Showing 285001 words to 288000 words out of 300844 words
ba mahaifiyarsa bace ba ba kuma kakarsa ba ce ba kanwar kakarsa ce, wannan ya saka shi tunanin me zaiji idan yaga mahaifiyar ta sa? Ko kuma auncle Hassan din da yaji ana ta magana? Wanne irin so suke yi masa wanda har zaifi wanda ya gani a idon wannan dattijuwar da ta kasa sakin sa sai shashshafa shi take yi.
Wayar ta da aka kawo mata ce ta saka ta cika shi at last ta fara waya tana kuka tana kuma dariya a lokaci daya, bai san da suwa take wayar ba amma dai labarin zuwansa take bayarwa. More relatives? How many if them are there? Ya kalli Sumayya yaga itama wayar take yi itama kuma da hawaye a idonta da kuma dariya a fuskar ta, ita ma wasu take gaya wa yazo, ya kalli Amatullah ita ma the same thing. Sai ya kalli dakin da suka fito daga ciki, idan yayi ra'ayi zai iya zamewa ya shiga dakin ya huce haushin sa akan wannan mokadaddiyar matar ta kwance amma kawai sai yaji a ransa baya son yi mata komai kuma, not anymore.
But har yanzu yana bukatar answers, sai ya mike ya koma gaban hoton dazu ya zubawa twins din ido yana kallon su, daya daga cikin su shine mahaifin sa, shine kuma baya duniya. Ya mutu ranar da aka haife shi kamar yadda ya karanta a labarin accident din daya karanta a littafin. Sai ya juya ya kalli Amatullah da take ta yawa tana bayar da labari, yayi mata alamar tazo, ta katse kiran ta taho gurinsa da sauri itama tana kallon hoton, ta tsaya a kusa da shi sai yace "waye Hassan waye Hussain?" Ta gane abinda yake son sani, mahaifin sa yake son banbancewa, tace "Hussain, kamar yadda Daddy kullum yake bamu labarin sa yace shine the most handsome man in Kaduna a zamanin sa, the youngest richest man a lokacin sa, the most carefree and generous man, the proud dangoten kaduna" ta karasa tana dora hannunta akan fuskar Hussain.
Sai kawai Amir ya samu kansa da yin murmushi, murmushin da ya zubo da kwalla daga idonsa, shima ya dora hannun sa a kusa da nata, a hankali tace "he lived the most beautiful life inji Daddy. Nothing but the best for Hussain. And he married a princess" Amir ya juyo da sauri yana kallon ta yace "Princess?" Ta gyada masa kai "yes, princess of Kano" yace "yar sarki Umar?" Tace "kanwarsa, zamanin babansu ne sarki" sai ya rufe idonsa tare da dora goshinsa akan hoton. Kullum abinda yake hangowa a matsayin mahaifiyarsa shine karuwa, ko wata marar daraja marar tarbiyyar da har zata iya cin ciki illegitimately ta haihu ta yar dashi, har yakan yi tunanin cewa itama kanta mahaifiyar tasa ba lallai ne ace tasan mahaifinsa ba, ace duk ba haka bane ba. Ashe shi din mai gata ne, gatan ma kuma mai girma sosai, ashe mahaifiyar sa mai cikakkiyar daraja ce fiye ma duk yadda tunanin sa zai iya bashi.
Ya daga kansa yaa kallon cikin idon Hussain, he looked so happy and contented. The smily face exactly irin tasa, sai shima ya samu kansa da mayar masa da murmushi kamar wanda yake ganinsa, sannan a hankali yace "am home, father".
