Showing 258001 words to 261000 words out of 300844 words

Chapter 87 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2101

kuma yi mata addu'a, amma a zuciyarsa har yanzu yana kan bakan sa na babu ruwansa da Ruqayyah har sai ta bi abinda ya ce tayi.

Lukman ma yana zuwa ya dubata, duk da bai taba cire ko kwandala a cikin kudinta yace a siya mata magani ba su kuma basu taba cewa ya bayar ba. Zuwa duba tan ma yana yi ne da yake samun updates akan yanayin jikin nata. Da yake matsalar Ruqayyah tana da dangantaka da maganin da Lukman ya saka ake bata a wancan asibitin da take na farko, wannan ya sa yanzu da aka daina bata irin su kuma aka koma treating matsalar da akayi diagnosing dinta dashi, sai gashi cikin watanni ta fara dawowa hayyacin ta har tana gane yan uwanta in sunzo dubata.

Ta kan gane Sumayya har tayi mata murmushi, tana gane Inna kuma musamman in taga tana kuka sai tayi mata alamar tayi shiru da hannunta. Wannan ta sa suka cigaba da kokari da kuma kara wa doctors din courage na cewa they can get there. Sanda su Sumayya zasuyi tafiya da yara ma Sumayya tazo tayi mata sallama tana ta yi mata hira tana bata labarin irin kasashen da yaran suka zaba da rigimar da suka yi tayi a tsakanin su akan hakan. Sai dai Ruqayyah ba komai takw fahimta a labarin ba amma ganin Sumayya tanata zabga murmushi ya saka Ruqayyah ira ma tayi tayin irinsa.

Da suka je suka dawo ma sai da Sumayya tazo ta nuna wa Ruqayyah irin hotunan da sukayi ta dauka a kasashen da suka je. Ga mamakin Sumayya sai taga kamar Ruqayyah ta gane twins dinta, ta dago tana kallonta sai taji tace "ina Hussain?" Wannan shine Magana ta farko da Ruqayyah tayi a kusan tsahon shekara daya. Farin ciki a gurin Sumayya har baya iya misaltuwa, taje ta samu doctors da bayani cewa an kuma samun wani cigaban.

Wannan ya tabbatar musu da cewa rashin samun kulawa a wancan asibitin shine ya saka Ruqayyah bata warke ba sai ma kara rikicewa da tayi. Sai kuma Sumayya ta fara bibiyar Hassan akan dan Allah ya bar yaran su zo Ruqayyah ta gansu. "Duk da shekarun da suka wuce, duk da girman da suka yi amma ta gane su kuma har ta lura cewa babu Hussain a tare da su" amsar daya bata kawai ita ce "no" daganan bai kara ko kalma daya ba. Dole ta hakura ta bar maganar dan tasan ba zai kara wata kalma akai ba, in kuma ta cigaba da matsawa to itama zai iya ya hana ta zuwa ganin Ruqayyah.

Sosai Ruqayyah take samun lafiya, cikin shekara daya ta gama gane kowa ta kuma tuna da duk labarin rayuwar ta wanda da aka saka drugs sukayi blanketing, sai kuma ta lura da yadda family dinta suke ta zarya akanta da suna kuma iyakacin kokarin su da aljihun su dan ganin ta samu lafiya da kuma kyakykyawar kulawa. And it touched her stoned cold heart, tana ganin duk abinda tayi musu, duk irin bujirewar da tayi musu da zaben kudi da tayi a maimakon su amma gashi su basu guje ta ba sun kula da ita a lokacin da take buƙatar kulawar. Kudin nata kuma bai yi mata amfanin komai ba dan tana sane da cewa babu ko kwandalar ta a cikin nemar mata magani. Sai dai abinda ya bata mamaki ya saka kanta a duhu shine yadda ta kasa yiwa Lukman magana akan hakan, ta kasa yi masa magana akan komai, dan ko breakdown na yadda abubuwa suka kasance a shekarun nan bata tambayeshi ba duk da kuwa cewa yana zuwa dubata.

