Showing 231001 words to 234000 words out of 300844 words

Chapter 78 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2076

nake yi kamar wata rana zai bayyana, out of no where zaki gan shi. Maybe ya zama dan saurayi ma, sai ki ganshi kamar Hussain tunda kin ce min da Hussain yake kama" sai ta samu kan ta da yin dan gajeren murmushi, tana tuno da fuskar baby a scan din da suka gani, ta sake wani murmushin sannan sai ta bude kofar motar ta fita, ya bita da kallo yana jin dadin yadda ta murmusa, ko a imo da sunan Hussain yake samun kanta, ko mai bacin ranta in ka tuna mata da Hussain sai ta sauko.

Ta leko ta window tana kallon sa tace "get your self a phone please, in zan kira ka bansan ta yadda zan same ka ba" ta dan daga kafada yace "ni mantawa ma nake yi cewa ana rike waya, sabo da yi" ta bude jakarta ta fito da kudi ta ajiye akan kujera tare da card mai dauke da number dinta tace "get your self a phone and call me" yace "an gama Madam. Thank you" sannan yayi reverse ya tafi.

A ranar da dare Fatima ta gana da mahaifinta, ta gaya masa dalilin ta na janye kara sannan ta gaya masa yadda sukayi da Ruqayyah. Ya gyada kai yana fahimtar ta sannan kuma yana tausayin sa, at her young age tayi going through abubuwa da yawa kuma yaji dadin yadda take daukan kaddarar ta. Yaji dadin hukuncin data yanke, da yadda ta bar Ruqayyah da Allah duk da cewa tana da karfin kwatar justice amma ta bar hukunci a hannun the most just. Sai kuma yayi maganar sake kiran wani meeting din da yanuwan Hussain, ya kuma sa aka kira Hassan aka gaya masa cewa su zo da weekend zasu yi magana da mai martaba sarki.

Kafin weekend din kuma sai ya sake zama da Fatima tare da mahaifiyarta Hajiya Fulani akan menene zasu yi mata dan su faranta mata. "Ni yanzu I just want a break Takawa, ina so in da matsa daga gurin mutanen da suka sanni suka san abubuwan da suka same ni, ina ganin wannt zai taimaka min wajen mantawa, duk da nasan ba zan manta ba amma zai rage min tunani akan maganar" Hajiya tace "to ko Dubai zaki tafi gurin Asma'u?" (Babbar yayar su) mai martaba yace "kin ga dama can suna da kwararrun likitoci, sai su cigaba da duba lafiyar ki, watakila a dace ki samu ki tuna da abinda kika manta" Hajiya tace "in kina sha'awa ma sai ki koma makaranta kiyi degree dinki nabiyu, in ma PhD kike so sai ki dora" Takawa yace "kuma hamid, mijin Asma'u yaro ne mai kirki, ba zai damu da zamanki a tare dasu ba"

Fatima tayi murmushi tana jin dadin yadda suke ta kokarin faranta mata, tasan zasu so zama da ita amma kuma suna da so su faranta mata shi yasa suke ta wannan maganar. Tace "bana so in kuma barin ku, nayi missing dinku sosai sannan bana tare da ku" Takawa ya dafa kanta yace "duk sanda kika ji kuma son ganin mu sai ki taho ki gan mu, ko kuma mu mu tafi mu ganki. Kuma kullum zamu ke kasancewa tare a waya, mu dai farin cikin ki kawai muke bukata"

Ta lumshe idonta, anya tana tare da sauran farin ciki kuwa? Anya? Ita yanzu fatan ta bai wuce kwanakin ta suyi sauri su kare ta mutu ta tafi gurin Amour ba.