A lokacin aka bude kofar palon da sauri sannan suka fara shigowa kuma duk suka doso inda yake tsaye kusan a tare, kowa yana so ya zama na farko daya fara rungume shi. Hussain da Abdulrahim da suka iso yanzu daga airport tare da daddyn su, Yusuf, Aminu, Abdullahi da Abdulrahman da suka taho urgently yanzu daga guraren aiyukan su, mazan su shida chif suka zagaye shi wannan ya runguma ya bawa wancan shima ya runguma, suna ta magana excitedly gabadayan su a lokaci daya babu wanda yake sauraren wani a cikin su kamar yadda shima Amir duk ba wai fahimtar abinda suke cewa yake yi ba, kawai abinda ya lura da shi shine duk yan'uwa ne kuma duk yanuwansa ne duk da bai san dangantakar ba, sai ya juya ya kalli Amatullah data matsa gefe ta basu guri da alamar tambaya a fuskarsa sai tace "cousins dinka ne duk, duk brothers dina ne"
Sai da Sumayya ta taso ta fara janye su tana cewa "ku barshi haka, ku barshi ya ga Baban sa kuma" sannan suka tuna cewa daddyn su yana tsaye a bakin kofa yana kallon su tunda suka shigo, sai kuma Hussain ya kamo hannun sa ya juyo dashi yana facing Hassan.
Hassan ya ganshi tun sanda suka shigo shida yaransa, ganin nasa ne kuma ya daskarar dashi a tsaye, baya bukatar tambaye tambaye ko wani dna test ko wani bincike, kallo daya yayi masa yasan cewa tabbas wannan daga jikin Hussain dinsa ya fito, ba kuma wai kamanni ba dan bakar fatar sa ta boye kamarsa da babansa, sai ya zamanto kamar dashi yake kama, sai dai wani soyayya da yaji ta yaron ta shiga ransa a lokaci daya, irin feeling din da rabon da ya ji irinsa tun sanda Hussain ya ja numfashin sa na karshe a duniya.
Sanda kuma Hussain karami ya juyo dashi suka fuskanci juna sai yaga kamar Hussain dinsa ne yake tsaye a gurin, sanda suka jero tare suka taho gurinsa kuma sai yaga kamar shida Hussain ne lokacin suna matasa, ya taka da kafarsa da take barazanar gaza daukansa ya hadu dasu a tsakiyar palon, sai Amir daya kada dauke idonsa daga kansa yana jin alhinin labarin rasuwar mahaifinsa da bai ma san da shi ba tana tafiya daga zuciyarsa dan yasan wannan mutumin, wannan strong babban mutum na gabansa is more than he would have ever asked for a father. Sai ya sunkuyar da kansa tare da kokarin durkusa wa dan niyyar gaishe shi amma sai yayi sauri ya dago shi sannan ya rungume shi a kirjinsa tare da runtse idonsa. Sai a lokacin yaji wannan sashen na ruhinsa daya fita tare dana Hussain ya dawo cikin jikinsa, sai a lokacin yaji shi ya koma complete.
Sai ya tuno da maganar Hussain da yake cewa "look after our children bro, all of them" a hankali Hassan yace "am sorry bro, I failed you" sai Amir ya kara rungume shi tare da cewa "no you didn't. Ban san me yasa baku neme ni ba amma soyayyar dana gani a idonku kawai tasa nasan you did all what you could" Hassan ya dago shi yana kallon idonsa yace "forgive me. Nayi failing. Duk laifina ne, duk abinda ya faru laifina ne. Dan ban aure ta ba, da ban nace lallai sai ita zan aura ba, da na nemi zabin Allah kafin inyi aure da baka tashi a gidan marayu ba ɗana"
