Showing 162001 words to 165000 words out of 300844 words
sannan ta fahimce shi, ta rufe idonta hawaye yana zuba, tace "ina jin ka, amma bana fahimtar ka, maganar bata clear" sai doctor din yayi murmushi cikin jin dadi yace "alhamdulillah. An samu nasara kenan" duk suka kalle shi cikin mamaki, Hassan yace "an samu nasara fa kace, bayan kana jin tace bata fahimta? Menene amfanin ji idan ba'a fahimta?" Doctor din yace "jin shine babbar nasarar da muka samu, ear drum din ya gyaru kenan ya fara receiving sound. Clearing sound din kuma sai anyi mata taimako da hearing aid. Zai kara enhancing ya kuma kara clearing din sounds yadda weak ear drums dinta zasu karbe shi sosai"
Ruqayyah dai tana kallonsu suna ta magana, bata jin mai suke cewa tana dai jin mixed voices dinsu kamar masu rada da juna tace "me kuke cewa ne wai? Ai kin bai yi ba ko? Na gaya maka ai mijina, aikin nan ba kyau zaiyi ba kazo mu tafi Germany din, a warkar min da kafata shima kunnen ayi min aikinsa acan, anan babu abinda za'a samu sai wahala. Dan Allah Hassan kar ka bari na kurmance" ta karasa tana kuka. Doctor din ya kalle shi yace "baka gaya mata ba?" Ga mamakin ta sai taji taji wannan tas, ta juyo tace "menene za'a gaya min" yace "cewa ba zaki kuma hawa jirgin sama ba ballantana har kije wata kasar. Likitocin dai da suke Nigeria damu zaki yi hakuri ki lallaba har zuwa karshen rayuwarki" ta zaro ido tana kallonsa sannan ta kalli Hassan tace "he is lying" likitan ya dauki takardun sa yace "in baki yarda ba akwai hanyar tabbatar wa, ki tafi airport yanzu ki hau jirgi ki gani. Ina tabbatar miki dan guntun jin da kika fara samu zaki rasa shi gabaki daya".
Daga haka ya fice ya bar su da rigima. Yasan bai kyauta ba yadda yayi breaking news din amma kuma shima haushinta dama yake ji yadda take ta nuna wa cewa basu iya aiki ba da sauransu, wai ita matar mai kudi. Yanzu sai yaga amfanin da kudin nata zaiyi mata.
Washegari suka bar asibitin dan Ruqayyah cewa tayi ba zata iya cigaba da zama ba. Hassan yayo mata order hearing aid din da zata ke amfani dashi, yaso kuma ace gida zasu koma amma taki komawa tace ita sai dai a chanja mata wani asibitin inda wani likitan zai sake duba kafarta tunda tana tsoron daring likitan kunne da yayi warning kar ta kuma shiga jirgi.
Wani private asibitin kashi ta tafi anan Kaduna, doctor din yayi mata alkawarin zai warkar mata da kafarta tana zuwa yayi admitting dinta ya fara karbar kudade yana sakawa a aljihunsa, tana asibitin aka kawo mata hearing aid dinta ta fara amfani dashi kuma alhamdulillah jinta ya dawo tana ji tas amma sai da shi, in ta cire sai dai taji kadan kadan kuma shima sai tayi stressing kunnenta tukunna. Daga baya ta fahimci cewa likitan bashi da clue akan abinda yake damunta dan haka ta nemi sallama kuma ya bata sai ta hada kaya sai Kano, AKTH, tana zuwa nan ma suka hau kanta da gwaje gwaje da hotuna da magunguna amma bayan shafe wata guda cur a cikin asibitin sai suka tabbatar mata da cewa su basu da idea me yake damun kafarta. A guri daya kuma kafar sai kara motsewa take yi kamar ta mai ciwon shan Inna, yanzu har kankancewar tata ya zama ana gani ake ganewa dan kana gani zaka gane daya kafar tafi dayar girma. A karshe sai likitoci suka yi mata cast, tun daga hips dinta har zuwa tafin kafarta dan ya taimaka mata wajen motsa kafar, daga nan suka ce babu abinda zasu kuma iya yi mata.
Ta zama mai kafa daya kamar yadda ta zama kurma.
