Showing 195001 words to 198000 words out of 300844 words
kwanta, saboda bata son ta kwanta tayi ta tunani, tana kwanciya kuwa tayi bacci abinta.
Da assuba ta tashi tayi sallah sannan tayi wanka sai ta koma ta cigaba da baccin ta dan sai yanzu gajiyar bikin ta ke sauko mata, duk da dai ba wani dogon biki tayi ba. Motsin Hussain ne ya tashe ta, ta farka ta ganshi ya kafe ta da ido yana ta murna wai yau sun kwana tare, daga nan sai ya saka ta a gaba da zance a dole ta mike duk da baccin ba isarta yayi ba ta ja shi xuwa toilet tayi masa wanka yana tayi mata hira "mommy wai yanzu kim dawo gidan daddyn mu ne? Anan zaki ringa kwana ko? Kin daina kwana a gidan Inna?" Tace "eh" yayi tsalle yana bata toilet din da kumfa "nima na daina kwana a gidan Aunty ko? Tare zamu ke kwana anan da su Aminu ko? To ina suke? Ko a dakin mu suka kwana? Daddy ya kawo mu jibi ya nuna mana dakin mu ya saka mana gado a ciki kowa da nasa yace banda fada. Kinga Daddy shi fada yake yi mana idan munyi fitina, Aunty kuma sai ta bamu sweet tace mu fita backyard muyi ball. Ni ban iya ball ba faduwa nake yi......"
Haka yayi ta zuba kamar fanfon daya lalace ita dai tana tayi masa dariya har ta gama masa wankan tayi masa brush da alwala ya fito ita kuma ta tsaya ta gyara toilet din sannan ta biyo bayansa ta tarar ya jawo drawers din dakin wai yana neman kayansa. Ta goge masa jikinsa sannan ta mayar masa da kayan da ta cire masa saboda bashi da wasu sannan ta saka shi yayi sallah, ya duddungura abarsa duk rabi wasa, ita kuma ta shirya cikin riga da skirt na atamfa da suka karbi jikinta sosai, ta gyara fuskarta dai dai gwargwado sannan ta gyara dakin shima ta dauki Hussain suka fito yana ta yi mata complain din yunwa yake ji "a gidan Aunty ina tashi aunty take bani tea nake sha ba ta yi min wanka sai nasha tea" suka fito tana lakuce masa hanci "ninkuma a gidana sai mutum yayi sallah yayi wanka sannan zai sha tea, in luma mutum bainyi abinda nace ba to zan mayar dashi gidan Aunty" ya kankame ta yana kwabe fuska "ni nafi son gidan nan, nafi son mommy na da Daddy na" ta rike fuskarsa a hannunta tana murmushi tace "nima ina sonka sosai sweetie pie"
Sai taji gyaran muryar Hassan a bayanta, suka juya da sauri, Hussain ya zame daga jikinta ya ruga gurinsa "daddy yau akan gadon mommy na kwana kuma banyi mata fitsarin kwance ba kuma tace a nan gidan zata ke kwana kuma bata bani tea nasha ba sai tayi min wanka" Hassan yayi dariya yana shafa kansa yace "kai, da kai da parrot ban san wanda yafibwani surutu ba. To gaya min gadon mommy da dadi?" Hussain yace "da dadi mana, wankan ta ma da dadi, dama tana yi min wanka in naje gidan Inna shi kuma Baba ya siyo min Mango"
Sumayya tace "Hussain baka gaishe da Daddy ba fa kake masa zance haka" Hussain yace "lah na manta, daddy good morning. Zaka bani tea insha?" Hassan ya dauke shi yace "zan baka, amma sai kayi shiru ka barni mun gaisa da mommyn ka tukunna"
