Showing 204001 words to 207000 words out of 300844 words
samu ilimi iri daya, hatta cup da plate din da suka ci abinci sanda suna tasowa iri daya ne gashi kuma kamannin su daya amma banbancin halayyar tamkar banbancin dake tsakanin annabi da kafiri ne. Kamar ace positive and negative sides of a battery ne.
Shine zai bada wannan shaidar sama da kowa tunda shine wanda yasan in and out of them, shi yayi zaman aure da duk su biyun a mabanbanta lokuta.
Shekarar farko ta bayan aurensu Allah ya azurta su da haihuwar da namiji wanda suka saka wa Abdullahi.
Tabbas, a farkon auren su har zuwa yanzu ma da suke shekara uku da yin aure sukan fuskanci financial problems, saboda Hassan yanzu ba ya aikin da zai ke samun albashi duk wata, sannan auren da yayi da kuma auren da yayi wa kanensa har biyu Khadijah da Nafisa ya dakatar da harkar gine ginen sa, estate din nan ta farko dai har yanzu ita ce, har yanzu bai samu ya kammala ta biyun ba, kuma gidajen yearly suke biyan sa rent ba monthly ba dan haka dan ma dai shi mai kulawa ne da lissafi a komai shi yasa har suke samun condition din da suke ciki a yanzu.
Akwai lokacin da har sai da ya siyar da motar sa yake hawa ta haya saboda rashin kuɗi, amma fa iyalinsa basu taba zamada yunwa ba. Sai Sumayya ta bashi shawarar kafin ya kammala wannan ginin ya yi shaguna a gaban estate din sai ya saka musu monthly rents yadda duk wata zai ke karbar wani abu, sannan itama kuma ta nemi ya amince mata ya nema mata aiki amma sai yaki yadda da maganar aikin duk da cewa ya ji dadin waccan shawarar data bashi ta shaguna, dan haka sai yace mata ya bata aiki a karkashin sa a matsayin personal adviser dinsa, zai ke bata salary duk wata, ita kuma taki yarda tunda already yana bata kudin da suke isarta yin duk bukatun ta.
Shi kuma sai yaji babu dadi, dan yasan yadda Baba yasha wahala akan karatun ta ya kamata ace iyayenta sun mori ilimin ta amma sai dai shi baya son ace matarsa kullum sai ta fita gurin aiki, baya son abar tarbiyyar yayansa a hannun yan aikin gidadan haka sai ya mayar mata da matsayin ta zuwa secretary dinsa sannan yayi mata office dinta anan cikin gidan su inda anan ne suke ajjiyar duk wasu takardu da duk wasu bayanai da suka shafi business dinsa, ta ce mai kula da komai. Sai ta karba saboda tana ganin aikin zata yi ai ba wai bada shawara kadai ba, kuma tasan idan ma bata karba ba dole zai dauki wani ko wata a wannan matsayin.
Kiri kiri Hassan ya hana ake kai su Aminu gidan Ruqayyah, yace "I don't want them getting confused su kasa gane wacece mommy din a cikin ku. In sun girma sun fahimta da kansu zasu je but not now" a dole Sumayya ta amince da hakan ba dan zuciyarta tana so ba sai dan bata taba yi masa musu, ko abu taga yayi va dai dai ba bata musa masa directly sai dai indirectly ta kawo masa shawarar da zata rushe waccan maganar ba tare da ya fahimci abinda tayi ba.
Wannan kenan...............
Bara mu leka Kano. Shekaru biyar bayan mai martaba Sarkin Kano tare da yayansa sunje sun binne konanniyar gawar mace da ciki, wadda suka yi tunanin ta yarsu kuma yaruwarsu gimbiya Fatima ce. Experience din da har yanzu yake fresh a zuciyoyin al'ummar gidan musamman mahaifanta.
