Showing 96001 words to 99000 words out of 300844 words

Chapter 33 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2080

bana son warin kitchen, kar in je in tayi muku amai in haramta muku abincin ku gwara inyi zamana kawai" sai Sumayya taji babu dadi dan haka ta dauko mayafin ta tabi Nafisa suka tafi. Suna zuwa Khadijah tace "bata taho ba ko? Dama ai nasan ba zuwa zata yi ba kawai dan kar in sagar muku da gwuiwa ne yasa banyi magana ba amma gashi nan kun tabbatar ai yanzu" ashe da rabon tata guiwar ce zata sace dan tana rufe baki sai ga Ruqayyah ta shigo. Nafisa tace "a'a, aman fa?" Tace "yaya zanyi? Abinda ya zama dole ai dole ne ayi shi. Wannan abu ai namu ne maganin a kwabe mu bare ma suka zo ballantana mu?" Sai duk suka yi shiru suna kallon kallo ban basu san waye bare a gurin ba.

A lokacin Sumayya ta koyi abubuwa da yawa ta fannin girki, musamman a gurin Fatima da kuma chefs din da aka gayyato sai ta fahimci cewa Ruqayyah sam bata da wayo kuma bata san ma me take so ba, da ta kwantar da kai da ta samu abubuwa da yawa daga gurin Fatima. Amma zafin ran ta da girman kanta ba zai barta ba.

Idan wani ya shigo gurin yaga yadda Ruqayyah ta kame tana bada order sai ka dauka itace matar gidan, sai ka lura sosai sannan zaka fahimci cewa kare ne da fatar kura dan kayan girkin da ake amfani dasu ma kansu ba sanin su tayi ba ballantana abinda za'a yi dasu. Sai wajen karfe biyar na yamma suka kammala komai, suka jera komai a gurin da za'a yi taron sannan kowa ya tafi da niyyar shiryawa kafin baki su fara zuwa. Ruqayyah tana komawa gida tayi wanka sai ta saka rigar zaman gida tayi sallah tayi kwanciyar ta tana chatting dinta a waya da sababbin kawayenta. Har Sumayya ta shirya ta fito ita kuwa tana kwance, tayi mata magana sai tace ta tafi kawai zasu taho tare da Hassan. Wannan yasa tayi tafiyar ta ta rabu da ita. A kofar shiga gurin ta ga Adam, and he took her breath away, all suit up kamar shine oga Hussain, ya tsaya yana kallon yadda tayi kyau itama cikin doguwar rigar lace dinkin bubu da akayi wa landing da red aka kuma yi mata ado da red flowers a gaban rigar, ta daura dankalin lace din sannan ta yafa red mayafi, fuskarta babu kwalliya sosai amma kyawun da tayi ba kadan bane ba. Ya mika mata hannu, smiling from ear to ear, ta makale kafada yayi dariya yace "a kwana a tashi dai" tace "Allah ya kaimu lokacin, but not now" sai ya dauka wayarsa yace "wannan kwalliyar sai nayi mata hoto dan in ajiye a gefen pillow na" tayi murmushi tana rufe fuskar ta da hannunta shi kuma yana yi mata hoto, sai daya gama tace "ban dauka zan ganka anan ba, tunda naji ance taron is for specific people" ya juya suka jera yana cewa "oga Hussain ne ya banj wadannan kayan yace in shirya in shigo tare dashi saboda in kula da manyan bakin sa, in tabbatar sun zama fully satisfied" tace "ohh kace taron ma yana hannunka gaba ki daya, to plate dina yana gurinka" yace "ke xe ta farko da zaki samu komai da kike bukata, ko oga Hussain ne sai dai ya jira ki gama tukunna" suka yi dariya a tare.

