Showing 189001 words to 192000 words out of 300844 words

Chapter 64 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2099

gida gobe zai zo ya dauke ta su je, gwara dai suje Kanon nan ko ya samu ta sakar masa mara yayi fitsari.

Data sanarda Baba sai yace "a dawo lafiya. Amma ki sani, ko kun samu Adamu ba zan bashi aurenki ba sai dai in Hassan ne da kansa yace ya janye ya bar masa"

Da sassafe Hassan yazo suka dauki hanyar kano, yana ta kokarin yi mata hira a hanya amma ita hankalin ta yana kan abinda zasu tarar a kanon, wannan shine last chance dinta na samun labarin Adam dan tasan Baba ba zai kara barin ta ta dawo ba kamar yadda ta san ba zai cigaba da kallon ta a gida ba dole zai yi mata aure ko da Hassan ko ma da waye amma dole zaiyi mata aure, ita kuma a yanzu batada wani saurayi dan babu wanda take kula wa duk kuwa da cewa babu ranar da wani a school ko a unguwa ba zai yi mata magana ba amma ita sam bata da interest, bata jin zata iya soyayya da wani idan ba Adam ba.

Ta fahimci duk wannan kame kamen da Hassan yake yi a kanta, tana kuma sane da alkawarin da Baba yayi wa Hassan din kuma tasan babu yadda za'a yi ta ketare maganar Baba musamman im tayi la'akari da abinda ya faru da Ruqayyah, bata so tayi breaking heart din iyayenta ta fama musu ciwon da Ruqayyah ta riga taji musu a zuciyoyin su, dan haka chnace dinta na gujewa auren Hassan guda daya ne shine samun Adam, idan suka sami Adam tana da tabbacin Hassan zai hakura ya bar masa ita wannan kuma zai saka Baba ya hakura da maganar. Amma idan ba Adam ba,bata jin Hassan zai barwa wani.

Hassan bai manta da address din gidan su Adam ba, tiryan tiryan suka tafi har bakin gate din gidan sukayi packing, zuciyarsa cike da abubuwa da dama itama tata zuciyar haka. Kamar yadda yayi tsammani gidan looks deserted kamar babu mutane a ciki, ya dudduba ko zai ga mai gadin da suka gani ranar nan amma bai gashi ba sai ya fita zai he yayi knocking ko yana ciki, a lokacin aka bude gata din gidan sannan wata mota ta fito. Macece a cikin motar, tayi packing kusa da su Hassan sannan ta fito ta koma tana locking gidan. Daga Sumayya har Hassan sai da suka yi mamakin ganin yarinyar, kamar an tsaga kara ita da Adam, ko ba'a fada ba kana gani kasan ciki daya suka fito.

Sumayya ta bude kofar motar da sauri ta fito, a lokacin da yarinyar take kokarin komawa cikin motar ta, Sumayya tace "Assalamu........ excuse me" yarinyar ta tsaya, hannunta daya rike da handle din mota tana kallon Sumayya sama da kasa tace "hi" Sumayya tace "dan Allah muna tambaya ne, Adam.....amm Joseph muke nema" tana kallon yadda expression din fuskarta ya chanja tace "and who are you if I may ask" Sumayya tace "am his friend, munyi secondary school tare, naji labarin ya bar gida kuma sai naji kamar ance ya dawo shine nake son in ji ko gaskiya ne" yarinyar ta kalli Hassan sannan ta kalli plate number din motar tace "Kaduna. Ba a Kaduna yayi secondary school dinsa ba ai" Sumayya ta rasa me zata ce sai tace "dan Allah......please, just tell me idan yana nan. Is he okay?" Yarinyar tace "he is fine alright, amma ba zaki ganshi ba. Cos baya North and he is never coming back to North, haka Daddy yace, duk family sun koma can nima dan ina karasa school ne shi yasa nake nan" Sumayya ta hadiye wani abu da bata san yaa makogwaronta ba sai yanzu tace "can you at least give me number wayar da zan same shi? Am worried about him" yarinyar ta girgiza kai tace "kune fa, irin kune kuka makala masa addinin ku kuka asirce shi ya bar mu, gashi nan har yau ana ta fama dashi har yanzu bai dawo dai dai ba, how can I just get you together again? If you are truly worried about him ai na gaya miki he is Okay, har an karba masa transfer dinsa ma ya koma school, they are both okay shi da girlfriend dinsa daya tafi da ita" Sumayya ta daskare "girlfriend?" Tace "yes, that beautiful lady daya tafi da ita" sai kuma ta lura da yanayin Sumayya sannan tace "ohhh, ko kema wata girlfriend din tasa ce?" Ta danyi dariya tana girgiza kai tace "he was double dating kenan, amma daga dukkan alama yafi son waccan tunda ya tafi da ita ke ya barki without even a phone number to call him with" daga nan ta bude motarta ta shige ta ci taya tayi tafiyarta.