A cikin ziyarar da yake kawo mata ne kuma ranar nan ta samu courage din yi masa magana "ya kamata bilks din kudin maganin nan su Sumayya su daina biya haka, hidimar tayi musu yawa" yayi murmushi duk da maganar tata tabashi mamaki yace "da ma ina so inyi miki magana akan hakan, suna kokari sosai gaskiya, suna sonki sosai musamman da kika yi wannan rashin lafiyar suka tabbatar da cewa ba ko aikata laifin da ake tuhumar ki dashi ba, it will break their hearts in suka fahimci ba haka bane ba.

Tace "ina Fatima? Ina Hassan?" Yace "suna nan lafiya, suna nan sunyi kudi sosai, enough money to send you to prison for life. Duk kudin da Sumayya taje ta wannan hidimar da shi na Hassan ne, Fatima tayi aure tana Dubai kuma a yanzu she owns as much as you do na H and H. Kin san wa ta aura?" Tayi shiru bata amsa masa ba, tana dai kallonsa, yace "wannan yaron da kika yi kokarin framing shi ta aura, suna can dubai tare, tare kuma da danki Hussain"

Ruqayyah ta zaro ido cikin tashin hankali "Hussain dina?" Yace "eh, babanshi ya bayar dashi ga Fatima tun a shekarar ki ta farko a asibiti" sai ta saka hannun ta ta cire sabon hearing aid dinta da Sumayya ta siya mata daga kunnen ta, bata son ta cigaba da jin wannan labaran. Hawaye ya a bin fuskarta, ta rasa wanne be zata roka a gurin ubangiji mutuwa ko rayuwa? Ita dai tasan rayuwarta bata da amfani a yanzu, ta kuma san mutuwar ta ita ce mabudin wahalar ta. Ko ta roki Allah ba zai yafe mata ba saboda ba shi tayi wa laifi ba, Fatima kuma ta tabbatar ba zata yafe mata ba ko mene zata yi balle Hassan, wanda tafi jin tsoron zuciyarsa akan ta Fatima.

A ranta tana so taga ƴaƴan ta, tana so ta kula dasu ta basu tarbiyya ko zasu zamo sanyin idaniyar ta wata rana amma tasan ko tana mutuwa tana dawowa duniya Hassan ba zai bata su ba. A dan fahimtar da tayi na short stories din da taji ta fahimci cewa kowa ya samu rayuwa mai kyau amma banda ita. Shin menene mafita a gareta?

Shekarar ta biyu ta warke sosai. Duk sababbin abubuwan da suke damunta sun tafi, Minal ma finally ta daina binta da kallo amma wannan jaririn, wannan jaririn mai shegen kuka yana nan yana cigaba da kukan sa a cikin kanta, amma ta saba dashi dan haka bata gayawa doctors ba dan bata so su kara jan zaman nata a tare dasu. Kuma a ranta tasan cewa ba zai daina yi mata kuka aka ba gar sai ranar da taje inda ta ajiye shi ta dauko shi ko kuma ranar da ta mutu ta bar duniya. Sai dai tsoron abinda dauko shi din zai haifar gare ta shi yasa ta cigaba da barin shi a can din.

Da za'a sallamota Lukman ya fitar da kudi a cikin kudinta sa saka akayi mata gyare gyare-gyaren gida, ya kuma daukar mata wasu sababbin yan aikin dan wadancan duk sun watse ya sallame su ya rufe gidan tun tafiyar ta. Ya gama shirya duk plans dinsa, fatansa shine aikin Malam ya cigaba da ci akanta ta cigaba da yi masa biyayya tare da cigaba da boye maganar yaron nan.

