Showing 12001 words to 15000 words out of 300844 words

Chapter 5 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2028

so suke sha'awar iyayen wasu suna cewa ina ma dai sune nasu" Sulaiman yace "haba dai Baba, ni da ace za'a sake haihuwa ta ace in zabi iyaye ai da ku zan zaba sau goma, kunyi mana komai sai fatan Allah ya saka muku da alkhairi ya bamu ikon yi muku biyayya da faranta muku".

Sai a lokacin Baba ya juya yana kallon Ruqayyah da take ta gugar ta kanta a kasa yace "Hassana. Baki ga na shigo ba ko gaishe ni baki yi ba?" Ta dago da murmushin yake a fuskar ta tace "na gaishe ka Baba, baka ji ni bane" ya girgiza kansa kawai ya fara cin abincin sa.

Sai da yayi nisa da cin abincin suna yar hirarsu da Inna sannan ya dago kai yana kallon Sumayya yace "Hussaina yaya jarabawar taku? Ana dai kokari sosai ko?" Ta rufe tukunyar data ke juyawa ta taho tana cewa "Baba alhamdulillah, ai mun kusa gama wa ma insha Allahu nan da sati biyu zamu kammala gabaki daya" Ruqayyah ta ajiye iron din hannunta wanda ta gama guga dashi tace "nan da sati biyu zamu gama Neco Baba, saura Waec" yayi shiru sannan yace "ita ce wadda ba'a biya muku bako?" Sumayya tayi saurin cewa "ai bata da wani muhimmanci Baba. Kaga Minal ita fa waccan shekarar ta gama amma har yanzu bata karbo waec dinta ba tunda taci duk abinda ake bukata a Neco" Ruqayyah ta zauna akan tabarmar tace "muhimmancin ta daya shine idan mutum bai ci Neco ba, ko kuma yaci rabi bai ci rabi ba, zai iya hada wa da waec sai ya samu duk abinda ake bukata a jami'a" Baba ya gyada kai kawai bai ce komai ba, amma fuskarsa ta nuna damuwa.

Inna Ade tace "maganar jami'a fa naji kuna yi, ita minal din bata gaya muku uban kudin da mamanta take bani labarin an kashe kafin a saka ta a jami'a ba? Ita kadai ma ballantana ku biyu?" Baba yace "abin ai na Allah ne, insha Allahu, indai sunci wannan jarabawar kuma suna so zasu je. Ko ba zan iya turasu su biyu a lokaci daya ba sai in saka daya wata shekarar sai a saka dayar. Abin ai na Allah ne"

Friday bayan sun tashi daga makaranta, suna tsaye a bakin titi suna jiran abin hawa sai ga wata taxi ta tsaya a gaban su. Ruqayyah ta sunkuyo da niyyar yi wa driver magana sai taga mutumin ranar nan ne, ta ja tsaki tare da komawa baya tana hade rai. Sumayya ta leka itama ta gashi zata matsa taji yace "ku shigo in kai ku" Ruqayyah ta leko tace "ko babu motocin haya a titin nan gwara mu tafi a kafa" ta kuma komawa baya ta tsaya. Yace da sumayya "ke shigo in kaiki" ta girgiza kanta "bazan iya tafiya ba tare da sister ta ba" yace "I understand" tace "mungode bawan Allah" yace "yes, ni bawa ne na Allah but sunana Adam" Ruqayyah ta leko "babu wanda ya tambaye ka sunanka saboda babu wanda ya damu daya sani" Sumayya ta kalle shi tana murmushi tace "Sunana Sumayya, yar uwa ta kuma sunanta Ruqayyah,".


Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.

Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only




Episode Six : Chloroform

Hira tayi dadi tsakanin Hussain da gimbiyar sa, har lokaci ya tafi ba tare daya sani ba, tun suna kan kujera suna hira har suka sauko kan carpet suna ta magana cikin yiwa juna murmushi da dariya, kasancewar duk su biyun masu fara'a ne sosai. Suna cikin hirar ne alarm ya kada a wayar Fatima, ta dauka ta kashe tace masa "lokacin tafiyar ka yayi kar kayi missing Flight dinka" yana kallonta da mamaki yace "wai kina nufin har alarm kika saka min?" Ta juya idonta tace "nasan zamu iya mantawa, kuma tafiyar ka tana da muhimmanci, bana so inso kaina da yawa"

Ya jinjina kansa yana jin soyayyar ta tana karuwa a zuciyarsa, sosai yake son yadda take gudanar da al'amuran ta, komai nata a tsare yake, komai nata a nutse take yinsa. Har airport ta kai shi sannan sukayi sallama a ransu suna jin kamar kar su rabu, Hussain yana ji a jikinsa cewa in sukayi aure duk tafiyar da zaiyi tare da ita zai ke yi tunda dai matarsa ce kuma babu abinda zata zauna tayi a gida.