Sumayya ta jima a gurin a tsaye har sai da Hassan yazo yace mata "lets go" sannan ta dago fuskar tadata jike da hawaye tana kallonsa, bata ce komai ba ta bude mota ta shiga shina ya zagaya ya shiga suka juya.

Tun da suka shiga mota ta rufe fuskar ta da hijab ta cigaba da kukanta, bai kulata ba shi kuma ya cigaba da driving dinsa. A hanya ya samu bakery ya siya musu snacks da lemo da ruwa ya ajiye mata a kusa da ita ya cigaba da tukin motarsa. Taci kukan ta ta koshi sannan bacci ya dauke ta. A haka har suka kusa shiga Kaduna sannan ta farka ta rarrashi kanta ta goge hawayenta sannan yace "he is fine, alhamdulillah, he is still a muslim, alhamdulillah" ta gyada kai tace "yes, alhamdulillah" sai yace "zancen girlfriend din nan zata iya kirkira ta gaya miki dan kiji haushi" ta sake gyada kai tace "karya take yi, na sani, bashi da wata budurwa karya take yi. But still it hurts me that yana nan lafiya kalau har ya koma school amma be neme ni ya gaya min cewa yana lafiya ba, ni ban damu da wai wani abu da yake tsakanin mu ba, abinda nafi damuwa dashi shine lafiyar sa at least dan hankali na ya kwanta kuma....." Yace "yanzu kin sani ai, hankalin ki ya fara kwanciya?" Sai tayi shiru bata bashi amsa ba.

Yace "Sumayya shi aure rubutacciyar kaddara ce, matar mutum kaddarar sa ce, idan Adam mijin ki ne dole sai ya zo daga duk inda ya tafi ya aure ki, idan kuma babu aure a tsakanin ku duk kukan da zakiyi duk neman da zakiyi masa ba ba zai aure ki ba ko da kuwa kun hadu din. Idan kuma shine kaddarar ki sai kin aure shi kamar yadda na auri twin sister dinki. Allah ya riga ya rubuta sai munyi aure kuma sai mun haifi yaya har uku da ita. Haka zalika idan da rabon ke ma sai na aure ki, maybe har da zuri'a a tsakanin mu, to babu yadda zamuyi sai hakan ta kasance tunda wani baya auren matar wani kamar yadda wani baya haihuwar yayan wani"

Jin yayi shiru yasa tace "Baba ne yake son wannan hadin" yace "Baba, da Inna da Aunty" ya kalle ta yace "da ni" tayi sauri ta dago jajayen idonta tana kallonsa sai ya daga kafada yace "yes, nima ina so, ke kadai kika rage yanzu, amsar ki kadai muke jira" tana girgiza kanta tace "nayi wa Ruqayyah alkawarin ba zan taba auren ka ba" da mamaki yace "Ruqayyah kuma? Yaushe kuka yi wannan maganar da ita?" Tace "ba yanzu bane ba, tun lokacin kana neman auren ta ta ji Baba yana baka shawarar ka aure ni ka rabu da ita, ranta ya baci a lokacin, and I promised her ba zan aure ka ba saboda in kwantar mata da hankali" Hassan yayi mamakin halin Ruqayyah, wato har labewa tayi taji maganar su da Baba, wato wannan shine dalilin rufa rufar hali da tayi tayi masa tana nuna masa ita ta kirki ce, ya tuno da lokutan da tayi kokarin bata Sumayya a gurinsa, yace "I don't think a yanzu dai akwai wani alkawari da yake kanki tsakanin ki da Ruqayyah. Mai yasa ba zaki bamu chance ba? Idan ninba mijinki bane ba babu yadda zanyi in aure ki ko da kuwa duk duniya suna son hakan. Just give us a chance muga inda Allah zai kaimu akan wannan maganar.

Tayi shiru tana tunani. Me yasa ne mutanen da tayi trusting the most sune sukayi hurting dinta the most, Ruqayyah, yanzu kuma ga Adam. Few months ya rage mata ta kammala karatun ta, ta san kuma tana gamawa Baba zaiyi mata aure ko da Hassan ko kuma da wani daban maybe ma wanda bata sani ba, kuma ance the devil you know is better than the angle you don't know, ballantana kuma Hassan is not a devil dan tun lokacin da yana neman Ruqayyah har zuwa auren su da zaman auren nasu ita dai a iyakacin abinda ta sani bata san yana da wani babban aibu ba, duk da dai ance kowanne mutum tara yake bai cika goma ba. Besides, tana son ta farantawa iyayenta rai.

