Showing 198001 words to 201000 words out of 300844 words

Chapter 67 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2108

abu ya dunkule a kirjin Sumayya, ya tokare mata hanyar da numfashi yake shiga hunhun ta. Ta mike tsaye tana kallon Aisha "tun jiya? Tun jiya da safe fa kika ce? Kuma ku baku yi tunanin ya kamata ku fada ba?" Tace "dama ita kadai taje zama, mun dauka idonta biyu ko dan bata son a dame tane ya sa ta rufe kofa, sai da muka ga duk abincin da muke kai mata bata tabawa sannan muka fara buga kofar kuma bata bude ba" ta share hawaye, "muna tsoron tayi mana fada ne shi yasa muke gudun damunta"

Cikin karkarwar hannu Sumayya ta dauki wayarta ta fara neman number din Hassan, shine a kusa shine namiji shi ya kamata ta fara kira, kuma shine zai bata izinin fita taga halin da yaruwarta take ciki. Sai dai tasan yana gurin kabarin Hussain ko zai iya daukan waya?

Bugu daya ya dauka "hello Noorie" bata kula da sunan daya kirata dashi ba tace "dan Allah kazo ka taimaka min" yadda yaji tashin hankali a muryar ta haka shima nashi hankalin ya tashi. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Me ya faru?" Cikin rawar murya ta fada masa abinda Aisha ta gaya mata, bai jira komai ba yace ta fita ta shiga gidan, ta kira mai gadi ko duk wani namijin da yake gidan tace inji shi yace su balla kofar dakin, shima gashi nan tahowa.

Kusan a tare suka je gidan, sai dai da yake shi namiji ne yafi ta doguwar kafa sai ya wuce ta zuwa saman, sanda taje already yana kokarin balla kofar amma being kofar da Hussain ya saka sai taki balluwa. Da sauri ya fita, a lokacin Sumayya ta gama rikicewa kuka kawai take yi tana buga kofar amma babu ko alamun Ruqayyah a ciki, a hargitse ya shiga dakinsa ya binciko key din part din Hussain da ya ajiye sannan ya dawo ya shiga part din Hussain ya nemo spare keys din gidan gabakidaya sannan kuma suka fara neman key din dakin da Ruqayyah take ciki.

A ransa yana cewa gidan da Ruqayyah take so fiye da shi shine zai zama ajalinta in tayi wasa, da kyar suka samu wanda ya bude kofar dakin sannan suka shiga.

Tana kwance a kan gado, idanunta a rufe, a gefenta da robar ruwa da sleeping pills. Da sauri Sumayya ta tafi kanta tana jijjiga ta, sai taga kamar ba Ruqayyan ta ba, kamar wata ramammiya mai kama da Ruqayyah. Hassan ya karaso yana janye Sumayya daga jikin Ruqayyah sannan a hankali ya dora hannunsa a gefen wuyanta yana so yaji heartbeat. Can ya jiyo shi da nisa, she is alive but barely.


*Unstable*

Sorry for the typos

Ya mike tsaye tare da ja da baya, sannan ya dauko wayarsa yayi dialing number din doctor dinsu, ya fita yana waya dashi, wannan ya sa Sumayya ta koma da sauri gaban Ruqayyah ta saka hannun ta a inda Hassan ya dauke nasa tare da kara dan yatsanta na daya hannun a kofar hancin Ruqayyah, ta jiyo heart beat din sannan taji hucin numfashin ta a hannunta amma bayan wannan babu alamar rai a tare da ita.

"Ruqayyah! Ruqayyah ki tashi dan Allah, ki tashi muyi magana dan Allah" tana jim Hassan ya dawo dakin yace "doctor yana zuwa yanxu" bata ce komai ba sai ya karaso ya dauki robar maganin yana karanta wa yace "maganin bacci ne, overdose tayi maybe" Sumayya ta gyada kai tana share hawaye tace "na gane shi, tun sanda ina jinyar ta a asibiti shi take sha kafin tayi bacci, bata iya bacci tsorata take yi duk dare" sai kuma ta fashe da kuka, tausayin halin da Ruqayyah take ciki take yi sosai, wannan wacce irin rayiwa ce yar uwarta ta dora wa kanta.