Aunty ta taho inda suke hannunta dafe da Amatullah ta ce "haba Hassan, sai yaushe zaka daina dorawa kanka laifin wannan abin daya faru ne? Idan da baka aure ta ba ta ina wadannan yaran zasu fito? Rayuka ba daya ba ba biyu ba duk ta ina zasu fito bayan kuma Allah ya riga ya kadarta musu rayuwa a duniya?" Ya juya yana kallon ta yace "amma Aunty ko bayan da na aure ta da na zama careful, dana ji maganar Hussain da duk haka bai faru ba. Hussain tun farko baya sonta ba kuma ya gaya min ba sau daya ba amma ban taba daukan maganar sa ba, ya kamata ace na lura cewa da wahala Hussain yace baya son mutum, shi mai son mutane ne, ace kamar yasan ita ce zata zama silar rusa mana farin cikin mu" ya kalli Amir yace "ashe babanka yasan ita ce zata tarwatsa rayuwar ka, his only child"
Amir ya girgiza kansa yace "rayuwata bata tarwatse ba Daddy, banyi rayuwa da ku ba amma nayi rayuwa mai kyau nima. Nasan da a gurinku na girma zan samu soyayya mai yawa, zan samu kulawa mai yawa zan kuma rayu cikin farin ciki amma yanzu komai ya wuce, soyayyar da na gani a iyakacin yau ma kadai ta ishe ni wacce nayi asara ta duk shekarun nan"
Sumayya ta dan daga murya tace "a'a bata ishe ka ba, ka ga wadannan?" Ta nuna cousins dinsa na gurin tace "one over six ne na cousins dinka na bangaren babanka kawai, sauran suna nan zuwa dan da yawa daga cikin su suna kan hanya already. Dan haka ina tunanin yau sai ka sha paracetamol kafin ka kwanta dan zaka sha runguma har sai ka gode Allah" duk a kayi dariya, sai Hussain yace "wannan kuma kafin ka hadu dana bangaren mamanka ne, sun fi mu yawa ma su nesa ba kusa ba, I know because am married to one of them" ya fada yana kallon Aunty dan yasan sai tayi magana, ta dake shi a a hankali da walk stick din ta tace "marar kunya fitsararre, to ni wai ko rashin kunyar a sunan take ne?"
Hassan yayi dariya yace "haka suke Aunty sai hakuri" tace "ni yanzu ban ma san ta inda zamu fara bawa Fatima wannan labarin ba, Allah sarki Fatima ina jin sai tayi suman dadi in taga dan jaririn ta ya dawo" sai amir yaji kunyar ance masa jariri, Hassan yace "abinda za'a yi shine, ina jin lokaci yayi da ya kamata mu kaiwa Fatima da Adam surprise visit in Dubai. Who is in?" Gaba ki daya suka ce "yes!"
Daga nan sai Hassan ya hada kan mazan gavaki dayansu suka fita zuwa Masallaci dan gabatar da sallah la'asar da ake ta kiran ta a lokacin, masallacin gidan suka bude wanda an jima ba'a yi sallar jam'i a cikin sa ba sai dai mai gadi ko wani a yaran gidan, Hassan ya jasu suka yi jam'i a tare, Amir kafada da kafada da yan'uwansa, a cikin masallacin da mahaifin sa ya gina a cikin gidan sa.
A cikin gidan kuma sallar suma suka fara yi sannan suka shiga kitchen, sun rasa dalilin da yasa kawai suka ji yau a gidan zasu zauna basa bukatar komawa gidan su, kamar attraction din da gidan yake dashi na mutane da a da ake ganin yayi loosing to yau ya dawo tare da asalin mai gidan. Sumayya da Amatullah suka duba kitchen suka ga abinda babu suka aika mai aiki ta karbo musu a gidan sannan suka saka aka bude katon dining room din gidan wanda rabon da ayi amfani dashi har an manta, masu aiki suka hau aikin sa suka share suka wanke ko'ina. Suna cikin aikin Jabir ya kawo Nafisa da ta taho a rikice na jin labarin bayyanar babyn yaya H2, tun daga nan Amir ta ya cigaba da karbar runguma, kafin ta gama Hassana ta karaso da yar autar ta Ummulkhairi, dan duk sauran yayan nata sun yi aure. Kafin magrib gidan ya cika taf har dakunan da suke a rufe duk an bude su sai girke girke ake yi ana saukewa ana ɗorawa. Amir kuwa tun yana gane bayanin mutanen da ake yi masa har ya daina ganewa, abinda yake fahimta kawai shine manyan sune iyayensa kananan kuma sune cousins dinsa kuma duk yayan Aunty ne.