Cikin sauri yaje gida, ya tarar Hassan ya gama hada masa kayan tafiyar sa ya zuba masa a mota dan haka wanka kawai yayi ya chanza manyan kayan jikinsa zuwa ƙanana sannan ya shiga mota Hassan ya mayar dashi airport. A hanya babu wanda yayi magana har suka je, haka kawai Hussain yaji jikinsa yayi sanyi and for the first time tunda ya fara tafiye-tafiye yaji cewa baya son tafiya, yaji cewa baya son ya rabu da danuwansa.

Sai da Hassan ya karkada masa key a fuska sannan ya juyo yana kallonsa yana kirkiro murmushi. Hassan yace "what's wrong? Tsoron jirgin kuma kake yi yau ko me?" Hussain ya duba agogon sa yana noticing mintinan daya rage kafin jirgin su ya tashi, wata zuciyar tana gaya masa ya juya ya koma gida amma sai yayi sauri ya girgiza kansa yace da Hassan "take care of yourself bro. Bazan jima ba dan bana jin zan wuce sati daya. Duk abinda ya kamata ayi to ayi kawai kar ace sai an jira ni. Ka bawa Aunty hakuri kace tafiyar ta zama dole ne bana so auction din nan ya wuce ni" Hassan ya rike dariyar da take taso ma sa yace "Badan na sanka ba da sai ince kamar tsoro nake gani a fuskarka kuma nake ji a muryarka, amma na sanka kuma nasan Hussaini baya jin tsoron komai, shi jarumin jamurai ne" Hussain yayi murmushin da ya tsaya a lips dinsa yace "bana jin dadi ne kawai. Amma nasan kafin mu sauka zan ware" ya sake kallon abogon hannunsa sannan yace "take care of yourself bro" Hassan yace "you already said that bro" sai hussain yayi murmushi yana bude hannu yace "okay take care of everyone at home" sannan ya bude kofa ya fita.

Hassan ya bishi da kallo har ya shiga kofar departure hall, sai daya daina ganin sa sannan ya tayar da motar ya bar gurin yana jin part of him ya tafi tare da Hussain. Amma dama ya saba da wannan feeling din, kullum in basa tare da Hussain sai yaji kamar rabin sa ne a gurin rabi kuma yana inda Hussain din yake, tun suna yara haka yake ji, duk fadan su duk rigimar su amma duk duniya babu abinda yake so sama da Hussain, baya jin kuma akwai wani abu da zai raba shi da Hussain.

Direct gida ya koma, yana ta lissafin abubuwan da suke gabansa abubuwan da ya kamata ya yi kafin dawowar Hussain daga Beijing. Dazu dai yayi wa kananan ma'aikatan da za'a dauka aiki a sabon kamfanin interview kuma har ya riga yayi grading dinsu, sai ya zauna zai yi final zabe sannan sai a kira wadanda aka zaba din a sanar musu. Shi komai yafi so yayi a hankali, ya tuna yadda suka yi da Hussain a lokacin da suke maganar daukan ma'aikatan. "Kaga Hassan, don't stress yourself akan maganar nan. Kananan ma'aikata ake magana fa ba manyan ma'aikata ba, ba takardu zaka duba ba ba komai ba, kawai just look at their physique ka tambaye su akan past experiences dinsu shikenan. Wanda kaga ya dace ka bashi aiki kawai a take wanda bai dace ba ka sallame shi kace masa babu aiki dan kar yaje gida yayi ta saka ran zai samu"

Hassan yace "so kake mu dauki baragurbi kenan mu bar masu kyau? Ai shi lamari na daukan ma'aikata a nutse ake bi ayi interview idan da hali ma sau biyu dan aga mai juriya, ni har medical certificate nake so suje suyi saboda in tabbatar da lafiyar su, sannan sai na zauna a nutse sai in tace wanda naga sun cancanta" Hussain ya mike tsaye yana bude hannu yace "do whatever you want. Ni dai abinda na sani shine, duk wanda Allah ya tsara yana da rabon samun aiki a *H and H* ko ka bashi yau ko kuma kayi ta delaying sai nan da shekara daya still dai sai ya samu. To gwara ka bashi ka huta shima kuma ya huta".

Hassan yayi murmushi yana kashe motar bayan yayi packing a compound din gidan su. Tun suna yara kusan kullum sai sunyi irin wannan musun kuma har yau babu wanda ya taba chanza ra'ayin danuwansa.

Ya shiga gidan. A kan dining ya hango yar autar su Zulaihat da takardu a gabanta tana karatu, shirye shiryen ssce take yi dan yanzu haka sun kusa kammala neco sauran su waec. Dama ita kadai ta rage a secondary School sauran yammatan duk suna jami'a dan Hassana har ta kammala ta kuma yi service dinta, ta kuma samu mijin aure dan yanzu so ake yi ma a hada bikin nata dana Hussain.

