Showing 234001 words to 237000 words out of 300844 words

Chapter 79 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2654

in suka balla kofar dakin babu abinda zai hana su balla kofar ban dakin. A jikinta taji cewa this is the end of her.

Ta kama bango ta mike da kyar, karkarwar jikinta shi ya kara wa mikewar tata wahala, ta dafa tagar toilet din tana girgiza bars din da suke jiki, babu abinda zai iya wucewa ta ciki in ba hannayenta ba, ko da ace zata iya wucewar ma ta yaya zata iya hawa tagar da wannan kafar tata mai suffar lagwani, in ta haura ma kuma ina zata je? Kofar shigowa gidan guda daya ce kuma ta can suka shigo, da wacce kafar zata gudu ta tsere musu? Waye zai taimaka mata?

Sumayya? Ta bar wayarta a falo, ko da wayar ma har yau number din Sumayya bata shiga in ta kirata. Har yanzu fushi take yi akan ta maganar gatawa iyayen Adam inda yaje da tayi, sai ta tuna cewa ashe yanzu abin ya wuce nan, ashe tayi sanadiyar da aka rufe Adam din ma gabaki daya, duk dadai tasan by now an fitar da shi. Amma yanzu ita tamkar wanda ya fada ruwa take, taimako take nema ta kowacce hanya, ko bakin tako bi ata miko mata karba zatayi.

"Sumayya!" Ta dage tun karfin ta tana kwalla mata kira, koma menene ta zama, koma wacece ita a yanzu ta tabbatar Sumayya zata taimaka mata a irin wannan yanayin "Sumayya, Sumayya ki zo ki taimaka min dan Allah zasu kashe ni. Sumayya! Sumayya dan Allah ki zo. Sumayya!" Amma Sumayya bata jiyo ta ba, saboda Sumayya bata gidan bata ma unguwar ta tafi gidan su tare da yara gabaki daya, sai ita kuma ba yar aiki ne da ita ba dan haka babu wanda yaji yo Ruqayyah. Aunty ma bata nan sun tafi kano ita da Hassan, Zulaihat ma taje gidan friend dinta, sai mai aikin su wadda cikin ikon Allah taji ihun Ruqayyah bayan taji hayaniyar mutane kuma mai gadi ya gaya mata abinda yake faruwa, sabuwa ce ita dan haka bata san takamaiman gaskiyar abinda yake faruwa ba, dan haka ta dauko wayarta hannu yana rawa ta kira Sumayya ta gaya mata abinda yake faruwa.

Ruqayyah ta saki karfen tagar tare da zamewa kasa saboda jikin ta ba zai iya cigaba da dauka ta ba saboda karkarwar da yake yi, ta saki kuka mai karfi, "wayyo Allah Sumayya ki zo ki cece ni" sai kuma ta mike zaune da karfi tace "Hassan!" Ita kanta bata san sanda ta ambaci sunan ba kuma batasan dalilin da yasa ta fadi sunan ba, bayan Fatima, Hassan shine mutum na karshe da zai taimaka mata.

Jin an fara bugun kofar toilet din yasa ta zabura ta koma can karshen toilet din, a coner ta rakube tare da jan guiwar ta ta hade da kirjinta, hakoranta na sama na dukan na kasa, a zuciyarta tana rokon Allah ya dauki ranta kafin su cimma ta, dan ita zancen wutar nan shi yafi komai dagamata hankali. Tayi bitar rayuwarta tun daga sanda ta bude idonta zuwa yanzu sai taga cewa idan da zabi za'a bata ace wanne stage din ne tafi so, wanne ne tafi kasancewa cikin farin ciki da zata dauki lokacin da take gidan su, lokacin da suke zuba wake da shinkafa a tray su ci tare ita da siblings dinta wani lokacin ma har tare da Inna suke ci.

