranta tasan bata son su taso a karkashin masu kudi, tafi son su taso a matsayin masu kudi kuma tasan she is going to make the right decision at the right time. Ta dauki wayarta ta kira layin Hassan na india. Kullum kamar lokacin suke yin waya duk da shi a gurinsa cikin dare ne amma ta fahimci kamar baya bacci sosai, ko kuma da rana yake baccin ne oho.
Ring daya ya dauka yace "yanzu nake tunanin kiran ku inji yadda yarana suka wuni" ta bata rai kamar yana kallonta tace "yaranka kadai? Ni ba zaka ji yadda na wuni ba? Allah sarki ni babu mai sona" ya danyi murmushi yace "ni na isa ince haka? Kin san yadda kike hana min bacci kuwa?" Tace "kamar gaske, baya ka fin ku tafin ma wani shashshare ni kake yi" yace "na tuba ai, kwana biyu da babu ke ai jiki na ya gayamin" tace "kai da baka da lafiya? Ko dama ciwon na yan gayu ne" ya danyi dariya, sai taji wani iri, yaushe rabon da taji yayi dariya ko a wayar ne tana iya jiyo rashin nutsuwa a muryarsa, tace "masha Allah, jiki yayi sauki kenan" ya juya ya kalli Hussain da yake ta danne danne a wayarsa, yace "sosai ma, alhamdulillah is all we can say" tace "alhamdulillah. Sai shirin dawowa kenan ko? Kaga ni ina son mijina ya dawo fa" ta fada da shagwaba, ya sake dariya "ki sha kurumin ki yarinya, in nazo har sai kin gaji dani". Suka jima suna hirar su, ko da wasa bata gaya masa taje unguwa ba, ta kara wa yaran wayar duk da basu san me take yi ba amma shi ya jiyo motsinsu kuma yaji dadi a ransa. Tabbas yaya rahama ne dan komai bacin ra sa ko zancen su yaji anyi sai yaji ransa yayi dadi. He can't imagine zuciyar Hussain, bayan wannan ciwon kuma ga babu haihuwa yet.
Washegari ta tashi da gyaran dakinsa tunda taji yace sun kusa dawowa. Duk da dai ba wani datti dakin yayi ba dan fes ya tafi ya barshi kuma tunda ya tafi bata bude dakin ba. Ta dan karkade kura ta gyara abinda yake bukatar gyara sai ta bari da niyyar sai ana gobe zasu dawo sai ta kuma gyarawa ta wanke toilet. Anan taga system dinsa a kan study table dibsa tare da takardu, ita ta dauka da ita ya tafi dan haka bata lura ma da ita a gurin ba, sai kawai ta dauka ta hau kan gado ta bude ta fara dudduba abubuwan ciki, babu komai dan shi ko irin videos din nan ma ba ajjiyewa yake yi ba duk yawancin tarkacen kayan office ne, har tayi kamar zata rufe sai kuma zuciyarta ta raya mata cewa ta duba e-mail dinsa, maybe ta samu something interesting. Ta bude ta fara bin mails din briefly, suma duk tarkacen office ne dan ba ma gane me ake cewa take yi ba. Sai kuma idonta ya sauka akan wani "re_suspected Cancer patient" ta bude ta karanta, ta kuma karantawa tana so ta fahimta, ta dauko wayarta tana duba ma'anar wasu daga cikin kalmomin da akyi amfani dasu, sai da tayi wa e-mail din filla filla sannan ta fahimci cewa wani doctor ne a india ya rubuto yana gayyatar "Hussain Aminu Abdullahi" yaje za'a yi masa gajin cancer. Ta duba date din taga kwanaki kadan kafin tafiyar su, sai kuma taga wani email ne na Hassan wanda ya turawa doctor din akan yana son ganinsa amma kuma info din na Hussain ne.
Ta cigaba da bincike amma takasa samun wani abu da zai kara fahimtar da ita cikakken ma'anar abinda ta karanta din, Cancer, Hussain, India. Haka ta wuni da abin a ranta kuma can kasan zuciyarta tana jin wani excitement yana taso mata. Tana jin maanar abin tana kwanta mata a zuciyarta, Hussain yana fama da cutar cancer, wannan shine dalilin zuwansu India ba wai zazzabin da Hassan yayi ba. Yes, ta samu wannan information din amma me ya kamata tayi dashi? Ta yaya zata yi amfani dashi to her own advantage?
