Showing 186001 words to 189000 words out of 300844 words
Adam bata sam cewa zata dauki zafi haka ba.
Shikenan kowa ya guje ta, kowa banda mutum uku, mutum ukun da take ganin har abada ba zasu taba gudun ta ba, ƴaƴan ta, suma kuma Hassan ya raba ta da su. Sai ta mike ta saka hijab dinta ta sauka kasa sannan ta fita, ta fita gate ta tsaya tana kallon gidan Aunty, ta san can ya kai su, tasan bashi da inda zai kai su idan ba can din ba. A fara bin katanga a hankali tana jan kafarta har taje bakin gate din gidan Aunty a dai dai lokacin ne kuma taga motar Hassan tazo gurin, ta dauke kanta gefe dan bata son su hada ido, not now. Tana kallon sa ya sauke glass daga alama kare mata kallo yake yi, tai expecting ya rufe ta da bala'i amma sai taga an bude masa gate ya cusa motar sa ciki, ta lura da yadda ya tsaya yayi magana da mai gadi tare da nuna ta sannan ya shiga gidan, duk da vata ji su ba amma tasan cewa maganar ta suka yi kuma tasan Hassan cewa yayi kar a barta ta shiga gidan, kar a barta taga ƴaƴan ta. How cruel!
Duk da haka bata hakura ba dan tana ganin ai itama ƴaƴan ta ne, amma kafin ta shiga sai maigadi ya tare ta yace "kiyi hakuri hajiya, yallabai yace kar in barki ki shiga, kiyi hakuri dan Allah kar ki matsa, bana son inyi miki abinda ba zamuyi dadi ba gabaki daya" ta tsaya tana kallon katon mai gadin, to in ma bata hakura mai zata yi masa? Ita dai ba zata kama shi da kokawa ba kuma ba zata iya kama katangar ta haura ta shiga gidan ba. Time din da take haura katanga ya riga ya wuce, those good old days!
Ta juya a hankali kamar wadda kwai ya fashe wa a ciki ta sake bin katangata koma cikin tangamemen gate din tafkeken empty gidan da yake matsayin nata, gidan da tunda ta dora idonta a kansa take son ta mallake shi amma yanzu data mallake shin take jinsa kamar wani prison. A ranar tayi kukan da rabon da tayi irinsa ita kanta ba zata iya tunawa ba. A daren ranar kuma bata yi bacci ba duk da maganin baccin da tayi ta bunkawa kanta, ba wai kukan jariri da idon Minal ne kadai suka hana ta bacci ba a'a abubuwan da suka cunkushe mata a ranta ba zasu kirgu ba.
Zuwa safiya ta yanke shawara. Tana idar da sallah ta dauko takardar da mai duban ya bata ta saka number din wayarsa data gani a ciki ta kira, ya dauka tare da sallama, bata amsa masa ba dan tana ganin bai cancanta ba tace "na amince zanke baka kudi kamar yadda ka bukata, amma ba amount din da ka nema ba, zanke baka rabi" yace "baki so a daidaita ba kenan. In rabi ne ki rike kayan ki ni kuma in fara tunanin inda zan fara aikawa da sako na, gidan su Minal? Kano? Ko kuma ofishin tsohon mijinki?" Ta lumshe ido ta bude tace "in nace zan baka duk abinda ka nema, ni zan tashi bani da komai kenan, in haka ya kasance ko zan gwammace in mayar wa da Hassan kudinsa in koma gidan mu, kaga dani da kai munyi two zero kenan. Ka karbi rabin dana baka ko kuma ni da kai duk mu rasa" ya danyi shiru sannan yace "na rage miki, ki bada kashi uku cikin hudu" ta girgiza kai kamar yana ganinta tace "rabi ko nothing. Karkari ta kashe zaka tona min asiri, ni kuwa a yanzu na kuna bana jin tsoron wuta, to waye ya rage min wanda zai guje ni in an san abinda nayi?" Yace "in ma bau wanda zai guje ki ai zaki tafi gidan yari ko? Kinsan....." Ta dakatar dashi tace "zan tafi prison ko kuma zamu tafi prison? Inajin a duban naka baka duba sosai ka ga wacece Ruqayyah ba, if I am going down I will surely take you down with me, zan ce tare da kai muka shirya komai kuma za'a yarda saboda in ba haka ba ya akayi kasani? Wannan takardar da ka bani da sunanka da account details dinka da kuma adadin kudin dazan baka ita ce shaidata, zan bayar daita a matsayin shaidar payment din da nayi maka na taimaka min da kayi gurin duk abinda nayi. Dan haka kayi tunani kafin ka yanke shawara" yayi shiru, tabbas sai yau ya tabbatar cewa yarinyar nan shaidaniya ce. Yayi gyaran murya yace "shikenan, ki ringa turo rabin" bata ce komai ba ta kashe wayar ta ajiye. Ta kama shi a inda ba zai iya kwacewa bakuma wannan kamun na farko ne, nan gaba sai yayi nadamar hada hanya da ita.
