Showing 90001 words to 93000 words out of 300844 words
duniya, ko babanta, ko brothers din ta babu wanda yake shiga Bedroom dinta ballantana yaga tsiraicinta. Idan a waje ne kuwa ko gashin kanta babu wanda zai ce ya taba gani saboda yadda take adanawa da tattalin jikinta. Amma yau Hassan, yayan mijinta.......
Ta sani cewa tun kafin ta auri Hussain ta san cewa Hassan baya sonta, but ta dauka ya fara saukowa tunda taga suna Magana yanzu sosai har suyi wasa da dariya, menene ya chanja lokaci daya? Ta tuna abinda yace mata "stay away from my wife" to me tayi wa wife din tasa? Ita dai tasan babu abinda tayi wa Ruqayyah sai alkhairi, babu wani abinda yaje zuciyarta a game da Ruqayyah sai alkhairi. Me yayi zafi haka shi ba wuta ba?
Hussain ya fara jijjigata kamar baby yana cewa "shshsh, ya isa haka. Kar kiyi ciwon kai kuma Princess. Ya Isa haka" ta dago jajayen idanunta tana kallon sa tace "babu abinda nayi masa, wallahi babu abinda nayi masa" yayi kissing idanuwanta da goshinta yace "I know, I know. Zan same shi kinji? Zai gaya min dalilin da yasa yayi abinda yayi idan kuma bashi da dalili zan dauki mataki akansa. Ki daina kuka dan Allah" ta dan ture shi daga jikinta tana cewa "ka ga fa a yadda ya shigo ya ganni, in gurin matarsa yazo ba zai tsaya a pao ya aiko a kira ta ba? Ko kuma yayi mata waya ta fita? Ko kuma daya shigo ya ganni a haka ai sai ya koma ko? Sannan kuma ya ce min munafuka, munafuncin me nayi masa? Me nayi masa?" Ta sake saka kuka. Ya ji ransa ya kara baci, bai san me zai ce mata ya lallashe ta ba, bai san wanne kalami zaiyi amfani dasu wajen nuna mata bacin da ransa yayi akan abinda twin brother din nasa yayi ba. Sai kawai ya jawo ta ya hade bakin su guri daya, wannan ya tsayar da kukan da take yi sannan a hankali tayi relaxing jikinta ya saki. Ya sauke ta yabi ta siraran stairs din da zasu kai ka har kofar bedroom dinsa, ya kaita ya kwantar da ita a kan gado ya lullube ta sannan ya sauka da sauri, zuciyarsa tana kuna cike da kishin matarsa.
Part din Hassan ya dosa da sauri, ya bude kofa kuma sai ya tsaya yana kallon hoton Hassan din da yake rataye a gurin, his twin brother, ya kuma tuna da maganar Annabi Muhammad SAW da yayi hani da yanke hukunci a yayin da mutum yake cikin fushi. Sai kawai ya saki kofar ya koma da baya. Dama fita zaiyi ya shiga da niyyar ya sanar da Fatima cewa zai fita, bai ma san suna tare da Ruqayyah ba balle ya saka ran ganin Hassan. Dan haka motarsa ya dosa ya tarar Adam har ya tayar da ita ya shiga suka fita.
Hassan yana dauka Ruqayyah mota ya kaita, tana ta dan kuka kadan kadan hannunta akan marar ta ya zagaya ya kunna motar suka fita daga gidan "Allah sarki baby na, wallahi ina sonka kar ka tafi dan Allah" ya dan kara gudun motar yana jin ransa yana kara baci, in wani abi ya samu babyn sa ba yar sarkin kano ba ko yar sarkin macca ce Fatima sai jikinta ya gaya mata. Ta samu yarinya yar karama tana neman ta cuceta saboda bakin hali irin nata. Saboda tana mata bakin cikin ita ta samu ciki ita bata samu ba. Dama tun farko sai data gaya wa Hussain ya kuma ja masa kunne akan auren yarinyar nan saboda ta riga ta saba da samun duk abinda take nema and now she can't stand ganin Ruqayyah da ciki ita babu. Tun kafin auren yayi nisa har ta fara nuna hali.