Sai dare sannan ta yanke shawara. Dakin Hassan ta koma ta samu wata newspaper ta zauna tana duba front page din a hankali har taga hotline dinsu, ta dauka a wayarta sannan ta sauka kasa ta aika a ka siyo mata sabon sim card, ta dawo dakinta ta zauna ta saka a wayarta sannan ta nemo waccan number din data yi saving ta tura message.
"Hussain Aminu Abdullahi, the CEO of H and H is suffering from cancer and currently receiving treatment in india"
sai ta rubuta address din asibitin data gane tare da email din ta tura. Sai data tabbatar ya tafi sannan ta zare sim card din ta balla shi ya jefar. Tayi murmushi yana jujjuya wayar a hannunta. "Let's see how Fatima will react to this".
**********. **********. *********
Tun tafiyar su Hussain Fatima bata jin dadi, ji take gabaki daya kamar duniyar tayi mata zafi duk kuwa da cewa kullum suna makale a waya amma empty take jin duniyar ta. Wannan yasa ta roke shi akan zata je kano ta dan zauna kafin ya dawo, bai yi tunanin komai ba ya bar ta ta tafi saboda tunda akayi auren su bata taba zuwa ta zauna a gida ba, on few occasions ne yake barin ta tayi weekend kuma yasan tana missing gidan sosai duk da bata taba yi masa complain ba. Babu bata lokaci ta shirya ta tafi, sai ta dauki Khadijah suka tafi tare dan babu abinda take yi a gida a lokacin.
Satin ta daya a gida, kullum sai sunyi video call da Hussain sau uku kamar yadda yayi mata alkawari kuma hakan yana debe mata kewa sosai. Sai dai problem dinta daya shine yadda taga kamar yana ramewa, tayi complain sai yace mata ai kewarta ce take damun sa. "To ku dawo mana" ta fada kamar zata yi kuka "bana jin dadi da baka nan, kullum zuciya ta sai in ringa ji kamar wani abin yana faruwa wallahi, ga faduwar gaba, kuma duk dan baka nan ne" yace "ya zanyi in taho in bar Hassan baya bashi da lafiya? Kimga ai ban kyau ta ba ko? Gashi ciwon nasa kamar karuwa yake yi ni duk hankali na a tashe yake, an bamu wasu test da za'a yi da hotuna da za'a tabbatar da me yake damunsa" sai kuma taji babu dadi, kamar ba ta kyauta ba da take cewa Hussain ya bar dan uwansa ya dawo gurinta. Tace "to maybe ma damuwar hakan ce ta saka nake ganin kamar ka rame, ka daina damuwa sosai kaji Mi Amour? Zai samu sauki kaji?" Yace "insha Allah. Amma duk da haka a zamu dade ba nan gaba, in anyi test din zamu taho in results ya fito ma dawo" tace "noo, ku tsaya kawai a bashi kulawa sosai. In abun zai dauki lokaci sai in dauko Ruqayyah muntaho tare kawai, na tabbatar shima zai bukaci matarsa a kusa dashi" Hussain yace "yeah right. Nima kuma ina bukatar matata a kusa dani."
A hankali take lura da yadda nayayin sa yake cigaba da kalacewa, kullum kuma sai tayi masa complain, hakan yasa ana gobe za'a yi masa aikin yace mata wayarsa ta lalace ba zata yi video call ba sai dai suyi voice. Wannan yasa ta sake tabbatarwa da cewa something is definitely wrong, tasan cewa karya yake yi mata amma sai ta kasa karyata shi din. Babu yadda za'ayi Hussain ya zauna da lalatacciyar waya, wayar da bata yi komai bama Hussain yana chanjata zuwa sabuwar yayi ballantana ace wayar da tayi lalacewar da zata hana shi ganin ta? He is definitely hiding something.
Wannan yasa ta tattara ta dauki Khadijah suka koma Kaduna, ta samu Aunty ta zayyana mata abinda suka yi da Hussain ita ma kuma auntyn ta tabbatar da maganar Fatima sai dai sun kasa gane dalilinsa na yin hakan, sai Aunty kawai ta bawa Fatima shawarar su yi ta addua, dan Hussain ba mutum ne mai boye boye ba tunda har ya boye to abu ne mai muhimmanci a gurinsa, ta tabbatar duk abinda yake boyewa in ya dawo a hankali zasu sani.