Yayi packing a kofar gidan su ya juyo yana kallonta yace "me kika ce? Zaki bamu dama ko kuma in hakura" ta sunkuyar da kanta tana jin wani iri a zuciyarta, wannan wani decision ne da zaiyi affecting rest of her life, amma kuma kamar yadda yace in ita ba matar sa bace ba bazai taba auren taba. Tace "na amince, zan bamu dama muga inda Allah zai kaimu".

And so it happened....

Ba wai soyayya ce Hassan sukayi da Sumayya ba amma akwai kulawa da mutum ta juna da aminci sosai a tsakanin su, duk wani abu daya shafe ta yana tsaye akai haka ita ma take yi a nasa affairs din. A hankali suka fara zama abokan shawarar juna musamman a harkar business dinsa wanda yanzu yake kokarin kammala ginin estate dinsa na biyu yayinda ita kuma take final exams dinta. A lokacin ne ya nemi permission dinta na turowa neman aurenta kuma ta amince masa. A take yayi wa Aunty magana wadda ba zaka iya tantance wanda yafi murna tsakanin ta da inna ba, ita ma nan take ta aika Gombe magabatansa suka zo suka tafi Zariya neman auren Sumayya, sai dai a nan ne aka fara samun matsala inda yan uwa da abokan arziki suke ganin rashin dacewar auren nasu musamman wadanda basu san abindaya raba Hassan da Ruqayyah ba. "Ta yaya zai auri Hassana ya sake ta bayan ta haifa masa yaya ta samu nakasa sannan kuma ya auri hussainar ta? Wannan wanne irin cin amana ne?"

Yan gari kuma sai suka dauka da gulma "dan ta samu nakasa shine yayi mata saki uku ya bata gida da kudi a matsayin cin hanci, sannan kuma ya koma zai auri yar uwarta sunkuma iyayen saboda kwadayin kudi suka bashi ita"

Yes, haka rumour din mutane yake, abinda kaji most of the times ba shine abinda yake gaskiya ba. There is more to it than you know.

But wannan bai hana komai faruwa ba saboda su immediate family dinsu sunsan ainahin abind ya faru kuma su suka fi kowa son wannan hadin musamman iyayen su da suke ta saka musu albarka tate da fatan alkhairi duniya da lahira.

Ba'a saka wani dogon lokaci ba kamar yadda Hassan ya buƙata, watanni uku aka saka bayan kammala jarabawar su Sumayya, wannan ma kuma dan Hassan yana bukatar lokacin gyare gyare-gyaren gida ne. Yana son yayi renovating gidansa completely dan ya cire duk wani traces na memory din Ruqayyah. Duk abinda yake gidan sai da aka fitar dashi sannan aka chanjawa gidan fasali yadda komai sanin da kayiwa gidan ba lallai ne ka gane shi ba yanzu idan ka ganshi. Dakunan kasa duk an rushe su sai aka mayar da palukan guda biyu, da nasa da nata, kowa kuma sai aka yi masa stairs din sa a palonsa zuwa samansa, a saman kuma sai aka hade palon sannan aka yi dakin yara a saman. Ta yadda in yayi baki babu ruwanta dasu ita ma inta yi baki ba zasu hadu bama.

Wannan karon Baba ya dage shi zaiyi kayan daki, wannan yasa Hassan ya bude hannu sosai a wajen kudin aure da kudin sadaki dan ya taimakawa Baban ba tare da ya nuna hakan a bayyane ba.

Aunty ce ta siyo lefe kamar yadda tayi lokacin auren Ruqayyah, dai dai gwargwado kamar yadda akayi na Ruqayyah. With that, komai ya gama kammaluwa ranar daurin auren kawai ake jira.


*Neighbors*

Hassan ya fitar da kudi masu dan kauri ya bawa Sumayya wai ko zata yi wasu events haka, amma sai taki karba tace ita babu abinda zata yi, sai yaji bai ji dadin haka ba tunda shi yasan ita din mai son kashe kudi a biki ce, sai yayi tunanin ko dan bata son sa ne ya saka ba zata yi ba? Sai ya bawa Zulaihat ta kawo mata kuma ta roke ta on his behalf ta karba, ita kuma sai ta karba din dan bata son ayi ta jayayya musamman tunda ya saka Zulaihat a ciki. Sai bayan Zulaihat ta tafi sannan ta kira shi tayi masa godiya yace "ko kefa, har na fara tunanin ko laifi na ne ya shafi bikina" tace "wanne laifi kayi kuma? Kawai dai babu abinda zanyi dasu ne shi yasa" yace "duk son ki da biki kuma sai a naki zaki ce ba kya so" tace "haka ne ina son biki, ina son ayi ta hidima haka da mutane ayi ta abubuwa amma ba hakan yana nufin ni ina da ra'ayin shiryawa da kaina ba. Kuma ni bani ma da kawayen da zanyi wa wata hidima" yace "ina kawayen ku? Wadanda kika gayyato da wancan bikin?" Baya son ambatar sunan Ruqayyah a duk lokacin da suke tare da Sumayya saboda baya son ya tuna mata tsohon matsayin sa a gurin ta. Tace "wai da bikin Ruqayyah? Ni ban san su ba fa, ita ta nemo abin ta, duk kawayen mu ma na school kin gayyatar su tayi tace basu kai matsayi ba" yayi shiru yana cihe baki, he thought as much, but so yake ya tabbatar, ya sake cewa "ohh na dauka naki ne ai, tunda naga ke ce kirjin biki a lokacin, harda yi min text din in kara muku kudin biki" ya danyi dariya "shi yasa nayi mamaki yanzu da kika ce ba kya so" ta bata rai kamar yana ganin ta tace "wanne text? Wanne kudi?" Tun kafin ya bata amsa yasan inda maganar ta dosa, ya fahimci Ruqayyah ce tayi masa text da number din Sumayya dan ta cigaba da yaudarar sa da kyawawan halaye, what more ne Ruqayyah tayi wanda bai sani ba? Sai yaji yana jin tsoron sanin wannan amsar.