Ruqayyah tana kwance har Hassan ya shigo a gaggauce, ya kalle ta yace "what? Wai baki shirya ba? Ki yi sauri Please ki shirya zan shiga in shirya nima, saboda ina so duk wanda zai zo ya tarar dani a gurin" kafin ta bashi amsa har ya shige dakinsa. Ta koma tayi kwanciyar ta har ya gama shiryawa ya fito yana daura agogon hannu, sai kawai ya tsaya yana kallon ta, fuskar sa tana nuna bacin ransa. "Hassana wai baki tashi ba har yanzu?" Ta tashi zaune tana yamutsa fuska tace "ni fa ba zan je ba mijina, kayi tafiyar ka kawai" sai yana yin fuskarsa ya chanja daga bacin rai zuwa concern yace "ba kya jin dadine precious? Ko jikin ne?" Ya zauna a kusa da ita sai ta fara kakaro kuka, hawaye yana zuba tace "ni ba zanje a wulakanta ni a cikin mutane ba. Ranar nan na shiga gidan da niyyar mu dai-dai ta tsakanin mu tunda naga ka damu da abinda ya faru, naga yadda kake son dan uwanka shine naje dan muyi sulhu, amma matar nan sai ta rufe idonta ta ci min mutunci wai naje cin arziki" ta kara sautin kukanta "babu irin zagin da bata yi min ba wai kar ta sake ganin kafata a gidan ta, harda cewa wai a gidan su banfi darajar bayin su ba, ita tafi ƙarfin tayi harka dani....." Ya daga mata hannu idanunsa sun kada sunyi ja. "Kinga dakata Hassana. Please not now. Kinga baki ne damu suna waje suna jiran mu ki tashi muje ki shirya mu fita" ta bishi da kallo tana sheshshekar kuka, bata ji dadin yadda yayi reacting ba, tace "yanzu kafi son inje a wulakanta ni a gaban jama'a? Kafi son a gaban kowa da kowa ta nuna wa duniya cewa ba mijina ne mai kudin ba mijinta ne?" Ya mike tsaye yace "she wouldn't dare. Kuma ita bata isa ta hanaki shiga gidan Hussain ba saboda ba gidanta bane ba. Babu yadda zata yi ta rabaki da ni kamar yadda babu yadda zata yi ta raba ni da Hussain. Ki tashi muje in gani in zata yi wani abu akai. I want to see her try something in yaso ni kuma sai in koya mata hankali" a dolen ta ta tashi ta shirya, amma ita ba haka taso ba, so tayi ace ya hau sosai ya tafi gurin taron ya ciwa Fatima mutunci ita kuma ta rama, sai taga Hussain wa zai zaba a cikin su. Ta riga ta san amsar, wannan shi yasa take son ta hada rigima a tsakanin su.

Haka suka shiga cikin gurin taron hand in hand, suka tsaya a bakin kofar shiga gurin tare da Hussain da Fatima, duk wanda yazo zasu tarye shi su gaisa yayi musu murna sannan ya shiga ciki, a haka har bakin suka gama zuwa sannan ya kuma kama hannunta suka shiga ciki suka sake zagaya bakin sannan suka he suka zauna aka fara gabatar da taro. A lokacin ne yan gidan su Ruqayyah suka shigo gurin, ita kanta bata san Hassan ya gayyace su ba kuma bata nemi ya gaiyace sun ba saboda tana ganin kamar zasu ata mata show ne, kamar zata wulakanta a idon mutane irin wadannan in aka ga Baba da Inna Ade a matsayin iyayenta.

Tana ganin su ta fara sunne sunne wai kar su ganta ai kuwa Hassan ya kama hannunta har gaban su ya hada su sannan ya koma gurin sauran bakin sa. Yana ta zuba ido yaga Fatima ko wani wanda ya danganci Fatima yazo yayi wa Ruqayyah ko wanda ya danganci Ruqayyah wulakanci amma bai gani ba, sai ma yaga Fatima ta nuna wa Hussain su Baba sannan sun tafi takanas sunje sun gaishe su.

