Showing 99001 words to 102000 words out of 300844 words
tunani sannan tace "I just want to be her. I want her husband, her house and her power" Sumayya ta zaro ido "Ruqayyah baki da hankali? Ta yaya zaki so mijinta bayan ga naki? Ta yaya zaki so gidan ta bayan ga naki? Ta yaya hakan zata yi wu?"
Ruqayyah tace "hakan ba zai yiwu ba na sani, na fahimci Hussain tun da nazo gidan nan na gane baya kaunata ko kadan, ko kallo ban ishe shi ba, bana jin ko babu Hassan a duniya Hussain zai kalli inda nake sai dai ko da niyyar taimako amma ba da niyyar aure ba. Wannan yasa na hakura dashi. Sannan nake so in mayar da Hassan shi ya koma Hussain din. So nake in mayar dashi CEO"
Sumayya tace "how?" Ruqayyah tace "niyya ta in hada rigima tsakanin Hassan da Fatima, ta hanyar amfani da abinda yake cikina saboda na fahimci irin son da Hassan da shi kansa Hussain suke yi wa cikina. So nake su yarda bata son abinda yake cikina yadda duk abinda ya samu cikin ita za'a yi zargi. So nayi in rura wuta tsakanin su ta yadda Hussain will be forced to choose between them kuma nasan cewa Hassan zai zaba duk kuwa da cewa rabuwa da Fatima zata yi destroying dinsa. And that destruction shi nake after. Idan ya zama ba zai iya cigaba da rikon kamfani ba dole Hassan will take over. Idan kuma something bad ya faru dashi komai ya zamana Hassan din"
Sumayya da mamaki ya ishe ta ta katseta ta hanyar cewa "something bad as in?" Ta daga kafada tace "babu wanda ya san gawar fari dan haka dan Adam babu abinda zai yi fata illar Allah ya bashi rayuwa mai tsaho" Sumayya ta dafe kanta tace "Ruqayyah wai kina nufin kima fatan Hussain ya mutu saboda Hassan ya samu gado" tayi shiru kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace "kowa ma wata rana zai mutu ai"
Ruqayyah tace "exactly, hakan yana nufin kema zaki iya kwanciya yanzu gobe kuma ba zaki tashi ba. Shi kuma Hussain zai iya ya kara shekaru saba'in ko fite da haka a rayuwa. Dan Allah Ruqayyah ki gaya min cewa ba wai kina tunanin harming Hussain bane ba saboda dukiyarsa. Dan Allah Ruqayyah ki gaya min babu wannan tunanin a ranki"
Ruqayyah ta bata rai tace "ni na isa in yi masa abinda Allah bai yi masa ba? Buri na ne dai kawai. Dan Adam kuwa ai ba'a raba shi da buri in dai akwai rai a jikinsa. Kuma wannan burin nawa ba zai cika ba indai har Fatima tana zaune a gidan sa saboy a kowanne lokaci zata iya samun ciki ta haifa masa da, samun da a gurinsa kuwa yana nufin ni da shiga gidan can sai dai da ziyara" ta mike zaune tana kokarin sauka daga kan gadon tace "besides, duk wannan burin nawa yabi iska tunda Hassan ya debi kasa ya watsa min a idona. Hussain zai cigaba da zama da fatiman sa ta haifa musu yaya and they will live happily ever after. Ni kuma da nawa yayan Hassan yayi conderming din mu to life of bakin ciki a karkashin dan uwan sa" sai da takai bakin kofa sannan ta juyo tace "kar ki damu yaruwa ta, the plan is off, shi yasa har nake gaya miki". Daga nan ta shige toilet.
Sumayya ta jima a zaune tana kallon kofar toilet din, zuciyarta tana gaya mata "anya lokaci bai yi ba da ya kamata ta shigo da Inna Ade da Baba cikin maganar Ruqayyah? Amma bata da mental related issues kuwa?"