Ana tsakiya da hidimomin yau da kullum kamar yadda aka saba, sai ga baki sunzo a airport taxi, tun daga bakin gate aka tsayar dasu ana tuhumar su da su fadi daga inda suke kuma wa suke nema. Hakan ya faru ne saboda lura da akayi da cewa ba hausawa bane ba, duk da cewa ba za'a iya fadin direct wanne addini suke bi ba.
Na mijin da yake gaba tare da driver ne yayi Magana
"Sunana Adam, ina son ganin maimartaba sarki"
Kallon da dogarin ya watsa masa ne yasa yayi saurin chanja maganar sa "ko kuma wani a cikin manyan gidan wanda yake kusa"
Dogarin ya kuma bata rai, gashi dai hausa yake yi amma yafi kama da inyamuri. "Me zaka yi musu in ka gansu?" Adam ya dauke kai, dama yasan haka zata kasance, shi yasa ya nemi da su fara aiko da sakon zuwansu kafin suzo dan shi baya ciki da wulakanci, zai iya fita yanzu ya wanke dogarin nan da mari. Ya hadiye bacin ransa, wai me yasa kananan ma'aikata suke da wulakanta mutane ne bayan su kuma manyan nasu ba haka suke ba.
Cikin bacin ra yace "kwadon su zanyi in cinye. Ina ruwanka da abinda zanyi musu, ji nake kai aikinka shine isar da sako kuma na baka sako ka tsaya kana bata min lokaci da tambayoyi marasa amfani" shima dogarin ya kufula "an bata maka lokacin, aikina ba isar da sako bane ba tunda ni ba masinja bane ba, aikina shine kula da lafiya da dukiyar mai martaba tare da iyalinsa, kai kuma kayi kama da marasa gaskiya shi yasa na tsare ka na hana ka shiga, kuma ko duk garin nan zasu taru wallahi ba zan barka ka shiga gidan nan ba"
Adam ya dube kofa ya fita "amma lallai zaka shirya yin azumi uku kenan na rantsuwar da kayi dan shiga gidan nan kamar nayi ne na gama ko kana so ko ba ka so, ko zaka bude kofa ko ba zaka bude ba ni dai sai na shiga, and I will be talking to the emir while you will be fasting saboda rantsuwar da kayi" dogari ya daga kafada yace "kai ka san me kace a karshe. In ma zagi na kayi to kai ma haka. Ni dai kofa ce ba zan bude ba sai dai ka fadi abinda zaka fada anan, in naji mai ma'ana ne in aika a fada a ciki, in marar ma'ana ne kuma in koma ciki in barka anan kayi ta maganganun ka kai kadai"
Adam yace "Ni ai da masu gidan nazo inyi magana, ma'ana mamallaka gidan ba masu saka ja da koren kaya suna tsayawa a kofar gida ba" dogari yace "in ma baki da fari ne mun saka din, gida ne dai ba zaka shiga ba"
A hankali aka sauke glass din tagar baya na motar, sannan kyakykyawar fuskar Fatima ta bayyana. Tana nan babu abinda ya ragu daga kyawunta sai ma fari data yi saboda chanjin weather, sai kuma rama da tayi sosai, ga wanda ya santa zai iya cewa ta kankance ta koma kamar sanda take secondary school, yanayin takuma yayi kama da yanayin marar lafiya. A tare da ita akwai wata mata wadda kana ganin ta kasan ita ta haifi Adam. Ta kare wa dogarin da suke cacar baki da Adam kallo, ta gane shi tsaf dan rayuwarta a gidan su bata daga cikin abubuwan data manta. For years, shine dogarin da yake gadin gate din farko na gidan, sannan tace "Auwal dogari" ya juyo da sauri jin an ambaci sunansa, suka hada ido sai ya makale a yadda yake, baki a bude yana kokarin mayar wa da Adam magana, tace "dan Allah ka bude mana kofa mu shiga" ya rufe bakin sannan ya mitstsika idonsa da sauri sannan ya sake kallonta, anya tsufa bai fara kama shi ba kuwa? Wannan kamar gimbiya Fatima fa. Gimbiya Fatima data mutu shekaru biyar da suka wuce.