Ya juya yana kallon Sumayya sai taji babu dadi, sai taji Kamar bata kyauta ba data fito babu hijab dan bata jin ta taba tsayawa a gabansa babu hijab. Ta dan rage tsaho ta gaishe shi ya amsa yana studying fuskarta "anya kuwa kinyi bacci sosai? Ko bakunta ce?" Ta danyi murmushi tace "nayi bacci fa" yace "amma ba sosai ba ko?" Tayi shiru, yace "kar ki damu, babu dodo a gidan nan" Hussain daya kwantar da kansa a kafadar Hassan yace "Daddy akwai dodo a gidan aunty, yana nan acikin closet aunty Zulaihat tace duk wanda ya kuma shiga ciki ya buya sai dodon ya kama shi kuma tace yana da manyan hakora da zai cinye mutum dasu kamar haka" ya fada yana kokarin demonstrating a wuyan Hassan, Hassan ya sauke shi yana cewa "a'a kar a fara cinyewa ta kaina a cuci amarya ta" Sumayya ta danyi dariya tace "ban san lokacin da bakin yaron nan ya bude haka ba, maganar sa tafi shekarun sa yawa, biyu da rabi yake yanzu fa" Hassan yace "sai next month ma zai yi two and a half years. Yawo be dashi da surutu da kirinki irin na mai sunan shi. Dama kamar su daya" Sumayya tabi Hussain daua fara tsalle tsallen sa a corridor din da suke tsaye tana tuno late Hussain tace "Allah yasa yayi halinsa" Hassan yace "banda iyayin" tayi dariya, sai ya bi ta da kallo yana jingina da jikin bango, ta hadiye sauran dariyarta tana kokarin kamo hannun Hussain yace "kinyi kyau sosai" Hussain ya juyo yace "yes mommy kinyi kyau, amma na jiki kyau" ta juyo tana kallon Hassan sai ya girgiza kansa yace "too late, har iyayin ya dauko".
Tana kokarin hada wa Hussain tea sai ga breakfast an kawo musu daga gidan Aunty, a tare da breakfast din akwai Aminu da Yusuf hannayensu ruke da kayan su wai sun taho ana gidan zasuyi wanka. "Mommy ce zata yi mana wanka yau, bama son wankan Aunty Zulaihat" Zulaihat ta dungure musu kai, "kar Allah yasa ku so din, kafin dai ayi daran akayi kwande" Sumayya tayi murmushi "tuba suke yi auntyn yara" sai ta jasu suma zuwa dakinta tayi musu wanka ta shirya su sannan suka dawo suka tarar Hussain ya saka Hassan a gaba da surutu shi kuma sai loda masa abinci yake yi yana ci yana kara wani zancen.
Suka hadu sukayi breakfast tare as a family, sai Hassan yaji bai taba jinsa complete ba irin na yau dan tun da yaran suka fara tashi basu taba samun sun zauna sunci abinci da iyayen su ba. Ko kafin su rabu da Ruqayyah ma mostly kafin ya tashi ta tura su gidan aunty. Suma kuma yaga abin yayi musu dadi sosai musamman yadda Sumayya take tarairayar su kowa yana zuba shagwabarshi son ranshi.
Tare suka gyara gurin da suka ci abincin, har da Hassan shima a dauke plate Sumayya tana tayi masa dariya sannan ya bisu kitchen yana kallon ta tana wanke kayan da suka bata yaran kuma suna tayata kifewa, har layi suke hawa in aka bawa wannan yayi drying plate ya kai cikin drawer sai a bawa wannan cup shima yayi drying ya kai, a haka har suka gama ita bata san Hassan video yake tayi musu ba sai data lura sannan ta rufe fuska tana dariya, sai ya dawo bayan ta ya tsaya sannan ya jera yaran a gabansu yayi musu selfie, Hussain yana ta gyara riga yana dago kai wai dan yayi kyau kuma kar a yanke shi.
