Showing 72001 words to 75000 words out of 300844 words
sannan ta kwanta akan gado yana mayar da ajjiyar zuciya. Ta lumshe idonta tana tunanin event din, gaskiya ya kayatar da ita, tayi ta kokarin ta gano fault a ciki amma ta kasa, sai dai kawai tasan kawayen Fatima sunfi nata haduwa, ta kuma san mutanen gurin sunfi bada karfin su ga Hussain da Fatima akan ita da Hassan.
Tana nan kwance ta jiyo hayaniyar kawayenta suna shigowa. Kamar yadda suka sabarwa kansu direct bedroom dinta suka zarce suna ta hayaniya. "Ni ban gane ba Ruqayyah, naji a gurin kamar ana cewa kanin mijinki ne mai kamfanin ba mijin ki ba, menene gaskiya wai?" Wata tace "ni kuma ji nayi ance nasu ne su biyu wai Hassan and Hussain shine h and h din" Sumayya data fara rage kayan jikinta itama tace "to ku menene naku a ciki? Me zaku karu dashi in kun san waye?" Minal da take kwance rashe rashe akan gado tace "dan musan yadda zamu yi pricing kudin siyan baki mana? Ai iya kudin ka iya shagalin ka ne abin" ita dai Ruqayyah baya ce musu komai ba, sai kuma suka koma hirar wai waye yafi haduwa a tsakanin angwayen, kowa tana fadar gwaninta tana kuma fadar dalilin ta. Can suka ji tsayuwar mota sai suka garzaya taga suna leken motocin da suka tsaya a gaban gidan Hussain. Wata tace "wai Allah! Wannan gida! Gaskiya Ruqayyah da sake, in dai har kamfanin nan nasu ne su biyu to ki tubure ki ce sai dai ku zauna tare a can gidan, ai zai ishe ku" wata kuma tace "ni ta mijin nake bata gidan ba, gayen ya hadu karshen haduwa gashi ya iya daukan wanka"
Ruqayyah ta mike ta shiga toilet ta rufe kanta kamar dazu, bata so su kara mata bakin ciki, ta samu zuciyarta ta dan kwanta su kuma suna so su kara taso mata da ita. Sumayya ta cire kayan ta ta saka simple ones sannan ta hada duk kayan da tazo dasu a jakarta, ana gam siyan baki itama zata tafi gida, sun riga sunyi magana da Adam yana jiranta a waje zai je ya kaita.
Suna nan zaune har Hassan yazo, suna jiran suga ya zo da motoci kanar yadda Hussain yazo dashi sai gashi daga shi sai Jabir. A palon sama suka zauna sannan Hassan ya kira wayar Sumayya yace mata gasu sunzo. A dole suka fito da Ruqayyah daga toilet suka kara gyara ta sannan suka lullube ta da mayafi suka fita da ita, sai taji a ranta cewa bata son mayafin ta irin alkyabbar gimbiya take so. Suka zaunar da ita a gefe sannan suka zagaye ta suna gaisawa dasu Hassan. Minal tace "ina sauran abokan?" Jabir yace "gani!" Tace "gaskiya kayi mana kadan kai kadai, ai munfi son da yawa yadda zamuyi ciniki sosai" yayi dariya yace "ciniki kuma sai kace wani kayan gabas?" Tace "ina jin dai ba ka kalli amaryar nan sosai ba, ai ta wuce kayan gabas ma ita" yace "wannan kuma sai dai a tambayi ango, ni ina ni ina kallon matar mutane?" Hassan ya dan leka kasan mayafin Ruqayyah yace "kinyi gaskiya, ta wuce kayan gabas, ta wuce kaya baki dayansu. Ni a gurina ta wuce komai fa. She is soo PRECIOUS to me" duk suka kwashe da shewa daya ta miko wa Hassan hannu tace "to kawo, tunda dai ka yaba sai ka biya" ya koma ya kwanta a jikin kujera yace "wanne biya zanyi kuma? Bayan na riga na biya sadaki ai na gama komai" tace "sadaki wannan nata ne, wannan kuma mu zaka sallama" Jabir ya zaro kudi daga aljihun sa wanda dama ta riga ya tanada saboda su ya ajiye a kan cinyar ta kusa dashi yace "duk tsadar ku dai wannan ya ishe ku" Minal ta dauka tana kimasta adadin kudin tace "wannan din, haba dai, kar ku bada mu mana, a matsayin sa na the whole CEO of H and H ai mota muka saka ran zai sallame mu da ita".