Those were the happiest days of her life............Those where the good old days

Rayuwar ta da Hassan would have been good too, but duk a zamanta da Hassan hankalin ta baya kanshi kuma baya kan auren, hankalin ta yana wani gurin daban. Ta tuna da ƴaƴan ta, ƴaƴan da sai ta taga take leken su lokacin tana sama, yanzu kuwa sai dai wani lokacin in gari yayi shiru sosai sai taji muryoyin su suna wasa da dariya. Tasan in ta mutu ma ba zasu damu ba, tasan yadda mutuwar tata zata kasance ma ba zata dame su ba, tasan ko nan gaba ba zasu yi missing dinta ba musanman in suka girma suka fahimci abinda tayi, in suka fahimci ta zabi kudi maimakon su, ko addu'a ma tasan ba zasu ke yi mata ba duk kuwa da cewa zata bukaci addu'ar sosai. Amma anya akwai sauran wanda ya rage wanda zai yi mata addu'a kuwa?

Daga cikin dakin taji ance "idan kofar ba zata ballu ba ku saka mata wuta, idan mu ba zamu iya shiga mu tarar da ita ba ai wuta zata iya shiga"


***************************

Hassan ne a cikin mota tare da Aunty, tun daga kano suka taho suna ta nishadi suna hira da dariya, Aunty har ta fara lissafin yadda bikin Zulaihat zai kasance da irin taron da zata shirya "irin wanda ba'a taba yi a gidan ba" ta fada dramatically. Hassan yayi dariya, "wato bikin auta ko aunty? Gashi kuma autar aunty zata auri dan sarki" Aunty tace "tabbas, Zulaihat mai yayye da yawa, yar gatan dangi" yace "amma fa ina tausaya miki aunty, in Zulaihat ta tafi zaki ji babu dadi. I mean saura ke kadai fa kawai duk girman gidan nan" tace "Hajiya yaya zanje in dauko a Gombe, sai kuma in nema a dangi a bani rikon yammata ko biyu ne haka" yace "ohh na dauka wai ko zaki.......ina nufin kema zaki.......kinga ai yanzu babu nauyin kowa a kanki zaki iyayin auren ki ba tare da damuwa ba"

Ta dauki jakar hannunta ta dake shi da ita a kafada, ya sosa gurin da hannu daya "ouch Aunty, driving fa nake yi" tace "mara kunya fitsararre" yace "Allah ya baki hakuri tunda ba kya so. Wai dama tayi ne nayi miki" ta harare shi tace "bana so din" sai kuma suka yi shiru hankalin sa yana kan traffic din dasuka tarar, can daga baya sai yace "da Hussain yana nan zai ji dadin wannan hadin auren na Zulaihat" sai tayi murmushi, a ranta tana hasko yadda fuskar Hussain take in yana farin ciki tace "sosai, zaiyi murna sosai. Allah baiyi zai gani ba, Allah ya kai rahama kabarin sa"

Hassan yace "ameen" sai kuma yace "Aunty, akan maganar nan gabaki dayan ta, me kike tunani aunty? Me kike gani? Kina ganin dan Hussain yana da rai ko kuma Ruqayyah ta kashe shi da gaske? Sumayya tana ce min ita bata yarda Ruqayyah zata iya kashe baby ba" aunty ta girgiza kanta tace "ban sani ba Hassan. Babu abinda zan iya cewa akai. Babu wanda ya gani, babu wanda yaji, babu wanda ya tabbatar. Shi kuma zato zunubi ne ko da ya zamo gaskiya. Kamar yadda mai martaba sarki ya fada, zata iya yiyuwa Fatima ta haifi dan babu rai tunda accident suka yi. Zata iya yiwuwa Ruqayyah bata ma san sanda Fatima ta haihu ba. Za kuma ta iya yiyuwa ta kashe dan da gaske. It can be anything. Babu yadda zamu yi mu tabbatar idan har ba Ruqayyah ce da kanta ta furta da bakinta ba. Dama ina so inyi maka magana akan maganar nan Hassan, ya kamata ka sakawa zuciyarka ruwan sanyi kamar yadda Fatima ta janye maganar nan kai ma ka janye ta, ko ba da komai ba ko dan Sumayya. Sumayya tana dauriya fa sosai. Ka tuna yadda suke ita da yaruwarta da, kafin ka auri Ruqayyah, ya kamata kake sanyaya zuciyar ka ko dan kayi mata alkunya dan duk munin halin Ruqayyah dole Sumayya zata ji wani abu a ranta in aka muzanta ta"