Wannan hoton shi ya dora a dpn sa kuma shine abinda Ruqayyah ta tashi dashi a yau. Dama jiya a palo bacci ya dauke ta akan carpet, shima kuma dan ance bacci barawo ne amma da babu yadda za'a yi ta iya yin bacci a yadda take jin zuciyarta. Bata taba shiga bacin rai irin na wannan karon ba, bata jin ko rashin kafarta ya yi affecting dinta kamar yadda auren Hassan to her twin sister yayi affecting dinta. Taji duniyar gabaki daya ta fitar mata a kai, taji tana son mutuwa ko zata huta da ganin wannan bakin cikin amma kuma bata san abinda zata tarar in taje can din ba, a lokacin ta fahimci frustration na matan da suke kashe mazajen su idan sunyi musu kishiya, kishiyar ma da babu dangin iya balle na Baba ballantana ita d mijinta ya auri twin sister dinta, anya kuwa an taba yi wa wata irin cin mutuncin da akayi mata? Kuma iyayenta? Wadanda suka haife ta?
Ta tabbatar cewa Baba ne ya hada wannan kwamachalar saboda dalilin shi baya son aurenta da Hassan dama tun farko, Inna kuma ta zabi tabi bayansa akan ta goyi bayanta ita yarta, ita kuma munafukar Sumayya ta amince, tasan kuma dalilin da yasa Sumayyan ta amince va dan komai bane ba sai dan ta rama rabatan da tayi da Adam.
Sai taji nadamar abinda tayi wa Adam yazo mata, da ta sani ta barshi yayi ta auren Sumayya tunda ita Sumayya bata fahimci gata tayi mata ba, ita tana so ta hana ta auren wanda nan gaba zata zo tayi nadama shine ita kuma ta huce by auren mijinta? Uban yayanta?
Tabbas da ace zata iya kama Sumayya a yanzu da sai tayi mata abinda duk su biyun sai sunji a jikinsu. Tabbas sai tace ina ma ta zabi ta bata ran Baba taki auren Hassan akan auren Hassan da ta zabi yi a yanzu. Sai taji tsanar family dinta a ranta, tsana mai tsanani kamar irin tsanar da take tunanin suna yi mata, tunda zasu iya hada auren Hassan da Sumayya.
Yan aikinta babu wanda ya zauna ya tattashe ta, sannan dama ita babu wanda yake zuwa gurinta ballantana ya rarrrashe ta. Tabbas a ranar tunanin lahirar ta ne kawai ya hanata kashe iamta cikin dare. Sai da assuba sannan ta ja jiki ta hau sama tayi sallah ta kuma kwamta akan sallayar bacci ya dauke ta.
Tana farkawa kuma ta farka da wannan mugun hoton da Hassan ya saka a dp dinsa. Yayanta data haifa da cikinta, mijinta, data sha wahala kafin ta samu, wai duk sun zama na twin sister dinta bayan gata nan da ranta a duniya.
Wannan hoto yafi saran maciji dafi a zuciyar Ruqayyah, yafi kuma kibiya tsini saboda sukar da yayi mata. Kamar yadda ta kwanta da kuka haka ta tashi da kuka tana neman Allah ya dauki ranta ta huta, to me zata yi musu ne ita yanzu? In ma tace zata yi musu wani abu dan ta rama abinda suka yi mata ta yaya zata yi musu bayan ita yanzu sauka kasa ma daga dakin da tayi wa kanta a sama ba karamin tashin hankali bane ba. Sharrin data saba yi wa mutane kuma yanzu ta yaya zata yi musu bayan babu wanda yake sonta hatta iyayen da suka haife ta.
Sai ta tashi ta ja kofar dakin ta rufe, locking herself in, dan bata son ganin kowa bata son kuma jin maganar kowa yau, duk da cewa ma tasan babu wanda zai zo gurinta sai yna aikinta, sai kuwa kawayen ta da sukan dan leko su gnta musamman in rashin kudi ya motsa musu.