Hassan ya danyi dariya yace "CEO na H and H? A ina kika samu wannan tatsuniyar?"
Duk kawayen suka yi shiru suna kallonsa kamar yadda shima yake kallon su daya bayan daya, sannan suka juya suka kalli Ruqayyah, shima ya juya ya kalleta duk da fuskarta tana rufe da mayafi. A hankali Ruqayyah ta saka hannu ta kamo hannun Sumayya ta rike a cikin nata, kamar me neman karin courage daga gareta. Minal ta sake cewa "wai kana nufin ba kaine CEO ba?" Hassan yace "ke waye ya gaya miki nine?" Jabir ya dafa kafadar Hassan yana kallon Minal yace "to ke menene naki a ciki? In shine in ma bashi bane ba ina ruwanki? Ku dai ba kudin siyan baki kuke so ba kuma gashi an baku?" Wata a kawayen tace "to ai matar tasa ce ta gaya mana shine CEO, wannan yasa muka fitar da kudi masu yawa muka yi kwalliya da sauran abubuwa dan kar azo aji kunya, kuma dan muna saka ran zamu fanshe kudin mu a jikin ku, yanzu kuma gashinan daga dukkan alamu ashe yaudarar mu tayi bashi bane ba ko kuma shine yake boye mana dan kar ya bamu abinda muke nema. Mu kuma ba za mu bar gidan nan ba sai an bamu mota"
Hassan yayi kokarin mikewa, ransa yana baci zuciyarsa tana baƙi, bai taba tsammanin yadda yake jin farin ciki a ransa lokaci daya zai iya komawa baƙin ciki ba. So yake ya kira security din gidan su zo su fitar musu da wadannan marasa kunyar yaran masu niyyar haddasa musu fitina a daren farkon auren su. Jabir ya sake rike shi fuskarsa da murmushi yace "to ke yanzu baiwar Allah da kike ta wannan jawabin akan lallai sai an baku mota in aka baku din me zakuyi da ita? Ku kusan goma sharing zaku ke yi?" Tana juya idonta tace "siyarwa zamuyi mana, mu raba kudin ko ma samu na kashewa zuwa wani lokaci" Jabir yace "shikenan, yanzu wata a cikin ku ta turo min account details dinta sai in tura muku kudin motar ku" Hassan yayi sauri zaiyi magana Jabir ya sake yi masa alamun yayi shiru da hannunsa. A take suka bashi kuma a take ya tura musu kudin. Yana shigar musu suka duba "ahhh wannan ai sai dai karamar mota zamu siya" yayi dariya yace "ku da ya kamata ku gode min na taimaka muku ba sai kunyi wahalar neman mai siyan mota ba? Kuma in kuka tashi siyarwa tayin wulakanci za'a yi muku ba lallai ne ma ku samu irin wannan kudin ba. Yanzu kuwa babu ruwanku da jira, kafin kuje gida ma zaku iya raba abin ku" da haka ya shawo kansu suka yadda, sannan suka dan saya fuskar Ruqayyah kadan yadda za'a gani. Jabir ya dan leka fuskar yace "to amarya, Allah ya sanya alkhairi, sai nazo cin ta tsotse" ya mike yana mikawa Hassan hannu "ango, Allah ya bamu alkhairi, na yi maka wannan yakin saura kai kuma kayi naka" ya fada da dariya a muryarsa amma Hassan bai mayar masa da dariyar ba kuma bashi da niyyar rama wasan da yayi masa. Minal tayi wa Jabir fari da ido tace "kuma tafiya zaka yi, ko dan ragin hanya babu?" Yace "rufa min asiri kar matata tayi min duka, sai dai ku fito a samo muku driver ya kai ku har gidajen ku, amma ni yanzu ma kira na take tayi nayi dare" ya fada yana duba wayarsa duk da babu wani missed call a kai.
