Showing 78001 words to 81000 words out of 300844 words
nata daga gida amma an kara mata, yammatan aunty kuwa tun da akayi auren gidan Fatima suke wuni su shiga duk inda suke so a gidan suyi duk abinda ransu yake so. In kika tarar dasu tare zaki dauka kannen ta ne. A bangaren Ruqayyah ma bakin suna dan leka mata, amma basa wani jimawa suke tafiya su koma gidan Hussain, abinda yake kara kona ran Ruqayyah kenan, ita gani take yi saboda kudin Hussain da tittle din Fatima ne yasa mutane suka fi zama a gurin su.
Tun da akayi auren bata taka kafarta part din Hussain ba, ba kuma ta jin zata shiga anytime soon dan bata jin tana da zuciyar da zata dauki abinda idonta zai gani, dan duk wanda ya shigo gidan ta indai ya shiga gidan Hussain sai ya bata labarin wani abin burgewa da ya gani a gidan. Bata kulasu sai dai kawai tayi musu fuskar shanu, wannan ne yake sawa su tashi su tafi dan kansu. And those comments are killing her inside. Ga nacin Hassan, shi ya kasa fahimtar ita ba wai son wannan abin take yi ba, tana dai bashi ne dan taga yadda yake tsananin son abin ita kuma top priority dinta shine ta kanannade komai nashi, yadda duk abinda take so zaiyi mata abinda bata so kuma ba zaiyi ba.
Ya na sakata ta shiga ta gaida Aunty kullum da yamma, a can suke haduwa da Fatima wasu lokutan. Ranar nan ma a kitchen ta tarar da ita da aunty da sauran yaran gidan wai tana koya musu wani tuwo da ake yi a gidan sarauta da ake kira da tuwon dalayi. A ranta tace "ji munafurci, sai kace ba bayi ne suke musu abincin a can ba" a lokacin ne Fatima take cewa da Aunty "aunty ni dai da zaki bi ta tawa da kin daina mana girkin nan haka, kiyi zamanki kiyi hutawarki" aunty tace "yanzun ma ai ina hutawa Fatima, babu fa abinda nake yi a gidan nan, ni ba aiki ba ni ba kasuwanci ba sai dai in saka TV a gaba inyi ta kallo" Fatima tace "duk da haka dai Aunty ki barshi, na gidan nan ma ku daina, in yaso su Nafisa suke zuwa can muna yi tare sai ake kawo muku kawai. Lokacin hutawarki ne yanzu. In kin gaji da zama guri daya sai a fitar dake ki zaga gari, in kin gaji da garin ma sai a kaiki wata kasar ki cigaba da hutawa. Ko Ruqayyah?" Ta juyo tana yiwa Ruqayyah wadda tun da ta shigo bata kulata ba murmushi, Ruqayyah tayi murmushi kawai, amma a ranta tana jin kamar ta rufe Fatima da duka, yanzu ita in aka daina kai mata abincin daga gidan nan ta ina zata fara dora abinci a gidan ta? Ita da bata iya irin wadannan girke girken ba.
Sai da suka gama tuwon suka jera a dining, wai yau duk a nan za'a hadu aci tuwon Fatima. Suka zauna a palo suna ta hira, anan taga Fatima ta kira Hassana suna magana a waya tana tsokanar ta wai tayi missing gashi nan za'a ci abinci gabadayan su banda ita, har tana cewa zata tura mata hotunan su. Yadda suke maganar ya nuna cewa sun saba sosai, sai Ruqayyah tayi realizing ita ko number din Hassana bata da ita kuma in banda rannan da suka gaisa a wayar Hassan basu taba waya ba tunda akayi bikin su. Wato dan ita yar talakawa ce kuma mijinta bashi da kudi shine suke wareta ko?