Can kasan makoshin sa yace "insha Allah Aunty, an daina" tace "yauwa. Kamar yadda sarki ya fada, in muna da rabon ganinsa zamu ganshi, in bamu ganshi anan ba zamu ganshi a can. Kowa da kaddarar rayuwarsa, babu wanda zaiyi wa mutum wani abu sai in Allah dama ya nufa cewa hakan zai faru. Idan har yana raye to kaddarar sa bata tare damu, tana wani gurin daban. Idan lokacin da kaddarar mu zata hadu yayi, zaka ganshi da kafafuwan sa yazo har gaban mu"..

A lokacin suka shawo kwanar gidan, taron mutanen da ya gani a kofar gidan Hussain suna ta hayaniya shi yasa ya daga kafar sa yana salati "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, kar dai rigima ake a garin nan bamu sani ba" aunty tana kallon taron mutanen ita ma tace "amma tun a hanya ai bamu ga alamar komai ba, gidan Hussain suka shiga, subhanallah, Hassan fita ka gani me yake faruwa" ya girgiza kansa yana lura da sandunan da suke hannun wasu daga cikin mutanen. "Bara in shiga dake gida first aunty, in kin shiga ki rufe kofa kar ki budewa kowa" Sai daya shigar da ita cikin gidan ta sannan ya bar motar a ciki ya fito da sauri, ita kuma sai taji hankalin ta bai kwanta sosai da fitar tasa ba, kar fa wani abun ya same shi shima.

Da sauri ya shiga gate din gidan, mutane ne suna ta zage zage ta fashe fashen tagogi a falon, hankalin sa ua tashi ya fara ratsa su yana tambayar su abinda yake faruwa, wadansu daga cikin su suka gane shi "yallabai abinda kuka kasa muka zo zamuyi mu. Wannan munafukar matar har ta isa ta halaka jaririn Alhaji Hussain ta kuma zauna akan dukiyar sa sannan mu kyale ta? Gata can an banka wa shegiya wuta, taje lahira tayi bayani a can"

Hassan ya bude ido cikin tashin hankali, no matter how much he hate Ruqayyah bazai so a kashe ta for hussain's sake ba, ba zai so karshen ta ya zama haka ba ko dan saboda Sumayya da iyayensu da kuma yayansa. Ya ture mai gaya masa maganar ya wuce ciki da sauri yana tafiya yana kiran number din police, ya lura wasu daga cikin mutanen ba wai fansa suka zo daukar wa Hussain ba sata suka zo yi dan kowa ya dauki rabonsa a cikin kayan da suke gidan. A palon kasa ya hango dakin da aka balla kofar sa still da mutane a ciki, kafin ya karasa ya ga hayaki ya fara tashi yana cika dakin yana fitowa waje, yayi sauri ya ture su ya shiga dakin. Kofar toilet din dakin yaga tana ci da wuta.

Hankalin sa ya kara tashi "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me kuke yi haka? Menene haka" wanda yake leading mutanen, Hassan ya gane shi tsohon dan daba ne wanda tasu tazo daya da Hussain har ya mayar dashi makaranta, yace "yallabai barka da zuwa. Wannan gurgun magen zamu aika lahira ta tarar da oga Hussain acan sai tayi masa bayanin abinda tayi wa dansa" Hassan yace "oga Hussain? Kuna tunanin Hussain zaijidadi idan kuka kashe ta saboda shi? Waye wanda ya baku Shari'a a hannunku?" Yace "yallabai tunda tafi ƙarfin Shari'a ai mu bata fi karfin mu ba, gama mata aiki kawai zamu yi kuma wallahi ruwa ta sha"