Sai dai hakan bai sa baccin Fatima ya dawo gare ta ba, sai dai ta dauki shawarar Aunty bata nuna masa ta fahimci yana boye wani abu ba kuma ta dage dayi masa addu'a da fatan alkhairi aduk abinda yake gabansa......
Sai dai sati daya bayan dawowar ta, sai gashi ya kuma kiranta video call, kuma sai taga yana looking much better than ganinsa da tayi na karshe sai dai shadow din da yake kwance a kasan idonsa. Tace "you look so handsome" yai murmushi yana saka hannu tare da kara gyara gashin kansa yana kashe mata ido yace "Hussain ne fa, Hussain will always look handsome" tayi dariya "kai ka fiya son kanka da yawa" sun jima suna hira, yana tabbatar mata da cewa Hassan ya samu sauki sosai kuma nan da kwana biyu zasu dawo gida. A ranar tayi bacci mai dadi sosai.
Sai dai..........
Washegari a morning news ana fadar major headlines na jaridun kasar nan taga katon hoton mijinta ya cika screen din tvn ta, da rubutu a kasa.....
"Hussain Aminu Abdullahi, H and H boss, is suffering from colon cancer and currently receiving treatment in India"
Ta saki kofin tea din hannunta idon ta a cikin na Hussain din da yake murmushin sa da baya rabuwa dashi. Sai news din ya cigaba yana nuno hotunan Hassan dana Hussain, kunnuwan ta basa jin abinda ake cewa, amma daga hotunan ta fahimci a asibiti ne sannan basu sani ba ake daukan su, kuma yanayin hotunan yana nuna Hussain din ne marar lafiyar. Screen din ya tsaya akan hoton Hussain a kwance akan dago, ga naurori a zagaye dashi, ga kuma doctors a tsaye a kansa.
Kwakwalwar ta tayi blacking out, sannan ita ma ta zame ta bi kofin shayin ta zuwa kasa.
Yarinyar ta da abin ya faru a gabanta ce ta saka ihu, sauran jama'ar gidan suka zo tare da Khadijah wadda tun tafiyar Hussain a gurin ta take, ganin halin da take ciki ya saka Khadijah ta kira aunty ta gaya mata sannan tace a samu driver a tafi da ita asibiti, ita Khadijah sam bata ga labaran ba saboda kafin ta futo daga daki an dauke gurin an tafi wani labarin daban.
Adam aka kira cewa ya kawo mota za'a je asibiti, sai dai yanayin da aka tarar dashi shima a rikice yake, dan shima akan idonsa akayi labarin. "Dama oga Hussain bashi da lafiya? Dama tafiyar da suka yi asibiti ya tafi?" A hakan dai ya dauko motar aka saka Fatima, Aunty da Khadijah suka shiga Aunty tana kiran doctor dinsu tana gaya masa gasu nan akan hanya. Sannan dauko robar ruwan data fito dashi a hannunta tana bismillah tana shafawa fatima a fuskarta, tana kuma zuba mata har cikin rigarta. Ta sauke ajjiyar zuciya a hankali tana dan bude idonta ta dora su akan Aunty. Aunty ta fara jera mata sannu, ta juya ta kalli Khadijah tace "ya dawo? Kun kira shi a waya ya taho?" Khadijah tace "waye?" Fatima ta juya tana kallon Aunty tace "Hussain Aunty ashe abinda yake boye mana kenan?" Sai ta rushe da kuka tana tuno fuskarsa a zagaye da doctors. "Na shiga uku ni Fatima Allah ka tashe ni daga wannan mummunan mafarkin. Dan Allah Aunty ki ce min mafarki nake yi Hussain lafiyar sa kalau" Aunty ta rungume ta "Hussain lafiyar sa kalau mafarki kika yi, ban san me kika gani a cikin mafarkin ba amma mafarki kika yi dan Hussain dina lafiyar sa kalau babu abinda ya same shi dan dazu ma munyi waya dasu" ta rike fuskar Aunty "ba mafarki nayi ba aunty a tv na gani. A labarai na gani sunce Hussain bashi da lafiya wai cancer ce take damunsa yana asibiti, har da hotuna suka nuna Aunty, Aunty Hussain dina....." Sai ta rufe fuskarta tana kuka mai