Tana tuno yarintar su da irin burikan Ruqayyah amma bata taba tsammanin cewa zata kai ta ga haka ba, bata taba tsammanin kaddarar su zata zama haka ba. Ta fara kallon fuskarta tana shafa kanta a hankali tana kiran sunan ta, ga dai kaya masu kyau a jikinta amma shi jikin bashi da kyau, ta rame fiye da tunanin Sumayya, dama kuma ita Ruqayyah bata da jiki sosai. Ta mayar da idonta kan kafarta marar lafiya taga yadda kafar ta kara motse wa ta yamushe kamar ma jini baya zuwa kafar.

Sai kawai ta fara karanto mata adduoi tana tofa mata a haka har doctor din ya karaso suka shigo tare da Hassan, suna shigowa Hassan ya dauki robar maganin ya mika wa doctor din suka yi maganganu sannan Hassan yazo ya kama hannun Sumayya ya daga ta tsaye sannan ya jata suka fito waje. Sai da suka fito palo sannan ya saki hannun, tayi sauri ta saka hannun a cikin hijab tana mummurza shi tana sunkuyar da kanta kasa, ya jingina da jikin bango yana kallon ta yace "wai dan na rike hannunki shine kike wannan abin?" Ta girgiza kai da sauri, amma a ranta tasan haka ne, ita wani namiji bai taba kama hannun ta ba kuma bata taba zaton cewa Hassan mijin twin sister dinta shine zai zama na farko ba.

Da tago kai suka hada ido taga har yanzu ita yake kallo yana murmushi, sai taja hijab dinta ta rufe fuskarta, ita bata san ya akayi yake tsokanar ta har yake murmushi ba bayan ga halin da Ruqayyah take ciki, yana nufin wai shi yanzu bashi da wani concern akan Ruqayyah? Ko babu komai ai sister dinta ce kuma uwar yayan sa. Tace "me Doctor din yace?" Ya dan daga kafada yace "yace zata warke, zai dai duba ta yanzu amma yana tunanin sai an kai ta asibiti sunyi flushing system dinta, in akwai sauran maganin duk zasu fitar mata sannan su saka naya drip sabida ta samu nourishment tunda ta kwana ta wuni bata ci abinci ba sannan kuma a jira sanda zata farka"

Sumayya ta gyada kai hawaye yana tarar mata a idonta tace "me yasa zata yi overdose?" Ya daga kafada yace "Allah masani, maybe ta gaji da duniyar ne" Sumayya ta girgiza kanta da sauri tace "no! She will never do that. Ni nasan Ruqayyah fiye da kowa" yace "really? I don't think so" ya mika mata hannu "ki zo mu tafi gida" sai ta girgiza kai "ina so in zauna a gurinta, in za'a kaita asibitin ma ina son in bisu can din" ganin kallon da yake mata ya saka ta sunkuyar da kanta tace "in ka amince".

Yayi ajjiyar zuciya, tabbas yasan akwai soyayya da shakuwa sosai a tsakanin Sumayya da Ruqayyah, amma shi yanzu Ruqayyah tsoro take bashi, yana gudun kar ta cutar masa da matarsa akan kishin da take iƙrarin tana yi duk da yasan cewa na karya ne, ita da bakinta ta gaya masa bata sonsa, ta aure shine saboda tana tunanin mai kudi ne shi. But, ba zai raba hanta da jini ba sai ya tafi ya zauna akan kujera yace "we will wait together then. Bazan taba barin ku tare daga ke sai ita ba" ta biyo shi itama ta zauna tana kallon sa tace "wai kana tunanin Ruqayyah zata iya cutar dani? She is my twin sister, she will never hurt me" yace "she already did hurt you, not once not twice, wanda na sani ma kenan, Allah ne kadai yasan sau nawa ta cutar da ke, bana fatan ta sake wani. I won't wait har sai ta sake kafin in raba ku"

Tace "nasan akan Adam kake wannan maganar, ita a nata juyayyen tunanin tana ganin kamar taumako na tayi data raba ni da Adam" ya daga mata hannu yace "mu bar maganar Adam please" tayi mamakin yadda ya hade rai, wato kishi yake yi kenan ko mene ne? Amma sai tayi shiru ta bar maganar kamar yadda ya bukata.