Hassan yace "waye yace muku tafi ƙarfin sharia? Mu da kan mu fa muka yanje karar saboda muna ganin barin ta da Allah yayi mata hisabi yafi duk wani hisabin da wani alkali zaiyi mata. Littafin ku daban nata daban, in kun kashe ta alhakin ta yana cikin littafin ku, shin kuna son ranar lahira a debo tarin alhakin ta a jibga akan ku?" Ya bude ido Yace "ina! Wannan muguwar, ai zunubin ta yafi karfin kafaduna"

Hassan ya lura wutar ta fara cin karfin kofar ga hayaki yana kokarin hana su numfashi sai ya fita da sauri zuwa kitchen din gidan, yasan Hussain ya saka fire extinguisher a different parts na gidan including kitchens, ya dauko ta da sauri ya dawo ya fara fesawa kofar, yana ji suna ta bala'i wadansu suna nuna basu so hakan ba, wadansu kuma suna so ya gama kashe wutar su shiga toilet din du dauko ta tunda sunsan yanzu kofar ta zama weak.

Wutar tana mutuwa sai yayi sauri ya riga su shiga, a can karshen toilet din ya hango Ruqayyah a durkushe a corner, hannunta rike da hand spray, daga dukkan alama niyyar ta tayi amfani dashi kurin kashe wutar in tazo gurin ta sai dai shi yasan da wutar tazo babu yadda zata yi da ita, a matuƙar tsorace take, daga inda yake yana iya hango yadda jikinta yake rawa, ta jike sharkaf da gumi. Ya karasa gurinta sai yaga ta yar da abin hannun ta ta kamo rigarsa ta kankame shi. Ya juya yana kallon mutanen gurin yace "ba zan barku ku taba taba, not in my brothers name, na kira police zasu zo yanzu, kuyi sauri ku gudu kafin su karaso"

Wadansu suka fara kokarin fita wadansu kuma suka fara mita "yawa ne da Allah, kabarmu mu cika mata aiki kawai" yace "if you want her, you will have to come through me". Siren din police ne ya saka suka fara fita daga gidan a guje, a waje police suka jejjefa musu tear gas sannan suka samu suka shigo amma still wasu sunanan, wadanda suka matsa ma gefe suka je suka tsaya suna jifa da duwatsu. "Wallahi indai ba'a dau mataki akan ta ba sai mun kashe ta. Police din nan duk basu san aikin su ba wallahi. Ku bari a nuna muku yadda ake adalci. An nafsi bin nafsi"

A cikin gidan a cikin toilet, Hassan ya cire hannun Ruqayyah da yake jikin sa ya juyo da ita yana kallon fuskarta, she looks so different, shi sai yaga ma kamar tayi tsufa akan shekarun ta. Yace "I just saved your life. Kamar yadda ranar nan kika yi saving mine. You now owe me nothing. Munyi one one. Sai dai banbancin shine ni nayi saving dinki ne saboda Allah ba dan wani abu da nake saka ran zan samu daga gare ki ba. Saboda abinda ya kamata musulmi yayi kenan a duk lokacin da yaga ɗan uwan sa musulmi cikin bala'i sai yayi kokari ya taimaka masa dan Allah. Na gama nawa, yanzu tsakanin ki da police ne su zasu baki kariya" sai ya tura ta baya, ya manta ma gurguwa ce sai daya ga ta fadi kasa a dai dai lokacin da police suka shigo toilet din.

Bai koma ta kanta ba ya juya yana magana da police din, biyu daga cikin su da aka taho dasu mata suka je suka daga Ruqayyah, bai ga me zasuyi mata ba ya yi tafiyar sa. Yana fitowa daga gidan motar sa da Sumayya ta tafi da ita gida tana isowa kofar gidan dauke da Sumayya, Baba da Inna da Sulaiman. Sulaiman ne yake tukawa dan Sumayya ba zata iya ba dan gaba ki daya a hargitse take tunda aka gaya mata abinda yaje faruwa. Inna taci kuka ta gode Allah kafin su kara so.

