Showing 225001 words to 228000 words out of 300844 words
gida amma taki. "Mu bamu guje ta ba, ita ta guje mu ta zabi dukiya akan mu. Ina fadar haka ne yanzu a gaban duniya ba wai dan bana son Ruqayyah ba sai don ina sonta sosai da sosai, ina fatan court zata kama ta da laifin da ake tuhumar ta, ina fatan za'a hukunta ta, kuma ina fatan hakan zai zamanto sanadiyyar shiryuwar ta".
Tabbas maganganun Baba sun taba kowa a court din, harda shi kansa alkalin, daga nan sai aka kira Sumayya ta dora da bayanin halayyar Ruqayyah, Hassan ne next, ya fadi duk abinda ta ringa yi na nuna son kudi, yadda ta ringa comparing dinsa da kaninsa saboda dukiya. A karshe yace "duk uwar da tayi ikirarin tarwatsa nasabar danta data haifa da kanta saboda kudi, bana jin akwai abinda ba zata iya aikatawa ba saboda kudi".
Haka akayi ta kiran mutane kowa yana fadar aibun Ruqayyah, shi halin mutum tamkar inuwarsa ne, duk inda ya shiga sai ya bishi kuma indai aka haska shi da fitila sai an gani.
Hatta kawayenta sai da suka bayar da labarin yadda ta dauki hayar su a bikinta da Hassan da yadda ta nuna musu shine CEO na H and H, sai daga baya suka gane ba shi bane ba.
A karshe aka kirawo Adam, shi kuma yayi magana akan ranar da suka fara haduwa a motar sa da abinda ya faru a tsakanin su. Ya gama zai koma kenan ya zauna sai Lukman ya mike yace yana da tambayar da zaiyi masa. Ya mike ya tsaya a gaban sa yace "ka tafi da Fatima garin ku, baka dawo da ita ba kuma baka sanar da kowa kana tare da ita ba sai bayan shekara biyar, menene dalili?" Adam yace "nayi hakan ne saboda in kare ta, ina gudun abinda mahaifina zai iya yi mata idan na ki bin sharudan daya kafa min" yace "menene yace zaiyi mata idan ka fadi tana tare da kai?" Direct Adam yace "yace zai kashe ta, amma bai yi mata komai ba tunda ban karya duk dokar daya kafa min ba" Lukman yace "kuma kai ka yarda in ka karya dokar tasa zai kashe ta din?" Adam yace "nasan zai iya" Lukman yace "na yarda da kai, 100%, akan cewa zai iya din, dan a dan binciken da nayi na fahimci cewa mahaifinka mutum ne mai tsananin ra'ayin rikau akan kiyayyar hausawa kuma musulmai, musamman saboda yana ganin sune sanadiyyar raba ka da shi, tabbas zai iya kisa akan hakan, musamman kisan dan jaririn da zai iya zama masa tonon silili da kawo masa cikas akan manufarsa"
Adam ya bude baki ya kasa rufewa, yace "kamar ya? Ban gane mai kake cewa ba?" Lukman yace "tambayar da zanyi maka ta gaba ita ce, me ya sa tun farko baka fada cewa kaga wata mai kama da Ruqayyah dauke da wani abu mai kama da jariri a kusa da inda aka yi accident din ba?" Adam yace "saboda kamar yadda na fada tun ranar nan ban tabbatar ba, bana so in fadi abinda ban tabbatar ba" Lukman yace "daga baya kuma, bayan kowa ya gama kawo shaidar sa sai ka yi volunteer ka fada, a lokacin ka tabbatar din kenan?"
