Showing 141001 words to 144000 words out of 300844 words
kiran wayata" Fatima tayi zumbur ta mike daga kwanciyar da tayi bayan ta gaji da kiran number din Hussain. Ruqayyah ta ce "Hello, yallabai" sai taji muryar Hassan yace "Hassana kuna ina yanzu?" Ta dan kalli Fatima tana girgiza mata kai sai tace "yanzu muke shigowa garin Abuja ni da Fatima, muna ta missing dinku a gida shine muka biyo ku dan ba ..........." Yace "listen to me please. Ki gaya wa Lawan ki ce inji ni nace ya juya mota ku koma Kaduna yanzu, muma mun gama duk abinda muke yi yanzu muke shiga mota zamu taho" tace "to mu karaso mana sai mu dawo tare?" Yace "Ruqayyah, just do what I said please. Ina Fatima?" Ta kalli Fatima da take zaune a edge of her seat tace "gata nan muna tare" yace "ki kula da ita please Ruqayyah, kuna zuwa gida u tafi part din Aunty ku jira mu karaso please. Dan Allah Ruqayyah kiyi haka kinji?" Tace "me ya samu muryarka ne?" Yace "mura nake yi" ta dan tabe baki tana jin haushin yadda yake jaddada mata ta kula da Fatima kamar wata yar gold, tace "shikenan, za'a yi duk abinda kace" yace "good" ya katse wayar.
A lokacin ne wani Doctor ya fito yana yi masa maganar yazo ya bude dakin da Hussain yake za'a yi preparing dinsa for release. Sai yaki basu key din instead sai ya mike da kansa ya tafi zai bude musu, dai dai nan yaji gabansa ya fadi, ya juyo da sauri yana kallon bakin gate yana jin zuciyarsa tana ingiza shi kamar ya fita da gudu ya tafi kaduna a kafa,ya juya kuma ya kalli cikin asibitin yana tuno gawar Hussain a daki. Sai ya dawo da baya ya samu Adam yace "Adam dan Allah tafi kabi su Fatima, in ka gansu a hanya ka kula dasu and make sure sunje gida lafiya, ni zan tsaya mu taho da Hussain a ambulance. Please. Adam ka kula da Fatima kaji?"
Adam ya gyada kai yana ganin ba sai an roke shi ba, abinda Hussain yayi masa ya wuce haka a gurinsa dan haka zai iya ajiye rayuwarsa for Fatima. Ya shiga motar da suka zo da ita ya tayar ya bar compound din asibitin.
A wata mota a gefen asibitin, wanda yake gaban stirring yace "oga, gashi nan ya fito, kuma kamar shi kadai ne a motar" wanda aka kira da oga yace "then what are you waiting for? Follow him. Maybe mu samu chance din kama shi shi kadai"
**********. **********. ***********
Fatima ta kalle ta "ba Hussain bane ba? Me yasa bai kira wayata ba bayan yaga ina ta kiran sa?" Ruqayyah tace "ba Hussain bane ba, Hassan ne yace mu juya mu koma gida suma gasu nan har sun gama zasu taho" Fatima ta fara girgiza kanta tana bubbuga hannunta a jikin kujera "ba dai Hussain ba, Hussain ba zai taba haduwa da Sadiq abokinsa bayan tsahon lokaci sannan su gaisa briefly ba, wani abun ne ya faru, wani abun ne ya faru da Hussain dina"
Sai Ruqayyah taji jikinta yayi sanyi dan itama taji abin odd, mai yasa Hassan zai kira ta da wayar Hussain bayan kuma Hussain din ai biyo lodin kiran da Fatima take masa ba? Bayan kowa yasan irin tsananin son da yake yi mata. Amma sai bata ce komai ba ta gaya wa Lawan sakon Hassan. Bai musa ba ya rage gudun motar lokacin duna gab da shiga cikin gari sannan ya fara kokarin juya motar ya koma hannun dawowa. A lokacin ne sukaji Minal da tun dazu ta dukufa akan wayarta tana ta danne danne ta rafka salati, "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" Fatima ta yunkuro kamar zata mike tsaye, babyn cikin ta ya harba da karfi. Minal ta juyo tana kallonsu idonta kamar zai fado kasa tace "Ruqayyah? Hussain din ku ba shine Hussain Aminu Abdullahi ba" Fatima bata ce komai ba, saboda ba zata iya magana ba, Ruqayyah tace "shine? Me kika gani? Me ya faru?" Ta juyo musu da screen din wayar ta tace "Ya mutu? Gashi nan ana fada a twitter ya mutu a wani asibiti a Abuja"
Idon Fatima ya juye ta zube akan kujerar ta, Ruqayyah ta dora hannu aka tare da rafka salati, and then, Lawan driver ya juyo yanason yaga sakon da Minal take nunawa, wannan abinda yayi hadi da karar kwana, ya saka ya saki stirring kuma maimakon ya taka burki sai ya taka accelerator.