Cikin rawar murya yace "gimbiya Asma'u?" Kanwar Fatima ce wadda suke yanayi. Fatima taji zuciyarta ta amsa da jin sunan kanwar ta, taji ta kosa da taga iyayenta da yanuwanta, ta kosa taga dan jaririn ta. Tace "ba Asma'u bace Auwal, Fatima ce" sai ya saki bulalar dogarai da take hannunsa, ya sake matsowa yana kuma lekawa cikin motar sannan kuma sai ya zabura kamar wanda akayi wa allurar karfi ya fita a guje, bai bude kofar gate din ba sai ya wuce cikin gidan a guje, ba zai bari wani ya riga shi kai wannan maganar cikin gida ba.
Sai dai yana shiga gate din gida ya fara kururuwa "jama'a ku zo ku taya ni gani, gimbiya Fatima ce gata can a cikin mota tare da inyamurai. Jama'a kuzo ku tayani dubawa ko ido na ne yake yi min gizo" nan take mutane sukafara cincirindon zuwa inda yake wasu kuma suna wucewa bakin gate, sai dai daga zarar sun ga abinda ya gani sai su koma da baya suna neman suma wadanda zasu gayawa.
Ganin haka yasa Adam ya tafi da kansa ya bude gate din gidan sannan drivern ya shigo da motar suka zarce zuwa gurin da aka tanada dan packing din motocin baki. Suka bude suka fito su uku sannan Adam ya biya drivern, yana tuna lokacin da shima yake a matsayin drivern taxi.
Fitowar Fatima ya saka sauran mutane suka karasa hargitse wa, wannan hayaniyar ce Adam baya so shi yasa yayi plan din neman audiance da mai martaba sarki ko wani mai fada aji direct yadda za'a yi maganar a tsanaki. Baya son hayaniyar tayi affecting Fatimah, not now, not when ta fara samun lafiya.
Suka fara tafiya, Fatima tana yi musu jagora dan babu abinda ta manta a tsarin gidan nasu, Maman Adam tana rike da ita, supporting her, irin rikon da akeyi wa marasa lafiya. A haka suka doshi cikin gidan, duk inda suka wuce sai mutane su dare su basu hanya, wasu kuma su fita a guje. Har suka isainda Adam ba zai iya wucewa ba sai ya dakata yana jin kamar ya bisu amma babu dama dan haka yace "Mama" maman sa ta juyo tana kallon sa sai yace "take care of her please" sai tayi murmushi ta gyada masa kai ba tare da tace komai ba.
A cikin gida, a dan karamin shamakin da yake tsakanin bangaren Hajiya Fulani mahaifiyar Fatima da kuma Hajiya umma abokiyar zamanta, kamar kullum da yamma, yau ma suna zaune tare a karkashin bishiyar da take gurin suna shan fresh air tare da jin labaruka daga barorin su.
Hajiya Fulani kawai jinsu take yi amma bata fahimtar hirar da suke yi, ita yau bata jin dadi sosai gabanta sai faduwa yake yi, dama kuma ita ba lafiya xe ta ishe ta ba dan tun lokacin da labarin rasuwar yarta Fatima ya iske ta, ballantana kuma jin irin mummunar mutuwar da tayi, tun daga ranar har yau bata kuma kasancewa cikin farin ciki ba, bata kuma jin wani labari dazai saka ta farin ciki ba, bata kuma jin dadin rayuwa ba, tana yin rayuwa ne kawai dan da akwai rai a jikinta.
Sai da yawa ta kan ce "ni kullum sai inke jin kamar Fatima zata shigo gidan nan, har jin taku nake yi kamar nata" sau da yawa idan tayi wannan maganar sai mai martaba ko kuma duk wanda tayi wa maganar ya amsa mata da cewa "ai dama dole zaki ke jin haka, tunda baki ga gawar ta ba, kullum gani zaki ke yi kamar bata mutu ba zata dawo". In mai martaba ne sai ya kara da cewa "ni ma kaina dana binneta da hannu na ji nake yi kamar ba ita na binne ba, tunda babu sauran wasu kamannin ta a tare da ita".