Taron ya kayatar sosai dan ko dinner din bikin su bata yi wannan haduwar ba musanman saboda wannan din babu mutane sosai kamar wancan. Sumayya tana ganin du Inna ta bar gefen Adam da da suke tare ta taho gurinsu tana nuna jin dadin ta, a ganin ta honouring dinsu Hassan yayi daya gayyace su zuwa inda sai wane da wane ne a gurin. Ita ta kai su gurin Aunty suka gaisa sannan ta samar musu gurin zama yayin da Adam ya tabbatar sun sami komai da suke bukata. Yayin da Ruqayyah tayi excusing kanta ta koma side din Hassan, ta gaya masa cewa bata son ta barshi shi kadai shi yasa ta dawo "naga kowa yaci kwalliya, har da yammata, bana son idon mijina yayi yawo nafi son ya tsaya a kaina ni kadai" yayi mata murmushi "ke ma kin sani ai ba sai na gaya miki ba, idanun Hassan will always be on Hassana".

Komai ya faru a gurin sai Ruqayyah tayi wa Hassan complain cewa anyi wani abu ba dai dai ba. Ko tace mutane sunfi kula Hussain a kansa, ko tace wata tayi mata kallon banza dan ba Fatima bace ba ko kuma tace wani ya tafi bai yi masa sallama ba amma yayi wa Hussain. Hassan Allah Allah yake yi a tashi saboda zuciyarsa gaba ki daya ta dawo makwogwaron sa. Ana fara tafiya bayan ya tabbatar personal abokan sa sun tafi kuma su Baba sun tafi sai ya jata suka koma gida. Suna shiga gidan tayi tsaki tace "ni duk raina a bace yake wallahi, ni ban ga dalilin ma da yasa za'a yi taron nan a gidan Hussain ba bayan kuma kaine babba, ko da yake dole ayi acan dan a nuna wa mutane babban gida" ya kama hannun ta bai ce mata komai ba suka hau sama. Suka wuce dakinsa tana cewa "dakina zan je in dan huta kadan naji wannan zirga-zirga ta sa mara ta ta fara ciwo" yayi murmushi yace "wani abu nake so in nuna miki a dakina" suna shiga ya wuce da ita valcony dinsa ya tsayar da ita ya tsaya a bayan ta yana nuna mata Hussain a tsaye a kofar gidan sa suna sallama da wasu baki daya rako yace "kin ga wancan mutumin?" Ta dauke kanta tace "wai Hussain kake nuna min? Na gane shi mana, ko dan show up dinsa da san a sani ai dole in gane shi ko a ina na hango shi" ya runtse ido ya bude ya sake juya mata fuskarta side din Hussain yace "ki kalle shi sosai" tayi kokarin dauke kanta amma ya rike fuskar a guri daya ya hana ta juyawa yace "ina so ki kalle shi sosai ki gane shi sosai. Sunansa Hussain Aminu Abdullahi, and he is my better half, kaf duniyar nan babu wani mutum ko wani abu da nake so sama dashi. In nace kowa ina nufin kowa, har wannan" ya fada yana dora hannun sa akan marar ta. "Har wadannan zan iya giving dinsu up for him. For a smile on his face. So I want you to listen to me carefully. Daga yau, bana son ki sake fada min wata magana marar dadi a kansa. Bana so, bana son ji. Am I clear?"


*New Chapter*

Ji tayi jikinta gabaki daya ya zama kamar na statue, ko hannunta ta kasa motsala, ko idonta ta kasa kiftawa, zata iya rantsewa cewa hatta zuciyarta ta tsaya da aikin buga jini zuwa sassan jikinta. Ya kawo bakinsa dai dai kunnenta ya sake cewa cikin rada but harshly "is that clear?"