Suna zaune sai ta dauko wayarta zata kira Inna ta sanar da ita sai ya hana ta "menene amfanin gaya mata? Hankalin ta ne zai tashi kuma Baba ba zai barta tazo ta ganta ba, ki bari kawai in kin tabbatar ta warke sai ki gaya mata daga baya yadda hankalin ta ba zai tashi ba" ta gyada kai cikin fahimta, tabbas Hassan ya san halin baba kuma yasan cewa in dai har Ruqayyah bata yi abinda yace ba to ba zata shiga gidan sa ba kuma Inna ma ba zata shiga nata gidan ba ballantana shi.

Suna nan zaune doctor din ya fito ya sauka kasa sai gashi ya dawo da kujerar marasa lafiya, Sumayya ta tashi tataimak masa suka dora Ruqayyah akai sannan suka kama shida Hassan suka sauka da ita kasa, doctor din yana cewa "akwai problem gaskiya, I tot zan iya farkar da ita tun anan amma abin ya gagara, dole zamu tafi da ita za'a yi mata some tests.

Nan take hankalin Sumayya ya kuma tashi, a dole Hassan ya dauke ta a mota suka bi baya ambulance din da doctor din yasa Ruqayyah a ciki suka tafi asibiti suna bayar da sakon cewa idan yara sun dawo su tafi gidan Aunty. A asibitin anyi duk abinda za'a yi dan ganin an tashi Ruqayyah daga bacci amma abin ya gagara, suna can suna ta abu daya har yamma har aka yi sallar magrib sannan ta farka tana jinsu suna ta maganganu can nesa, babu hearing aid dinta dan haka bata fahimtar abinda suke cewa, sai ta bude idonta a hankali ta sauke shi akan Sumayya da take tsaye suna magana da wata nurse akan tests din da doctor din ya rubuto wa Ruqayyah, yawancin su akan lafiyar kwakwalwar ta.

Ruqayyah ta mayar da idonta ta rufe sannan da dan karfi tace "me kike yi anan?" Sumayya ta juyo da sauri tana tahowa inda take sai Ruqayyah ta daga mata hannu tana yi mata alamar ta dakata daga inda take "babu ni babu ke. Maci amana. Kamar yadda kika ce babu ke babu ni saboda adam to nima babu ni babu ke saboda Hassan" Sumayya ta tsaya daga inda take ta kasa karaso wa ballantana tayi kokarin kare kanta. Duk da tasan ko tayi maganar ma Ruqayyah ba jinta zata yi ba tunda babu hearing aid a kunnenta.

Ruqayyah ta dafa gado ta mike zaune, tana jin jikinta wani iri sannan kuma kanta yana wani mugun sarawa kamar zai tsage biyu, ga cikinta kamar an yashe duk abinda yake ciki. Idonta da yake cike da tsana akan Sumayya, bata taba tunanin akwai ranar da zata zo wadda a cikin ta zata tsani Sumayya ba amma sai gashi yau ranar tazo. Ta dauke kanta ta daina kallon ta cikin tsawa ta kuma cewa "ki fita daga nan nace. Bana son ganin ki ba tsane ki na tsani kowa na tsani komai, bana bukatar ku babu ni babu ku kar ku sake nema na kar ku sake zuwa inda nake kar ku saje tunanin ma akwai wata alaka a tsakani na da ku"

Sumayya ta karasa da sauri ta kama hannunta sai ta ture ta da karfi, dai dai lokacin da Hassan ya shigo, kallo daya Ruqayyah tayi masa ta juyar da kanta gefe hawaye masu zafi suna zubowa daga idon ta.