Yau ma wannan feeling din take ji, kamar Fatima zata zo ta zauna a tsakiyar su kamar yadda ta saba yi in dai tana gidan. Takan ce "tsakiyar ku yafi dadin zama, in juya duk ta side din da nake so in kwanta akan cinya".
Hayaniyar da gidan ya dauka shi ya katse labarin da wata baiwa take basu, sannan kuma sai ga wasu bayi su biyu sun shigo gurin a guje kamar an koro su, jakadiya ta mike "kai! Lafiyar ku kuwa? Wanne irin rashin hankali ne haka?" Suka zube a kasa suna tuba sannan daya tace "wata mata muka gani yanzu mai kama da gimbiya Fatima" Hajiya Fulani ta mike tsaye, Hajiya umma ta mike itama tana tambayar "a ina? Ko yar uwa ce?" Sai suka ce "gasu nan zasu shigo nan gurin ita da wata mata, kowa gudu yake yi in ya gansu, kamar an tsaga kara ita da marigayiya".
Hajiya Fulani ta fara tafiya da sauri zuwa hanyar shigowa gurin daga waje, zuciyarta tana gaya mata Fatima ce ba mai kama da Fatima ba, kafin ta karasa su ka shigo, Fatima a rike a hannun Maman Adam. Kallo daya tayi mata tasan cewa yarta ce Fatima, tasan cewa gawar dasu Mai martaba suka binne bata Fatima bace ba.
A hankali Fatima ta saki hannun Maman Adam sannan ta mika wa Hajiya Fulani hannu tace "Hajiya ta, umma na na dawo gida"
Jin muryar ta ya tabbatar wa da Hajiya Fulani cewa Fatima ce, mai makon ta amsa mata ko kuma ta kama hannun data mika mata sai ta zame ta yanke jiki ta fadi.
*Back From The Dead*
Appreciate this please......
Cikin mintuna da basu kai talatin ba gaba ki daya gidan sarautar kano ya hargitse, masi gudu nayi cike da tsoro da fargabar sunga fatalwa, wasu kuma suna tahowa da gudu dan gani ya kori ji, suna so si tabbatar wa da idanuwan su cewa gimbiya Fatimah data mutu shekaru biyar itace yanzu ta shigo cikin gidan da kafafuwanta.
Fatima ta karasa cikin sassarfa ta durkusa a gaban hajiya Fulani tana girgiza ta kadan "Hajiya? Hajiya ta?" Umma da tun shigowar Fatima ta daskare a gurin ta matsa inda Hajiya Fulani ta fadi ganin cewa jakadiya da sauran barorin da suke gurin duk sun tsorata sun ki zuwa gurin. Ta jijjigata sannan ta dauko robar ruwa ta yayyafa mata tana kiran sunanta har suka ji ta sauke ajjiyar zuciya sannan a hankali ta bude idanunwanta, ta sauke su akan Fatima datake rungume da ita tana hawaye "Fatima? Fatima zahra ke ce wannan a duniya ko dai mutuwa nayi nima nake ganin ki a can?" Fatima tace "hajiya nice mana, baki gane ni ba ko? Na rame ko? Rashin lafiya nayi sosai. Nasan kuna ta nemana duk shekarun nan" sai ta kara kukan ta tace "nima ina ta neman ku Hajiya, ina ta so in taho gurin ku amma babu dama".
