Showing 255001 words to 258000 words out of 300844 words

Chapter 86 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2051

tough but he will eventually get that space da yake nema a zuciyar Fatima.

A cikin gida ma shagalin ake tayi kamar yadda ake yi a waje, masu kidan kwarya nayi nasu kidan shantu nayi, masu sauran wasanni suna yi suma. Kasancewar daurin auren ba'a shirya masa ba ya saka sai yanxu yan'uwa suke shigowa gidan, kowa kuma yana fadar albarkacin bakinsa akan auren da kuma angon. Kamar yadda Hajiya Fulani da Hajiya Ummah suka riga suka sani, wadan su daga cikin yan'uwa musamman mata suna nuna kamar auren bai dace ba, "yar sarauta mai daraja kamar Fatima za'a dauka a bawa tubabben inyamuri?" Amsar da suke bayarwa mostly itace "shi wanda ya bayar da ita din ai yafi kowa sonta, mu menene namu a ciki" da wata kanwar takawa ta dage sai Hajiya Ummah tace "to ko ayi miki iso ne a gurinsa sai kiyi masa bayanin rashin dacewar abinda yayi?"

Kamar yadda abin yazo wa Adam a shekara shock haka ma yazo wa Fatima ita ma. Bata san dalili da kuma amma bayan labarin yayi sinking a zuciyarta sai taji kamar an dauke mata wani nauyi daga kafadunta. Tayi addu'a ta nemi zabin Allah sannan ta bawa mahaifinta zabi dan haka tasan Allah shi yayi guiding Takawa gurin zaba mata Adam, dan haka tana saka ran cewa shine mafi alkhairi a gurin ta insha Allah. It is going to be tough at first tabbas, amma tasan insha Allah with time babu abinda baya chanjawa. Ko menene kake ji a zuciyarka, give it time it will go away eventually.

Tasan kallon da da yawa a family suke yi kuma zasu yi wa auren nata, amma bata damu ba saboda immediate family dinta suna tare da ita dan sun san ko waye Adam kuma sun san ya cancanta ya aure ta. Ta ga duk Calls din Adam har guda biyar amma taki dauka dan bata shirya yin magana dashi yanzu ba, bata san me zata ce masa yanzu ba.

Sisters dinta sunzo kuma sunyi iyakacin kokarin su gurin cheering dinta up, sun debe mata kewa sosai kuma sun gaya mata maganganu masu dadi sosai dasuka kara kwantar mata da hankali suka kuma tsayar mata da hankalin ta akan abinda ya tunkaro ta. Tana ta aikin gofe hawaye Asma'u tana kallon ta tace "da ace ba Adam din bane bana jin akwai wanda zai dauki wannan arhar hawayen naki" Fatima ta harare ta amma hawayen basu daina zuba ba. Wannan shine abinda ya rage na daga trauma din mutuwar Hussain, komai kankantar abu sai tayi kuka, tasan kuma kukan mutuwar Hussain ne take tayi har yanzu kuma she will continue har sai ta bar duniya.

Sai dare ya turo mata text bayan ya sake kira bata dauka ba. "Am sorry. Nima ban san za'a yi ba. Bani na zaba ba" sai ta mishi reply "I know. Allah ne ya zabe ka"

A daren ranar bayan kowa ya watse sai Adam ya kira Maman sa ya gaya mata abinda ya faru, and she cried, bata taba sanin cewa alkhairin da yake bin dan nata ba kenan bayan su yanzu suna cikin matsaloli ta ko'ina. Mijinta yana cikin rigima yana hannun police, Samuel babu ruwansa dan ita rabon data ganshi ta manta, Martha tayi ciki saurayin ya gudu ya barta kuma cikin yaki fita, Gloria ce kadai mai dama dama, ita ce kuma take kara jan ra'ayin ta akan su dawo Kano su zauna, su kuma nemi Adam yayi guiding dinsu zuwa hanyar da yake ganin zata bulle dasu, irin hanyar da shi ya bi kuma har yakai ga ci.