A yanzu plan dinta shine zata ke biyan mai duba rabin kudin da ya nema a cikin kudin da za'a ke kawo mata na ribar share din da Hassan ya bata a H and H, sauran kudin kuma bayan ta fitar da abin bukatun ta na yau da gobe zata ke tarawa a hankali sannan sai ta fara neman maganin ciwon ta, zata gwada na hausa dana islamic chemist har in Allah ya taimake ta ta samu kafin nan kuma ta san yadda tayi tayi maganin malamin duba sannan sai ta koma gida, at least dai taji da talaucin ba tare da nakasar ba.
A ranar sai ga mai aikin Aunty ta shigo mata da su Aminu wai inji Aunty tace suzo su gaisheta, murna a gurin Ruqayyah harda hawayenta, ta jawo su jikin ta ta rungume tana kallon yadda suke fes fes dasu babu alamun wata matsala a tattare dasu, at least tana da kwanciyar hankali ta wannan bangaren, tasan ƴaƴan ta suna hannun tiko na gari duk da tasan albarkacin Hassan suke ci .
Haka rayuwa ta tafiyar wa Ruqayya tsahon wannan shekarar, kudi suna shigo mata daga kamdani ita kuma tana bawa malamin dubanta sannan tana tarawa, bayan ya taru kuma ta fara neman magani dashi, duk inda taji mai magani daya danganci kafa ko kunne sai taje amma shiru babu sauki sai a wurin Allah, kafa kullum kara motsewa take yi har ta kai cast din ma yayi mata girma ta koma amfani da crutches, kuma har yanzu bata iya ji da kunnenta sai ta saka hearing aid, har yanzu kuma bata iya bacci sai ta sha sleeping pill, har yanzu kuma bata samu hanyar da zata bi ta rabu da wancan karfen kafar ba.
Rayuwar Ruqayyah kenan......
Sorry guys.... bacci....ina typing ina bacci......ayi hakuri da wannan duk da kankantarsa.
Tomorrow zamu dan fara rushing things up yadda zamuyi covering shekarun da wuri.
*Destiny*
Tun ranar da Aunty tayi wa Hassan maganar Sumayya bai kuma yi mata maganar ba ita ma kuma haka, amma ya dukufa da addu'a, duk sallah sai ya gaya wa Allah ya kuma roki yayi masa zabin mace ta gari wadda kuma zata zama uwa ta gari a gurin yayansa, waɗanda yake dasu da kuma wadanda zai samu nan gaba. Sai kuma ya mayar da hankalinsa kan business dinsa. Sai dai lokaci zuwa lokaci maganar tana fado masa amma sai ya kawar da ita dan shi bai san da wacce fuskar zaije yayi sallama da Sumayya yace mata yana sonta, shi kansa sai da yadafe kansa daya aiyana abin, wannan ai abin kunya ne kuma zubar da girman sa ne a gurin yarinyar da yake gani kamar kanwarsa. In ma za'a yi to yana ganin sai dai manya su shiga maganar in yaso in anyi auren sai yasan yadda zaiyi. Even at that ma bai san ta yadda zaiyi din ba. To shi ma kenan da yake namiji kna gaita da take mace? Ta yaya zata so shi irin soyayyar aure? Ta ya kuma zata iya muamalar aure da shi? Musamman in yayi la'akari da yadda take girmama shi sosai. Amma ta ko'ina im ya duba sai yaga ita din ce dai a sama a cikin zabin sa. Dan yayansa, dan farin cikin iyayensu, dan nutsuwar zuciyarsa, dan abubuwa da yawa.
Tunanin abin ya sa ya kara kaimi gurin addu'ar sa, yana kuma rokon Allah ya bashi kwarin guiwar tunkarar ta da maganar indai har ita ce alkhairi a gare shi. Daga nan sai maganar ta fara damun shi sosai har ta kan hanashi bacci sometimes, ya saka ya warware, har mafarki yake yaje ya gaya mata yana son auren ta ita kuma tayi mishi masifa tace masa maci amana, a wani mafarkin kuma sai ta karbi tayinsa ta ce Allah yasa hakan shima nafi alkhairi, ya san dole a cikin biyun nan daya ne zai faru amma bai san wanne ne ba, ba zai kuma sani ba har sai ya gwada, Sumayya kamar wani unopened page ce a littafin rayuwarsa, ba zai san menene a ciki ba har sai ya bude, courage din budewa ne kuma ya rasa.