Gani tayi yayi mata kyau, irin kyan da bata taba tunanin yana dashi ba, irin kyan dabata taba gani a gurin sa ba sanda yana nata sai yanzu da ya zama ba nata ba tukuna. Sanda yana nata bata kallon sa, wadansu take kalla shi yasa bata taba zama ta yabi surar sa ba, kamar yadda gidan Hussain kafin ya zama nata take ganin sa kamar shine aljannar duniya yanzu kuma daya zama nata sai ya koma mata kamar makabarta, sanda bata da kudi kuma sai ta ke kallon masu kudi a matsayin wadanda basu da wani problem a duniya, yanzu kuma da tayi kudin sai taga a yanzun ne ma problems suka fara mata.

Kaicho....

Hassan yazo da sauri ya rike Sumayya yana janye ta daga kusa da Ruqayyah, ya saka hanu ya goge mata hawayenta a kunnenta ya rada mata "let's go home".

Har sun kai bakin kofa Sumayya ta sake juyowa ta kalli Ruqayyah, sai suka hada ido and she can see the heart break da yaje idon Ruqayyah and her heart went out to her. Har suka je gida basu yi magana da, suna tsayawa sai Sumayya ta roki Hassan ta shiga gidan Ruqayyah ta saka aisha ta hada kayan da ta san Ruqayyah zata bukata a asibiti ta hada da hearing aid dinta sannan ta saka driver ya tafi da ita asibiti ita kuma Ruqayyah ta dawo gida.

Dakinta ta wuce direct tayi alwala tayi sallah sai ta samu kanta da kuka a sujjadar ta tana rokawa Ruqayyah dai-dai to a rayuwarta. Sai data idar sannan ta shiga toilet tayi wanka. Tana fitowa suka hada ido da Hassan a zaune a bakin gadonta, a guje ta juya ta koma bandakin tare da rufo kofa, dariya ta kama Hassan, dama yana sane ya zauna dan yaji motsinta a toilet din yasan kuma zata fito babu kaya. Sai yaja pillow ya kwanta kafafuwan sa a kasa hannayensa a rungume a kirjinsa idonsa akan toilet din. Ya san dole zata fito shi kuma yana nan yana jira.

Ta jima a tsaye tana mayar da numfashi, Inna lillahi, yau ya zata yi? Ta yi ta dube dube babu wani abu da zata rufe jikinta dashi, towel din nan na jikinta shikenan sa dan ko kaya dama bata shigo dasu ba da towel din ta shigo. Ta jingina a jikin kofar tana tunanin abinda zata yi, ta jima a haka sannan ta leka ta ramin key ta hango shi yana nan a kwance akan gado. Ta dafe kanta tana jin ana kiraye kirayen sallar ishai, ga sanyin toilet din ya fara ratsa ta tasan kuma in tayi wasa yanzu zata kama zazzaɓi.

Ta danyi knocking kofar toilet din sannan ta dan bude kadan. "Dan Allah yaya Hassan ka miko min zani da hijab" ya gyara kwanciyar sa yace "saboda me?" Tace "saboda Allah. Wallahi sanyi nake ji, zanyi mura da zazzaɓi" yace "to ki fito mana ki shirya, ni ina ruwa na dake" taji kamar zata yi kuka tace "ba zan iya shiryawa a gaban ka ba, dan Allah ka tafi dakin ka" yace "nan ma dakina ne, dan dakin matata ne" tace "ai Allah nace maka. Kaga ana kiran sallah zaka rasa jam'i" yace "shikenan sai muyi tare, in mukayi tare ma zamu samu ladan jam'i ni dake"

Ta dora goshinta akan kofar idonta a rufe tana jin sanyi yana ratsa ta tace "dan Allah dan Annabi daddyn Hussain ka fita, wallahi sanyi nake ji" ya mike zaune yana kallon toilet din yace "to ke me yasa ba zaki fito ba sai na fita, ni ba mijinki bane ba?" Tace "kunyarka nake ji Allah, ba zan iya fitowa babu kaya a gaban ka ba" yadda tayi maganar kamar zata yi kuka yasa ya ji tausayin ta, ya mike yai kamar zai shiga toilet din, yaga ta rufo kofar da sauri har da murda key sai yayi dariya yace "na fita to. A shirya lafiya, amma zan dawo".