"Princess" ta fada, "they let you marry a princess Adam?" Yace "yes Mom" yana realising cewa yaune rana ta farko data kira shi da sunan Adam.

Babu wani biki da Fatima tayi a nata bangaren, Adam ma bai shirya komai ba dan yaga alamar bata so, shi kuma yanzu lallabawa yake yi dan har yanzu taki yarda suyi magana ko a waya ne ballantana su ga juna, har yau taki yi masa magana. Shi kuma sai ya mayar da hankalinsa ka family dinsa da suka tattaro suka dawo Kano suka bar Samuel a can, Daddy kuma basu ma san inda yake ba ya kuma cika wandon sa da iska. Abinda ya fara yi shine tabbatar wa da sun karbi shahada kamar yadda suka nuna masa suna so, bayan sun karba kuma ya tabbatar ya ajiye musu duk abinda yasan zadu bukata na amfanin gida anan gidan su na Kano ya kuma samar musu malamar da zata ke koya musu addini sai ya koma Dubai dan ya cigaba da shirye-shiryen sa a can.

Gidan da yake zaune a ciki Takawa yace yabar masa saboda yace a matsayin sa na dan sa hakkin sa ne ya bashi muhalli. Shi kuma Adam sai yayi gyare-gyaren da yake ganin gidan yana bukata, acan aka yiwa Fatima jerenta ta hannun Aunty Maryam, Aunty Maryam din ce kuma ta taimakawa Adam gurin hada lefen Fatima wanda ya cinye kusan duk ajjiyar sa, Aunty Maryam din kuma ya roka ta taho Nigeria ta kawo, sai kuma ya kira mamansa itama taje tare da sisters dinsa akayi dasu. Sannan aka saka ranar tariyar. Tariyar ma Fatima cewa tayi ba zata yi taro ba, kai amaryar ma tace babu wanda zai raka ta ita da kanta zata tafi, duk suyi zamansu duk wanda ya samu lokaci ya je daga baya yaga dakin ta, amma sai a gida aka ga rashin dacewar hakan, aka hada kan yanuwanta da surukan gidan suka tafi can gidan Aunty Maryam suka shiryawa Fatimah walima sannan da dare suka kaita gidan mijinta.

Sai a ranar Adam ya samu ganin matarsa, ya kuma samu damar yi mata magana. "Abinda na roka ranar nan shi zan kara roka ya ma. Just a space a zuciyar Zahra, ko bazai ishe ni zama ba zanyi hakuri in tsugunna ko dana tsahon shekaru nawa ne" ta dago kai tana kallonsa, this is the first time data ganshi tunda aka daura auren sai a hotunan da aka nuna mata na daurin aure, tace "ka tabbatar ba zaka fadi ba? Shekara da shekaru a tsugunne?" Ya gyara zama tare da zabga tagumi yana kallonta yace "to ya zanyi? Abinda na samu ba da shi zanyi amfani ba? Amma in za'a taimaka min sai a dan kara min space dan in samu in zauna"

Tace "ya danganta da irin yanayin yadda ka kula da space din da aka baka daga farko, in ka kula dashi sai a kara maka wani" yayi murmushi "Nagode sosai" tace "bar saurin godiya. Akwai sharadi" ya bude ido "sharadi kuma?wanne irin sharadi?" Tace "sharadin shine zaka kara aure nan gaba" sai abin ma ya bashi dariya, yayi dariya ita kuma ta bata rai "dariya na baka ma?" Yace "shine sharadin naki? To na amince" ta bude ido "ka amince fa kace?" Yace "yes, abinda duk kike so shi za'a yi. Na amince. Amma a bisa nawa sharadin" tace "na me fa?" Yace "idan har nayi failing gurin chanja ra'ayin ki akan wannan maganar to zanyi abinda kika ce din" tace "I will never change my mind" yace "really" sai ya gyara zama yace "kin san me? I assure you, ki bani shekara daya, ke da kanki zaki ce "Darling dan Allah kar ka yi min kishiya" tayi dariya, rabon da tayi dariya tun ranar Birthday din little Hussain, tace "I will never say that" yace "kar ki cika baki, dan zaki sha mamaki. Kin amince da sharadi na?" Ta gyada kai tana kallonsa fuskar ta still da murmushi.