Suka kwashi tarkacen su ba tare da wata kyakkyawar sallama ga Ruqayyah ba ballantana ga mijinta daya tasa ta a gaba yana kallon ta , fuska babu walwala. Suna fita gidan yayi tsit kamar an kawo sakon mutuwa. Sumayya ta cire hannun ta daga na Ruqayyah tana jinta totally out of place ta mike. "Tooo da haka haka, nima bara in kara gaba" Ruqayyah ta sake rike mata hannu "ba sai gobe zaki tafi ba? Dare fa yayi sosai" ta sake zare hannunta daga nata tace "ai ina da me kai ni, tun dazu ma yana waje yana jirana" ta fada tana kallon fuskar Hassan tana jiran ya bata amsa tunda yasan wanda take nufi amma sai taga ko kallonta bai yi ba. Ta shiga daki da sauri ta dauko jakarta ta fito sannan tace musu sai da safe ta sauka da sauri tun kafin bomb din ya tashi da ita, tana fita taga Adam a tsaye a jikin mota yana danna wayarsa, ya dago kai yana kallon ta yace "I thought you are never coming out" tace "kai dai tunda na fito shikenan" bata jira ya buɗe mata kofa ba ta bude baya ta saka jakarta sannan ta bude gaba ta zauna. Ya shiga ya kunna motar suka bar gurin, ta juya tana kallon gidan Hassan a ranta tana jin kamar wani ticking bomb ne a gidan wanda zai iya exploding any time. Ta san dama shi ramin karya kurarre ne amma bata san zai kure tun a ranar farko ba. But something yana gaya mata Ruqayyah will find a way out of this.
Sun jima a zaune, ita kanta a kasa, hannayenta a kan cinyarta, shi kuma yana facing dinta ya jingina bayan sa da jikin kujera. Studying dinta yake yi, amma sai ya kasa karantar fuskarta, so yake ya hango guilt ko kuma tsoro ko kunya amma bai ga komai ba sai dan guntun murmushi a fuskarta. Ta danyi gyaran murya yace "CEO? Really?" Ta dan dago fuskarta ta kalle shi sai ta mayar da kanta kasa tace "ceo? Menene ceo?" Ya bata fuska yana jin confusion yace "kawayen ki suka ce kince nine CEO na H and H" ta daga kafada tace "ba fa kawayena bane ba, ni kasan ba kawaye ne dani ba, da za'a yi bikin ne Sumayya da Minal suka gayyato su dan su tsaya a matsayin kawayena tunda bani da kawaye" yace "wacece Minal?" Tace "yar makotan muce a wancan gidan, wadda ta zauna anan" ta fada tana nuna inda Minal ta zauna. Ya sake cewa "amma suka ce kince musu nine CEO?" ta danyi dariya tace "ni fa na ce maka bansan abinda hakan yake nufi ba" yadda ta fadi maganar so innocently ya sa ya fara yarda da ita, to ita ina zata san wadannan business terms din? Yanzu fa ta gama secondary school kuma ga yanayin gidan su. A ina zata san me duniya take ciki? Yace "amma da suka fada me yasa baki karyata su ba a gabansu, duk da baki san term din ba sai ki musa ki ce ke baki fada ba, dan nan gaba kar su sake yi miki karya" ta dan sunkuyar da kanta tana dan rufe fuskarta kamar mai jin kunya tace "siyan baki na fa akeyi, in ana siyan baki fa ba'a magana" ya dafe kansa da hannu biyu yana jin kansa yana neman fara ciwo. Zuciyarsa da kwakwalwar sa suna yaki a tsakanin su, but son Ruqayyah yana rinjayar sense dinsa. Ya cire hannun sa daga kansa sannan ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna. Ya kamo hannun ta ya rike a nasa, ta sunkuyar da kai cikin jin kunya tana kokarin karbe hannunta amma yaki cikawa sai ta bar masa.