Adam yace "no, naga mai laifi tana neman ta tsallake shi yasa na fada ko hakan zai taimaka wa Shari'a" Lukman yace "zai taimaka wa Shari'a ko kuma zai taimaka maka wajen rufe naka laifin? Idan Ruqayyah ta dauki laifi shikenan babu wanda zai kuma bibiyar maganar jariri kuma" Adam cikin mamaki yace "me kake nufi ne wai?" Lukman yace "ina nufin bayan anyi accident, kai ne mutum na farko da ya ga Fatima, ita kanta Fatima ba zata iya tunawa da lokacin da ka ganta din ba, dan haka babu wanda yake da tabbas din cewa da ciki ka ganta ko babu ciki" Adam yace cikin bacin rai "babu ciki, na fada ai tun wancan karon, sanda na ganta babu ciki a jikinta kuma da alamar a lokacin ta haihu"
Lukman yace "haka ka fada, amma kai kadai ne kasan da haka mu duk bamu sani ba, zaka iya samar mana da shaidar cewa babu ciki a jikinta sanda ka ganta?" Yace "eh. Ina ganin ta babana yazo tare da yaran sa su biyu, a aika azo dasu zasu bayar da shaida" Lukman yace "nasan zaka ce haka, shi yasa tun kafin muzo nan na bibiya har garin naku har gidan naku amma sai na tarar da labarin cewa tun da ka dauko Fatima ka gudo da ita shi ma ya hada kayansa ya kara mai, ba'a san inda yake ba. Baka ganin yayi haka ne saboda yasan za'a tono wannan laifin?"
Adam ya dafe kansa, tabbas tun da suka zo Kano sun nemi numbers din daddyn sa sun rasa, sai sister dinsa ce take gaya musu cewa ya bar gida shima. Sun dauka fushi ne yayi dasu amma zai huce amma yanzu ga wannan batu. Yace "ba saboda wannan ne ya bar gida ba. Kuma bashi kadai ne shaida ba, akwai yaransa guda biyu da yazo dasu gurin zasu tabbatar da abinda nake fada" Lukman yace "in kace yaransa kana nufin masu yi masa dirty work, kana nufin zasu bayar da shaida akan abinda idan ma an aikata shi sune aka saka suka aikata"
Ran Adam ya gama baci, yace "na gaya maka ban dauki Fatima da ciki ba, babu ciki a jikin ta sanda na ganta, babana ko ni bamu da hannu a batan babyn Fatima" Lukman yace "baban naka da a yanzu kake furucin cewa zai iya kisa? Yanzu kuma kake cewa bai yi ba?" Adam ya buga hannun sa akan bench din gabansa yace "zai iya da yayi are two different things. Bai yi ba, kuma ba zan taba xewa yayi ba no matter how much I don't like him. If you like kayi min komai and I assure you I will be the last person da zakayi wa sharri, I will be the last person da ke" ya fada yana nuna Ruqayyah da hannu yace "zaki yiwa sharri"
Lukman yace "wannan ya nuna irin zafin zuciyar da kake dashi. Mai zafin zuciya kuwa ya kan iya aikata komai a lokacin da ransa ya baci" Adam yace "you can't prove anything" Lukman yace "tabbas, duk shaci fadi ne kawai nake yi, kamar yadda duk shaidun da ake gabatarwa akan Ruqayyah suke shaci fadi" sai yayi gaisuwa ya koma ya zauna
Alkali ya gama rubuce rubucen sa sannan yace "kotu ta dage karar zuwa mako mai zuwa, kafin na za'a sake mayar da Ruqayyah a kuma duba kwakwalwar ta kamar yadda masu kara suka bukata, sannan court ta bayar da order a rike Adam Clement a hannun yan sanda har zuwa sanda za'a gudanar da bincike a kansa"
Sumayya ta mike da sauri "karya suke yi masa wallahi" ta juya gurin Ruqayyah, "ta hanyar da kika ɓullo kenan? Ta inda kike tunanin zaki rama kenan? Dan na auri Hassan shine zaki yi sanadin da za'a rufe Adam?" Adam ya koma ya jingina da jikin kujerar da yake zaune akai ya rufe idonsa. Yana ji ana ta hayaniya a court din yayin da security suke kokarin saka order. Yana ji har aka zo aka kama shi aka saka masa handcuffs za'a fita dashi daga gurin. Aka bi dashi ta gaban Fatima, sai ya tsaya ya dafa table din gabanta yana kallonta cikin ido yace "i didn't do it".