Shima yana murmushin, yana jin dadin ganin murmushin ta at last, yana kuma lura da yadda ta kara yin kyau sosai daga dukkan alamu ta sha gyaran amare yace "I really did miss you Zahra" bata amsa masa ba sai ta mika masa hannun ta tace "where is my ring?" Ya bude ido sai kuma ya mike da sauri ya fita wajen mota neman zoben da ya ajiye, ya dauko shi ya dawo da sauri ya durkusa a gabanta, ya kama hannunta ya saka mata yana lura da yadda yayi mata kyau kamar yadda yayi hasashen zaiyi. A hankali ya dago hannun ya kai bakinsa yayi kissing. Tayi saurin karbe hannunta tana wayencewa da kallon zoben tace "yayi kyau sosai" sai ya dawo kusa da ita ya zauna yana bata details labarin yadda akayi zoben.

Shekara guda bayan nan ta haifa masa yarsu ta farko Islam, bayan shekaru uku akayi Iman, Sai Huda, sannan auta Muhammad. Sai kuma little Hussain da yake tamkar shine babban dansu. And their life continue.

A Dubai suka yi basing rayuwarsu, saboda Adam ya samu aiki mai kyau a can kuma yana samun budi sosai da sosai. Ya kuma gina musu katon gidan su anan Kano inda suke sauka idan sunzo Nigeria. Fatima kuma bata aiki amma a yanzu ita take owning half share na kamfanin H and H wanda zuwa lokacin ya baza branches dinsa har garin Kano, Umar kusan ya rasa duk shares dinsa saboda baya investing, yanzu Fatima da Ruqayyah ne owners din su biyu. Former matar Hassan da former matar Hussain. That's the irony of life.

Shekaru biyar bayan auren Adam da Fatima lokacin an haifi Islam da Iman Allah yayi wa maimartaba sarki rasuwa, Umar ne ya gaji sarautar sa.........

Bara mu bar Fatimah da Adam anan su huta. Tomorrow zamu koma bangaren su Ruqayyah suma muyi concluding sannan mu koma ga Amir.

Sorry for the late posts. It has not been easy lately.


*Re-married 2*

Ranar da aka daura auren Fatima da Adam, bayan an gama reception da sauran hidimomin da akayi a waje gurin maxa sai Baba da ƴaƴan sa, with Hassan a matsayin babban Da, suka je suka sake yiwa Adam godiya gurin mai martaba sarki sannan suka yi sallama suka tafi. Dama a motar Adam suka taho, yanzu kuma ba tare da Adam zasu koma ba, niyyar Adam shine in sun gama ai samu driver ya mayar dasu Kaduna amma yanzu tunda ga Hassan sai suka koma tare. Haka suka tafi a hanya suna ta hirar abin, da kuma hirar rayuwa in general, sannan suna godewa Allah da abubuwa suke kasance suna tafiyar musu cikin sauki. Baba kuma yana ta cigaba da yi musu nasiha akan lamarin rayuwa.

Sai da Hassan ya ajiye su gida sannan ya tafi nashi gidan. Ya san Noorien sa tana can tana jiran dawowar sa tare da daddadan abincin ta. Yayi murmushi, tabbas sunan da yake kiranta dashi yayi tsananin dacewa da ita, she really is the light of his life dan tun auren ta dashi bau abinda yake samu sai alkhairai ta ko'ina, kullum zuciyarsa cikin haske take har mantawa yake yi da cewa da ya kasance cikin tashe tashen hankula da jarabawowi. His family is now settled, sisters dinsa kowa tana gidan mijinta lafiya lau ga yayansa guda bakwai chif da Allah ya bashi shida maza daya mace, to menene kuma sauran abinda yake bukata?

