Showing 150001 words to 153000 words out of 300844 words
gare ku damu baki daya" sai ya mike tare da daga kansa ya kalli dogon gidan Hussain wanda tun daga nesa ake hango shi saboda girmansa da kuma kyawunsa, sannan ya sunkuyar da kansa ya kalli kabarin Hussain. Lallai wannan ma wani darasi ne da mutum mai hankali ne kadai zai iya ganewa.
Yana komawa cikin gidan ya karbi gaisuwa daga mutanen da suka taru suna jiran sa, sama sama yake ganesu, sai ya sanar musu da cewa babu zaman makoki kowa ya tafi gida yayi wa Hussain addu'a daga can. Ranar sadakar uku sai azo ayi addu'a a kuma watsewa ranar bakwai ma haka dan baya so yadda mutane suke da yawadin nan a zauna ayi ta zaman hira zaman gulmar mutane, wasu ma har mamacin gulmarsa suke yi a gurin zaman makokin sa. Dan haka sai yaga zaman bashi da wata ma'ana tunda ubangiji yana ko'ina kuma yana amsa addu'a duk daga inda aka yi ta.
A haka ya lallaba ya shiga cikin gida, inda ya tarar fa labarin wai an tafi da Aunty asibiti saboda jininta ya hau sosai. Shi bai san Aunty tana da hawan jini ba sai dai in yanzu ta samu. Ya tuna Ruqayyah, tun da akayi accident din ma bai ganta ba yaji dai ance tana asibiti amma ko waya bai samu yayi mata ba. Ba zai iya zama ba dan yana son ganin jikin Aunty dana Ruqayyah sai dai kuma mutane ta ko'ina tahowa ake yi zuwa yi musu gaisuwa musamman wadanda basu samu janaza ba, kuma kowa yazo shi yake nema tunda duk auncles din su da cousins dinsu ba'a san su ba sai few wadanda suke aiki a kamfanin su. Dan haka dole ya dan zauna sama sama yana amsa adduar mutane har lokacin sallar azahar yayi suka tashi sukayi jam'i aka sake doguwar addu'a ga Hussain da iyalinsa sannan aka gaya masa cewa an dawo da Aunty daga asibiti, sai yace a kaita part dinsa inda babu hayaniya dan ta samu ta huta sosai. Shima kuma ya samu ya zare jiki ya tafi, yana tafiya kamar iska zata kayar da shi.
Yana shiga twins dinsa suka taho da gudu suka rungume shi. Ya durkusa a gabansu yana jawo su jikinsa tana jin wani iri a ransa, kamar yayi neglecting dinsu gashi uwarsu tana asibiti an barsu a gurin yan aiki. Shima kansa Hussain junior yana gurin mai reno tun jiya. Suna ta tsallen murnar ganinshi, sai kuma suka fara leka bayansa suna "ancol, ancol" ya runtse idonsa dan ya gane auncle din su suke nema. Sai ya rungume su yana maimaita "auncle is no longer with us, he is gone and he is never coming back" yayi ta fada yana maimaita wa a hankali duk da yasan ba fahimtar sa suke yi ba amma kamar kansa yake tunawa, kansa yake consoling.
A lokacin Sumayya ta shigo, ta taho daga asibiti zata daukar wa Ruqayyah abubuwan bukata. Ta tsaya tana kallon su tana jin abinda yake cewa, sai taji matuƙar tausayin Hassan ya kama shi, Allah ne kadai yasan abinda yake ji a zuciyarsa a yanzu, kuma ta jinjinawa jarimtarsa sosai da sosai dan duk da bata san me yake ji ba bata tunanin zata iya surviving irin situation dinsa, ita tana da uwa tana da uba tana da twin sister dinta, tasan kuma duk yadda take ji dasu a zuciyarta so she can't imagine ace duk bata dasu, her life will have no meaning. But menene meaning din rayuwar ma? Dama ai Allah ya halicce mune with the sole purpose of worshipping Him dan haka duk wani abu da muke yi secondary purpose ne, worshipping din shine primary purpose din mu amma munyi neglecting munfi mayar da hankali akan abinda ba zai amfane mu ba.
Ta karasa shiga ta zauna akan kujera tana kallonsa, idonsa yana rufe, hawaye yana bin kumatunsa, bakinsa yana motsi a hankali yana ta maimaita maganganu daya. Ta hadiye abinda yake tsaye a makogwaronta, itama jiya yadda taga rana haka taga dare saboda abubuwa da yawa, na farko alhinin abubuwan da suka faru, na biyu irin yadda Ruqayyah ta ringa zabura tana sambatu, tunda take da Ruqayyah bata taba ganin tsoro a fuskarta ba sai jiya, kuma bata yi mamaki ba dan tabbas wanda yaga irin abinda Ruqayyah ta gani zai iya zaucewa ma ba sambatu ba, har sai da aka yi mata allurar bacci sannan ta samu ta rintsa, shima kuma tana yi tana firgita dan haka ita Sumayya ta zauna tayi da yi mata adduoi tana tofa mata.