*Ina mai bawa wadanda suka sayi littafin nan hakuri na rashin jina da basuyi ba jiya, nayi tafiya ne kuma gurin da naje suna matsalar nepa, naso in muku typing da yawa dan in wanke muku zuciya amma shima ba zai samu ba. Ayi min afuwa. Biki ne muke yi na dana, zaku jini shiru yau da gobe amma insha Allah jibi za'a samu mai tsaho kuma mai dadi. Zamu ji third wave din da zata yi hitting Ruqayyah.*
Ayi hakuri Please
Wannan littafin na siyarwa ne, in kin ganshi a wani gurin na sata ne. In kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020
*The Third Wave*
Kusan watanni biyu kenan da rasuwar Hussain. Kusan watanni biyu kenan da rushewar farin cikin rayuwar Hassan. A cikin wata biyun nan ba zai iya tunawa da ranar da yayi murmushi ba ko da kuwa na yake ne, ba zai iya tunawa da ranar da yaji farin ciki a cikin zuciyarsa ba komai kankantarsa kuwa kuma baya jin zai kuma jin farin ciki a kusa, bao san abinda ubangiji ya tanadar masa in the future ba amma ya san da wahala ya samu waniabu da zai maye masa gurbin abinda ya rasa, babu abinda zai maye masa gurbin Hussain da family dinsa including his own family.
Amma kuma duk da haka yasan abinda ya rasa, bayan rashin Hussain ya rasa wanda zai rarrashe shi ne kuma wannan rarrashin da kalamai masu dadi da kantar da hankali su yake bukata, soyayya da kulawa yake bukata, babu kuma abinda ba zai iya bayarwa ba dan yaga ya samu abinda yake so amma shima kanta yasan abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Dan inda zai samu wannan, wadda take da hakkin bashi wannan ita yanzu sam hankalin ta baya kansa ma kwata kwata yana kan nemawa kanta lafiya. Yes, yasan abinda ya faru da ita is quite unfortunate yasan dole ita din abar tausayi ce amma abinda yaso tayi shine ta fawwalawa Allah komai ta gode masa akan niimomin da already ya riga yayi mata bawai ta tayar da hankalin ta kamar yadda ta tayar a yanzu ba. Ba zai iya tuna ranar da yaje dubata ya tarar bata kuka ba, ko kuma ranar da suka yi waya yaji muryarta babu alamar kuka ba. Yanzu gashi doctor din da yake dubata yanzu yace jinin ta ya hau, on top of everything kuma tana kokarin ta dora wakanta hawan jini.
Tunda aka yi mata aikin kunne aka samu nasara kuma aka saka mata hearing aid jin ta ya dawo yaso ace ta dauki kaddara ta dawo gidan ta ta zauna a hankali har asan yadda za'a yi da matsalar kafarta, tunda dai kafar ba wai ciwo take yi mata ba amma sai taki yarda ta tubure masa ta fara bin asibitoci desperately tana neman miracle, kuma kowanne likita in taje gunsa abinda zai gaya mata daban da wanda wani likitan ya fada. Yayi yayi taki hakura, su Baba ma sunyi taki jin maganar su, har ta fara tunanin wai dan nakasa ta same ta shine ba zasu taimaka mata ta samu lafiya ba, shi kuma tace masa dama ba sonta yake yi ba so yake ta zama nakasashshiya dan ya ajiye ta a gefe ya sake sabon aure, shi yasa yace ba zata nemi lafiya ba.
Jin haka yasa ya rabu da ita, kuma duk bill din da akayi masa na magani yana bayarwa amma baya zama tare da ita yana gida yana jinyar tasa zuciyar, dan shi yanzu sam baya son barin gida, baya son abinda zai saka yayi nisa da kabarin Hussain inda kusan kullum nan ne gurin zamansa. Indai ana nemansa a gida nan ake zuwaa same shi ya tasa kabarin a gaba ya zuba tagumi yana tunani, nan ne spot dim tunaninsa tunda dama Hussain ne abokin shawarar sa to yanzu tunda babu Hussain din shine ya mayar da garden din da aka binne Hussain gurin zam yayi tunani, a cikin tunanin ne kuma ya yanke shawarar da tun sanda Hussain ya raba dukiyar sa biyu ya bashi yabi ya fara yinta. Kuma babu gudu babu ja da baya abinda zai yi kenan.