Suna zuwa asibiti aka karbi Ruqayyah aka shiga da ita, Hassan yana rike da hannun ta doctor ya gama duba ta yayi mata tambayoyi akan abinda take ji sai tace marar ta ce take mata ciwo, ya tambaye ta wanne irin ciwo sai tace "bazan iya yi maka bayani ba, ciwo dai sosai kamar zan mutu" doctor yayi murmushi yace "kar ki zama raguwa mana, in lokacin haihuwar yazo kuma ya za'a yi kenan? Kuma ba zaki mutu ba kinji?" Ya saka ta kwanta yayi mata scanning yana duba lafiyar cikin yace da Hassan "Babu wani problem da na gani gaskiya, duk babies din lafiya kalau suke mahaifar ma haka" Hassan yace "babies?" Doctor yace "eh fa, double gestation na gani. But zaku iya dawo wa after two weeks ku sake confirming, but am sure" Hassan ya bude baki cikin murna, yana jin duk fushin sa yana tafiya. Blessing often blessing. Allah ya na sonshi sosai babu abinda zaiyi masa sai godiya dan shi kam duk burikan sa na duniya suna ta cika.
Doctor din ya tambayi abinda yasa Ruqayyah ciwon marar sai Hassan yayi masa bayani kamar yadda Ruqayyah ta gaya masa, likitan duk ya gama dube dubensa bai ga problem ba amma sai yace su koma gida on bed rest, ta daina yin zirga zirga sosai ko daukan abi mai nauyi ko makamancin haka, amma zata iya yin normal tafiya just dai kar ta gajiyar da jikin ta sosai. Daga nan ya rubuta mata pain reliever da prenatal vitamins ya sallame su. Har suka dawo gida still tana kwance tana dan complain dama sama, har dakinta Hassan ya kaita ya kirawo Sumayya da sai a lokacin ta tashi daga bacci ya gaya mata abinda ya faru sannan ya fita da kansa ya siyo mata drugs din.
Hussain suna mota tare da Adam, abinda ya faru a gida yana ta yi masa yawo akai and even without bincike kawai zuciyarsa Ruqayyah take pointing at. Ita ce a tsakiya, duk abinda ya faru ta sani dan tana tare da Hassan kuma tana tare da Fatima. Ya tuno maganar da yaji Hassan ya fada wa Fatima "stay away from my wife" ya juya kansa, tabbas koma menene Ruqayyah is at the bottom of it. Yasan Hassan baya son Fatima amma bai kai har hakan ba, dan shi ya dauka ma wannan maganar ta wuce, to ko dai Ruqayyah tace da Hassan Fatima tayi mata wani abu ne? Gabansa ya fadi tunawa da yayi da cikin jikin Ruqayyah. Yes, that must be it. Cikin nan shi ya saka Hassan reacting the way he did. But me tace an yi mata? Dan shi har cikin zuciyarsa yasan Fatima ba zata yi harming pregnant woman intentionally ba, sai dai in a rashin sani. To ko sharri tayi mata?