Sakon sarki ya samu Hassan kuma sun shirya sun taho dan honouring gayyatar sarki, sai dai wannan karon daga shi sai aunty ne suka taho. Suna zuwa bayan dukan gaggaisa an kuma gabatar musu da kayan refreshment sai aka yi musu iso. A hanyar tafiya suka hadu da Adam. Shima har dashi aka kira duk da baisan dalilin kiran ba tunda family issue ne. Suka gaisa awkwardly, sai Adam yace "ya Sumayya da baby? In an koma a gaishe su please" Hassan yadan shafa kansa yace "zasu ji" suka jera suna tafiya sai Hassan yace "thank you Adam, for understanding" Adam ya gyada kai yana dan murmushi yace "nine da godiya".

Daga nan suka shiga gaban sarki tare da yan uwan Fatima da kuma ita kanta Fatiman. Bayan sunyi gaisuwa daya bayan daya kuma sarki ya amsa sai ya fara godiya ga Allah sannan ya gode musu a bisa hadin kan da suka nuna akan wannan case din, "Allah ya saka muku da alkhairi ya kara hada kan ku ya kuma bar zumunci" sai kuma yayi jinjina tare da yabawa ga Fatima da kuma abinda ta aikata. "Hakan da tayi shine dai dai. Tabbas gaba ki dayan mu zuciyoyin mu sun tafi a kan cewa ita waccan yarinya ta aikata laifin da ake tuhumar ta dashi, amma gabaki dayan mu bamu da hujjar da zata tabbatar da haka, dan haka duk da cewa muna da ƙarfin ikon da zamu hukunta ta amma ba zamuyi din ba har sai mun tabbatar da tayi din. In kuma tayi din ma bamu da tabbas din hauka ne ya saka ta tayi ko kuma da sanin ta tayi. A yanzu haka Allah ne kadai yasan gaskiyar lamarin nan dan haka abar masa lamarin shine dai dai. Shi zaiyi hukun ci, idan ta aikata tabbas hakki zai fita, idan bai fita a duniya ba zai fita a lahira"


"Maganar gadon Hussain da aka riga aka raba a kan cewa Fatima ta mutu da ciki, a yanzu ma a sharian ce za'a bar shi ne a haka. Abinda za'a gyara kawai shine kason Fatima da za'a damka mata kayanta. Amma sauran za'a barsu saboda bamu da tabbas din cewa da rai Fatima ta haifi abinda yake cikinta ko babu rai, bamu da tabbas din mace ta haifa ko namiji"

"Shi kuma ko ita kuma abinda aka haifa din, zamu cigaba da addu'a in dai yana raye ko tana raye Allah ya bayyana mana shi ko ita, Allah yasa watarana ya tako da kafafuwan sa ya shigo cikin gidan nan ya kawo kansa gare mu, ko kuma mu Allah ya bamu ikon fahimtar inda yake ko take, mune mu taho dashi. In kuma baya duniya, Allah ya hada fuskokin mu a lahira, inda za'a hadu kuma ba za'a sake rabuwa ba har abada"

"Magana ta gaba shine jinjina da godiya gare ki Amina akan irin rikon da kika yiwa yaran nan, da kuma rikon da kika yiwa Fatima sanda tana hannunku, tabbas ke din abar yabawa ce dan macece ke mai kamar maza, ina takaicin zumuncin da muka kulla a tsakanin mu kuma mutuwa ta katse mana shi. Bana so muyi asarar wannan zumuncin shi yasa nake neman alfarma a gurin ki idan kin amince. An sanar dani cewa Allah ya albarka ce ki da yaya mata, idan akwai wadda bata yi aure ba a cikin su ina son zamu tura Abubakar yaje ya ganta su daidaita in Allah ya amince sai ayi musu aure"

Aunty sai murna, baki yaki rufuwa, lallai ba karamar karramawa sarki yayi mata ba. Lallai jinkirin Zulaihat alkhairi ne a gare su gabaki daya. Abubakar kuma ya sunkuyar da kansa yana murmushi, duk d abai san yarinyar da ake magana akan ta ba amma yasan ba zai taba bijirewa maganar da mahaifinsa ya fada a gaban mutane ba. In dai har yarinyar ta karbe shi to anyi an gama.