Motar tayi gaba kamar fitar kibiya, ta daki edge din titi sannan tayi adungure da sauri, kasanewar gurin slope ne mai tattare da duwatsu ya saka ta cigaba da gangarawa da sauri tana yin cikin daji. Babu mota a kusa dasu dan haka babu wanda yaga faruwar abin.
Ruqayyah tana salati, tana jiyo salatin drivern tare da Minal banda Fatima da already ta riga ta suma tun kafin abin ya faru, a haka har kanta yayi buguwar da ta daina ganin komai ta kuma daina jin komai. Ta suma.
Lokacin data farfaɗo jin kanta tayi yayi mata nauyi sosai. Ta saka hannu tana dafe kan tare da kokarin yin salati, amma sai taji ba wai kan bane kadai yayi nauyi gabaki daya jikin tane yayi nauyi, ta jima a kwance a inda take sannan ta fara samun karfin bude idonta, abinda ta fara lura dashi shine duhun da gari ya fara yi. Ta dafe kanta ta mike zaune tana numfashi da sauri da sauri har ta samu ta dawo hayyacin ta. Abu na farko da taji a jikinta shine azabar zafin da yake tahowa daga kafarta zuwa sauran sassan jikinta. Gabanta ya fadi tana kai duba izuwa kafafuwan ta. Wani karfe ta gani ya huda naman cinyarta ya wuce. Ta kama shi da hannu daya sannan ta dafe kafar da hannu daya ta zare shi daga jikin ta tana jin azaba tamkar ranta zai bar jikin ta. Sai ta samu kanta da godewa Allah da bata taho da Hussain karami ba. Ta yanki gefen dankwalin ta ta nannade ciwon tana tsayar da zubar jinin da yake yi.
Sai a lokacin tasamu damar karewa gurin da take kallo, motarsu tana can gefe ta daki wata bishiya ta tsaya a kife, tayoyinta a sama, daga inda take tana iya jiyo kauri kamar wani abu yana konewa. Ta mike a hankali tana dai-dai ta tsayuwar ta sannan ta fara jan kafa zuwa inda motar take ta leka ciki, sai ta dawo baya da sauri tana rufe bakinta idanuwan ta kamar zasu fado kasa, kallo daya tayi wa drivern ta san ya mutu saboda yadda wuyansa ya karkace gefe, ta hadiye kukan daya taso mata tana zagayawa barin da Minal take. Idanuwan ta a bude suna kallon Ruqayyah amma ita bata kallon ta, jini yana fita ta kunnen ta da hancin ta. Ta girgiza ta. "Minal, Minal, Minal" amma ita kanta tasan babu Minal ta tafi inda ba'a dawowa. "Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun" ta fada tana kallon katon cikin Minal din wanda ake saka ran haihuwarsa ko yau ko gobe. Ta zame gefe daya ta zauna hannun ta akan ta tana rusa kukan rashin kawarta aminiyarta tare da abinda yake cikinta.