Zulaihat ta amsa sallamar sa tana binsa da kallo sannan ta kalli bayansa da sauri sai kuma ta sake kallonsa "ina yake?" Ta fada tana kara kallon kofa. Ya jawo kujera a can karshen dining table din ya zauna tare da jawo food warmer din daya gani a gurin, yasan duk gidan sunfi son Hussain a kansa, sunfi sabawa da Hussain saboda ya fi shi faran faran da wasa da dariya, ya fishi kuma kashe musu kudi da shagwaba su, shima kuma yana taya su son Hussain din. Ta sake tambaya "yaya H1 ina yaya H2 yake? Bai dawo daga kanon ba?" Ya fara zuba abinci sannan yace mata "ya tafi China" ta bude ido da baki tana kallonsa sannan ta ajiye littafin hannunta ta tashi a guje ta tafi saman Aunty. Yayi murmushi yana cigaba da zuba abincinsa. Sai daya fara ci sannan yaji saukowarsu kusan gabaki dayansu . Duk suka taho inda yake, Aunty ta zauna a kujera tana kallonsa "ina Hussaini?" Ya dago kai shima yana kallonta yace "ya tafi China, suna kan hanya ma yanzu".

Ta fara fada "yanzu lamarin Hussain har ya kai haka Hassan? yanzu ni a gidan nan ban ma isa a gaya min in za'ayi tafiya ba ballantana in saka ran za'a nemi izini na kafin ayi? Yanzu har sai yayi tafiyar ma sannan zai aiko ka ka gaya min?" Bai ce komai ba har ta gama fadanta sannan ya ajiye spoon din hannnunsa yana kallonta yace "tsakanin ku ne Aunty, kun fi kusa. Nasan in ya sauka zai kira ki sai ki yi masa fadan. Nima sai dana gaya masa rashin dacewar hakan amma sai yayi min bayanin cewa in ya gaya miki hana shi tafiya zakiyi kuma in kika riga kika hana shi ba zai iya tsallake maganar ki ba, sannan kuma tafiyar mai muhimmanci ce sosai saboda injinan da za'a yi amfani dasu a sabon Companyn yin flour nan su zai siyo, in ya aika kuma za'a iya siyo masa fake shi yasa ya tafi da kansa. Kinsan halin Hussain, he settled for nothing less than the best"

Tayi shiru tana tunani, yayin da yammatan suka fara mita, Safiyya tana korafin ai yayi mata alkawarin tare zasu tafi kuma shine ya tafi ya barta. Aunty tace "yanzu yaushe zai dawo kenan?" Hassan yace "sati daya yace zaiyi" tayi ajiyar zuciya tace "Allah ya kaimu, ya kuma dawo mana dashi lafiya. Ni wallahi na ƙagu azo ayi bikin nan nasa ko zai rage wannan yawon, tunda naga yana son Fatima sosai dole zai ke son zama anan tare da ita" Hassan yayi murmushi yace "in yana son yawon zai iya daukan matarsa su tafi tare, menene a ciki?" Aunty ta bata rai "don't put that idea into his head" yayi dariya yana bude hannu "nayi shiru. Amma ina tunanin already idea din tana cikin kan nasa sai mu jira ayi auren mu gani. Hussain ne fa, bana jin aure zai saka ya zauna guri daya"

Suka yi shiru gabaki daya, Hassan yana cin abincin sa amma kuma yana jin idon Aunty a kansa, take ya fahimci tunanin me take yi, sai yaji tace "kai kuma fa?" Ya gane me take nufi amma sai yayi keeping blank expression yace "ni kuma me aunty? Ni ma yaushe zan tafi chinan?" Ta hade rai tace "kai ma yaushe zaka yi auren? shine abinda nake tambaya, kai ko budurwar nan ma ta zamani baka da ita, kaki kula duk yammatan da suke sonka"

Nafisa tayi saurin cewa "ai kuwa Aunty akwai wata course mate dina, baki ga yadda take son shi ba, kullum sai ta tambaye ni ina yake" ya harare ta yace "hala bata ga Hussain ba? Am sure tana ganin sa zata ce shi take so bani ba" Aunty tace "Hussain ai ya riga ya samu matarsa, a very good girl from a very good family. Family dinta is one of the best a duk fadin kasarnan. Kai ma ya kamata ka kara kokari ka samo wa Fatima yaruwa" ya shafa kai yace "za'a samo wa Fatima yaruwa Aunty, amma sai a hankali, kuma ba irin Fatima za'a samo ba dan ni bana son abinda yake all covered in gold and praises. Saboda nasan most of the books with good cover basu da good contents. Ni am more interested in the content" Aunty tana girgiza kai tace "ai kuwa ana samu Hassan, ana samun wanda yake da goodness in both the cover and the content, ko ita fatiman ai haka muke fata" ya girgiza kansa yace "I am not going to take that risk gaskiya, nafi son in nayi aure ya zamana har abada, mace daya in na samu irin wadda nake so ta ishe ni har abada. Nafi son in auri mace from a lower background than ours, yadda ba xata ke looking down on us ba, yadda zata ke girma ma ku iyaye na kuma ba zata ke yiwa sisters dina magana anyhow ba kamar yadda take yiwa bayin gidansu. Nafi son wadda duk abinda na bata, no matter how small zata yi appreciating ba zata raina ba saboda ta saba da wanda yafi shi. Nafi son me low life style irin nawa not extravagant kamar Fatima"