Abu na biyu kuma shine Adam, tunda labarin mutuwar Hussain da Fatima ta same ta take kiran number dinsa wai dan ta samu tayi consoling dinsa dan tasan matsayin Hussain a gurinsa amma ta kasa samun sa, farko wayar tana ta ringing ba'a dauka daga baya ma kuma bama ta shiga, sai ta dauka rudewa ce ta saka yayi misplacing wayar tasa. Amma har gari ya waye shiru, har akayi janaza shiru, ba su Baba suka je asibitin ma sai data cire kunyar idonta ta tambayesu ko sunga Adam amma suka ce basu ganshi ba, sai dai babu wanda ya dauki abin da wani abu saboda irin yadda mutane suka cika a gurin dan baka ga wani ba ba zaka ce baya gurin ba. Yanzu ma da tazo gidan baza ido tayi tayi tana son ganinsa amma babu ko takalmin sa. Mai gadin gidan su Ruqayyah ta tambaya amma sai ya amsa mata da cewa "anya kuwa Adam ya kwana a gidan nan? Tun jira da suka fita tare da marigayi ban kuma ganinsa ba, motar daya tafi da ita ma bata dawo gidan nan ba" ya fada yana kara duba inda tarin motocin Hussain suke.
Wannan ya kara daga hankalin ta, me ya faru da Adam? Yana ina? Lafiya kalau yake?
Tana shigowa cikin gidan kuma sai ta tarar da wannan tashin hankalin. Dan halin da taga Hassan a ciki ya taba zuciyarta sosai. A hankali ta kira sunan sa "Yaya Hassan" ya dago kansa yana kallon ta da jajayen idanuwan sa. Tace "Allah yana nan. Yana kallon halin da kake ciki kuma yasan zaka iya daukan wannan kaddarar shi yasa ya dora maka ita. Allah baya taba dora wa bawansa abinda ba zai iya ba. Nasan kayi babban rashi wanda ni ba ma zan iya kwatanta yadda kake ji a zuciyarka ba. Amma ina so in tuna maka wani abu, kalli nan..." Ta fada tana numa masa yaran da suke gabansa. Ya kalle su sannan ya kuma kallonta, tayi masa murmushi tace "su wadannan yaran misali ne na irin Blessings din ubangiji gare ka. A duk lokacin da ka rasa wani abu da kake so kar ka kalli irin girman rashin da kayi but ka kalli irin abubuwan da kake dasu. Always count your blessings not your losses, a lokacin zaka san how blessed you are. You have a hidden Strength wanda kai kanka baka san kana dashi ba sai yanzu da wannan abin ya same mu sannan zakayi finding dinsa, kai kanka sai kayi mamakin what you can do alone in kayi concentrating on your blessings. Ka kuma godewa Allah da niimar sa. A lokacin shi kuma zai cigaba da tallafa maka".
Ya dauke kansa daga kanta ya kuma kallon yaran da suke ta jan rigarsa suna masa gwaranci sai ya samu kansa da yin murmushi, yana goge hawayen idonsa yace "Nagode Sumayya, nagode da kulawarki gare ne. Nagode da kika bude min idona naga haske" sai ya mike yana daukan yaransa ya tafi dakin da ya ke tunanin an kai Aunty can. Ya samu tana bacci sai Khadijah a tare da ita tana karatun Alkur'ani. Ya karbi bayanin da likita ya rubuta ya karanta sannan ya kuma daukan yaran ya fita dasu kar su dame ta.
Yana fitowa Sumayya tana saukowa daga sama da karamar jaka a hannun ta, ta karbi Yusuf tace "kawo su in tafi dasu can, sai Inna ta tai dasu gida su zauna acan. Dama dazu na aiko Zunnur ya karbi Hussain ya tafi dashi dan tun jiya bai sha nono ba" ya dafe kansa yana tunanin kamar ya gaza, tunda har ya manta cewa Hussain yana bukatar uwarsa. Sai yace mata ta jira shi ya dauko key din mota su tafi tare ya gano Ruqayyan. Ta jira shi ya hau sama ya sauko sannan suka fita tare, ita da Yusuf a hannunta shi kuma da Aminu suka je gurin mota suka saka yaran a baya sannan suka shiga gaba suka fita. Sai da suka dauki hanya sannan yace mata "ya jikin nata? Akwai wani major ciwo ne?" Ta girgiza kanta tace "Babu. Kafa ce kawai ta rike ta kasa motsa ta har yanzu, anyi hoto ance jijiya ce ta tabu, in an jima zasu sake wani hoton dan suga exactly inda ta tabun" tayi shiru tana kallon gabanta sannan tace "sai kuma tsorata" ya gyada kansa cikin fahimta, a ransa yana jin dadin yadda bata samu babbar matsala ba, yace "dole akwai tsorata dama, dan ma dai Ruqayyah ce" ta gyada kanta itama tace "dan ma itace. Da ni ce da sai na samu mental problem or worst" ya kalleta yace "yanzu kike min magana akan inner strength, da ke ce you will find out that you are stronger than you think".
Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne, idan kina son ki karanta halaliyar ki ki yi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020
*A Lost Soul*
A zaune suka tarar da Ruqayyah akan gado tana shan tea, Inna Ade tana zaune akan kujerar gaban gadon da Hussain a hannunta tana fada "in baki samu kin sha tea din ba yaron nan ba zai samu abincin sa ba fa shima. Ki daure ko rabi ne ki sha, ai yayi kokari ma" sallamar su ta saka Inna dago kai tana kallon su, Ruqayyah ma haka. Kallo daya ta yiwa Hassan ta sunkuyar da kanta kasa, ji tayi ta kasa hada ido da shi, wani irin nauyi take ji a zuciyarta in ta kalle shi. Musamman da taga irin yadda ya koma a cikin kwana daya. Shima a nasa bangaren kallon baki da ramar da tayi a cikin kwana daya yake yi, tayi zuru zuru idanunta duk firfito waje. Ya dan durkusa yana gaishe da Inna ta amsa masa cikin muryar tausayi tana kara yi masa gaisuwa "ya karin hakuri? Ohh Allah. Insha Allah Hussain da Fatima suna aljanna, kowa yana yi musu kyakykyawan zato kaji? Allah kai kuma ya kara maka hakuri tare damu baki ɗaya dan rashin na kowa da kowa ne" kansa a kasa yace "ameen Inna. Nagode." Yana jin wave din zafin mutuwar Hussain tana kara dukansa, haka yake ji duk sanda wani yayi masa gaisuwa, kuma yasan haka zai cigaba da ji har ranar da shima zai daina numfashi.
Ta mike ta fita daga dakin, Sumayya ma ta ajiye kayan hannunta ta kuma ajiye yan biyun da suke ta zillo sunga uwarsu. Sannan ta fita itama. Ya jawo kujerar da Inna ta tashi daga kai ya zaune yana kallon yadda kirjin Ruqayyah yake hawa da sauka kamar wadda tayi gudu ko kuma take cikin jin tsoro. Sai ya kamo hannunta guda daya a cikin nasa biyu ya rike yana cewa "it is okay Hassana. You are safe kinji? Kina tare da mu yanzu, babu abinda zai same ki kuma. It is over" ta gyada kai hawaye yana zuba daga idon ta, sai ya hau kan gadon sosai ya jawo ta jikinsa ya rungume ta yana dan jijjiga ta kadan. Ta zagaye shi da hannayenta tana cigaba da kukan ta. "sun mutu Hassan sun mutu, gaba dayan su sun mutu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya kara rungume ta a jikinsa yana jin tsananin tausayin ta, what she went through, what she witnessed, yana jin rayuwarta ba zata taba komawa dai dai ba kamar yadda yasan ta sa rayuwar ba zata koma dai dai ba. Ta dago kai tana kallon sa, "na dauka mutuwa zanyi mijina, na dauka ba zan kara ganin ka ba mijina" ya saka hannu yana goge mata hawayenta "am here, ina nan tare da ke babu abinda zai same ki insha Allah" sai ta juya tana kallon kafar tace "kafata ce take ciwo mijina, na kasa motsa ta, tsoro nake ji kar in zama gurguwa" ya girgiza kansa "uhm uhm ki daina fada, babu abinda zai samu kafar ki kinji? Me Doctor din yace?" Ta nuna masa takardar da likitan ya kawo ta hoton da yayi wa kafar dazu da safe tace "yayi hoto, yayi bayani no ban gane me yace ba. Ni tsoro nake ji kar in rasa kafata. Bana so in zama gurguwa Hassan" ya dauki takardar yana dubawa sannan yace "yace zasu yi wani hoton ai ko? Ki daina kuka please mu bari su sake yin wani hoton mu gani kinji? Sun san abinda suke yi duk abinda ya kamata suyi akan kafar zasuyi" ta rike hannunsa tana girgiza kai "ni dai kawai ka fitar dani waje, ai kuna da doctors masu kyau a waje wadanda zasu kyara min kafata a lokaci daya. Ka fitar dani kawai waje tun kafin lokaci ya kure suce an makara" yayi ajjiyar zuciya yana jin kansa yana fara ciwo, ya kamo fuskarta a cikin hannunsa yace "Hassana. Hussain ne ya mutu, shi da Fatima da babyn su gaba ki daya. Jiya suka mutu, yau aka binne su. Hassana ba zan iya daukan ki mu fita kasar waje yanzu yanzu ba, gidan ma yanzu dan ina son in ganki ne kawai yasa na yi karfin zuciya na fito na taho nan, amma ba zan iya barin garin nan ba ballantana kasar nan. Kiyi hakuri. Wannan likitan is the best a garin nan, in mun fita wajen ma irin sa zamu gani ko kuma ma wanda bai kai shi kwarewa ba, matsalar kayan aiki ne, idan yaga cewa kina bukatar kayan aikin da basu dashi a nan shi da kansa zai fada kuma yayi referring dinki zuwa kasa da kuma asibitin da yasan suna da kayan aikin da kike bukata" a karasa yana jin babu dadi dan ba zai iya yi mata abinda take so ba, amma wani barin na zuciyarsa yana ganin bai dace ba tambayar tasa ma da tayi bayan tasan halin da yake ciki, amma considering halin da ita din take ciki sai ayi sauri ya kawar da batun daga zuriyar sa. Yayi ta rarrashin ta har ta daina kukan sannan yayi kokarin kara mata kwarin guiwa, ya kuma yi mata bayanin abinda yasa ba zai zauna tare da ita a asibiti ba tunda ya bar mutane masu zuwa gaisuwaa waje.