Tun farkon sanda ya lura ta fara warkewa ya yanke shawarar sa. Idan ma yayi kokarin kashe ta ko wani abu to zai rasa dukiyar ne dan bashi da gadon ta, yasan iyayen ta ma ba zasu karba ba, maybe a karshe kudin ya kare da tafiya baitil mali, dan haka shawarar sa itace ya aure ta. In yayi haka zai samu damar cigaba da huya dukiyar ta hankali kwance, kuma inya kasance mai saa ma, in ta haifa masa Da, zai kuma samun dama akan dukiyar da yasan wadancan yayan nata ba zasu karba ba. Kuma samun wani dan a gurin ta zai kara dakusar da yunkurin ta na bayyana gaskiya.

A ranar da aka sallame ta Baba da Inna basu zo ba dan har yanzu Baba yana kan bakansa, musamman yanzu da ya ga ta samu lafiya sosai. Sumayya ma bata zo ba dan Hassan bai barta ba. Sulaiman da Zunnur ne suka zo sai kuma Lukman da ya riga ya gama shirin sa, ya kuma cika wa Malam aljihu da kudin Ruqayyah akan yayi masa addu'a akan kudurin sa, har da sabuwar wheel chair yazo mata da ita mai remote control sannan kuma a gaban su Sulaiman ya gaya mata cewa yana so idan ta amince zai aure ta.

Aure shine abu na karshe a zuciyar Ruqayyah a lokacin, dan ita bayan rabuwar ta da Hassan bata taba tunanin zata yi aure ba kuma tunda ita ba wai sin abin take yi a rabta ba amma sai ta samu kanta da kasa yi masa musu, a gaban su Sulaiman ta amsa masa tace zata aure shi, amma sai tace yaje gurin Baba tukunna suyi Magana. Ba Baba ba hatta sauran yanuwa sai ta suka yi mamaki da wannan batun, a take Baba yace babu ruwansa shi ba zai daura mata aure ba. Sai Lukman bisa jagorar Sulaiman ya tafi har Zaria ya nemi auren Ruqayyah ahannun dangin Baba kuma suka bashi. Ya kuma bayar da sadaki a ka daura musu aure. Yes, kamar yadda dukiya ta jawo wa Hussain mutane ta jawo wa Ruqayyah ma, banbancin shine kalar mutanen da ta jawo mata din.


*The Final Wave*

Aure ya tabbata tsakanin Ruqayyah da Lukman, da farkon auren a can kasan zuciyar Ruqayyah ta san karya yake yi da yace yana sonta, tasan cewa ba ita ya aura ba kudin ta ya aura, kuma ta saka masa ido sosai tana so ta ga iyakacin gudun ruwansa amma kuma sam ta kasa yi masa magana ko kuma yin wani yunkuri na karbe wani abu daga hannunsa. Sai kuma daga baya zuciyarta ta fara karkata akan tunanin to ko yana sonta din ne da gaske? Tana lura da irin wadda yake nuna kulawa a gareta, ya tattare gaba ki daya a wajenta ya ajiye matarsa ta farko da yara biyu da suke dasu a gefe, kullum yana tare da Ruqayyah yana kula da ita tare da kula da dukiyar ta. Yana paying attention to duk wasu bukatun ta musamman a gadon aurensu, abinda tunda ta nakasa take tunanin ta rasa kenan har abada amma sai yazo yana bata ba tare da kyama ba amma fa sai dai maganar kudinta ne babu su babu lissafinsu dan ko zancen baya yi mata ita ma kuma ta kasa samun courage din yi masa maganar, wannan shine kadai matsalar ta dashi a farkon auren su, yadda take kasa musa masa akan duk abinda yace mata ko da kuwa a ranta tasan ba haka bane ba gabaki daya ita ta manta da zancen malamin tsubbun da ita ta hada shi da shi kamar yadda Minal ta hada ta da shi.