Yayi saurin cewa "forget about it, ki bar maganar kawai, and saboda ina son in faranta miki duk abinda kika shirya zanzo" tace "a'a fa, kayi zamanka kawai, babu abinda zanyi sai walima tare da few friends dina shikenan, sai abinda zasu yi a gida kawai"

A dole ya hakura ya rabi da ita duk da dai yaso ace ta saki jiki tayi bikinta sosai, amma ita kuma a nata bangaren ta ki yin komai a bikin ne dan bata son maganganun da mutane suke yi akan auren, ta san duk kawayensu na unguwa da na primary da secondary school duk sun san mijin Ruqayyah zata aura dan haka duk ba zata gayyace su ba dan kar suzo su kara mata wani takaicin akan wani, kawayenta na jami'a kadai zata gayyata suyi walimar su a nutse inda Inna Ade da kanta zata yi hosting walimar ta kuma yi musu wa'azi akan zaman aure a musulunci. Yan uwa da abokan arziki ma dukka are invited dan walimar ita zata yi serving a matsayin yini, bayan ita kuma sai ayi kamu da daurin aure shikenan da dare akai amarya. Ita albarkar auren take nema, tana kuma neman Allah ya bata ikon cin jarabawar ta dan wannan auren ta san shine jarabawarta. Ta kuma daura damarar karbar sa hannu bibbiyu da fatan samum dacewa albarkar biyayyar da zata yiwa iyayenta.

Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya inji Hausawa, ranar da aka saka tazo kuma aka daura auren Hassan Aminu Abdullahi da Sumayya Yusuf. Sumayya ta sha kuka kamar ranta zai fita duk dauriyar da ta ringa yi akan maganar amma labarin daurin aure ta yana zuwa kunnenta ta fara kuka, dan wannan labarin shi yake tabbatar mata da cewa tayi bye bye da Adam, ita dashi sai dai wata kaddarar da ita kanta bata yiwa kanta fatan ta dan zata so ace zaman auren su da Hassan ya dore har tsufansu, sai ta samu kanta da tambayar kanta ko yaya Adam zai kalli auren nata in labari ya je masa? Musamman in ya san wanda ta aura din? Shin zai fahimci maganar ko kuma zai saka ta a matsayin cin amana? Kamar yadda tunda aka fara maganar take tunanin Ruqayyah a zuciyarta, shin tasan da maganar ko bata sani ba? Ya zata dauki maganar?

Ita ta fi kowa sanin cewa Ruqayyah bata son Hassan, tun sanda suna gida kafin ayi aurenta ta san bata son Hassan kudinsa take so kuma yanzu ta samu kudin, shin zata damu idan taji cewa twin sister dinta ta auri tsohon mijinta uban ƴaƴan ta. How will she reacts?

Ai kuwa dai Ruqayyah bata da labari sam dan ita gidanta kamar kango yake, ga shi dai hadadde kayatacce amma kuma babu kowa sai yan aiki, su kadai suke bidirin su a gidan dan ita sai ta kwana biyu ma bata sauko kasa ba dan yanzu saukowar tana yi mata wahala sosai, sai dai da safe a shiga a gyara mata dakunan ta sannan akai mata breakfast, in an gama na rana ma akai mata, duk abinda babu kuma a gaya mata ta bayar da kudi a siyo.

Sometimes sai take wondering wai kudin nan ma kamar yan aikin ne suke cinye su dan ko ba komai abincin da take siya duk wata ba ita take cin kashi daya cikin goman shi ba, bata so kuma ta matsa musu kar su tarwatse su barta, ga kuma albashi da take basu duk wata. Wannan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login