Daga nan sai ya juyo kan Adam, yace "Adam. Fatima ta bani dukkanin labarin ka, kuma na fahimci cewa kai din na musamman ne ko a gurin ubangiji ma, dan irin ƙarfin imanin ka kafin a samu irinsa a cikin al'ummar mu sai an bincika sosai. Kayi sacrificing abubuwa da dama saboda musulunci kum kayi sacrificing abubuwa da dama saboda yar mu Fatima, saboda kuma gujewa rikici da samun zaman lafiya tsakanin kabilar mu da taku. Babu abinda zamu ce maka sai godiya da fatan alkhairi a duniyar ka da kuma a lahirar ka. Ba zamu iya biyan ka ba tabbas amma zamu gwada faranta maka iyakacin kokarin mu tare da kokarin replacing maka abubuwan daka rasa da wadansu. Misali itaye, daga yau ka dauke ni a matsayin mahaifin ka, ni ma daga yau ka zama dana kuma dukkanin wani guri da dan dana haifa a cikina zai taka kaima na baka uzinin takawa, duk wata alfarma da za'a yi wa dan dana haifa a cikina kai ma daga yau za'a yi maka ita. Zaka tattaro kayan ka ka dawo gidan nan dan gidan nan ya zama gidan ku yanzu"

Adam sai murna, yama rasa mai zaice, shi bai san yadda ake nuna godiya ga sarki ba, sai yaga yayan gidan suna yiwa sarki godiya a madadin sa kamar yadda suke yi aduk lokacin da akayi wa wani daga cikin su wata kyauta ko wata alfarma. Shima sai yayi yadda suka yi. Yaga Umar da Abubakar wadanda sune maza suna jansa jikinsu suna taya shi murnar shigowa family. Sai kuma yaji sarkin yace "yanzu ina so ka fada min menene burin ka a rayuwa? Menene abinda kake so kayi? Aure? Karatu? Kasuwanci? Me kake so?"

Sai Adam yayi shiru yana shafa kai, sai kuma ya juya yana kallon Fatima wadda ita ma shi take kallo fuskarta tana nuna jin dadin ta akan karramawar da mahaifinta yayi wa Adam, ta fahimci kamar shawara yake nema sai tayi mishi alamar yayi magana, ya fadi abinda yake so, ya juya yana kallon Takawa yace "karatu ran sarki ya dade. Ina son in cigaba da karatu"

Sai Sarki yayi murmushi yace "to alhamdulillah. Dama abinda nayi maka sha'awa kenan, amma a koda yaushe abinda ake so iyaye suke yi shine su vawa yayan su dama su fadi abinda suke so su kuma sai suyi amfani da wannan su basu shawara ba wai su yanke hukunci ba tare da sunji abinda yayan su suke da ra'ayin yi ba. Ga dan uwanka nan Umar, ka same shi ku zauna ku bincika duk makarantar da kake so ya nema maka ka tafi kayi karatun ka, Allah ya baka sa'a, Allah yayi maka albarka".

Daga nan aka gabatar da adduoi aka tashi.

Bayan an fito, Adam yana ta murna ya tafi gidan su na Kano inda babu kowa a ciki yanxu sai shi, ya kwaso kayansa ya dawo, Abubakar da kansa ya taimaka masa suka saka aka kai masa part dinsa aka gyara masa daki daya a ciki aka saka masa, suttura kadai ya debo, dan babu abinda yake bukata bayan su dan ya samu komai har ma abinda bai saka ran samu ba, ya samu family, Royal family.