Bayan an uwa kuma sai ga yan unguwa nan sun fara shigowa suma suna ganin Amir musamman wadanda suka san babanshi. Kusan Duk wanda ya ganshi kuwa sai yayi kukan tunawa da Hussain, musamman in suka ga yadda ake bude gidan ana ta hada hada kamar yadda ake yi sanda Hussain yake da rai, wadanda suka san shi sai suke ganin kamar shine ya dawo.
Har Zulaihat da take a kano a ranar ta taho tare da yayanta maza su uku, Halifa, Hafiz da dan autan ta Haidar. Ranar duk sai akayi wa gidan aunty da gidan Hassan kaura, masu kwana ma duk cewa suka yi anan gidan zasu kwana suka ringa bude dakunan gidan suna bajewa son ransu.
Sai da dare yayi duk wadanda ba yan uwa ba sun gama tafiya sannan suka hadu gabaki daya a babban palon gidan, manya suna zaune a kan kujeru yara kuma gabaki dayan su suna zazzaune a kasa, Amaty tana kusa da Amir dan ita ce mai yi masa bayanin kowa, duk wanda yayi masa magana sai ya tambaye ta waye shi.
Bayan sun gama zama sai Aminu wanda shine babban jika ya gabatar da addu'a suka shafa sannan sai Aunty tayi musu introducing Amir, duk da cewa duk sun ganshi kuma sun fahimci ko wanene shi, amma sai ta sake yi musu bayani, ta kuma hada da tsokana cewa duk mazan ta da suke gurin ta daina auren su yanzu tayi sabon miji dan taga alamar sai ya fisu iya rike iyali. Bayan sun gama dariyar joke din Aunty sai Hassan ya fara yiwa Amir bayani, labari ya dauko masa na tarihin babansa, maraicin su da irin struggle din da yasha gurin kafa Kamfanin sa na H and H, anan Amir yasha mamaki "H and H Daddy?" Hassan yace "tabbas, kamfanin mahaifinka ne, shi yayi founding dinsa kuma har zuwa gab da rasuwar sa shine sole owner of H and H. Wannan kamfanin kuma da wannan gidan da muke ciki, zan iya cewa saboda sune aka batar da kai, dan kar ka mallake su".
Sai ya bashi labarin yadda aurarrakin su suka kasance, da brief labarin Fatima da irin soyayyar da suka yi da Hussain da kuma irin yadda yanayin zamansu a gidan ya kasance, samun ciki sa da dara rashin lafiyar Hussain, da yadda suka dauki son duniya suka dora wa cikin da kuma yadda Hussain ya boyewa kowa rashin lafiyar sa yayi faking cewa ya warke dan kar ya tayar wa da yan'uwansa hankali, yadda yayi finding out da kuma kyautar da yayi masa ta rabin kamfanin sa, har zuwa ranar da ya rasu.
Sai Hassan ya kasa cigaba da maganar, har yanzu mutuwar Hussain jinta yake yi kamar jiya akayi ta, har yanzu yana missing danuwansa fiye da tunanin mai tunani. Ganin yayi shiru sai Sumayya ta taya shi da bayanin accident din da su Fatima suka yi da kuma yadda suke tunanin haihuwar sa ta kasance a wajen accident din. Batan Fatima da kuma yadda Ruqayyah tayi replacing Fatimah da kawarta Minal wacce itama take dauke da tsohon ciki a lokacin. Tayi masa bayanin irin tashin hankalin da suka shiga na tunanin Fatima ce ta mutu da shi a cikin ta sannan kuma ta bashi labarin yadda greed din Ruqayyah ya jawo rabuwarta da Hassan bayan ta rasa jin ta da tafiyar ta, da kuma auren ta uta Sumayya da shi Hassan.