Sai dai kuma tana kwanciya taji kukan jaririn nan ya cika gidan gabaki daya, har amsa kuwwa gidan yake yi da kukan nasa. Ta saka hannayenta ta toshe kunnuwan nata tare da rufe idonta"dan Allah kayi hakuri ka rabu dani, kayi hakuri dan girman Allah" amma rufe idon yasa ga ganin gawar Minal a idon nata, kamar kullum ta zuba mat ido tana kallon ta.
Tayi saurin bude idon nata taba numfashi sama sama, har wani duhu duhu take gani da wani jiri da yake fibanta duk da cewa a kwance take, ta mika hannu ta bude side drawers ta jawo sleeping pills dinta da kuma robar ruwan da tane ajiyewa permanently a nan saboda bata iya bacci in bata sha ba.
Ta mike zaune tare da bude robar maganin ta debo a hannunta, sai dai maimakon ta debo biyu kamar yadda take sha kullum sai ta devi guda biyar sannan ta watsa su a bakinta ta bisu da ruwa.
Ranar through out Hassan yana gida bai fita ko bakin gate ba, kawai duniyar ce take yi masa dadi duk da cewa ba wai angwancewa yayi da Sumayya ba amma shi gani yake ko haka ta barshi ta biya shi. Yana jin dadin yadda suke yi da yaran, da shima yadda take yi masa, duk da yasan bata sonsa amma ko a fuskarta ba zaka ga alama ba.
Yan uwansu na Gombe suka zo yi musu sallama zasu tafi, ta durkusa har kasa ta gaishe su tare da rufe fuskarta tana jin kunyar tsokanar ta da suke yi, sai ya tuna da aurensa da Ruqayyah rana irin ta yau yadda ta tari yanuwansa, sai yayi mamakin kansa ta yadda bai lura da komai ba a lokacin sai ynazu.
Da zasu tafi Sumayya ta hau samt ta bude lefenta ta debowa yammatan kayan kwalliya masu yawa a leda, manyan kuma ta basu turaruka, suka yi mata godiya kowa yana saka mata albarka sannan ta kama hannun twins dinta suka raka su har bakin gate. Suna ta tsokanar yaran da cewa sunga gidan amarya sun guji Aunty saboda ita tsohuwa ce, Hussain yana ta zuba musu surutu da iyayi har suka tafi.
A daren ranar Sumayya duk yara ukun ta jere akan gadonta tace duk anan zadu kwana, Aunty ta aiko a tafi dasu suka hada kai suka yi ta zunduma kuka su bazasu koma gidan aunty ba, Hussain har da bada sakon a gaya wa aunty ta aiko masa da kayan sakawarsa da kuma kayan wasan sa. Haka Hassan ya saka su a gaba ya zuba tagumi yana kallon yadda suka kankame Sumayya suka bacci, exhausted, saboda kiriniyar da suka yi tayi.
Ya gaji da tsaiwa ya kuma gaji da hamma, yana lura da Sumayya ba bacci take yi ba idonta biyu amma ta rufe ido sai yace "zan tafi in kwanta" ta dan bude ido kadan tace "sai da safe" ya tsaya yana kallon ta sai tayi sauri ta mayar da idonta ta rufe. Ya juya a hankali ya kashe musu fitila ya fita, ba zai taba takura mata ba, yasan tana bukatar lokaci kuma zai bata as much time as possible dan yafi son duk abinda zai faru a tsakanin su ya faru da son ranta ba wai bisa tursasawa ba.
Washegari ma suka tashi kamar jiya, sai dai yau yara suna da school dan haka da wuri Sumayya ta tashe su tayi mudu wanka tana tunanin yadda zata taso Hassan ya karbo musu uniform dinsu a gidan Aunty sai gashi Aunty ta aiko musu har da abinci a lunch boxes dinsu. Dan haka Sumayya ta saka musu kayan ta hada musu tea duk suka sha sannan sai ga Hassan ya sauko dakansa yace zai kaisu duk kuwa da cewa drivern su yazo already, but yafi so ya kai su da kansa dan yanzu fatherhood din yake ji sosai.