Umma da take jin su ta kamo hannun Fatima tace "mu bama neman ki Fatima, mu bamu taba neman ki ba ko sau daya saboda mu ce mana akayi kin mutu, mu a gurin mu kin mutu dan har anyiwa gawarki suttura an binne ki"
Fatima ta bude ido cikin mamaki, sai kuma ta waiga tana kallon yadda kowa a gurin yake kallon ta,wasu tana hango tsoro a idonsu. A lokacin Asma'u kanwarta ta shigo gurin, ita ma labari ya iske ta a dakinta cewa Fatima tayo fatalwa tana yawo a gidan, tana shigowa kuwa taga Fatima a durkushe kusa da iyayen su, ai kuwa sai ta zunduma ihu ta juya a guje, Fatima ta mike "Asma'u? Asma'u Fatima ce fa, Asma'u nice Fatima wallahi ba mutuwa nayi ba, karya ake yi min wallahi ban mutu ba" kuka yaci karfinta, tana jin zafi a zuciyarta cewa yan uwant data gama cin burin zuwa ta gansu ta rungume su taji dadi sune suke gudunta sun dauka fatalwa ce, wai ashe duk tunanin da take cewa babanta yana nan yana zazzage Nigeria yana nemanta ashe ba haka bane ba shi ya dauka bata duniya, for five full years, hakan yana nufin har sun fara mantawa da ita kenan. Hakan yana nufin badan Mama ta taimaka mata ba, da sai dai ta karashe rayuwarta a rufe babu mai zuwa cetonta kamar yadda da take tsammanin babanta zai yi bincike ya gano inda take sannan ya taimaka mata.
Sai ta juyo ta rungume Maman Adam, "Mama dan Allah ki gaya musu, ki ce musu wallahi ba mutuwa nayi ba ina tare daku, ki gaya musu su bar guduna ni ba fatalwa ba ce ba" kafin Maman tayi magana Hajiya ta tashi ta rungume ta, "ba sai kin rantse ba Fatima, ba sai kin nemo ma yi miki shaida bani nasan kece, tunda aka ce min kin mutu jikina yake bani kina raye kuma zaki dawo wata rana,ni na san bagawarki suka binne ba".
A lokacin suka jiyo maganar shamaki, "takawa sannu, zaki ɗaukawa sannu, sunkuye alher" Hakan yana nufin mai martaba sarki ne da kansa ya taho gurin, abinda baya taba yi, baya taba shigowa bangaren matansa sai dai in watace a cikin su bata da lafiya ko wata a cikin yayansa. Jin haka yasa ka Fatima ta saki Hajiya ta kuma fita a guje zuwa inda yake tahowa, ita dama can tun tana karama yar babanta ce, ma'ana tafi shakuwa da babanta akan kowa, yaga tahowar ta, yakuma gane ta, ba ko girgiza ba ballantana yaji tsoro sai ma farin ciki da ya cika zuciyar sa cewa labarin da aka kai masa gaskiya ne, Fatima bata mutu ba kuma ta dawo gida.
Tana zuwa ya shige jikin sa tana kuka, "wallahi ban mutu ba Takawa, ina imo, ina can an rufe ni an hana ni tahowa, ina can bani da lafiya Baba". Bai amsa mata ba sai ya rungume ta yana shafa kanta, a ransa yana tasbihi ga ubangiji daya dawo masa da Fatima duk da cewa bai taba addu'a akan hakan ba, bai taba yi ba saboda bai san cewa hakan zai iya kasance wa ba, bai san cewa tana da rai ba.
Sai kuma ta cika shi da sauri ta dago kai tana kallonsa sa, zuciyarta a karye, yana yin fuskarta kadai ya isa ya saka mai karyayyiyar zuciya yayi kuka, tace "Baba ina Hussain? Ina Hussain dina? Baba dan Allah ka gaya min ba gaskiya ba ne ba abinda naji, dan Allah ka gaya min bai neme ni ba saboda shima ya dauka na mutu, ka gaya min cewa yana nan yana kukan rashina ba wai ni ce zanyi kukan rashin sa ba".
Dauke kansa yayi gefe ya lasa hada ido da ita, hakan yana kara tabbatar mata da maganar da Adam ya gaya mata amma kullum take gayawa zuciyar ta cewaba haka bane ba, kullum take saka ran cewain ta dawo goda zata tarar cewa ba haka bane ba, amma expression din fuskar maimartaba sarki