Sai ranar nan dai da sukayi magana da Zulaihat ta gaya masa cewa suna exam din first semester ta final year dinsu, ma'ana semester daya ta rage musu a karatun su na jami'a, sai ya fahimci cewa time yana kure masa, lokacin da Baba ya bashi ya kusa karewa tunda cewa yayi alƙawarin yana nan daga lokacin zuwa sanda zata gama jami'a, yasan kuma Baba jira yake kawai ta gama jami'a ya aurar da ita ko gare shi ko ga wani, wanin kuma yasan ba Adam bane ba tunda dai Adam har yanzu babu labarin sa, dan shi kansa yasan Baba yayi kokarin barin ta har ta gama jami'a ba tare da miji ko kuma wani tsayayyen mane mi ba dan iyaye irin Baba musamman wadanda ba yan boko ba da wahala suke barin haka ta kasance ga ƴaƴan su, maybe ma Baban ya barta har yanzu ne saboda shi, saboda ko zai zo yace ya karbi tayinsa.
Dan haka a ranar sai ya shirya da yamma ya tafi gidan nasu a fili da niyyar gaishe da Baba amma a ransa so yake ya ga ko zai samu wata kafa da zai fake da ita. Sai dai cikin rashin Sa'a sai ya tarar Baban bayanan, duk gidan ma babu kowa duk suna makaranta dan Sulaiman shima ya shiga jami'a last year Zunnur ne dai yake kokarin kammala secondary school dinsa, sai Inna kadai ya tarar a gidan, ya shiga ya gaishe da ita tana ta tambayarsa mazajenta tana korafin cewaya kwana biyu bai kawo mata suba "ko da yake ba laifin ka bane ba laifin Sumayya ne, dama ita ceai zuwa ta dauko su kuma yanzu ta daina wai dan taji muna maganar ku kai da ita ranar nan da Amina a waya. Shine ta daina zuwa gidan dan kar Amina tayi mata maganar" sai ya sunkuyar da kansa kasa shima yana jin kunya, wato har maganar suke yia tsakanin su tun kafin su wadanda za'a yiwa auren su amince. Kuma daga yanayin da Inna tayi maganar itama sai ya fahimci tana son hadin, Aunty ma tana so, Baba shi yayi initiating, saura su kadai ya rage.
Ya tashi yayi mata sallama tare da alkawarin kawo mata maxan ta ranar Friday idan anyi hutu tunda sun fara zuwa school yanzu. Sai dai kuma yana fita kofar gida suka kusa yin karo da Sumayya tana kokarin shigowa gidan a gajiye, kallo daya yayi mata sai ya rike baki yana boye dariyarsa. Ga jaka ga lecture notes a hannunta, ga uban hijabi har kasa wanda daga dukkan alama zafi take sha a cikinsa, fuskarta kadai zaka kalla kasan tsabar gajiyar da tayi da kuma irin yunwar da take kwakwular cikinta. Ta bata rai "dariya kake min ko?" Yayi saurin girgiza kai dan yasan yana bude baki dariyar zata fito, tayi kwafa, "dan ma dai kaima kayi karatun kasan wahalar da ake sha" sai ya bude bakin yayi dariyar sannan yace "ni sanda ina zuwa makaranta da ace kin sanni a lokacin da ba zaki damu dan na yi miki dariya ba, dan kin fini kyan gani, ni kamar skeleton nake komawa baƙi na kuwa ko bayan tukunya nan ya ganni ya bari" tace "ni ma ai kamar skeleton din nake yanzu, hijabi ne ya biye ramar" Yace "an kusa gamawa ai, wahalar ta kusa karewa" ta langwabe kai tace "ameen. Bismillah ko har ka shiga ka fito?" Ya girgiza kai pretending as if bai shiga ba yace "ashe Baban baya nan" ta dan duba wayarta tace "ya kusa dawowa ai, bara in bude maka dakin soro sai ka zauna ka jira shi" ta shiga gidan da sauri bata jima ba ta dawo da key ta bude masa dakin ya shiga ya zauna yana kallon dakin kamar yay ya fara gani, sai yake jin memories na da suma dawo masa, memories din sanda yake zuwa gurin Ruqayyah suke zama a dakin. Yayi sauri ya ture tunanin a gefe dan baya son ya bata mood dinsa, yaji dadin yadda Sumayya ta tarye shi bata bata rai tayi mishi kallon wanda yake forcing kansa a gurinta ba.