Ta sake tashi tana leka bayan motar tana neman Fatima, babu ita babu alamun ta.
"Fatimah! Fatimah" ta fara kwalla kiran Fatima da duk iyakacin karfinta amma shiru. A lokacin ne ta lura da abinda yake kauri, motar ce take kamawa da wuta daga kasa, nan take tsoro ya kama ta fara kokarin jawo gawar Minal daga gurin da take dunkule a tsakanin karafunan inji amma ta kasa, duk da ita ba likita bace ba daga yanayin kwanciyar Minal din ta tabbatar tayi rugu rugu. Ta zagaya side din driver tayi kokarin fito dashi shima amma injin motar da kuma kujerar sa sun matse shi a guri ɗaya. Ta ja baya tana mayar da numfashi tana kallon yadda wutar take kara ruruwa har ta fara cin seat din baya, hasken ta yana haska gurin, a lokacin ta lura da alamar sawun mutum ya bar gurin motar ya shiga cikin bishiyoyi. Fara bin sawun tana kiran sunan Fatima, tana dauke ganin ta daga wutar da take cin gawawwakin a cikin mota.
A hanya taga wayar Fatima, ta dauka tana lura da cewa bata mutu ba duk da cewa screen din ya fashe amma tana ganin hoton Hussain a jikin screen din yanayi mata murmushi, ta tuna da labarin da Minal ta basu a mota wai Hussain ya mutu. Ta cigaba da kiran Fatima tana kara kutsa kai cikin bishiyoyi, suddenly ta ganta a gabanta kamar an jeho ta tana kallon ta da budaddun idanuwa tana cewa
"help me please, ki taimaka mini dan Allah"
gaban Ruqayyah ya fadi saboda fahimta da tayi cewa wadannan suna exact words din da Hassan ya gaya mata ranar da ta fara ganinsa a toilet din su, and it seemed like a long time ago amma shekaru biyu ne kawai. Ta rike ta "Fatima lafiya kike? Babu abinda ya same ki? Minal ta mutu ita da driver" Fatima tace "mafarki nake yi, ki tashe ni dan Allah. Mafarki nake yi wai Hussain ya mutu, wai munyi hatsari a hanyar Abuja, wai ina labor zan haihu a daji" sai a lokacin Ruqayyah ta lura da jinin da yake bin kafafuwan Fatima. "Innalillahi, na shiga uku, Fatima haihuwa zaki yi" Fatima tace "ki tashe ni daga bacci dan Allah, ki kira min Hussain dan Allah" surutai kawai take yi wanda Ruqayyah tabbatar ba a cikin hankalin ta take ba, ta jata gefe ta kwantar da ita, a haka ta haihu a hannun Ruqayyah, danta namiji katoto dashi lafiyayye.
Ruqayyah ta daga dan bayan mabiya ta fito , ita bata san yadda zata yi ta yanke masa cibiya ba dan batada wani abun da zata iya yanke cibiya dashi. Ta daga shi tana nuna wa Fatima, "gashi kin haihu, kin samu da namiji" Fatima ta karbe shi ta rungume shi a kirjinta duk da ba'a hayyacin ta take ba amma taji matsananciyar soyayyar abinda ta haifa. Hawaye ya zubo mata, Sai kuma ta mikawa Ruqayyah tace "ki kaiwa Hussain shi shima ya ganshi, burinsa kenan yaga abinda zan haifa. Bana so in ganshi ni kadai ba tare da shi ba" Ruqayyah ta karba tana kallon babyn, kamar an tsaka kara shida Hassan, hakan yana nufin kamannin Hussain ne dashi kuma da fatar Hassan tunda yafi Fatima ma duhun fata. Ta mayar da dubanta ga Fatima sai ta ji ta shiru, ta girgiza ta da hannu daya "Fatima Fatima" amma shiru.