Ya nemi lauyoyin H and H group of companies sun zauna meeting, ya gaya musu kudirin sa kuma kamar yadda ya riga yayi tsammani sun nuna masa rashin amincewarsu. "Ba haka ake business ba Sir" ya mike yace "am not a business man, dan haka ba business ne a gaba na ba. Hussain ne business man kuma yanzu baya duniyar, cigaba da business daga inda ya tsaya ko kuma akasin haka ba zai kare shi ko ya rage shi da komai ba. An riga an rufe littafin sa, abinda zai amfane shi kawai shine sadakatul jariya da yayi sanda yana da rai ko kuma akayi da sunan sa. Ko kuma sadakar da akayi da sunan sa bayan bashi da rai, ko kuma yayan da ya bari a duniya, to shi bai bar Da a duniya ba dan haka abinda ya rage wanda zai amfane shi a yanzu shine sadakar da akayi da sunan sa" ya jawo takardar da already ya riga yayi drafting har ya saka hannu ya mika musu yace "I am going to sell H and H group of companies and all its assets. Zan kuma rabar da dukkan kudin, nawa share din da nasa, ga mabukata da niyyar Allah ya kai ladan kabarin Hussain"
Sai yaga dukkan jikinsu yayi sanyi. Yaji shima zuciyarsa ta karye, yana tunawa da duk irin fadi tashin da Hussain yayi gurin kafa Kamfanin, but keeping kamfanin ba zai amfani Hussain da komai ba a yanzu, bai kuma bar dan da zai gaji sunansa ba ya kuma cigaba da running kamfanin, shi kuma da ya ke da share mafi yawaya gadonsa bashi da wani interest a yin kudi ko kuma living lifestyle irin na Hussain, bashi da interest din zama Hussain dan yasan shi ba Hussain din bane ba, shi a yanzu ma bashi da wani interest na rayuwa kawai dai yana yin ta ne. Abinda zai amfani Hussain kawai yake nema dan da ace idan yayi sallah za'a kaiwa Hussain ladan da kullum in yayi tashi sai yayi masa shima. Dan haka ya yanke wannan shawarar.....
Bayan ya koma gida ya dauko wayarsa da take ta faman ruri tun dazu amma baya cikin mood din amsa waya dan haka yaki dauka, sai da yayi packing sannan ya daga yaga sunna Ruqayyah, sai da gaban sa ya Fadi dan yasan complain din wani abu zata yi masa ko kuma kuka zata yi masa. Ya dauka, kukan kuwa yaji tana yi "tun dazu nake kiran ka mijina kaki ka dauki wayar" yace "am sorry Hassana. Ina meeting ne da lauyoyin H and H shi yasa ban dauka ba" ta danji sanyi a ranta, at least dai dukiyar ta na nan, at least dai komai nakasarta still ita matar mai kudi ne, still ita matar CEO din H and H ce dan haka zata shana kuma zata huta ko da kuwa a Nigeria din ne kadai. In ma kuma kasar take son bari ai ana iya tafiye tafiye a mota ko a jirgin ruwa, yes, zata iya yin tafiya a jirgin ruwa tunda dai mijinta yana da kudin da zai kaita duk inda take so.
But before that, tana bukatar kafarta.
Tace "doctor ne dama ya rubuta mana sallama" Hassan yace "to alhamdulillah. Masha Allah" ta fara kuka "haka ma zaka ce? Ba zaka kira shi ka gaya masa cewa ban warke ba? Ta yaya zai sallame ni bayan ban warke ba?" Ta kwantar da kansa yana dora hannun sa a goshinsa yace "Hassana alhamdulillah fa nace, idan bam godewa Allah ba me kike so ince masa? Ko a bakin kura nake dole ne na godewa Allah tunda har ya halicce ni kuma yasa na rayu cikin imani har lokacin da yayi niyyar daukan raina" tace "kullum haka kake cewa, sai kake acting kana making dina ina feeling guilty ina jin kamar bana godewa Allah bayan da bana gode masa da yanzu zuciya ta ta buga na fadi na mutu" yace "ni ya akayi tawa zuciyar bata buga na mutu ba? Bani da uwa bai da uba dan uwana kuma ya tafi, ina ma zamu iya exchange din guri ni da ke? A dawo min da iyayena da Hussain a karbi kafata daya da kunnuwa na, ke ni ko da idon aka ce za'a hada zan bayar dan nasan Hussain zai kula da ni kamar yadda Sumayya take kula da ke. But you never appreciate her. Ban taba jin kin gode mata ba ko kuma kinyi mata magana mai dadi ba duk da kokarin da take despite halin da ita ma tata zuciyar take na rashin masoyinta" ai kuwa kamar ya tsokano wata rigimar "ni ina mamakin ku kai da Sumayya, yanzu duk halin da nake ciki amma wai baku manta da maganar inyamurin drivern nan ba, baku san irin takaicin da kuke saka min a zuciya ta in kunyi maganar sa ba....." Sai ya cire wayar daga kunnensa ya ajiye ta a gefe ya lumshe idonsa, baya bukatar wani bacin ran in ba so yake shima nasa jinin ya hau ba, sai da ya bar wayar ta huta a gefe sannan ya dauka ya mayar kunnensa yace "hello" tace "shine kayi shiru ko?" Yace "to ai babu abinda zan ce miki ne. Gobe zan taho kanon da wuri insha Allah, ku shirya kafin inzo, ina zuwa sai mu karbi takardar mu taho gida" daga nan ya katse kiran sannan ya kashe motar ya fita, ya daga kai yana kallon gidan Hussain wanda har yanzu yake a rufe, har yanzu ya kasa samun courage din shiga ballantana ya samu damar duba personal kayayyakin Hussain.