Abu daya yake fata, bai sani ba kuma ko zai tabbata ko kuma bashi da rabo amma zuciyarsa kullum tana yi masa wannan kwadayin, ko Allah zai saka maybe wata rana idinsa ya gane masa dan ko yar Hussain. Duk da kaso tamanin cikin dari na hope dinsa yana gaya masa cewa abinda aka haifa din baya duniya, amma kaso ashirin dinnan yana kuma tuna masa da cewa anything is possible. Kamar yadda kullum Sumayya take gaya masa, "ni ban yadda Ruqayyah zata kashe yaron nan ba, ko da ba'a cikin hayyacin ta take ba ban yadda zata iya kisa ba" a lokuta da dama yakan share ta yayi kamar baiji me take cewa ba. Baya son musu da ita akan Ruqayyah saboda baya son bata mata rai amma shi a nasa ganin gani yake yi babu abinda Ruqayyah ba zata iya aikata wa ba in da akan kudi ne..

Sanda yaje gida kuwa kamar yadda yayi tsammani haka ya same ta a falo ta chanchada ado kamar amaryar da aka kawo yau, da two years old Amatullah a gefenta ita ma anyi mata kwalliya har da sabon kitso. Yana shiga uwa da yar suka fara rige rigen zuwa rungume shi, sai ya fara tarar uwar yana manna mata kiss a lips dinta, Amatullah ta saka kuka tana bubbuga kafa a kasa, suka yi dariya duk su biyun sai ya durkusa ya dauke ta ya daga ta sama yana yi mata chakulkulin daya saka ta dariya. Yace "duk wannan ƙwalliyar Amaty tawa ce" tace "eh, mommy yi min kyau" ya shafa kitson ta yace "kai amma Allah yayi wa mommy albarka, wannan kitson yayi kyau sosai" Sumayya ta fara shagwaba "nima fa nayi kitson ko baka gani bane ba?" Ta fada tana fari da idonta, ya ajiye Amatullah ya kunche daurin dankwalin yana kallon kananan kitson da aka jera mata, yace "matar nan shagwaba ni kike yi da yawa, daga zuwa kano daurin aure shine akayi min wannan taryen?" Tace "kano ai tana da girma, nasan yammata nawa ka gani a a can? Ko kaga wata ta fito da kitson ta ya burge ka? Kasan sai anayi ana updating fa kar ina zaune inji na zama outdated"

Yayi dariya sosai yace "idanun Hassan a guri daya suke a tsaye ko rawa basa yi, saboda Sumayyan sa kuma hasken zuciyarsa kullum kara zama amarya take yi" tace "wacce amarya kuma ka jika da zolaya. Haihuwa hudu wasa ce" ya jawo ta jikin sa yana dora hannun sa a marar ta yace "saura ta biya" ta zaro ido shi kuma ya kashe mata nasa idon yace "please" yana hade hannayensa guri daya, ta rike hannun "da wahala fa Habibi,hudun ma ai nayi kokari" yace "kinga Amaty bata da yaruwa, ya kamata a sama mata sister" tace "in kuma na sake haihuwar namiji kuma fa? Sai in sake wani cikin again?" A lankwasa kai kamar abin tausayi sai ta ja hannun sa tana jansa ciki, ya kalli yadda bayanta yake motsawa in tana tafiya yace "I will convince you one way or another".