Automatically kanta ya motsa da alamar eh, ya saki fuskarta sannan ya dan buga kafadar ta yace "good girl" sai kuma yayi kissing side din fuskarta ya juya ya bar gurin. Ta lushe idonta tana jin zuciyarta data zama kankara tana narkewa ruwan yana taruwa a idanunta, ko a cikin mafarkinta bata taba tsammanin Hassan zai iya furta mata wadannan kalaman ba, yes, ta san he is strong tun sanda yana zuwa zance gurin ta amma bayan bikinsu, irin son da taga yana yi mata ta dauka ta kama shi a hannun ta, musamman a matsayin da take rike dashi na wadda tayi saving life dinsa ga kuma darajar abinda yake cikin ta. Ta dauka zai zabe ta akan kowa a duniya, amma shine ya furta mata to her face cewa yafi son Hussain akan komai, harda jaddada mata in yace komai yana nufin komai, harda misaltawa da abinda yake cikinta, wato ita bama ta cikin layin da Hussain din yake ciki.

Taji duk wani shiri nata yana kuncewa yana bin iska. Taji duk wani abu da yake kanta yana sauka kasa yana farfashewa. Taji duniya tayi mata zafi.

Tasa hannu da niyyar goge hawayen da ya taru a idonta amma sai taji babu. Ita dama haka take in ranta ya baci irin wannan to sai hawaye yaki zubar mata sai dai tayi na zuci. Sai dai in kukan karya ne to da gudu hawayen yake zuwa. Ta mayar da hankalinta zuwa inda Hassan yayi forcing dinta ta kalla taga Hussain har yanzu yana tsaye hannunsa rike dana Fatima suna dariya tare da wasu mutanen su da suka rako waje. Ta dauke kanta gefe tare da rufe idonta, mafarkin ta yana karasa tarwatsewa a gaban idanun ta.

Ta saki karfen, sannan ta juya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta shiga dakin Hassan, ta jiyo motsin sa a toilet daga dukkan alama wanka yake yi sai ta fita daga dakin a ranta tana cewa "yau sai dai kaje ka rungume Hussain ba dai ni ba"

Dakin ta ta tafi ta yar da jakar hannunta a kasa sannan ta haye kan gado tana kara jin zafin maganganun Hassan a ranta. Tabbas sai ya san ita ya gaya wa haka, sai yayi nadama. Ta jima a kwance taji motsin shigowar Sumayya, sai ta jita ta murda dakin ta shigo da sallama. Bata motsa ba har tazo gaban gadon ta dan taba ta tana cewa "Ruqayyah ki tashi ki cire kayan ki mana, a haka zaki yi bacci? Kiyi wanka mana ki tafi dakin mijin ki" ta karasa maganar cikin nishadi, da alama tana cikin farin ciki, to mai zai hana ta farin ciki ita kuwa tunda bata da wani problem a rayuwa? Komai yana tafiyar mata yadda take so ga Adam kullum yana kara cika ta da kaunarsa?

Jin Ruqayyah bata ce komai ba yasa ta kuma taba ta, ta dauka bacci take yi. Sai taga ta bude idonta tana kallonta a take gabanta ya fadi, tasan irin wannan jan idon tasan irin wannan kallon, tace "Ruqayyah? Me ya faru?" Ruqayyah tayi juyi tana kara hayewa can saman gadon, tana jin kamar zuciyarta zata fito waje ida bata gayawa Sumayya ne yake damunta ba.

Sumayya ta zauna a kan side drawer tace "me ya faru Ruqayyah? Wani ne ya bata miki rai a gurin taron?" Ruqayyah ta dauke kai gefe tace "mijina ne, baya sona kuma yanzu, yace yafi son Hussain a kaina. Kamar yadda Baba yace yafi son ki a kaina" sai kuma hawayen suka fara zuba. Sumayya ta hau kan gadon ta jawo ta jikinta tana cewa "Ruqayyah, ba wai ke ce ba'a so ba kuma kema kin sani, duk muna son ki sosai da sosai kawai wasu daga cikin halayen ki ne ba'a so. Na tabbatar shima wani abu kika yi masa har ya fadi haka, amma son ki daban a ransa son Hussain kuma daban, ai ku din ba abu daya bane ba kowa da gurbin da yake zaune a kai" Ruqayyah ta fara kokarin kwace jikin ta daga Sumayya tana cewa "cewa fa yayi har abin da yake cikina zai iya hakura dashi saboda Hussain yayi murmushi, wanne irin so ne wannan? Wacce irin magana ce wannan?"