A daren ranar Fatima ta kira shi a waya suka hadu a gurin saukar baki tace "maganar school nake so muyi, kun fara maganar da yaya Umar?" Yace "a'a, bamu yi ba tukuna" tace "tayi dama zanyi maka na inda zanje, let's go together, in na samu abokin karatu maybe zan iya yi, dan a yanzu ji nake yi bazan iya ba" yayi sauri yace "zaki iya mana, in dai ba so kike kiyi ta samun carryovers ba har in gama in barki" tayi murmushi "maybe, maybe zanyi ko dan kar ka gama ka barni".

Sai ya dauko sabuwar wayarsa ya saka number din Maman sa from memory, ya kira ta dauka yace "Mama" da sauri tace "Joseph. My son is that you?" Yace "it is me mother. It is Adam" tace "thank you Jesus. I was so worried about you. Ko bacci bana iya wa" ta fadi maganar so emotional, ya danyi mata shagwaba "bayan Kin gudu kin barni. Baki damu dani ba" tace "how can you say that. Wa na damu dashi duk duniya sama da kai? Na barka ne saboda kayi learning lesson ka gane mutanen nan ba kaunarka suke yi ba, they will always used and dump you. Haka halin su yake..." Yana kallon Fatima yace "not all of them mother. Fatimah ce ta fito dani, ta hakura da damar da might lead her to find out about her baby saboda ta fitar dani. Because she believe in me. And her father took me in, yanzu ina gidansu. Har sun fara maganar fitar dani waje inyi karatu. They are good people Mama, excellent people".

***********************

A Kaduna, Ruqayyah tana kwance a dakinta na kasa inda ta dawo da zama yanzu, saboda hawa bene ya kare mata. Tun da Hassan da Fatima suka shigo suka fita take kwance a dakin tana kuka, kukan da ita kanta bata san na menene ba, dan Lukman ma daya dawo da niyyar ta sallame shi bata kula shi ba a haka ya hakura ya tafi yace zai dawo. Tafiyar su Hassan kano babu jimawa, ita kuma Sumayya ta hada kan yara suka tafi gidan Baba zasu wuni a can. A lokacin ne kuma Ruqayyah ta fara jin kara kamar ana ruwan sama da kankara, ta na jiyo karar kamar ta fashewa glasses, Sannan kuma da hayaniya kamar a waje.

Ta danna kararrawar da ta saka saboda kiran yaranta, sai ga Luba a guje, idonta kamar zai fado, tace "Aunty, mutane ne a waje suke jifan gidan nan, sun balla gate sun shigo, masu gadi duk sun gudu, Aunty mun shiga uku kashe mu zasu yi" Ruqayyah ta bude baki "mutane kuma? Me suke so?" Luba tace "ban sani ba, kamar dai ke suke so su kama" cikin Ruqayyah ya kada, taji kamar zata yi kashi a wandon ta, me tayi musu? Me tayi musu?

Da gaske babu abinda tayi musu, not directly, amma Hussain, Hussain ya kyautata musu iyakacin kyautatawa dan da yawa daga cikin su suna a matsayin da suke a yanzu ne saboda Hussain. Wasu kuma saboda sadakar da Hassan yayi da sunan Hussain. Kuma duk abinda ya faru, duk shari'ar da akayi, mutane sun gani kuma sunji labari a media, sun kuma fahimci tabbas ita ce ta salwantar da da daya tilo da Hussain ya mutu ya bari kuma ta zaune akan dukiyar da ya bari, Shari'a bata kama ta ba saboda babu shaida, shine su suka zo zasu kamata suyi mata hukunci irin nasu. Suyi mata justice din da law ba zata yi mata ba, suyi mata jungle justice.


*One One*

Ina neman afuwar masu karatu saboda maimaicin suna da aka samu na yaya da kuma kanwar Fatima, Asma'u. To zamu bar sunan a matsayin na kanwar Fatima, yayar kuma sai mu chanja mata wani, let's say Maryam.