A hankalin take jin hankalin ta yana kwanciya da shi, tana jin cewa kamar shi din wani solution ne na dukkan problems dinta tunda ya cigaba da taimaka mata wajen boyewa iyaye da yanuwanta ainahin gaskiyar lamarin ta, a ganinta boyewar ne ya saka suka sauko yanxu suke kula ta ba kamar da ba, duk da yanzun ma ba kamar da can ba, tana ganin shi a matsayin wani shield ga dukiyar da ta samar wa kanta, dan tasan zamanta a matsayin mace mai kudi babu miji zai iya zamanto wa hatsari gare ta da kuma dukiyar ta, amma shi ya bata protection kenan.

A hankali sai ta fara farin ciki, thinking that she deserves happiness ita ma a rayuwar ta kamar yadda Fatima da Sumayya suka samu. Tana ganin Fatima da take bazawara ta samu auren zankadeden saurayi kamar Adam, kuma kasancewar yadda Matsayin ta yake ta san Adam yana can yana riritata kamar kwai, giving her all the happiness, to in Fatimah zata samu wannan why not her? Dan haka sai tayi kokarin ganin ta yi accepting Lukman a zuciyarta dan tayi making kanta happy.

And then she yearns for children, tana ganin sune zasu zaman to kamar wani murfi na farin cikin ta, su zasu taimaka mata gurin kara binne laifuffukan ta a zuciyarta, su zasu cika mata dadadden burin ta na haifa tare da raising yaya a cikin dukiya saɓanin irin tashin da ita da yanuwanta sukayi cikin talauci. Akansu take burin gyara yarintar ta.

Shima kuma Lukman a tasa zuciyar abinda yake so kenan dan haka suka hadu suka yi ta nema and three years after aurensu God granted their wish, Ruqayyah ta samu ciki, cikin da akayi ta rikita wa, Ruqayyah feeling like ita ce Fatima take samun kulawa daga Hussain, sai dai ita tata kulawar iya kacin cikin gida ne sai sometimes ya dan fita da ita taga gari ya kuma dawo da ita gida amma ko hanyar airport bata zuwa ballantana ta hau jirgi, ita da wata kasar kuma sai dai a mafarki. Ita da jirgin sama sai dai ta taga kai ta kalle shi idan zai wuce ta saman gidan ta.


A haka har ciki ya girma ya isa haihuwa akayi mata cs aka fito mata da kyawawan yayanta guda biyu namiji da mace. Wannan ranar a lokacin Ruqayyah zata iya kiran ta da happiest day of her life, yayanta manya masha Allah, gasu kyawawa masu kama da ita, ga kuma tarya mai kyau da ubansu yayi musu, duk da dai tasan da kudin ta ta ne akayi, but she is just happy cewa anyi din, komai daga waje aka shigo mata dashi irin yadda take so, kuma duk da cewa Lukman yana da wasu yayan amma yadda yake yi akan wadannan yaran zaka dauka bai taba haihuwa bane ba, shi ganin su yake yi a matsayin source of arzikin sa, a matsayin security dinsa, duk da Ruqayyah ta nuna masa ba zata yi suna ba amma sai yace sai anyi, shi a gurinsa yana so ya samu as many witnesses as possible na cewa Ruqayyah ta haifa masa yaya, ita kuma a nata bangaren tasan ba lallai bane yanuwanta su je gurin sosai, ta san in tayi taron bakin ciki zata kwasa kawai shi yasa ta ji bata so, amma kasancewar bata iya ce masa a'a dole aka yi taron suna.

Sumayya bata samu Hassan ya barta ta leka wa Ruqayyah suna ba, duk da dai ya barta taje gurinta a asibiti amma da yaga tana shirin suna sai yace ma kasar zasu bari gabaki daya, "I want my children as far away from her children as possible". Haka ya tattara ta da yaran gabadaya duk da yaran ba hutu suka yi ba suka tafi San Francisco sukayi sati daya sannan suka biya ta Dubai suka dauko Hussain zaiyi musu hutu suka dawo gida. Bayan sun dawo ne Sumayya ta sami Hassan da maganar yaran "Habibi, yaran nan fa girma suke kara yi kullum. Aminu da Yusuf fa yanzu fifteen years suke Hussain yana Fourteen, ba ka ganin lokaci yayi daya kamata su san maganar Ruqayyah?"