Sun tafiya ta koma saman da sauri ta shiga dakinsa, ta yaba da tsaftar dakin sosai dan ba zaka taba cewa dakin namiji bane ba ta gyara masa gadon ta share ta wanke toilet ta fitar da kayan wanki sannan ta koma bata dakin shima ta gyara. Kafin ya dawo har ta kusa gama gyaran gidan, sai ya dage wai lallai sai ya taya ta aikin ta hana shi yakinyarda sai ta bashi duster ya fara goge goge, tana tayi masa dariya, ita sai taga abin mamaki namiji da aiki, hannun sa kamar yayi wa duster din girma, sai shi kuma ya fara bata labarin yadda yake aikin gidansu sanda yana saurayi "Hussain baya komai sai bata guri, ninake yin kusan komai a gidan lokacin su Hassana basu girma ba aunty kuma bata da yan aiki. Har wanke wanke nayi wa aunty. A haka na saba, ni ina enjoying gyaran gida ma sosai sai inji kamar wani responsibility ne daya kamata inyi"
Tare suka gama komai har kitchen ta gyara ta hada wa Aunty kayan abincin da ta aiko musu dashi jiya, kamar hadin baki tana fitiwa dashi ana aiko musu da wani sai ta bayar da na jiya aka tafi dashi sannan ta dauko musu plates suka zauna a kasa akan carpet ta zuba masa zata zuba nata yace sai dai su ci tare, sai taji wani iri dan jiya ma da daddare haka ya dage ta hada musu abinci gabaki daya har yara a tray suka ci gabaki daya, but wancan da yara, wannan kuwa su biyu ne kawai.
Amma bata son yi masa musu, tayi wa kanta alkawarin ba zata ke yi masa musu ba dan haka ta saka chokali a nasa suke ci tare, ya lura a takure take sai ya fara yi mata hira, a lokacin ta lura da wani abu a tare dashi, da wahala yayi dogon sentence ba tare daya ambaci sunan Hussain ba, sai ta tuna da tata twin din, ko a wanne hali take ciki? Ta dauka zata dawo da safe amma shiru har gari ya sake wayewa.
Bayan sun gama ne ya hau sama ita kuma ta gyara gurin da suka bata. Bai jima ba ya sauko yace mata zaije gidan Aunty "zanje gurin Hussain". She was confused sai daga baya ta tuna a gidan aka binne Hussain, kabarin sa zaije kenan. Sai takara jin tausayin sa sosai, lallai shi din ya hadu da jarabawowi da yawa a rayuwa, lallai shi din abin a tausaya masa ne, lallai yana bukatar mai faranta masa rai a yanzu.
Bayan ya tafi ta koma dakinta tayi wanka ta shirya tsaf da ita ta bade kanta da turare, sannan ta hada kayan wankinsa data dauko da nata dana yara da suka cire da towels din da suka yi amfani dasu duk ta je toilet din yara inda taga washing machine sabo a ciki, ta dauki manual dinsa taga yadda ake amfani dashi sannan ta dauko detergent din da ta gani a toilet dinsa ta wanke kayan tsaf ta matse su, ta zagaya baya ta backdoor inda tasan akwai igiyar shanya tun Ruqayyah tana gidan ta shaya kayan ta dawo palo tadauki wayarta tana duba messages din da kawayenta da kuma yan uwan da basu samu damar zuwa bikin ba suka turo mata.
A lokacin ne aisha ta shigo, tsohuwar yar aikin Ruqayyah ce tun tana tare da Hassan, Sumayya ta tashi zaune tana kallon ta ganin tashin hankali a rubuce a fuskarta. "Aisha lafiya? Aisha ta fara hawaye "Aunty Sumayya dan Allah ki zo, Aunty Ruqayyah tunda ta kwanta jiya da safe har yanzu bata tashi ba. Kofar dakin arufe munyi ta bugawa bata bude ba"
Wani