Ruqayyah ta jima a toilet tana wanka, tana jin kamar tana wanke bakin cikin da Hassan ya cusa mata sannan tana bin maganganun sa a hankali tana digesting tana so ta fitar da ma'anar su. Abinda ta fahimta shine, babu wani abu daya gane a kanta, frustration dinsa kawai shine maganganun data fada akan Hussain, amma da sannu in ta cigaba a kan wannan hanyar data dauko to sai komai nata ya bayyana gare shi dan haka dole ta rufe wannan babin ta bude sabon babi, this will be the end of her first chapter yanzu zata bude second.
Sanda ta fito daga wankan bata tarar da Sumayya ba, dama ba'a dakin take kwana ba a kasa take kwana saboda bata son ta takurawa Hassan. Ta zauna akan dressing chair tana goge jikinta sai kuma ta dauko wayarta ta nemo number din Minal ta kira sai taji waya take yi, ta ajiye tana saka kayan baccin ta sannan tai Minal din tayi mata flashing, ta dauka tana cewa "ke yanzu da girman ki kike flashing?" Minal tace "ke babu wani girma anan, ke yanzu ai hajiya ce dan haka gwara ke ki kirani dan ni lallaba katin waya ta nake yi. Ya akayi? Ina mijin naki har yanzu baki kwanta ba?" Tace "ni ba wannan ba da Allah can, so nake ki damu lokaci ki zo akwai maganar da nake so muyi" Minal tace "dama gobe nake cewa zan shigo in karbi tsaraba ta, naga baki da niyyar zuwa ki kawo min har gida" Ruqayyah ta kalli cikin closet dinta, ita in ba shiga tayi ba har mantawa take yi ta lodin kayan da Hassan ya siyo mata a matsayin tsaraba, tace "akwai tsaraba kam, in kin zo kya karba" tace "to sai nazo din. Akwai wata magana nima da zamu yi" daga nan suka yi sallama ta kashe wayar ta ajiye sannan tayi shirin bacci ta kwanta tana jin wani freedom a ranta. Yau dai zata kwanta tayi ta juyin ta babu wanda zai dame ta.
Washegari da safe Sumayya ta shirya tace gida zata tafi. "Naga kin warke ai, kuma kina da yan aikin ki gwara in koma gida in cigaba da taya inna ayyukan gida" Ruqayyah ta bata rai "ba dai akan maganar jiya zaki tafi ba ko?" Sumayya tace "maganar jiya ai mun gama ta tunda kince kin rufe wannan babin, ni dai zan yi ta miki addu'a kullum, sauran kuma tsakanin ki da mijin ki ne".
A lokacin Hassan ya fito daga dakinsa, daga dukkan alama yanzu ya tashi dan fuskarsa da alamun bacci. Sumayya ta gaishe shi Ruqayyah ma haka, ya amsa yana kallon Ruqayyah ita kuma ta dauke fuska gefe tana kara bata rai yace "Sumayya ya na ganki da jaka haka da sassafe ko karyawa baki yi ba?" Tace "na karya ai duk kuna bacci. Akwai abinda nake so inyi a gidan ne da safen" yace "ohh. To bara in dauko key sai in kaiki ko?" Tace "lah, kayi zamanka, ina fit zan samu abin hawa" yayi murmushi yace "I insist" daga nan ya koma daki ya fito yana cewa "Precious bara in kaita in dawo ko" can kasa tace masa "a dawo lafiya" sai yayi murmushi, yasan fushi take yi.