Ya bata rai yace "akan maganar matar nan fa na raba ki da kasar gabaki daya, shine kuma yanzu daga dawowar mu zaki dora a inda kika tsaya? Kinsan Allah? Saboda bana so muyi nisa da Aunty shi yasa kika ga har yanzu muke unguwar nan amma da tuni mun tashi mun tafi as far away from her and her sting as possible"

Ta sauko daga kan kujera ta dawo gabansa ta durkusa tace "ba maganar Ruqayyah nake yi maka ba Habibi, maganar yayan mu ne. Ina jin tsoro ne wallahi. Kasan yanzu a duniya mutum ake kiyo ba dabba ba, maganar nan a fili aka yi ta ba'a sirri ba dan duk wanda yake unguwar nan yasan da maganar nan, social media duk ta san da maganar nan, ina tsoron kar wani ya tari yaran nan a hanya ya gaya musu maganar nan. Ko zuji a cikin friends dinsu ana maganar, ina jin tsoron kar aje a kara musu gishiri da maggi a cikin maganar su zo suyi mata fahimtar bai bai. Yaran nan suna da hankali, ina ganin in muka zaunar dasu muka yi musu bayani da kanmu zasu fi fahimta akan ace a wani gurin suka ji"

"Ba sai lallai sai sunje sun ganta ba in baka so, ba sai lallai mun gaya musu komai in details ba in baka so, but at least let them know from us not from an outsider. Please Habibi. Maganar zata yi affecting dinsu sosai idan suka ji a wani gurin"

Cikin sa'a sai ya yarda, a daren ranar suka tara yaran manyan sukayi musu bayani iyakacin wanda suke ganin kwakwalwar su zata dauka. Ai kuwa dai sunga rikici dan sai da Sumayya tayi nadamar matsawa akan maganar shi kuma Hassan sai yanzu ya fahimci Sumayya ta fishi gaskiya dan da a wani gurin sukaji da sai tashin hankalin yafi haka, a ranar babu wanda yayi bacci a gidan dan hatta kananan yaran sai da suka fahimci something is wrong duk da basu san menene ya faru ba. Kwana biyu bayan nan Hassan ya amince Sumayya ta shirya yaran gabaki dayansu suka shiga gidan Ruqayyah. Katon gidan da kullum suke daga kai suna hangowa amma basu taba shigar sa da wayon su ba, duk da dai twins din suna da memories na kamar da suna shiga amma ba zasu iya tuna me suke yi a gidan ba.

Suna shiga falon suka tsaya suna kallon katoton hoton da yake rataye a sama yana kallon su, hoton Hassan da Hussain wanda duk cikin shekarun nan Allah bai bawa Ruqayyah ko Lukman ikon sauke hoton ba. Ruqayyah da take zaune akan kujera tare da wasu matan abokan aikin Lukman da suka zo musu barka tayi kokarin mikewa kuma babu kafa. Da sauri ta fara sallamar bakin nata zuciyarta tana bugawa da karfi. Tana jin excitement din ganin yayanta Musamman Hussain da ba zata iya tuna rabon data ganshi ba, a gefe kuma tana jin tsoron irin yanayin da taga fuskokin su a ciki. Bakin suka fara mikewa suna ajjiye jariran hannun su suna kallon yan samarin yayan da suka jeru a gaban hoto suna kallo, sai dai kallo daya zakayi musu kasan cewa daya daga cikin na cikin hoton ne suka haife su.

Sai da suka fita sannan Ruqayyah ta mayar da hankalinta kan bakin nata, "Hussain" ta fada tana dafa kujera da rawar murya, Hussain ya juyo yana kallon


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login