Suna nan zaune har Hassan da Hussain suka shigo, suma suka zauna aka cigaba da hira, Hassan yana ta kokarin ya saka Ruqayyah a cikin hirar amma sai dai tayi murmushi kawai ta sunkuyar da kanta, ita ba zata iya irin wannan rashin kunyar irin na Fatima ba.
Loma daya tayi wa tuwon taji ba zata iya ci ba, zuciyarta har ta fara tashi kamar zata yi amai, wani iri taji shi a bakinta. Amma sai taga su ci suke tayi suna santi, har da Hassan dinta dan abin kunya, wannan ai kunyata ta yakeyi. Sai da suka gama sannan Hussain yake cewa "aunty dama ina so in gaya miki monday muke so zamu tashi zuwa honeymoon" Hassan ya rankwashe shi sannan"yanzu auntyn kake gayawa zaka je honeymoon saboda baka da kunya?" Hussain yace "ouch, Fatima kina ganin sa zai nakasa miki miji ko? So yake ya hargitsa min ƙwaƙwalwa ta in kasa lissafi" Ruqayyah ta dauke kanta tana dan karamin tsaki, shi komai sai y nuna shi mai kudi ne, ko me y kawo zancen lissafi? Fatima Ta daga kafada tana masa alamar kunfi kusa, Aunty tace "Masha Allah, Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya. Ruqayyah kin shirya dai ko?" Zulaihat tace "ni na shirya Aunty, dani zaku tafi" Khadijah ta harare ta "ke kin fiya sakarci wallahi" Ruqayyah ta juya tana kallon Hassan, shima ita yake kallo, Hussain yace "ask him ooo Aunty, Mr Tsimilmila cewa yayi wai ba zasu je ba" Hassan yace "cewa nayi ba zamuje kasa biyar ba, me za'a je ayi a kasashe har biyar? Guda daya ko biyu in muka je sun ishe mu" Hussain ya kalli Aunty yace "kinji ba" Sannan ya juya gun Ruqayyah yace "convince your husband akan kuzo mu tafi tare, idan kika biye masa you are going to miss a lot." Ruqayyah tana jin tunda akayi auren yau ne Hussain yayi addressing dinta directly.
Ta tura kujerar ta baya tana mikewa, abinda yasa Hassan shima mikewar yana tambayarta lafiya? Aunty ma tace "lafiya Ruqayyah? Ko abincin kirki baki ci ba" Tace "bana jin dadi ne sosai, wannan tuwon kamar bai karbi cikina ba. Zan dan koma gida, Aunty sai da safe" Aunty tace "ki je ki kwanta to, Allah ya baki lafiya, zan aiko miki da wani abu ki ci ko tuwon ne ba kya so".
Hassan bai zauna ba ya bita da sauri a baya, amma saboda saurin da take yi da kyar ya kamota har ta kai kofar karamin gate din da ke tsakanin part din su dana aunty. Ya ruko hannunta "Hassana" ta juyo, tun daga idanuwan ta yasan ranta a bace yake yace "lafiya wai? Menene yake damun ki?" Ta juyo gaba daya tana rike kugu, tace "me akayi min? Okay yanzu na gane inda problem din yake" ta karbe hannunta tana kara sauri. Baya son ya ja hankalin ma'aikatan gidan zuwa kansu, dan haka sai ya rabu da ita ya koma cikin gida ya karasa cin abincin sa duk da hankalin sa yana kanta. Yana gamawa ya tashi ya tafi gida. A daki ya tarar da ita tana kwance da waya a hannunta. Ya zauna a kusa da kafafuwanta yana mammatsa mata su yace "ya jikin naki? Hope kinji dadi yanzu" ta ajiye wayar tana tashi zaune tace "naji dadi, dama tuwon ne naji ya tsaya min a kirji ya ki karasa wa" yace "akan maganar tafiya honeymoon ne? In kina so sai muje, bana son mu biyewa Hussain ne " Ta girgiza kai tace "I don't care about honeymoon, in baka so muje ba zamu je ba, duk abinda kake so shi zamuyi. What i care about is you mijina. Raina ya baci ne saboda naga ana neman a gaya maka magana a cikin mutane" ya dan bata rai yace "magana kuma? Wacce