A hanya suna tafiya yace da Sumayya "ina saurayin ki? I half expected to see him a waje yana jiranki, na dauka shi kuka yi dashi zai kai ki gida" ta danyi dariya tana wada da bakin hijab dinta tace "yana gidan mu ai yanzu. In kaje zaka ganshi a can in dai har ba zasu fita da sassafe da Hussain ba" ya dan bata fuska yace "gidan ku kuma? Me zaiyi acan da sassafe bayan kuma ke kina nan gidan?" Tace "karatu, karatu yake zuwa dauka acan kullum da assuba sannan kuma da daddare in ya gama da Hussain" ya maimaita "karatu?" Tace "yes, kasan ai...." Yace "I know, but kawai nayi mamakin boldness dinsa da zai je gidan surukai koyon karatu" ta dan ji kunyar kalmar surukan da yace. Suka cigaba da tafiya shiru, sannan yace "a gida Ruqayyah tana da fada ko? Baba ya taba ce min tana da fada" ta dan kalle shi tana hango damuwa a fuskarsa sai taji tausayinsa har ranta, tace "haka ne, kasan kowa da halinsa, amma I believe zata daina" ya gyada kai yace "eh zata daina, nima haka nace da baban a lokacin. Sai me take dashi bayan fadan?" Tayi shiru, a ranta tana tunanin wadannan tambayoyin Hassan kamata yayi ace yayi su tun kafin ya auri Ruqayyah ba wai yanzu da take dauke da cikin sa ba.
Ta dan yi murmushi a lokacin da yake packing tace "a hankali duk zaka fahimci yar uwata. Kai dai yanzu kayi ta addu'a kana hakuri kuma kana saka ido, komai zai wuce" ta bude kofa ta fita.
Bayan Hassan yayi breakfast, wanda shi kadai yayi kayansa dan kafin ya koma Ruqayyah har ta gama nata ta shiga daki, sai ya shirya ya leka ya ganta a kwance ya gaya mata ya fita. Yana so ya zauna suyi magana amma kuma akwai abinda zasuyi a office yau dashi da Hussain dan haka dole ya fita da wuri.
Da rana Minal tazo, Ruqayyah ta tare ta sannan ta jata zuwa dakinta. Minal tace mata "ke wani gara ne fa na samu nake wanka, shine ya kawo ni gidan nan ma yanzu. Har ya fara yi min maganar aure" Ruqayyah tayi dariya "kuma shine kike ce masa gara?" Minal tace "ke babba ne fa, a haife zai haife ni wallahi, zan baki labarin sa amma gaya min abinda yasa kika kirawo ni".
Sai Ruqayyah ta bata labarin rigimar da suka yi da Hassan jiya. Tace "to ni yanzu duk komai ya kunce min wallahi. Shawara nake so ki bani ta inda zan dora"
Minal tayi tsaki tana hararar ta tace "ke matsalar ki shine har yanzu baki ware ba wallahi, gidadan ci ne yake damun ki ba kadan ba. Ba tun yau ba na baki shawarar yadda zaki yi amma kin kasa fahimta. Kuma wallahi in kika cigaba a haka to ina yi miki albishir da komawa gidan Baba a matsayin bazawara" Ruqayyah taji wata irin faduwar gaba tace "Allah ya tsari bakin ki, kije ki kuskure bakin ki dan Allah. Kin ga ni fa aurena da Hassan mutuwa ce kawai zata rabamu" Minal tace "ai kuwa kina gab da tafiya in gaya miki. Mutanen nan fa wayayyu ne kuma ilimi ya ratsa su ta ko'ina, ba zaki taba iya hada su ba wallahi saboda kafin ki gansu ke sun ganki. Kinga wannan gimbiyar, to wallahi idan ke baki kore ta ba tabbas ita zata kore ki with just a blink of her eyes. Dole sai kin ajiye wannan zafin kan naki da wannan gidadan cin naki. Kinsan abinda yake zaune da ke a gidan nan? Son da mijin ki yake yi miki ne ba wani abu ba. In kuka cigaba a haka kuwa son zai dusa she then zaki zama baki da sauran wani madogara kuma"