Ya kalli Adam yana tunanin sake gwada sa'ar sa ko zai samu wani bayani a gurin Adam din. Yace "Adam, kana tunanin Ruqayyah is capable of sharri?" Sai yaji Adam ya danyi dariya yace "ohh dariya ma na baka?" Adam ya yi shiru yana kallon reflection din Hussain ta center mirror, yana yinsa yana nuna cewa he is serious. Adam yayi gyaran murya yace "sorry sir" Hussain ya kuma cewa "amana zan karbi maganar ka, nayi maka alkawarin ko Hassan bazan gaya wa ba balle wani. Ina so inji ne kawai for the mental health of my family" Adam ya saje yin shiru yana jujjuya maganar a ransa, sannan yace "ranar da na fara haduwa da Ruqayyah da Sumayya sharri Ruqayyah tayi niyyar yi min. Ta dauka bana jin hausa sai take shiryawa yar uwarta plan din yadda zasu damfare ni naira hamsin. Yar uwarta taki yarda kuma ta nuna mata rashin dacewar hakan. Bata ci nasara ba, wannan yasa har yau take jin haushina duk da cewa banyi mata laifin komai ba. Dan haka your answer is yes, Ruqayyah is capable of hada sharri" Hussain yayi shiru yana tunani sannan yace "kana ganin zata iya hada sharrin da zai raba aure? Ko ya raba yan uwa?" Adam ya girgiza kansa yace "ban sani ba sir, but ni sharrin data yi niyyar hada min irin wanda defending on my destiny zai iya sawa mutanen unguwarsu suyi min duka, ko kuma su kona min mota, ko kuma su hada dani da motar su kona, kowanne daga cikin wadannan zaibiya jawo rikicin tsakanin kabila wanda zai iya jawo asarar rayuka da dukiyoyin daruruwan mutane. So ina ganin haddasa husuma a tsakanin mutum biyu ba wani abu bane a gurin ta".
Hussain ya koma ya zauna sosai yana kokarin digesting yadda zai bullowa maganar amma sai yaji ya kasa, Hassan yayi masa shield, sannan ga cikin da yake jikin Ruqayyah.
Sai yamma ya dawo gida, shima kuma ba wai dan ya gama abinda suke gabansa ba sai dan yana son yazo yaga halin da Fatima take ciki duk kuwa da cewa bayan kowacce awa yana kiranta, kuma daga muryar ta ya fahimci cewa ta daina kukan sai dai still akwai miki a ranta, mikin da dan uwansa ya dasa mata. A dining room din su ya sameta, ta cika masa shi da kayan abinci kamar yadda itama taci kwalliya kamar babu abinda ya faru. Ta tare shi tana zura hannunta cikin nasa. "Welcome Mi Amour. I made your favorite dises for you" kyawun fuskarta kadai ya saka shi yaji rabin damuwarsa ta tafi. Yayi murmushi yana kokarin kissing dinta, ta juya kanta gefe tana dariya "zaka bata min kyalliya ta tun kafin ka gama gani" ya juyo fuskar yana kare mata kallo sannan yace "na gama gani, can I kiss you now please?" Tayi dariya sannan ita tayi kissing dinsa da kanta, sai kuma ya hana ta janyewa sai da ya sake ta dan kansa sannan yace yana kallon ta idonsa cike da kaunarta "me yafi wannan dadi?" Tace "kiss din?" Yace "that included but ina nufin mutum ya dawo daga aiki ya tarar da kyakykyawar matar sa tayi masa kwalliya ta tare shi fuskarta da murmushi ga abinci ta jera masa, this is perfect, komai yayi dai dai my life is finally complete" ya bata fuska tace "complete? Tun yanzu? Tun kafin suzo?" Ya bude ido "ohhh kinga wannan kwalliyar taki ta saka ni na manta da babies dina ko? Wannan ko sunzo din in dai zaki cigaba da irin wannan kwalliyar to mantawa zan ke yi dasu" tace "hmmm really? Kai din kuwa? Duk ran da muka haihu a gidan nan ina jin ni kaina kaiyade min lokacin daukan jaririn zakayi" yace "kamar kin sani, dashi zan ke fita a mota, in bashi madara a office" suka yi dariya. Tace "to Baban baby, wanka ko abinci?" Yace "wanka ya kamata, but this food is so tempting har na kasa controlling appetite dina" ta sunkuyar ta dauko masa samosa guda daya a cikin wadanda ta jera da tayi arranging dinsu a shape din heart, a tsakiya kuma ta zuba tomato sauce din da tayi garnishing da vegetable. Ta saka masa a baki tace "kayi taste sai muje ayi wanka" ya cinye yace sai ta kara masa ta kara masa daya sannan ta jashi zuwa toilet yayi wanka, wanda rabi ita tayi masa dan cewa yake wai hannunsa baya kaiwa, anan aka karasa bata kwalliyar sannan suka fito suka shirya suka dawo gurin cin abinci, a nan kuma yayi ta hadama, komai sai yaci, ita dai tana tayi masa dariya tace idan tayi tumbi babu ruwanta.