irin magana kike magana akai Precious?" Ta bude ido Tace "wai baka ji abinda Hussain ya gaya maka bane ba? Mr Tsimilmila fa yace maka, it is insulting ni a ganina" sai taga yayi murmushi sannan yayi dariya yace "my dear precious wife. Ba magana Hussain ya gaya min ba kinji? Wasa yake min, tun muna yara, tun primary school yake gaya min haka, mr Tsimilmila ko mr Careful duk haka yake ce min in yana so ya zolaye ni" ta daga kafada "okay, maybe dan ni macece shi yasa naji raina ya baci akan hakan, kasan mu mata muna da daukan karamin abu mu mayar dashi Babba. Dan haka ko da ace yana gaya maka haka a tsakanin ku bai kamata ya gaya maka a gaban mu ba, musamman a gaban matarsa, wannan ai sai ta zo ta raina ka tana yi maka wani kallo da daban, ni kuma ba zan iya tolerating wannan ba in tayi min na kyaleta bazan kyaleta ba in ta taba min mijina" Hassan yace "hold it! Fatima tana yi miki wani abu ne?" Ruqayyah ta koma ta kwanta sannan tace "bana son in fiya complain ne shi yasa ban taba gaya maka ba. But dama ya kake tunanin yar sarki zata yi treating yar mai gadin kamfani? Kamfanin ma kuma na mijinta. But ni ban damu ba ......." Ya kamo ta ya tayar da ita zaune, idanunsa suna nuna bacin ransa yace " yar sarki da yar mai gadi, dukkan ku matsayin ku daya a gidan nan, duk kan ku zaman aure kuke yi a gidan nan. Daga yanzu duk ranar da ta kara miki ko da kallon banza ne ki gaya min ni kuma zan nuna mata cewa she is no longer in her father's palace"
Wannan littafi na siyarwa ne, in kina so ki yi min magana ta WhatsApp through this number 08067081020
Da fatan munsha ruwa lafiya, Allah ya karbi ibadun mu ameen.
Not edited
Ruqayyah tace "uhm uhm, ni bance kayi mata magana ba, kar taga kamar na hada ta da kai, ka barni da ita kawai ni ce dai dai yin ta va kai ba" sai kuma tayi murmushi tana ratayo hannunta a wuyansa "sorry mijina, na bata maka mood dinka" ya danyi mata murmushi yana shafa gefen fuskarta, kullum kyau take kara yi masa yace "kar ki kula ta kema kinji, ki fita daga harkarta kawai bana son wani abu ya hada ku saboda Hussain. Kinji? Promise me ba zaki kulata ba, one day zaiyi realizing abinda ya auro cos na gaya masa tun dadewa. I warn him about her" tayi ajjiyar zuciya tace "shikenan, duk abinda kace shi zanyi".
Ya mike ya fita sai gashi da system dinsa ya dawo, ya zauna akan kujera tare da kiranta "Precious zo ki gani, kinga guraren da Hussain yake son muje. In kina so sai mu bi su mu tafi tare" ta taso ta zauna a gefen sa tana kwanto da kanta jikinsa, ta karanta sunayen guraren, ita ko sunan ma vata taba ji ba kuma bata san wadanne kasashe bane ba. But koma ina ne tunda har jirgi za'a shiga a bar kasar nan ai kuwa va za'a barta a baya ba. Amma sai ta boye excitement dinta tace "ba naji kace ba zamu je ba?" Yace "in kina so sai muje" tace "ina ganin muje din kawai, kar Hussain yaji babu dadi, kaga har ya kai kararka gurin Aunty" yace "ai ya riga yasan saboda menene. Ni bani da lifestyle irin nasa" sai kuma yayi murmushi yana kallon dan karamin bakinta yace "but since we are talking about a honeymoon tare da ke, I think I can make an exception" lips dinta suka bude tana murmushi, yayi murmushin shima yana kallon fuskarta, duk wata damuwarsa tana wucewa tare da murmushin ta. "I am going to enjoy this" ya fada yana jan fuskarta zuwa gare shi.