Yace "amma kunyi magana dasu akan aikina?" Ta daga kai tace "sun tambayeni aikin ka nace ban sani ba, amma sai na basu labarin daukan Baba aiki da kayi a H and H. Ina jin daga nan suka samu kalmar CEA din" yayi dariya yana girgiza kansa yace "CEO ake cewa. It means Chief Executive Officer, wanda shine matsayin da yafi Kowane matsayi girma a Company, shi yake da final say a duk decision making, wani ceo din kuma shine mamallakin Company, shine founder, shine kuma sole share holder" ta dago idanu tana kallonsa tace "and are you?" Ya girgiza kansa yace "noo, am not" taji dan sauran hope din da take dashi yana bin iska. Ta sunkuyar da kanta kasa, Ya sa hannu ya kuma dago da fuskar tata suna kallon juna yace "Hussain shine CEO kuma owner na H and H bani ba. Ni ko share ma bani da ita a cikin Companyn. Duk group of companies din nasa ne shi kadai. Ni maaikaci ne a karkashin sa nake aiki. Matsayina shine chief of staff, duk wani maaikaci na kamfanin a karkashi na yake, ni nake daukan su kuma Ni nake kula dasu. Nima Hussain albashi yake bani kamar yadda yake biyan sauran ma'aikata albashi. Gidajen nan guda biyu duk nasa ne, shi ya gina su, duk motar da kika gani a gidan nan da kuma gidan Aunty to Hussain ne ya siye ta, yana da passion for mota shi yasa yake chanjata kamar yadda yake chanja sutura. Duk abinda kika gani a gidan nan tun daga kan gadon da kika kwana akai zuwa chokalin da zamu ci abinci dashi Hussain ne ya siya" ta sunkuyar da kanta kasa tana fighting kukan da yake taho mata. Dama abinda ta aura kenan? Solobiyon miji wanda zai zauna kaninsa yayi masa komai? Shi me yake yi a lokacin da Hussain yake neman kudin? Ta rabu da Baba ta dawo hannun Hassan. Ita dai bata da Sa'a a rayuwa.
Ya sake dago kanta da hannunsa yana cewa "do you have a problem with that?" Ta girgiza kanta da sauri tace "babu matsala, kayansa ai kamar kayan ka ne. Kuma wata rana Allah zai hore mana namu mu tasar masa daga gida" yace "yes, da banyi niyyar zama anan ba, gida nayi niyyar in gina mana da kudin da nake ta tarawa. But ganin Baba ya fi mu bukatar gidan shi yasa na siya masa sauran kudin kuma nayi amfani dasu a biki, yanzu zan sake tara wasu kafin nan kafin mu tara zuri'a sai muyi ginin mu, shi yasa ban bari Hussain yayi mana gini irin nasa ba, saboda ba lallai bane mu gina irin nasa, kuma bana so in mun zo tashi muga kamar munci baya ne gwara muji cewa munci gaba. Kin fahimta?"