Aunty tace "to Allah ya kawo mana ita, Allah yayi muku zabin alkhairi baki daya" ya amsa da ameen. Sun jima suna hira, yana updating dinta akan shirye shiryen bude sabon company, sai gata ta dauko masa wani dogon list wai daga Gombe aka aiko dashi inji uncles da auntys dinsu na mutanen da suke so a dauka aiki. Ya karba kawai yayi murmushi amma shi a ransa yasan babu wanda zai bawa aiki sai wanda ya cancanta sai dai duk abinda za'a ce ace.

Daga nan part dinsu ya nufa, ya shiga palo yana karewa luxurious kujerun da suka kawata falon kallo, amma last dawowar Hussain daga Japan yana shigowa palon cewa yayi "what? Wannan kujerun har yanzu ba'a cire suba? Wadannan ai sun zama old models yanzu sam ba'a yayinsu" Hassan yayi murmushi yana jin kewar danuwan nasa, Hussain sarkin rikici. Ya bude kofar dakinsa ya shiga, komai tsaf tsaf kamar yadda ya barshi. Yayi wanka ya chanja kayansa zuwa kanana sannan ya fito ya rufe dakinsa ya shiga na Hussain. Komai na dakin abin kallone, ko bakasan kudin kaya ba kana shiga dakin zaka san cewa tabbas an kashe kudi a gurin tsara dakin zuwa kayan da aka zuba a ciki. Sanda Hussain zaiyi renovating babu yadda baiyi da Hassan ba amma yaki yarda a gyara masa nasa dakin "ni dakina babu abinda yayi bana bukatar a gyara min shi, wannan ai almubazzaranci ne, Ni fa da ka ganni yanzu zan iya yin 10 years nan gaba ba tare dana chanza komai a dakina ba".

Sai dai Kamar yadda Hassan yayi tsammani a hargitse dakin yake, kaya sun kai set goma duk a baje a kan gado kuma yasan duk a kokarin shirin zuwa gurin Gimbiya ne aka hargitsa kayan. Yayi tsaki kawai ya wuce wata drawer ya dauko takardar da yazo nema, sketch ne na sabon companyn da ake gina wa wanda kusan an gama komai yanzu, finishing touches kawai ake yi. Ya dauka ya fita, a compound din gidan ya kira wani amintaccen yaron su Salisu, salisu tun babansu yana da rai yake gidan shi da babansa, bayan rasuwar baban nasa sai Hassan da Hussain suka cigaba da zama dashi a matsayin amintaccen su wanda shi kadai yake da access da dakunan kwanan su da abincin su da komai nasu da yake personal, yace "kaje ka gyarawa Hussain dakinsa, ni zanje site sai magrib zan dawo" sannan ya ja motar ya tafi.

Site din ginin ya tafi. So yake yaje yabi ko ina ya tabbatar yadda aka yi sketching din haka aka yi aikin. Dama sunyi waya da engineer dan haka already a can ya same shi sai dai ma'aikatan sun fara tafiya gida tunda magriba ta fara gabato wa. Haka suka yi ta zagayawa sako da lungu na gurin Hassan yana yi yana duba sketch din hannunsa a tsanake duk inda yaga kuma ba'ayi dai dai ba sai yayi magana sai engineer yayi masa bayani in bayanin ya gamshe shi shikenan in kuma baiyi ba yace a gyara. A haka har suka gama, engineer yayi masa sallama ya tafi shi kuma ya tsaya ya dan yi rubuce rubuce a takarda ya saka a cikin sketch din sannan ya fito.

Sai daya fito sannan ya lura da yadda gari yayi duhu, masallatai ana ta sallah wasu ma har sun idar. Da sauri ya bude motarsa yana jin takaicin missing jam'i da yayi, ya ajiye takardar hannunsa a kujerar kusa da driver sannan ya zauna a kujerar driver yana zura key a jikin ignition.

Wani abu mai sanyi yaji ya taba wuyansa, sanyi irin na karfe. Da sauri ya kalli side mirror sai idanunsa suka sauka a kan yar karamar bindiga da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login