A gurin Aunty Fatima tayi hirar darenta, Hussain yai ta zungurin ta akan su tashi su tafi tana share shi. Sai ya mike yana kirkirar hamma "na gaji sosai yau din nan. Aunty sai da safe zan tafi in kwanta" Aunty tace "Allah ya bamu alkhairi" ya kalli Fatima yace "sai da safe" ta dauke kanta tana kokarin rike dariya. Yana fita Aunty tace mata "tashi ki bi mijin ki, dan ba ta ido ce dashi ba zai iya sake dawowa ya sake yi mana wata sallamar" Dole Fatima ta mike Khadijah da Nafisa suka raka ta har kofar part dinta.
Tana shiga ta amsa gaisuwar bayinta su biyar da suke da dakuna a karamin palonta na kasa, inda anan din ne dai kuma yan aiki da Aunty ta bata suke. Sai data dan yi hira dasu kadan sannan ta wuce kitchen. Yarinyar ta da taje da hakkin kula da kitchen ta bita a baya da sauri, suna shiga ta tambaye su abincin da suka dafa, ta gaya mata sai ta yamutsa fuska tana girgiza kai sannan ta bude freezer ta saka yarinyar ta dauko kaza, tace "ina irin pepper soup din nan da muke yi a gida mai dankali?" Yarinyar ymta gyada kai da sauri tace "shi za'a yi miki? Yanzu kuwa zanyi miki" Fatima tace "shi zakiyi, amma bani zaki yi wa ba in kin gama ki zuba a mazubi mai kyau ki je ki kaiwa Ruqayyah kice gashi in ji ni" da sauri ta amsa da "to ranki ya dade, an gama" daga nan Fatima batakuma tsayawa ba sai turakar mijinta.
A dakinsa ta same shi daga shi sai towel yana ta zagaye da waya a hannu. Ya juyo yana kallomta sai ya yar da wayar ya rike kugu, ta jingina da jikin kofar tana murmushi yace "da baki taho ba ko, da zuwa zanyi in dauko ki aka tun daga gaban Aunty har nan" ya fada yana nuna kan gadon sa. Ta bata rai tana kallonsa tace "na yi fushi, shine kayi wankan ka ka rabu dani ko?" Ya tako zuwa gabanta yace "waya gaya miki nayi wanka? Ni na isa? Ta yaya zan wanke baya na?" Ta dan taba gashin kansa tana dubawa ko da ruwa a jiki, yayi dariya yace "banyi ba fa na gaya miki" tace "da kayi wanka ka barni ko, da yau ba zanyi wanka ba haka zan kwanta" ta fada cikin shagwaba. Ya jawo ta zuwa jikinsa, hannunsa a bayanta yana zuge zif din rigarta yace "na gaya miki ai, ba zan sake wanka ni kadai ba" ta fara dariya kuma sai ta dauke wuta saboda hannun sa da taji a cikin rigarta.