Ta mike tsaye tana kallon Fatima sannan kuma ta kalli babyn da yake hannunta yana ta tsanyara kuka da dukkan karfin sa. Shikenan yanzu bashi da uba bashi da uwa kenan? Shikenan yanzu shine....... Sai kuma wani tunani ya fado mata. Yanzu wannan jaririn na hannunta shine sole heir na H and H and all its assets. Dogon gidan Hussain, tarin motocin sa, kamfanonin sa na shinkafa, fulawa, sukari, siminti duk yanzu na wannan yaron ne na hannun ta. Wannan yaron na hannunta shine kadai yanzu abinda yake tsakanin ta da H and H, tsakanin ta da zama matar CEO. Wannan yaron da bai fi ta taka shi ta wuce ba.
Tayi saurin katse wannan tunanin daga ranta tana realizing cewa wannan moment din da take ciki, right here right now shine maganar da malamin duban nan yayi mata. A yanzu tana da options guda biyu, ko dai ta tafi da yaron nan gida ta kaishi gurin Hassan da dauran yan uwa su raine shi ya girma su cigaba da rayuwar su a karkashin sa, maybe ma in ya girma ya wulakanta su tunda basu duka haife shi ba ko kuma ta bayar dashi right here and right now and her husband will have majority share ta H and H. Already ta haifa masa maza guda uku, already gidan sa nata ne.
Ta girgiza kanta da sauri, no no no, no matter how much take son dukiya, no matter how much take son ta zama mai kudi she can never kill for it, ko babba ba zata iya kashewa ba ballantana wannan dan jaririn. Ta tuna da maganar malamin "zabi ya rage naki" ta sake girgiza kai kamar yana kallonta, ta kalli Fatima, tana tunawa da Matsayin ta da martabar ta, sai ta tsallake ta ta wuce, ta fara tafiya a hankali har yanzu vata yanke shawarar abinda zata yi ba. Ta cire dankwalin kanta ta nannade jaririn tare da mahaifarsa a ciki sannan ta cigaba da tafiya, a haka ta fito bakin titi tana kallon motoci suna wucewa amma saboda bata yanke hukuncin abinda zata yi da jaririn hannunta ba sai ta kasa tsayar da mota ta nemi taimakon su, ta cigaba da tafiya a kafa ta cikin bishiyoyin bakin titi, tana cikin tafiyar ne taga wata mota kamar ta Hussain tazo wucewa, sai tayi sauri ta buya, jaririn hannunta ya fara kokarin kuka sai ta toshe masa baki, sai taga kamar motar tayi slowing down kamar zata tsaya sai ta kara shigewa cikin bishiyoyi da sauri.
Kamar daga sama taga wani katon gini a gabanta, a jikin gate dinsa an rubuta baro baro "Nationa Orphanage of Nigeria" ta tsaya tana kallon rubutun sannan ta kalli yaron da yake hannunta "orphane" bashi da uba bashi da uwa dan haka orphane ne kuma babu inda ya dace dashi irin Orphanage. Ba tare da tunanin komai ba tabi inuwar jikin ginin zuwa bakin gate din sannan ta sunkuya ta ajiye shi tana kawar da ganinta daga kansa dan kada tausayin sa ya hana ta aikata abinda ta riga ta yanke shawara.
Ta juya da sauri tana barin gurin, sai kuma ta tuna da dankalin ta da yake jikin yaron, evidence ne, za'a iya amfani dashi a binciko wadda ta ajiye shi dan haka ta koma da sauri ta zare dankwalin nata daga jikinsa ta koma cikin bishiyoyi da sauri, tana jin gurin gabaki daya yana amsa kuwwa da karar kukansa. Ta saka hannayenta ta toshe kunnuwan ta tana kara sauri, zuciyarta tana gaya mata yanzu za'a dauke shi dan ta tabbatar kukan ya shiga har cikin gidan.
Sauri take yi sosai tana retracing steps dinta har ta dawo gurin accident din, wutar har tayi kasa sosai ta kusa karasa mutuwa, a gefe taga jakar Minal tare da karafunan motar da suka fita, ta dauka ta jefa ta cikin wutar tana kallon ta ta kama tana konewa, tana jin wani abu a zuciyarta wanda ta kasa fasaltawa.