Bata ce masa komai ba aka wuce dashi.
Anje an sake gwada kwakwalwar Ruqayyah. Again, the result shows mental instability.
A ranar Fatima ta zauna da lawyers dinta. "Koda alkali ya yarda ta aikata laifin, hukuncin dazai iya yanke mata kawai shine a kaita gidan mahaukata tayi receiving treatment. Idan kuma ba gamsu tayi ba zai iya sakin ta free"
Fatima da take zaune emotionless tace "sannan zai iya sentencing Adam idan bai yi presenting shaidun da zasu gamsar dashi cewa bashi da laifi ba" babu wanda ya bata amsa sai ta mike tace "none of which will bring back my son" daga nan ta dauki jakarta ta fita.
Washegari, ranar daya kamata ayi zaman court sai ta riga kowa zuwa, tana zuwa tace "nazo zanyi withdrawing case din gabaki daya. Na janye kara".
* The Wishes*
Ba'a barta tayi signing ba sai da lawyers dinta suka zo, su kuma at first suka nuna mata rashin jin dadin su akan hakan "munyi winning fa, am sure with all the behavioral witnesses da muka gabatar shi kansa alkalin is convinced cewa ita tayi, yana holding Adam ne kawai for precautions amma ba zaiyi sentencing dinsa ba" tace "ita kuma me zata samu, two or three years a gidan mahaukata sai ace ta warke a sallamo ta? While only God knows where my son is? And in na bar case din Adam zai cigaba da zama a hannun police har sai ya gabatar da shaidar da zai nuna cewa ba shi ya dauki babyn ba. I won't let him suffer akan laifin da ni na san bai yi ba. I won't add this to his list of sufferings".
Dole suka hakura suka barta tayi signing komai, kafin su Ruqayyah da Lukman su zo gurin. Sannan suka karbi release letter daga gurin alkali suka tafi zasu fito da Adam tun kafin a taho dashi court.
A bangaren Adam, tun ranar da aka kama shi aka rufe yake cikin kunchi da damuwa, abubuwa ne suka taru suka yi masa yawa ta ko wanne bangare na rayuwarsa. Shi ba wai kama shi din ne ya dame shi sosai ba, zafin sharrin da akayi masa a gaban mutane ne, a gaban Fatima, a gaban Sumayya da duk wani wanda yake ganin mutuncinsa. Duk da yasan da yawa ba zasu yarda cewa yayi abinda aka ce yayi din ba amma dole ko yaya ne sai zargin sa ya shiga zuciyar wasu daga cikin su. Fatan sa dai shine zarginsa ko mai kankantar sa ya shiga zuciyar Fatima.
Shi yafi kowa sanin yadda Fatima take son dan nan nata, dan dashi ta dawo cikin hayyacin ta, son ganin sa ne ya taimaka mata gurin tuna ko wacece ita, sannan shi ya jawo ta zuwa dawowa cikin yan uwanta. Shin ya zata ji a ranta idan zargin shine ya rabata da danta ya shiga zuciyarta?