Tun kafin motar ta gama tsayawa Sumayya ta bude kofa ta fito kamar zata fadi ta taho da gudu gurin Hassan, ya kamata "she is okay, she is okay. Allah yasa nazo da wuri da abin ba zaiyi kyau ba, amma she is okay yanzu tana hannun police" Sumayya ta rungume shi ba tare da tunanin inda suke ba tana kuka tace "mun gode, Allah ya saka maka da alkhairi" a dai dai lokacin police suka fito da Ruqayyah daga gidan, nan take mob din da suke jira suka bisu da ruwan duwatsu, sai da suka saka shield suka kare amma duk da haka sai da wani ya samu Ruqayyah a tsakiyar kanta, nan take jini ya wanke mata fuska, amma duk da hakan bata kasa ganin Sumayya rungume a jikin Hassan ba.

Da kyar police din suka saka ta a mota suka tafi, suna tafiya mob din suka bisu a baya, sai Hassan shima suka shiga mota tare da Baba da Sulaiman suka bisu a baya, amma an bar Sumayya da Inna a gida tare da Aunty. Asibiti ya kamata a kai Ruqayyah saboda jinin da take zubarwa a kan ta amma hakan ba zai yiwu ba dole aka tafi da ita police station saboda tsaro, acan aka samu akayi dressing din ciwon, wanda sai da aka aske tsakiyar kanta sannan akayi mata dinki.

A kofar station din kuma saboda yawan mutanen da suke gurin sai da commissioner yazo da kansa, ya kuma hana mutanen sa suyi wa mutanen komai, instead sai ya fito ya tsaya yayi magana dasu "me kuke so?" Wani yace "justice" yace "akan me?" Wani yace "matar data salwantar da rayuwar dan Hussain Aminu Abdullahi, ita muke so a yanke mata hukunci dai dai da laifin ta" commissioner yace "yanke hukunci ai aikin alkali ne bana police ba, mu aikin mu shine mu kama mai laifi kuma mu bamu kama matar nan da laifi ba, bamu ne muka kai karar ta ba, wadanda suka kai karar tata ma kuma da kansu suka janye karar. An riga an rufe file din shari'ar" wani yace "mu duk bamu gane wannan jawabin naka ba, mu kawai muna so a yanke mata hukunci" commissioner yace "to abinda zakuyi a shawarce shine kuje court ku shigar da sabuwar karar akan ta, sai ku gabatar da hujjojin ku in sun gamsar da alkali sai ya yanke mata hukunci. Amma ku sani. Matar nan takarda daga asibiti ta nuna cewa tana da matsala a kwakwalwar ta, dan haka ko kunje Court akwai yiyuwar ba zaku iya shari'a da ita ba saboda ba'a shari'a da mahaukaci" wani yace "in na mahaukaciya ce shikenan sai a barta a gari tana kashe mana yaya, ba akwai imda aka tanada saboda ajiye masu tabin hankali ba? Akaita can mana in dai da gaske bata da hankalin" commissioner yace "yauwa, yanzu kuka yi magana, in har haka kuke so ni zanyi muku jagora zuwa ga hukumar da abin ya shafa dan a tabbatar an killace ta a gida mahaukata kamar yadda kuka bukata" da haka aka samu suka yarda, amma suka ce in dai aka sake suka kuma ganin Ruqayyah a gari to duk abinda ya same ta babu ruwan su, kuma suma ba zasu bar shaidar da za'a kamasu da ita ba.

Sai washegari aka samu aka kai Ruqayyah asibiti aka duba ta properly, sai kuma a washegarin ne Sumayya da Inna suka samu damar ganinta duk da cewa har lokacin tana cikin matsanancin shock, Sumayya tayi kuka kamar babu gobe daga nan kuma sai ciwo, tayi mamakin Hassan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login