Bai jima ba ta shigo da sobo mai sanyi da ruwa ta ajiye masa tace "yanzu zai dawo" sai kuma ta zauna a gefe tana wasa da hannunta, ya zuba sobon data kawo masa ya daga yana sha yana kallon hannun da take wasa da shi, sai daya ajiye cup din sannan yace "fadi, ina jin ki" ta dan kalle shi kadan suka hada ido tamayar da kanta kasa tace "dama ina ta son in tuna maka maganar nan damukayi ranar nan, kuma bana so kaga kamar na dameka shi yasa na kasa yi maka maganar" ya gane maganar da take nufi amma sai ya nuna kamar bai gane ba yace "wacce maganar kenan?" Tace "maganar zuwa Kano, kace zamu je tare kuma har yau bamu je din ba, kuma ni ba za'a barni naje ni kadai ba. Na san Baba yana jin maganar ka dan Allah ka tambaye shi ko kai ba zaka samu damar zuwa ba ni sai inje" ya rungume hannunsa yana kallonta, a ransa yana jinjina soyayyar ta ga Adam, ina ma dai zai samu irin wannan soyayyar ta gaskiya, soyayyar da za'a yiwa mutum ko da a bayan idonsa ne. Sai kuma wata magana da Hussain ya taba gaya masa akan mata ta fado masa
"the way to a woman's heart is through kyautata wa, tausayawa, nuna soyayya da kuma kyauta. In kayi mata haka you don't need to say I love you, zata gane, itama kuma zata so ka".
Yace "shine abinda kike so? In munje kano gidan su Adam mun nemi labarin sa zaki ji dadi?" Yadda yayi maganar ya sa ta dago kanta suka hada ido, amma hakan bai hanata gyada kai ba, yace "good, in dai haka kike so to haka za'a yi, zanyi wa Baba magana, in ya amince kuna gama exams sai muje" tace "yaya Hassan muje da weekend din nan mana" sai kuma ta sunkuyar da kanta tace "that's if you are not busy" ya gyara zamansa yace "am not, amma kinga exams kuke yi, abinda zamuyi finding out a kano zai iya ya taba ki emotionally hakan kuma zai iya taba exams dinki, ni kuma ba zanso hakan ba. Shi yasa nace after kun gama exams sai muje. Kinji?" har cikin ranta taji maganar sa, sai ta gyada kai lokacin da taji tsayuwar sabuwar Napep din da Baba ya siyar da waccan ya cika ya siya kwanan nan, sai ta yashi da sauri ta shige gida, a ranta bata son Baba ya ganta tare da Hassan kar yayi tunanin wani abu.
A ranar Hassan yayi wa Baba maganar yana son zasu je kano da Sumayya su bincika labarin Adam, amma sai Baba ya nuna kin amincewar sa yace "ina so a ji labarin Adamu, amma me yasa lallai sai Sumayya taje? In zuwan za'a yi ai gwara kai din kaje tare da ni ko tare da Sulaiman, amma ita menene nata na zuwa?" Hassan yayi kokarin kare Sumayya, "Baba kasan dangantakar Sumayya da yaron nan, kasan kuma ita zuciya tafi yarda da abinda taji ko abinda ta gani ba wai abinda wani yaji ko ya gani ba, in ba ji tayi da kunnenta ko ta gani da idontaba ba lallai ta yarda ta cire yaron daga xuciyarta ba" Baba ya tsaya yana kallon Hassan yace "ita ce tayi maka maganar sa ko?" Hassan ya girgiza kai da sauri "kawai dai naga kamar hankalin ta har yanzu yana kansa, ina so ne ta samu nutsuwar zuciya" Baba ya fahimci boye laifin Sumayya Hassan yake son yi, kuma yaji dadin hakan dan wannan shine alaka ta gaskiya ba wai kayi ta kokarin kawo karar mutum kana nuna shine mai laifi a komai ba. Sai ya nuna ya amince, ba dan Sumayya ba sai dan Hassan.
Ranar Friday aka yi wa yara hutu sai Hassan ya dawo tare da ƴaƴan sa duk su ukun, ya kira Sumayya a waya yace tazo ta shiga dasu suna ta murna an kawo su gurin mommy, ya fahimci cewa basa banbance Sumayya da Ruqayyah kuma yaji dadin hakan dan baya so su gane Ruqayyah ce ta haife su, at least not now. Bayan ta gaishe shi tana ta murnar ganin yaran suma suna ta makalkale ta sai ya dauko wata yar karamar jaka irin ta computer ya mika mata "laptop, nasan zaki bukace ta saboda project" ta karba da murna, fuskarta tana nuna irin farin cikin da zuciyarta take ciki tace "you are are real life savior Yaya. Kamar kasan yadda nake ta fama da hada project a waya ina ta rigima da yan café. Thank you thank you" yayi dariya, "you are welcome, sai a dage aci jarabawa sosai"
Daga lokacin sai ya samu excuse din kiran wayar Sumayya sai ya nuna mata kamar yaran ya kira su gaisa, wani lokacin kuma sai ya fake da tambayar ta yaya exams, a haka har suka gama exams din, ranar da suka gama a ranar Sumayya ta kira shi da kanta ta gaya masa sun gama sannan ta tuna masa maganar tafiya Kano, sai yace ta fada a