Abu na biyu da yake damunsa shine maganar da maman sa tazo tayi masa tun a ranar da aka kama shi kuma daga nan vata sake dawowa ba "ka gani ko? Ka ga abinda muke fada maka kullum ko Joseph? Wadannan mutanen ba mutanen kirki bane ba, basu damu da kai ba, basu damu da rayuwar ka ko mutuwar ka ba, kaga sakayyar da suka yi maka ko? Bayan kin jin maganar mu da kayi ka zabe su a kan mu sannan bayan duk wahalar da kasha akan yarinyar nan har sai da ta kaini nima nayi disobeying Baban ka dan ka taimaka musu ka dawo musu da yarsu amma kalle ka a yanzu? Ina fatan wannan zai zama darasi a gare ka, ina fatan idan ka fito zaka fahimci damu da su waye a side dinka, waye yake son ka da gaskiya. Ni zan tafi inje in nemo babanka duk da bansan inda zan same shi ba, amma zan nemo shi, zan kuma bashi labarin irin sakayyar da your muslim friends suka yi maka"
Tun da ta tafi yake juya maganar a ransa, a shekaru biyar din daya kasance tare da family dinsa, tare da Fatima, babu abinda yake yi besides kula da Fatima sai kokarin janyo hankalin mahaifansa da yanuwansa zuwa ga addinin Musulunci, kuma ya fahimci ya fara nasara a hankali musamman a bangaren Maman sa da sisters dinsa, complain dinsu shine basa son yadda Musulmin da suka sani suke behaving. "Suna da karya, yawancin su makaryata ne, ga cin amana, yaudara, munafurci, da sauran munanan halaye" ya kan yi dariya yace "wannan individual choices ne, it is not religious, teachings din addinin musulunci babu komai a cikinsa sai dabi'u masu kyau, duk wanda kuka ga yayi akasin haka to shi ya zabawa kansa kuma yana yi ne against addinin sa. Kunga kamar a Christian, shiga marar kyau, shaye shaye, zinace zinace, duk dabi'u ne munana a cikin addini amma kuma sune manyan dabiun da wasu Christians din suka rika a matsayin halayya. Dan haka ni da na zabi musulunci na zabane saboda addinin ba wai saboda masu addinin ba".
A lokacin sun gamsu da bayanan da yayi, dan har yana tunanin idan yayi Sa'a kafin babansa ya gama fushi ya dawo maybe maman sa ta musulunta dan ya lura ta rage zuwa church sosai, haka sisters dinsa, amma wannan abin da akayi masa tabbas ya dawo da lissafin sa baya dan ta kufula sosai, shi kuma ko kadan hakan bai sa soyayyar da yake wa musulunci ta ragu daga zuciyarsa ba. Tabbas akwai mutanen kirki a mudulmai kamar yadda akwai mutanen kirki a Christian.
Abu na uku shine maganar Sumayya, bai dauka haka maganar aurenta zata daga masa hankali ba, tunda tun yana can kullum yana kokarin gaya wa kansa cewa Sumayya ba zata jira shi ba zata yi auren ta, ya dauka yai bracing kansa for the news, kuma sanda news din yayi hitting dinsa sai yaji bai ji zafin sa sosai ba amma sai.....sai aranar da aka yi zama court na farko, a ranar da yaji wannan lawyer din na Ruqayyah ya ambaci Sumayya a matsayin matar Hassan, a ranar ne yaji labarin ya dake shi sosai, amma sai ya cigaba da karyata wa a zuciyarsa yana ganin kazafi ne irin na lawyers, Sumayya ba zata bata auren Hassan ba ko da mazan duniya sun kare.
Wannan ya sa yayi calming kansa down har aka tashi daga court din inda sam Sumayya taki yarda su hada ido dashi kamar yadda taki yarda su hada ido a gidan su Fatima, inda ya fara ganinta bayan dawowarsa. Kuma ko a can din ma dama yayi mamakin abinda ya kaita tunda yaji maganar cewa Hassan ya saki Ruqayyah. Bayan an tashi daga court din kuma sai yaga Hassan ya buɗe mata mota sun shiga tare sun tafi.