Babu wanda yasan sun taho da Minal, maybe mai gadi ya ganta shima kuma in ya fada zata iya cewa a hanya suka ajiyeta ta tafi gida, babu mai musa mata. In akazo gurin motar abinda za'a gani shine gawar driver da mace mai ciki a gaba, babu wanda zai ce ba Fatima bace ta mutu tare da abinda yake cikin ta. Problem solved.
Ta juya tana kallon hanyar inda Fatima ta haihu, ta kunna fitilar wayar Fatima da take hannunta ta tafi gurin tana tunanin yadda zata yi ta kawar da gawar .
Amma.........
Babu gawar Fatima babu alamar ta.......
Ta cigaba da haske haske a gurin amma babu ko trace na Fatima sai jini a inda akayi haihuwar. Hankalin Ruqayyah ya tashi. Taji kafarta da taji ciwo ta rike, ta kama ta amma sai taji ta sandare, sai ta fara janta tana barin gurin, tsoro kuma yana zuwa mata zuciyarta. Kamar daga sama taji wayar Fatima da take hannunta tayi kara, network ya dawo kuma, "Mi Amour" taga an rubuta, ta dauka da sauri "hello" taji muryar Hassan da alamar tashin hankali a tare dashi "Hassana ina kuke? ina Fatima? Ya akayi baku karasa gida ba har yanzu" a rikece ta amsa masa "Hassan mun shiga uku, kuzo ku taimaka min, accident muka yi, duk sun mutu, duk sun mutu Hassan na shiga uku" shiru taji a wayar, sai hayaniyar mutane a background amma babu muryar Hassan.
**********. ************ *********
Adam yana ta kwarara gudu a hanya, hankalin sa a tashe, lokaci zuwa lokaci yana share kwallar idonsa da take kokarin kare masa ganin titin da yake gabansa, yana kuma dudduba motocin da yake wucewa ko zai ga motar da su Fatima suka taho da ita. Mutuwar Hussain ta daga masa hankali ba kadan ba, yaji duniya gabaki daya ta fita daga kansa yaji duk wasu birikan sa ashe duk shiririta ne. Duniya gabaki dayan ta zancen banza ne.
Yana barin gari ne ya hango wata mata tana tafiya a gefen bishiyoyin bakin titi, hannunta kamar da jariri kanta babu dankalin, ta mirror ya ga kamar tayi masa kama da Ruqayyah. Sai ya dan daga motar yana so ya gani sosai amma sai ya neme ta ya rasa, ya girgiza kansa, maybe idonsa ne yake yi masa gizo. Yana yin gaba kadan kuma sai yaga wani abun daya daga masa hankali ya saka ya taka burki da sauri. Fatima, a tsaye a bakin titi, jikin ta futi futu kamar tayi wanka da kasa. Ya yi packing ya fito da sauri yana kallon ta dan ya tabbatar ita din ce, kallon sa kawai take yi kamar bata gane shi ba sai kuma ta miko masa hannu tace "help me"
Ya lurada ciwo a kafadar ta yana jini, sannan ya lura da kasan rigar duk jini da kasa, sai kuma ya fahimci babu ciki a jikinta. "Madam? Me ya faru daku? Accident kuka yi, ina sauran suke" tace "Hussain. Ka kaini gun Hussain dan Allah" ya ji zuciyarsata karye, hankalin sa kuma ya tashi, daga gani a rude take bata san ma me take cewa ba, ya fara kalle kalle dan ya tabbatar a kusa da gurin ne suka yi accident din tunda ya ganta a gurin kuma a kafa. Ya kama ta ya zaunar da ita sannan ya dauko wayar sa ya fara neman number din Hassan amma bai san ma me zai ce masa ba, yana tsananin tausayawa halin da Hassan din yake ciki, ga