Sai da ya fara cin abinci yace "tun a hanya nake addu'ar Allah yada yaran nan badi daeo daga school ba, in dan samu in mori matata kafin su zo su kwace min" tayi murmushin da yake kara mata kyau a idon sa, tace "kasan islamiyyar su sai sunyi sallar magrib sannan ake sallamar su" yace "good, da suna nan da yanzu hidima tayi miki yawa" tace "lah! Yaran nan fa basu da fitina fa, ina jin ana fadar fitinar boys amma ni nawa kam alhamdulillah suna da nutsuwa tunda basu taba burning down gidan nan ba" ta karasa sarcastically, yace "gado suka yi ai, babar su ce mai nutsuwar shi yasa ta koya musu duma suke yi" tace "da kuma babansu mai kula ba? Ai hannu daya baya daukar jinka, tare muke shukawa......." Yace "tare kuma zamu girbe insha Allah" suka yi dariya tare.

Sai daya gama cin abincin sannan ya fara bata labarin daurin auren da abubuwan da suka faru, sai yaga tayi tagumi tana kallon sa tana ta zabga murmushi, yace "what's funny?" Tace "life. Gaba ki daya rayuwar ce lamarin ta ya saka ni nishadi. Fifteen years ago babu daya daga cikin mu da yake saka ran sai samu kansa a inda yake a yanzu. I remember sanda kake zuwa zance gurin Ruqayyah and the way da kake nuna mata soyayya ko? Mhen! And I was so in love with Adam then. Ka tuna sanda kake kiransa a waya ka bani muyi hira ta wayarka?"

Yayi dariya, tace "I never thought cewa one day kaine zaka zamo jini da tsokar jikina ba" yace "and I never thought Adam zai zama mijin gimbiyar Hussain ba" tayi dariya, "duk wanda aka fadawa a cikin mu a lokacin zai ce wannan tatsuniya ce marar ma'ana" yace "tabbas. Dukkan mu a lokacin muna da plans for our lives, but Allah ya riga yayi mana nasa plan din kuma in muka duba yanxu in muka waiga baya sai muga abubuwan da muka samu sunfi wadanda muka rasa. Saboda shi ubangiji shine ya fi mu sanin menene dai dai damu" ta gyada kai.

Yes. Kowa a cikin su abinda ya samu yafi abinda yayi tunanin samu. In dai har kabar wa Allah zabi kabi komai a sannu, tabbas va zaka taba kokawa ba, in kuwa ka nuna iyawarka ce iyawa to kuwa zaka yi kuka da idonka, zaka yi nadama mai tsanani. Hassan is a living example of that.

Yace "and Hussain. Hussain lived his life to the fullest. Ban taba ganin carefree mutum irinsa ba yayi tapping duk wami goodness na duniyar nan kuma ba tare da ya tsallake limit na ubangiji ba, hakan yana nufin mutum zai iya samun both duniya da lahira masu kyau kenan, hakan yana nufin kudi if used a kan hanyar dai dai zasu iya samar maka duniya su kuma samar maka lahira. Kudi yana iya jawo maka mutane, yes, but depending on abinda kayi da kudin har ya jawo maka mutanen shi zai yi determining wadanne irin mutane ne zaka jawo din. Ko wanne second a raruwar mutun is an opportunity for him, Hussain has been saying this to my ears amma ban taba dauka ba, but I think it is about time da zan dan dauki page daya daga pages din rayuwarsa".

Ta tsaya tana kallon sa cikin rashin fahimta sai yayi murmushi yace "am planning a trip for us idan yara sunyi hutu, any country of your choices, kowa ya zabi daya" Sumayya sai murna, ta kama hannun Amatullah suna rawa duk da ita Amatullah bata san murnar me ake yi ba, sai ya mike yana kallon su yana jin dadi a ransa yace "amma in muka je da kanwar Amaty zaki dawo a cikin ki".

********************************


Ruqayyah tana private psychiatric hospital inda ake kula da lafiyar kwakwalwar ta. Sumayya, Sulaiman su suke ta hidima da aljihun su akanta, musamman ma Sumayya tunda shi Sulaiman yanzu yana da iyali, Inna Ade kuma da Zunnur su suke yi da jikin su kullum suna zirga zirga, Baba bai hana su ba kuma shima yana dan lekawa ya ganta ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login