Sai da suka gama cin abincin su, wanda akan cinyarsa taci nata, sannan yayi mata magana "Princess kiyi hakuri kinji? Akan maganar Hassan kiyi hakuri. Ba halin sa bane ba treating mutane that way ballantana ke da kike matata. Naso inyi masa magana dazu amma kuma raina ya baci sosai bana son in dora akan barnar ya shi ya riga yayi, na fi son in zanyi masa magana ya kasance maslaha ce zamuyi" ta gyada kai kanta a kasa tace "kar ka damu, dama na riga nasan baya sona tun kafin auren mu, amma bansan kiyayyar sa gare ni ta kai haka ba. Ka rabu dashi kawai, yace in rabu da matarsa ni kuma na barta har abada. Ba zance babu ni babu ita ba saboda matar dan uwanka ce ita sai dai bazan kuma nemanta ba sai dai in ita ce ta neme ni, bazan shiga gurin su ba but she is welcome to come here anytime. Shi kuma ka gaya masa kar ya kuma trying daga min hannu dan wata rana hannun sa zai iya gocewa ya same ni. Duk kanin mu kuma bama fatan haka ta kasance" Hussain ya girgiza kansa "I promise you Princess, hakan ba zata taba kasancewa ba kinji?" Ta danyi murmushi. Yace "zan je in ganshi in an jima. We will talk things out kinji?" Ta kuma gyada kai.
Hussain baya son ya shiga gidan Hassan suyi magana a can saboda bai son Ruqayyah ta shiga maganar su, ba kuma yaso taji mai zaice. Yasan kuma ko ya kira shi nashi part din ba zai zo ba dan haka ya tafi palon Aunty ya zauna, yasan duk dare yana shiga ya gaishe ta su danyi shawarwarin su. Dan haka ya kwanta akan kujera ya rufe idonsa yana jiransa. Ganin haka yasa aunty ta kora yammatan ta sama ita kuma ta zauna suna hirar dinner din da yake shiryawa ta family and friends na taya shi murnar bude sabon kamfanin sa, a lokacin yake gaya mata motocin da ya siya wa Fatima tare da Ruqayyah. Tayi murna kuma tayi masa godiya.
Sunanan a zaune Hassan ya shigo, ya kalli Hussain ya dauke kai ya gaishe da Aunty suka dan yi magana kadan sai ta tashi ta basu guri dan ta fahimci akwai dan tension a tsakanin su. Tunda basu saka ta a ciki ba kuma bata son ta saka kanta gwara ta barsu su warware kayan su. Tana tafiya Hussain yace "me Fatima tayi maka?" Hassan yace "wrong question, abinda ys kamata ka tambaya shine 'me Fatima tayi wa Ruqayyah?" Hussain "as far as I know babu abinda tayi mata face kokarin taimaka mata" Hassan yace "okay haka ta gaya maka? Taimakon nata ne ya kai Ruqayyah asibiti? Ko baka san cewa she is now under bed rest ba? A saboda Fatima?" Hussain ya bata rai yace "ban gane ba, dukanta tace tayi ko me?" Hassan ya bashi labarin duk abinda Ruqayyah ta gaya masa, har da shawarar da tace Fatima ta bata na cewa ta zubar da ciki bata isa haihuwa ba.