Sai a lokacin Amir ya fahimta, dan shi tun dazu tambaya be ya kasa yi amma ya kasa fahimtar uta Sumayya menene role din ta a cikin gidan, ya dauka gaba daya yaran yayan Ruqayyah ne. Sai yanzu ya banbance kuma yaji dadin hakan, dai kuma yanzu ya fahimci cewa ita ce ta tura masa da sako kuma ita ta rubuta masa littafi kuma ya fahimci dalilin ta na yin hakan.
Bayan ta dakata ne Hassan ya dora da labarin dawowar Fatima da kuma rigingimun da suka biyo baya, shari'ar da akayi da kuma zaman Ruqayyah a gidan mahaukata har na tsahon shekaru. Fitowar ta, aurenta, haihuwarta da kuma mutuwar twins dinta da kuma komawarta yadda take a yanzu. Sumayya ta fadi yadda Ruqayyah tayi mata nuni da cewa yana da rai just few days ago, da kuma yadda ta gaya wa Hassan aka kuma fara neman sa, sai Hussain yayi bayanin binciken da suka yi using satellite images da kuma zuwansu Abuja abinda ya gudawa tsakanin su da orphanage home din, sai kuma Sumayya ta fadi email din data tura masa da kuma littafin data rubuta masa ta kuma fadi dalilin ta na yin haka.
"Ba lallai ne kowa ya fahimci abinda nake ji a raina ba, amma ina saka ran daddyn Amatullah zai fahimce ni tunda yana da abokin tagwaitaka kuma yasan irin soyayyar da take tsakanin yan biyu, ita Ruqayyah wani bari ce na jiki na da ba zan iya cire wa a koda kuwa ta mutu ne ta bar duniya, dan na tabbatar har yanzu kana jin Hussain a cikin ranka, to ina so ka fahimci nima haka nake jin Ruqayyah. Ka saka kanka a matsayi na ka kuma saka Hussain a matsayin Ruqayyah ka ga cewa zaka iya taimaka masa dan ya samu ra rage nauyin da yake kansa ko ya samu dacewa a lahira? Tunda duniyar ta kare va tare data samu komai a cikin ta ba sai wahalhalu da masifun da ita ta jawo wa kanta"
Ga mamakin ta maimakon Hassan yayi mata fada sai taga ya riko hannun ta yace "Sumayya! Na fahimce ki and Believe me kusan kowa a gurin nan ya fahimce ki a yanzu, but ki gane wannan, you can't force a heart to forgive musamman a lokacin da mutum yake cikin fushin abinda ake rokon sa gafara akansa. Ki barshi ya huce da kansa, idan yayi niyya shi da kansa zai ce ya yafe mata idan kuma baiyi niyya ba ko ya fada bashi da amfani dan Allah da niyya yake aiki ba da maganar fatar baki ba".
Amir bai ce komai ba kuma bai dago kansa ba dan nauyin Sumayya yake ji da kuma su Hussain, amma baya jin zai iya yafewa Ruqayyah, ba zaiyi mata komai ba da sunan ramawa dan Allah ya riga ya gama rama masa amma kuma ba zai iya yafe mata ba, at least not now.....
Sai aunty Khadijah ta tambaye shi nasa labarin "an ce ka taso a gidan sarkin Abuja, ance a america ma kayi duk karance karancen ka. Bamu labari"
Sai a lokacin Amir ya dago kai yana murmushi, yana jin zuciyarsa tarwai kamar wata dan daren goma sha biyar, wai kuma wannan duk kafin yaga mahaifiyar sa ne. Sai ya basu labarin yadda tasa rayuwar ta kasance, dan abinda zai iya tunawa na daga zamansa a orphanage da kuma zamansa a gidan sarautar Abuja, wahalhalun da suka sha da kuma rayuwarsu a america, hiding the bad side tunda ya daina kuma babu amfanin fadar hakan ga wadanda basu riga sun san cewa yayi ba. Sai ya gaya musu labarin aurensa da kuma albarkar da aka samu a cikin auren.
"A aika a dauko min