Da kyar ta cika shi, ita tana ganin bai kyauta mata ba da ba zai fita da ita waje ya nema mata magani ba ko kuma ya zauna yayi jinyarta ba, bayan kuma a ganinta a yanzu babu wanda ya kaita muhimmanci a gurinsa tunda dai Hussain din da yake ta ambato to yanzu babu shi. Ta kara jin dadin hukuncin da ta yanke akan dan Hussain dan tasan da yana nan da bata jin ko kallo ita da ƴaƴan ta zasu ke samu daga gurin Hassan da yanzu yana can yaa rainon sa. Dan haka sanda zai tafi ma fushi ta nuna tana yi, wannan ya kara masa rashin jin dadi a zuciyarsa amma kuma a hakan dole yayi mata sallama ya kuma yi sallama da ya'yan sa ya fito. Sumayya ta biyo shi a baya, taa ta so ta tambayeshi Adam amma kuma tana ganin kamar hakan ba dai dai bane ba considering halin da yake ciki. Har sai da yaje bakin mota zai tayar sannan ta daure tace "Adam acan Abuja kuka bar shi ne?" Sai da yayi blinking idonsa sannan ya juyo yana kallon ta, tabbas bai ga Adam ba, tunda ya dawo bai ga Adam ba kuma bai tuna da neme shi ba.
Ya dafe kansa da hannu daya yace "noo, ba acan muka baro shi ba. In fact, ya riga ni tahowa ma, shi yayo gaba neman motar su Ruqayyah ni kuma na tsaya na taho da Hussain. Kin neme shi a waya?" Idonta ya kawo kwalla, tace "nayi ta kiransa tun jiya wayar tana shiga baya dauka, daga baya kuma bata shiga sam, yanzu ma kafin ka fito sai dana kira amma switch off" yace "kar ki damu, am sure mutane ne da kuma alhinin wannan abin ya hana shi dauka. Amma in naje gida I will get him to call you" ta goge hawayen ta tace "baya gidan, bai koma gida ba, bai dawo daga Abuja ba" yayi shiru yana kallonta bai ce komai ba, tace "dazu da naje gidan na tambaya duk babu wanda ya ganshi. Mai gadi ma yace bai shigo gidan ba, yace motar da kuka fita da ita ma bata dawo gidan ba". Sai Hassan ya rasa me zaice mata, yaji hankalin sa yana tashi amma sai yayi karfin hali yace mata "am sure yana wani gurin ne, ko school ya tafi ya kwana acan kinsan tunda gidan da mutane ba zai ji dadin zama ba" ta girgiza kanta again tace "na kira abokin sa na makaranta baya can, sunce suma nemansa suke yi they were supposed to meet yau da safe suyi karatu" yanzu hankalin sa ya kuma tashi, but baya so ya nuna mata yace "still, think positive Sumayya, yana da abokai a cikin gari wata kila yana tare dasu ne. Shima nasan wannan mutuwar ta taba shi, maybe he just needed space ne ya danyi cooling down" ta gyada kai da sauri trying to believe him, hoping abinda ya fada shine abinda ya faru din. Sannan taja baya shi kuma ya tayarda motar ya tafi.
Amma shi zuciyarsa duk ta tsinke, me ya faru da Adam? Babu wanda ya ganshi, shi kuma yasan babu yadda za'a yi Adam yayi missing jana'izar Hussain in dai har yana da rai yana kuma da lafiya, sannan kuma zai kira Sumayya yagaya mata lafiya kalau yake, dan haka shi kansa bai yadda da abinda ya gaya wa Sumayya na