Hussain ya bude baki yana mamaki. Ko a mafarki bai taba tsammanin Ruqayyah zata iya wannan mugun sharrin ba kamar yadda bai taba tsammanin Hassan zai yarda da wannan maganar ba. Tabbas da gaskiyar Adam da yace "he should be very worried" .
Yace "and you believe that bro?" Hassan ya daga kafada yace "what's there not to believe? Kar ka manta Ruqayyah yarinya ce karama, only 18 years, bata san komai akan abinda duniya take ciki, I doubt it in tasan ma ana shan pills dan a zubar da ciki kamar yadda I so much don't believe zata iya hada magana irin wannan ta fada" Hussain ya dafe kansa yace "and you believe Fatima zata iya yin abinda Ruqayyah tace tayi mata?" Hassan yace "sosai. Ta fita shekaru ta fita wayewa ta fita wayo da sanin duniya" Hussain ya gara zamansa yace "I dated Fatima for full four years kafin in aure ta, nasan 90 percent na halayen ta kuma nasan duk abinda ka fada na cewa tana da shekaru, wayewa, ilimi, wayo, dabara duk yes tana da su amma kuma hakan bai sa ta zama mai munanan halayya ba. Fatima tana da kirki fiye da yadda kake tunani, yes, tana da flows dinta kamar kowa amma ba zata taba cutar da mace mai ciki ba, ko a mafarki ba zata aikata haka ba. Duk da nasan ka sani, maybe wani abu ne yaje rufe maka idonka baka gani amma nasan kasan cewa age is just a number, halayyar mutum bata da alaka da shekarun sa ko background dinsa ko ilimin sa ko yanayin tarbiyyar da aka bashi, wadannan duk suna shaping halayyar mutum ne amma ainahin halayyar da ita ake haifar kowa. Shi yasa tagwaye suke tashi da mabanbantan halayya duk kuwa da cewa sun samu komai iri daya. Bance Ruqayyah bata da hali mai kyau ba amma ina tuna maka da cewa baka san ko da kashi daya cikin uku na halayyar ta ba saboda wata uku da sanin ta ka aure ta kuma ba.... "
Hassan ya daga masa hannu, "nasan cewa baka son Ruqayya, tunda ka fada min haka tun farko amma kar kayi kokarin tura laifi kanta saboda kana son ka kare matarka. Idan baka manta ba in tuna maka, Ruqayyah saved my life. Ta saka rayuwarta a danger saboda tana son ta kubutar da rayuwar wanda bata taba gani ba a lokacin daga danger. She could have lost her life a ranar nan saboda ni. Wannan kadai shi ya nuna min kyawun halayyar ta. Babu wanda zai aikata abinda ta aikata sai mutumin da bashi da son kansa, mutum wanda duniya bata gabansa, mutum mai kyakykyawar zuciya wanda ba zai iya harming wani ba, mutum.... " Hussain ya daga masa hannu yace "kasan wani abu bro? Tun ranar da Allah ya dawo min da kai gida ranar daka bani labarin taimakon da Ruqayyah tayi maka da kuma hanyar da tabi gurin taimaka maka din, tun a lokacin naji bata kwanta min arai ba amma ban taba sanin dalilin da yasa hakan ba sai yanzu da kake wannan maganar. Yes she helped you and I am very grateful for that. Amma inda matsalar take shine hanyar da tabi wajen taimaka maka din. In reality, idan yarinya karama kamarta wadda bata san komai na duniya ba mai bla bla bla ta shiga toilet taga mutum cikin jini yana neman taimako abinda ya kamata tayi shine taje ta taso mahaifanta ta nuna musu shi su taimaka masa, but Ruqayyah sai ta kama katanga ta haura ta fita. Taje ta yaudari manyan matured top criminals har ta dalilin ta police suka kama su. Ta haka musu rami suka rufta ciki. If her brain can work out that plan a cikin mintuna kadan Allah ne kadai yasan abinda brain dinta take shirya mata a yanzu. In