Sumayya tayi murmushi tace "Ruqayyah! Hassan duk duniya bashi da kamar Hussain kuma har a nade ta ba zai samu kamar Hussain ba. Abinda yake cikin ki kuwa zaku kuma samun wadansu har goma ko fiye da haka, kinga kuwa ai ba za'a taba hada soyayyar su a guri daya ba. Amma ke me kika yi masa haka da zafi har ya gaya miki wannan? Na tabbatar kin kure hakurin sa ne" Ruqayyah tace "dama ai ba hakurin ne da shi ba, fada ne dashi da saurin fushi. Shine har da yi min warning wai kar in kara gaya masa laifin Hussain baya son ji"

Sumayya tace "ai tun farko dama sai dana gaya miki, nasan duk boye boyen halinki da kike yi dole sai ya sani tunda shi hali ai baya boyuwa indai har za'a zauna tare ballantana zama irin na aure. Kin nuna masa ke mai hakuri ce da kawar da kai bayan kuma ba haka bane ba yanzu zafin zuciyar taki da mita kika nuna masa ko? Ni bansan halin maza ba amma nasan ko a matan ma ba kowa ne yake son zama da mutum mai mita ba. Ballantana har ki kai ga fadin aibun dannuwansa a gaban idonsa. Gaskiya baki kyauta ba, kuma duk abinda ya gaya miki ke kika jawo wa kanki. Amma nasan hakan daya fada ba wai dan baya sonki bane ba sai don yana so ya nuna miki cewa abinda kike yi din ba dai dai bane ba. Nima kuma na gaya miki ba dai dai bane ba, dan nasan yadda nake sonki nasan kuma ko menene zaki yi na rashin kyautawa ba zan so inji wani ya fada ba ballantana kuma in naji anyi miki sharri"

Ruqayyah ta dago kai da sauri "sharri? Au sharri nake yi masa? Bashi da son a sani ne da nuna wa mutane basu isa ba? Shi fa jinsa yake yi tamkar sama yake da kowa, jin kowa yake yi a kasan sa dan nayi kokarin ankarar da danuwansa shine nayi laifi? Dan shi fa nake yi ba dan wani ba, dan in kwato masa yancinsa nake yi badan komai ba" sai tayi shiru tana kallon hannunta, Sumayya ta gyara zamanta tace "gaya min, menene plan dinki? Me kike so kiyi archiving? What are you up to?"

Ruqayyah ta danyi tsaki fuskarta tana nuna bacin ranta ta share hawayen da ya rage a idonta tace "ke kinfi kowa sanin ban taba tunanin zan auri mutum kamar Hassan ba sai da na ganshi. Na kuma dora raina akan cewa kudin nan nasa ne, na riga na gama saka zuciya ta akan hakan. Bayan naga Hussain naso ace shine Hassan, naso ace shi zan aura, naso ace shine wanda na tarar ranar nan a toilet amma kuma na hakura na karbi Hassan din tunda a lokacin ina tunanin shi yake da kudin, yanzu kuma na fahimci suma kudin ba nasa bane ba" ya danyi tsaki tana girgiza kanta tace

"na tsani wannan Fatiman ta fiya iyayi da gulma da munafurci da nuna isa, na kuma fahimci Hussain yana matukar sonta, sannan yana son Hassan sosai" ta sake yin shiru kamar mai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login