Gidan Aunty ya shiga, ya tarar tana cin abinci shima ya zauna ta zuba masa da kanta ya fara chachchakula kamar mai cin magani, tunda akayi rasuwar nan haka yake cin abincin sa dan shi kansa ba xai iya tuna ranar da yayi enjoying abinci ba. Ta zuba masa lemo tana cewa "Fulani Hadiza, kishiyar Maman Fatima tayo min waya jiya" ya tsaya da taunar abincin ya dago kai yana kallonta yace "me tace?" Tace "cewa tayi gobe idan Allah ya kaimu zasu aiko a debi kayayyakin Fatima" ya ajiye chokalin yana jin abincin ya tsaya masa a kirjinsa, a idonsa yana tunawa da ranar da aka zo akayi jeren kayan Fatima ana ta kide kide da fara'a da wasa da ɗariya, babu wanda zaiyi tunanin shekara biyu ne kadai ya rage mata daga ita har mijinta a duniya, yatuna da irin lodin kayan da aka zuba mata har sai da aka juya da wadansu duk kuwa da yawa da kuma girman dakunan ta.
Can cikin makwogwaron sa yace "Allah ya kaimu goben. Akwai keys a nan ko?" Tace "eh akwai" sai ya gyada kai kawai yana ture abincin. Zuciyarsa tana yi masa zafi, tragic deaths of family din dan uwansa yana dawo masa sabo. Aunty ta lura da chanjin yana yin sa sai ta fara kokarin cheering dinsa ta hanyar bashi labarin twins dinsa da da irin rigimar da suka yi tayi mata da taje gurin Inna ganinsu suna cewa sai sun biyo ta,ta san babu abinda yake faranta masa kamar labarin ƴaƴan sa amma sai taga ko murmushi bai yi ba ballantana dariya, yi yayi ma kamar baya jin abinda take cewa har sai da yaji tayi shiru sannan ya mike yayi mata sallama ya fita.
A ranar da daddare ya bude gidan Hussain ya shiga. A palon farko ya tsaya ya kunna fitila, idonsa ya sauka a kan katon hotonsu shi da Hussain, ya taka a hankali ya je gaban hoton ya tsaya ya a kallon fuskar Hussain, a kansa yana bitar maganganun da suka yi lokacin da akayi hoton da yadda Hussain ya ringa gyara zama wai shi lallai sai yayi zaman da yafi kyau. "Ka tabbatar na fishi kyau fa!" Ya gaya wa camera man din. Hassan ya saka hannu ya shafa fuskar sa, a hankali yace "ranar da ka bar duniya kafi kyau akan kowacce rana".
Sai ya juya ya doshi stairs din da sauri kafafuwan sa har suna hardewa cikin junansu. Bangaren Hussain ya shiga ya kunna fitila yana kallon gurin kamar yau ya fara shiga, taste din Hussain yana da karfi sosai dan haka sai yake ganin kamar komai na gurin kama yake yi masa da Hussain. Sannan ya wuce cikin Bedroom dinsa, ya tarar da komai a gyare tas kamar jiran mai dakin ake yi yazo, sai dai yar kura da dakin yayi. A kan bedside ya ga hoton su replica na wanda yake dakinsa, ya dauka yana kallon yace "mai gasa kawai. Dan na saka a dakina shine kasa a dakin ka ko?" Sai yaji a ransa kamar Hussain yace masa "ni ba zanyi fada da kai ba" shima sai yace "nima ba zanyi fada da kai ba" sai ya ajiye hoton ya zauna akan gado, har yanzu ya kasa yanke hukuncin abinda zaiyi da gidan, shima da yayi niyyar zai siyar da shine kamar yadda zai siyar da duk sauran gidajen Hussain amma yanzu da ya shigo gidan, da yaga gidan, sai yaji kamar ba zai iya siyarwa din ba, akwai memories na mutanen gidan sosai a cikin gidan, sweet sweet memories da ba zai so ya rabu dasu ba. Da ya shigo dakin sai yaji ya rage jin loneliness, kamar Hussain din yana tare da shi.
Ya ja pillow ya dora kansa yana tuna ranar da Hussain yaje kan gadonsa ya kwanta har ya tsokane shi yace pillow din Ruqayyah ya kwanta akai, shima sai ya ture pillow din kamar yadda Hussain ya ture a lokacin, a nan ne idonsa ya sauka akan diary din, diary din da Hussain kullum yake ta faman rubutu a ciki kuma ya hana kowa karanta wa. Ranar nan babu yadda baiyi ba ko page daya ya bashi ya karanta amma ya hana shi. Ya saka hannu ya dauka a ransa yana tambayar kansa if it's right ya karanta a yanzu. Shin Hussain zai so ya karanta a yanzu da bashi da rai ko kuma zai so yayi destroying ba tare da ya karanta ba? Ya jima yana lissafin abin sannan a karshe ya yanke shawarar