Sai data leko ta tabbatar ya fita sannan ta fito da sauri taje ta murda key din dakin. Ta jingina da jikin kofar tana ajjiyar zuciya, a ranta tana rokon courage daga gurin ubangiji. Ta shirya cikin plain doguwar riga budaddiya sosai mai adon stones a wuyanta kuma hannayenta. Mai kawai ta shafa sai turaruka a jikinta amma ko hoda bata shafa ba ta saka hijab tatayar da sallah, tana idarwa ta ji ya murda kofar amma ya jita a rufe sai ya wuce. Ta tashi ta nade sallayar sannan ta dan kara turare a jikin ta sannan ta bude kofar sau suka hadu dashi yana hawowa da basket din abinci a hannunsa, daga dukkan alamu daga gidan Aunty aiko musu.

Ta karba daga hannunsa da sauri, ya juya yana cewa ki kai mana dakina" sai ya juyo kuma yace mata "yau dinner in bed zamuyi" daga haka ya koma kasa da sauri. Tayi kamar zatayi kuka amma sai ta wuce ta tafi dakin nasa ta ajiye basket din tare da budewa tana ganin abincin da yake ciki amma sai taga gasashshiyar kaza ce da aka yayyankata aka kuma bade ta da yaji, tana budewa kamshinta ya cika dakin gaba kidaya. Ta bude dayan food flask din shi kuma ta tarar da farfesun kifi mai kyau, daga dukkan alamu yanzu aka sauke shi dan turiri yake yi sosai kamshinsa yana chakudewa tare da na kazar.

Taji an bude kofar dakin an shigo, sai tayi sauri ta rufe ta mike tsaye tana rarraba ido, ya bita da kallo sannan ya kalli basket din yace "kwadayi ko? Daga baki sako sai kizo kina budewa?" Taji kunya ta kamata sai ta wayance da cewa "ina yarana? Ka aika a dauko su please" ya zauna yana ajjiye drinks din hannunsa a kan table yace "kina da number din Aunty ai, ki kirata kice ta dawo miki da ƴaƴan ki" sai ta tura baki, wato magana ya gaya mata kenan.

Ta zauna akan kujera, rnata yana son kifin nan data gani, kuma tana son tayi masa maganar Ruqayyah ta gaya masa abinda nurse ta gaya mata akan case din Ruqayyah, tana so ta gaya masa abinda nurse ta tsegunta mata na cewa doctor yana tunanin Ruqayyah ta hadu da mental related disorder. Amma kuma ta lura tun da aka fara zancen aurensu har akayi har yau kuma bai taba yi mata maganar Ruqayyah ba, bai ma taba ambaton sunan Ruqayyah ba.

Shin ita tayi masa ko ta barshi kawai tunda baya so........? Amma mental health din Ruqayyah ai abu ne muhimmanci ko?

Amma sai ta kasa samun courage din yi masa maganar.

Ta mike zata fita yace "ina zaki? Ki zauna inyi wanka in fito sai in sammiki nama ki ci, dan naga kina ta hadiyar yawu" ta dan bata rai "ni na koshi, ni bana cin nama dama, baka sani bane ba" ya fara cire kayansa, ta rufe idonta, yace "amma ai kina cin kifi ko?" Ta girgiza kai "shima bana ci" ya zo gabanta ya tsaya "to me kike so ki ci?" Idonta yana rufe tace "bana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login