Bayan Hassan ya gama nunawa Ruqayyah guraren da zasu je sai ta sake komawa dakinsa zai mayar da system dinsa, a lokacin ne ta jiyo maganar mutane daga waje, ta daga labuke ta leka window ta hango Fatima dasu Nafisa a kofar gidan Hussain, sai taga su Nafisa sun juya sun koma Fatima kuma ta shiga. Ta tabe baki, wayo gimbiyar ba ma zata iya tahowa ita kadai ba sai an take mata baya, amma ita sanda zata taho ai babu wanda ya rako ta duk kuwa da cewa ta nuna bata jin dadin jikinta. Ta fara kokarin cire kayanta da niyyar yin wanka, so take yau tayi amfani da rashin lafiyar da take ji ta gudu daga gadon Hassan. Tana fitowa daga wankan Hassan ya dawo dakin, shima har yayi wankan sa ya saka na bacci, ya bibta da kallo tana shafa mai a jikinta. Ya karaso yana karbar robar man. "Menene aiki na a gidan nan idan har na barki kina shafa mai da kanki" ta dan bata fuska "shafa mai ai ba aiki bane ba, zan iya da kaina" yace "akwai guraren da hannun ki ba zai kai ba. Ki kawo in shafa miki ko ina da ina, in tabbatar ko ina ya samu" ta lura da irin kallon da yake yi mata sai ta dan rike cikin ta kadan tana yamutsa fuska. Yace "ya dai? Ko cikin ne?" Tace "dazu ma sai da nayi amai, kuma yanzu yunwa nake ji. Ni tunda aiki kake nema ma da abinda zanci ka samo min" ya dan shafa kansa kadan yana kallon kirjinta "kuma shafa man fa?" Ta tura baki, ni ina jin yunwa ina zan damu da wani shafa mai" yayi ajjiyar zuciya "shikenan, let me go and get you something". Ta bishi da ido har ya fita, sannan tayi dan karamin tsaki. "Duk an bi an lugwuigwuicewa mutum jiki an bar ni da ciwon jiki".
Key din mota Hassan ya dauka ya fita, bai ma san inda zai samu abinci ba, shi ba mutum ne da ya saba da cin abinci a waje ba dan haka bai san guraren cin abinci ba. Yana fita yarinyar Fatima tana kaiwa Ruqayyah abincin da ta aika mata dashi. Tata yarinyar ta karba sannan ta hau dashi sama saboda ta ga fitar Hassan, ta shiga dan madaidaicin dining area dinsu ta ajiye sannan taje tayi knocking a kofar Ruqayyah, sai data ji tayi magana sannan tace "sako ne gimbiya Fatima ta aiko miki dashi". Sai da Ruqayyah ta gama shafe shafen ta sannan ta saka doguwar rigar bacci wadda ta tsaya a gwuiwar ta mai siririn hannu ta fito tana daure kanta da ribbon, a ranta tana mitar tunda tazo gidan kullum sai ta wanke kanta gashi har gashinta ya fara lalacewa. Ta bude warmer din abincin a take taji yawunta ya tsinke, ta saka spoon ta dandana sai ta ja kujera ta zauna ta fara ci, sai data kusa koshi sannan ta tuna ta tura Hassan neman abinci. Ta dauko wayarta ta kira shi "kina ta jira na ko? Yanzu na kira Jabir yayi min kwatancen wani guri" tace "ka bar shima, har na dan dafa wani abu ma naci" yace "ayyah. Sorry Precious. Jikin yayi sauki kenan" tace "babu laifi"
Sauran data rage yazo shima yaci "amma yayi dadi sosai, sharp sharp haka har kin gama? Kai amma yayi dadi sosai" tayi murmushi kawai. Ita bata taba ganin irin wannan abincin ba ma ballantana har ta iya. Sai kuma ya ajiye chokalin hannunsa yana kallonta, ta gane kallon dan haka ta mike zata gudu, ya jawo ta ta fado cinyarsa. Wannan dai wankan da bata son yi sai data yi shi.
Washegari yace mata ta shirya zasu je ayi mata passport. Ta roke shi kuma zata je ta yiwa yan gidan su sallama. Ta shirya sosai tayi kyanta, shima haka, sannan suka fito tare suna hirar su yana yi mata alkawarin zai koya mata mota in sun dawo. "Duk san da zaki fita ko ina office ne sai kiyi tafiyar ki kawai" a kofar gidan ne taga abin mamakin da ya saka ta tsaya ta kasa motsi. Adam ne a tsaye a jikin mota yaa goge ta,