Wani dutse aka jeho wanda ya fasa glass din window ya zo har gaban Ruqayyah, ta kalli dutsen idanuwan ta a waje tana lura da girman sa, da ace a goshinta ya sauka da tsaf zai fasa goshin in ma da karar kwana ya aika da ita lahira, lahirar da bata shirya zuwa ba yanzu. A guje Luba ta kwasa tayi hanyar kitchen, daga nan kuma Ruqayyah tasan waje zata fita ta kofar baya, ta juya tana kallon kofar shigowa palon sai taji an fara jijjigata ana dukan ta da abin da yayi kama da sanda, dan ma mai kwari ce yasa basu iyaballa ta ba yet, taji ance "ki bude kofa, shegiya mayya, in baki bude ba sai mun saka miki wuta mun kone ki da ranki, munafuka, macuciya, mayaudariya, azzaluma".

Ta rikice, kalmar konewa tana ratsa kunnuwan ta tana shiga har zuciyarta tare da saka matsanancin tsoro a ranta, jikinta ya dauki karkarwa har ta kasa driving kujerar ta ballantana ta gudu, to in ta gudun ma ina zata je, babu abinda take tunawa sai yadda wuta ta kama gawar Minal da ta driver tana cin su, da irin kaurin konewar naman su da ya cika dajin, su da suka kone bayan sun mutu kenan, ita kuma fa? Da ake barazanar kone ta da ranta?

Ta tuna da zafin da take ji idan ta taba tukunya mai zafi ko kuma wuta unintentionally, ta tuna da irin azabar da take ji idan mai ko ruwan zafi sun taba ta, ta tuna da abinda tataba karantawa cewa the most painful thing in the world is to be burned alive. Allah da kansa ya haramta azaba da wuta komai kuwa laifin mutum.

Bata san sanda ta mike daga kan kujerar ba, sai ganin ta tayi ta fadi, a dai dai lokacin da wani dutsen ya kuma faso glass din taga ya sauka akan dagon bayan ta, taji zafin saukar sa ta kuma ji zafin faduwar da tayi amma tsoron azabar wuta ya saka ta shanye zafin ta fara jan kafa da sauri ta tafi hanyar da dakin da take zaune a yanzu yake. Girman falon ya saka ta sha wahala kafin taje dakin, tana zuwa kofar dakin suna balla kofar falon, tana jin wani yana cewa "gata can, gata can. Gurguwar banza" ta shiga dakin da sauri sannan ta rufe kofa ta murda lock, ta jingina da kofar jikinta yana karkarwa kamar mazari "wayyo Baba, wayyo Inna ku taimaka min zasu kashe ni. wayyo Allah na" ta matsa daga jikin kofar da sauri sanda taji an taba kofar. "Ba zaki bude ba? Sai munyi gunduwa gunduwa da namanki in muka kamaki".

Ta ja da baya da sauri, jikinta gabaki daya yana karkarwar yadda ta ma kasa motsawa daga inda take kamar yadda kwakwalwar ta ta toshe ta kasa lissafa mata abinda ya kamata tayi. Tunanin daya fara zuwa mata ranta shine Inna da Baba, ina suke? Me yasa ba zasu zo su ceceta ba? Sai ta tuno da last ganinta da Inna ranar nan data leka ta taga ta ganta a compound din gidan Hassan tare da Sumayya, last ganinta da Baba kuma a court ne inda ya fede biri har wutsiya a kan halayyar ta, amma duk da wannan tasan su biyun nan sune kadai zasu iya zuwa ceton ta a yanzu, bata jin akwai sauran mai kaunarta yanzu a duniya bayan su da suka kawo ta duniyar.

Ta kare wa dakin kallo tana neman wani gurin buyan dan taji har sun fara saran kofar dakin da Adda, duk karfin kofar kuwa tasan zasu balla ta dan da gaske suke ba wasa ba. Idonta ya sauka akan kofar toilet din da yake cikin dakin, ta ja jiki da sauri tana rarrafe ta shiga toilet din sannan ta tura kofar ta saka lock dinta ita ma, amma ita kanta tasan bata tsira ba dan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login