Ta juya tana kallon side din gidan Hussain, ta nuna da hannu tace " you mean....... Irin wancan zai gina mana......sai ka hana shi kasa ya gina irin wannan........?" Yayi murmushi ganin irin tarin mamakin da yake kwance a fuskarta yace "eh mana. Har fushi yayi ya kaini kara gurin aunty" wasu hawayen takaici masu zafi suka zubo mata, wannan wanne irin rashin rabo ne da Hassan? Ya saka dan yatsa ya gogi hawayen yace "kuka? Kukan me kike yi kuma?" Sauran kukan ya kwace mata gaba daya, tace "kukan godiya nake yi ga Allah, wanda ya bani miji mai gudun duniya da hangen nesa kamar ka" ya zauna sosai yana kwanto da ita jikinsa yace "it is okay. Ki bar kuka, you have cried a lot a cikin kwanakin nan. Murna zamuyi muyi godiya ga Allah kinji" ta gyada kai tana tashi daga jikinsa. Ya mike yana mikar da ita itama. "Ki tashi muje to muyi sallah mu gode masa, in mun gode masa sai ya karo mana. Haka yace da kansa" ta mike tana goge idonta da bayan hannunta.
Sai da ya kai ta har dakin ta sannan ya fita, har yanzu bai debo kayansa daga tsohon dakin sa ba, yan kayan da zai bukata kawai ya dauko ya dawo gidan. Ya kai kayan dakinsa sannan ya koma dakinta ya tarar tana toilet har yanzu. Ya koma dakin sa ya shiga wanka shima.
Sai da ta yi kuka mai isarta a toilet sannan tayi wanka tayi alwala ta fito ta saka doguwar riga tayi sallar ishai da bata yi ba. Tana tashi yana shigowa da basket a hannunsa ya ajiye akan side table yace "kar dai har kinyi sallah kin barni" tace "sallar ishai nayi ai" yace "ohhh okay" sannan yazo ya shiga gabanta suka gabatar d sallar sunna da annabi ya umarci ma'aurata suyi. Bayan sun idar Hassan ya yi musu adduoin neman albarka a auren su, neman samun dacewa a duniya da kuma a lahira.
Suka shafa ya juyo yana kallonta ya dan hade rai yace "idonki, kamar ya kumbura, duk kukan ne?" Ta sunkuyar da kai tace "da rashin bacci ma, kasan in mutum yazo bakon guri baya iya yin bacci" yana murmushi yace "kar ki damu, yau zakiyi bacci har da munshari" ta mike tana jin wani iri a jikinta, sai yanzu take tunanin yama akayi ta yadda tayi aure yanzu ne? Ita yar karamar ta ina zata kai wannan mutumin? So take tayi tunanin ta yadda zata zille masa amma kwakwalwar ta ta toshe ta kasa aikin tunanin yadda zata yi dashi dan ita sam yau bakar rana take gani kar yazo ya kara wa ranar ta duhu dan bakikkirin take ganin sa.
Ta mike tana kokarin shiga closet taji hannunsa ya rufe kofar sannan ya murda key, ta juyo da sauri sai gata a kirjinsa, ya saka hannunsa a dayan side din ta yadda ta kasance a tsakiyar hannayensa. Ta fara yayyarfe hannu sauran kukan da bata karasa dazu ba yana dawowa. Yayi dariya yace "cry cry baby, tunda kin zama baby let me treat you as a baby" ba tare daya jira amsarta ba ya daga ta chalak kamar baby, ya zauna akan gado yana dora ta a cinyarsa, ya lura da yadda jikinta yake rawa kadan kadan, ta boye fuskarta a jikinsa. Yace "bafa wani abu zanyi miki ba, look at me, look at me precious" ta dan dago kai tana kallon serious face dinsa yace "nace ba wani abu zanyi miki ba, I just want to feed you that's all. Na ga dazu baki ci abinci a gurin dinner ba, am sure da rana ma ba ci kika yi ba" tace "to ka sauke ni, zan ci da kaina" yace "to zan sauke ki, amma sai kin gaya min a fruits me kika fi so?" Tace "ni banason komai, ni bana shan fruits ma" ya dauko ayaba yana barewa yace "in dai kika cinye wannan to zan sauke ki kuma ba zan yi miki komai ba" ya fada yana kaiwa bakin