Ruqayyah tace "ni duk ba wannan ba, ki gaya min abinda zanyi nace ba wai kike min bitar abinda na riga nayi ba" Minal tace "na gaya miki ai, kissa xaki bisu da ita, ki kama mijin ki ki kama surukarki ki kama yan uwan mijinki. Kinga wannan fatiman? To itace gidan nan ki kama ta hannu bibbiyu ina gaya miki. Zan je gidan Aunty Hafsa yanzu xan gaya mata halin da kike ciki zata saka ki a group dinsu na matan aure zasu koya miki duk yadda zaki bi da su. Sannan kuma sai kin hada da addu'a, ke kina yi kuma kina sakawa ana yi miki, kina musu kissa kuma kina toshe bakin su da addu'a yadda ko sun ga wani abu ba zasu iya magana ba. Akwai wani malami da Hajiya Binta kawar Aunty Hafsa ta hada ni dashi yayi min addu'a akan wannan garan da nake gaya miki. Kinga shi matarsa ce bata haihuwa shekara da shekaru ga uban kudi kamar ya kashe shi, shi kuma son matar yake kamar me, ya kasa yi mata kishiya, da kyar Alhaji Kabiru ya hada ni da shi yana ta yanga amma dana samu naje aka tottofe min shi shikenan. Yanzu bina yake kamar jela"
Ruqayyah tana girgiza kai tace "bana son harka da bokaye, bana son in rasa sallolina na kwana arba'in" Minal tace "ke dalla can ba boka bane ba, malami ne, da ayoyin Alkur'ani da sunayen Allah zai rufe miki bakunan su gam"
*The Fortune Teller*
Ruqayyah tayi shiru tana kallon Minal, abubuwa da yawa suna yawo a cikin kwakwalwar ta zuciyarta tana rabuwa kashi kashi, ta girgiza kanta. "Minal tsoro nake ji, irin wadannan malaman da su da bokaye duk tafiyarsu daya. Baki san wanda yasan Alqur'ani yasan irin sirri kan da ke cikin sa kuma in zuciyarsa bata da kyau to there is no limit to what he can do ba? Kuma wadannan laifin su yafi na boka muni ba? Kinga kakan mu, Malam Shehu? Babu abinda ba zai iya yi da ayoyin Alqur'ani ba amma baya yi din, ya zabi yayi aikin alkhairi dasu saboda ya zabi lahirar sa akan duniyar sa, inna Ade ma haka, ko kin san Inna Ade tafi baban su ilimin Alqur'ani? Amma ta zabi ta koyar da shi ga mutane saboda shine abinda take so. Nima nasan iya kacin abinda na sani, banbanci na dasu shine ni ina so in samu duniya sannan itama lahirar in samu yayinda su kuma suka ajiye duniyar a gefe suke neman lahirar. Duk iskanci na Minal bana wasa da ibada ta, ba zance bana zunubi ba dan ina yin karya da sauran kananan zunubai amma ban taba aikata wani a cikin manyan zunubai ba kuma ba zan fara ba. Kinga zuwa gurin boka ko malamin tsubbu to shirka ce, ita kuma shirka ita ce oga kwata kwata saboda in kayi ta tamkar ka bar addini ne, wanda kuwa duk ya bar addini kuma ya mutu ba tare daya dawo hanyar dai dai ba to ya mutu a kafiri. Ni kuwa Minal ba zanso in mutu a kafira ba bayan ita kanta duniyar ba samunta nayi ba, two zero kenan".
Minal tayi tsaki tace "ke kam ana baki kina kin karba. Na gaya miki ba boka bane ba kuma malamin tsubbu bane ba. To gaya min, shi Malam shehun da kike yin magana akan sa mutane basa zuwa gurinsa ya taya su da addu'a akan wani abu daya shige musu duhu ko wani abu daya taso musu?" Ruqayyah tace "suna zuwa mana" Minal tace "exactly, shima wannan haka yake. Na gaya miki sunayen Allah kawai zai kira sai kuyi addu'a ku shafa shikenan. Kinsan ita addu'a baki baki ne, wani yana yi kamar yankan wuka haka take wani kuma sai yayi tayi bai samu nasara ba. Ke kina yi shima can yana yi miki shikenan" Ruqayyah dai tayi shiru tana tunani sannan tace "baya duba kasa?" Minal tayi dariya tace "babu kasa ma a gidan sa. Charbi kawai zaki gani da Alqur'ani a gaban sa".