Farko yaji daci sosai a zuciyarsa, dacin da har ya saka shi ya fasa zuwa Kaduna ya gaishe dasu Baba kamar yadda da yayi niyya, yaji a zuciyarsa auren Sumayya da Hassan tamkar cin amana ne a gare shi. Yaji wani irin kishi, kishin da bai taba tunanin yana da irin sa ba, shin wai waye ma ya bada shawarar ayi wannan hadin gambizar auren ne? Ya san Baba ne, dan haka yayi fushi yaki zuwa ya gaishe shi ya koma kano ya cigaba da jinyar zuciyarsa kuma yana fatan cewa lift ne Hassan ya bawa Sumayya zai ajiye ta a gidan ta shima ta tafi nasa gidan.
Amma ranar zaman court na biyu, ranar da aka kama shi, sai yaji Baba da bakinsa ya fadi maganar auren kuma yace shi ya hada shi, sannan yaji Hassan a nasa bayanin ya fada sannan Ruqayyah ita ma ta fada. Wannan ya tabbatar masa, beyond doubt, cewa Hassan shine mijin Sumayya. Kuma wannan shine abinda ya fara hana shi bacci a kwanakin sa na farko a cell. Sai dai a hankali sai ya fara fahimtar cewa it is for the best, at least yasan Sumayya is in good hands dan Hassan mutumin kirki ne, a little strict but mutumin kirki ne.
Kama shi da akayi ko kuma tunanin hukuncin da za'a yanke masa duk basu daga masa hankali ba, yasan yana da gaskiya, yasan masu kokarin yi masa sharri basu da wata shaida mai karfi, dan haka yasan dole a karshe za'a sake shi ne. A haka har ranar zuwa Court ta zagayo yana lissafe, amma maimakon ya ga anzo an tafi dashi kamar yadda ya saka rai sai ya ga anzo an bude masa kofa ance "you are free to go".
A waje daya fito ya ganta, a tsaye a jikin mota tana magana da wasu maza su biyu wadanda ya gane a matsayin lawyers din ta, sai kuma yaga sun yi sallama kowa a cikin su yaje ya shiga motarsa ya tafi. Ta juyo tan kallon sa, sai yaji kunyar chukurkudewar kayan jikinsa, tace masa "let's go" yace "ba court zamu je ba? Na ga ba police" tace "will you like to drive ko ni in tuka?" Ya karbi key din a hannunta yace "I am your driver kar ki manta" ta zagaya ta zauna a gaba shi kuma ya zauna a seat din driver sannan tace "you are not my driver, kai drivern Hussain ne" yace "duk daya, abin Allah ai na annabi ne" ya tayar da motar yace "court?" Ta girgiza kai tace "an gama zaman court ai, na janye kara" ya bude ido "what? Why?" Bata amsa masa ba sai ta gyara zamata ta daura seat belt sannan tace "Kaduna zamu je. Gidan da Ruqayyah take. I want to talk to her".
**********************
Satin nan gaba ki daya Hassan ya zama very edgy. Shi kansa ya sani dan haka yake raba kansa da mutane, kusan koda yaushe idan baya tare da lawyers ko kuma tare da umar to yana garden din Aunty gurin kabarin Hussain. Baya shigowa gida sai ya gaji sosai yadda yana zuwa wanka kawai zaiyi ya kwanta. Sumayya ta fahimci hakan, kuma ta jingina hakan ga cewa fushi yake yi da ita saboda tayi magana akan kama Adam da akayi. Sai dai bata yi masa maganar ba kamar yadda shima bai yi mata maganar ba. Asali tamkar ya cire ta daga dukkan plans na shari'ar.
Sai dai hakan bai hana ta lissafin ranar komawa court din ba, ranar kuma tana tashi bayan ta shirya yara sun tafi school ta kuma hada wa Hassan ruwan wanka tare da fito masa da kayan da zai zaka ta kuma hada tare da ajiye masa duk abinda tasan zai bukata a kusa da kayan, ta fesa turare a jikin kayan kamar yadda ta saba yi masa kullum sai ta kom dakin ta ta shirya ita ma tare da Abdullahi sannan ta fito, a lokacin shima ya ke fitowa daga nasa dakin yana