Ruqayyah tace "shikenan, zan zo muje din amma in naga wani abu da bai kwanta min ba zan gudu, ehe, dan ba zan zo duniya a banza in koma a banza ba sannan in tarar da can din ma wayam"
Sai suka shirya plan akan cewa Ruqayyah zata je gidan su ta kai musu tsarabar tafiyar da tayi, daga nan zata ce zataje gidan su Minal din ta kai mata tata tsarabar daga nan zata wuce gida. In yaso sai suje gidan malamin tare.
Bayan tafiyar Minal ne Ruqayyah ta shiga kitchen dinta. Yau ne rana ta farko data shiga kitchen din da niyyar girki, ta bude freezer taga akwai naman da bata ma san lokacin da aka zuba shiba, sai data tambayi yan aikin ta suka gaya mata ranar da zasu dawo Aunty ta aiko aka zuba musu duk kayan amfani a kitchen dinsu. Ta bude store taga akwai kayan garar ta suna nan suma jingim dan babu wanda aka raba wa duk zuba musu kayan su akayi a store. Har da drinks a jere a gefe wanda shima aka ce aunty ce ta aiko da shi.
Tayi shiru tana tunanin me ya kamata ta dafa ne, in dai har zata bi maganganun Minal to dole ta koyi abubuwa da yawa a ciki kuwa har da girki dan ta rike Hassan a hannunta. Ta tuna Fatima tayi mata alkawarin zata koya mata girki in sun dawo Nigeria amma yanzu kuwa anya in taje zata kulata? Maybe ma ta bita da bakar magana. Ta danyi tsaki, gaskiya lamarin nan sai ta dage sosai sannan zata cimma burinta, ita zuciyarta a kusa take, ita bata iya munafurci ba shi yasa har suka fara harbo jirgin ta. Amma dole ta koya koda kuwa a gurin Hassan ne dan dama shi tun tana gida take rufe shi a bai bai kuma yake rufuwa yanzu ne dai kawai frustration dinta akan Fatima ya saka ta fara bude masa kanta shi kuma a take ya buga mata warning.
Ta kalli yan aikin tana realizing ita ko sunayen su ma bata tsaya ta wani rike ba, tace "wace ta iya girki a cikin ku?" Duk su biyun suka ce sun iya. Tace "to ayi mana girki, tuwon shinkafa miyar agushi a saka nama sosai" suka ce shikenan ? Ta daga kafada tace "eh shikenan" sai bayan ta tafi sai ta tuna ai yan gayu abinci ba kala daya suke yi ba ko? Kamar har da snacks ake hadawa da kuma dan farfesu haka. Sai ta koma ta gaya musu suyi farfesun kaji sai su saka naman kasuwa a cikin miyar. Suka gaya mata babu fresh kayan miya sai markadaddu, babu kuma kayan kamshi, ta koma sama ta dauko kudi ta basu tace su bayar a waje wani ya siyo. Tayi kamar zata zauna suyi aikin tare, maybe ta koyi wani abu, amma sai ta kasa zaman kar su fahimci bata iya ba su raina ta. Ta debi drinks ta tafi dasu sama ta zuba a fridge din daya ke can ta kunna sannan ta koma dakinta ta gyara inda suka bata ita da Minal ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atampa wanda daya ne daga cikin dinkunan da ta bayar kala ashirin kafin su tafi honeymoon. Tayi kwalliya irin wadda taga Fatima tana yi, daurin dankwalin ma shigen nata tayi. Sannan ta saka awarwarayen gold kamar yadda taga