Showing 159001 words to 162000 words out of 300844 words
fitowa ba sai kuma dare, kafin nan police sun tashi. Station din jiya ta sake komawa, har yanzu yaran da aka kama da motar suna tsare, sai dpo din ya shigar dashi office dinsa suka zauna yace "yaran nan ina ganin iyakacin gaskiyar su suka fada, bana jin sun san inda yaran nan yake. Barayi ne, irin kananan barayin nan na unguwa masu sane da satar waya, suna yafiya kawai suka ga motar a bakin hanya ita kadai, sun dauka ko mai motar ya fita ne zai kama ruwa shine suka tsaya da niyyar su tsorata shi su karbi wayar sa da yan kudaden hannunsa. To sai suka ga babu kowa a cikin motar, ga kuma key a jikin ignition shine kawai suka dauko motar suka shigo da ita Kaduna da niyyar su siyar da ita, to amma kasancewar motar babba ce dan irin ta guda uku ce a Kaduna sai ya sa suka kasa batar da ita, ta ki siyuwa har aka kama su da ita. Sun ga wayarka a cikin motar, sun cefanar da ita" Hassan yayi ajjiyar zuciya yace "wayar yaron fa?" Yace "basu ganta ba, mun duba motar kuma ba mu ganta ba muma". Hassan ya mike yace "ku yanke musu hukuncin duk daya dace, ni bani da case dasu, ni case dina shine na yaron nan" dpo ya mike shima yace "muna iyakacin kokarin mu, amma yaron tamkar wanda ya bace ne a cikin iska".
Da dare Hassan ya koma gurin Ruqayyah, tare da Aunty da dukkan kannensa da aunties dinsa guda uku. Suka duba ta ita kuma tayi musu gaisuwa. Sannan suka yi mata sallama suka koma gida, Hassan ya karbi number din Alhaji Kabiru a hannun Sumayya, sannan shima ya tafi. Da safe ya kira shi suka hadu yayi masa bayanin da Ruqayyah tayi masa na inda suka rabu da Minal da kuma yadda suka yi. Ya kuma roke shi alfarmar cewa duk abinda ake ciki ake sanar dashi, duk kuma wani taumako da ake bukata na kudi ko na wani abu azo gurinsa zai taimaka. Da haka suka rabu. Sai yaji a zuciyarsa yana tausayin Alhaji Kabiru, batan mata matar ma kuma mai tsohon ciki lallai akwai tashin hankali a ciki...
Kwanaki suka wuce har akayi sati daya da rasuwar Hussain. A cikin satin nan ba karamar wuta Ruqayyah ta hura wa Hassan ba akan lallai sai ya fita da ita waje taga likita dan har yau wannan likitan da yake ganinta bai gama tabbatar da abinda yake damunta ba. Ita gaba ki daya a tunanin ta fita waje shine babban solution din problem dinta. Dole Hassan ya nema musu bisa ita da Sumayya zuwa Germany, inda aka hada shi da wani doctor da akace ya kware a bangaren jijiyoyi, a hakan ma sai data nuna rashin jin dadin ta dan ita tafi son su tafi tare tana ganin zata fo samun kulawa in tana tare da shi, shi kuma yaki binta saboda he is not mentally ready, ji yake yi kamar yau ne Hussain ya mutu.
Ya riga ya gama shirya musu komai, daga asibiti za'a turo mota har airport ta dauke su,a asibitin kuma suna da duk abinda zasu bukata na yau da kullum, a kwai kuma mota idan suna son shiga cikin gari su nemi wani abu da babu a asibitin, duk bill kuma za'a turo wa Hassan. A haka suka rabu, ya kai su airport suka tashi sannan ya juyo da niyyar dawowa gida.
Amma sai me? Tun kafin ya karasa gida sai ga kira da number din Sumayya. Yayi packing gefe yana jin hankalin sa yana tashi ya dauka "Sumayya lafiya? Naga fa tashin ku da ido na, me ya faru" muryarta yaji cikin karkarwar baki tana magana "yaya Hassan, gamu a Abuja" yace "Abuja kuma? Me ya faru Sumayya kiyi magana mana" tace "jirgin yana tashi Ruqayyah ta fara complain da kunnenta wai kamar zai yi bursting, na dauka raki ne sai naga ta rude har da faduwa kasa tana kuka tana cewa azo a taimaka mata. Muna dubawa sai muka ga jini yana fitowa daga kunnuwan ta. Dole jirgin yayi emergency landing a Abuja aka ajiye mu, kafin mu sauka har ta suma".
Hassan ya dafe kansa yana maimaita innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Sai da yaji nutsuwa sannan yace "kuna ina yanzu?" Tace "muna hanya za'a kaimu asibiti. Ma'aikatan airport din ne suka dauke mu zasu kaimu" daga cikin wayar yana iya jiyo kukan Hussain Junior, Sumayya kuma duk a rude take kamar ma kuka take yi. Sai yace ta bawa driver wayar, ya tambaye su asibitin da zasu kai su suka gaya mishi sai ya kashe wayar sannan ya kifa kansa a jikin stirring yana mayar da numfashi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Me yake faruwa da su ne?
Daga nan bai karasa gida ba sai ya juya zuwa airport, bai kuma kira Aunty ya gaya mata ba saboda tana gudun duk wani abu da zai tayar mata da hankali. Sai daya je airport din sannan ya kira Jabir ya gaya masa in case ko za'a neme shi. Daga nan ya samu jirgi sai Abuja.
Kafin ya sauka har anyi admitting Ruqayyah kuma likitan kunne ya hau kanta yana bincikar abinda ya kawo mata ear bleeding. Sai bayan ya fito sannan Hassan ya karaso dan haka direct office dinsa ya wuce sai doctor yayi masa bayani kamar haka. "I am sorry sir, but matarka ta hadu da ear problem a sanadiyyar shiga jirgi da tayi with an ear infection wanda kuma it is not advisable. Ear drum dinta yayi bursting, sai munyi mata surgery a kunnuwan ta duk biyu sannan maybe jin ta zai dawo, but bani da tabbas din zai dawo dai dai. Sannan kuma abinda nake da tabbas akai shine, ko anyi nasarar aikin ko ba'a yi nasara ba, kar a kuma barinta ta hau jirgin sama ever again, in ta kuma hawa kuwa, zata yi loosing hearing dinta completely ko ma ta rasa ranta baki daya"
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, idan kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020.
*The Second Wave*
Hassan ya saki baki yana kallon doctor din, ya girgiza kansa yana dan dukan goshinsa wai dan ya farka idan bacci yake yi amma sai ya ganshi still a gaban doctor din da yake kallonsa. Ya bude bakinsa amma ya kasa magana. Ya kasa tabbatar da cewa dai dai kunnuwan sa suka jiyo masa, kamar fa ji yayi likitan yana cewa Ruqayyah ta kurumce. Matar sa Hassana. Precious wife dinsa.
Yace "doctor? What are you trying to say? Ni duk ban gane bayanin ka ba kayi min gwari gwari Please. Kana nufin Hassana ta kurmance ko me kake so ka gaya min" doctor din ya gyada kansa yace "haka nake nufi, ina nufin dodon kunnenta na dukka kunnuwa biyun ya samu matsala. A yanzu haka bata ji, in kayi mata magana ba zata ji ka ba but in ka saka hannu anyi mata aiki da gaggawa zata iya dawowa tana ji kadan kadan ba kamar da ba. Sai dai kuma kamar yadda na fada ina bada shawarar kar ta kuma attempting shiga jirgi ko da kuwa nan da Kaduna ne"
Hassan ya kuma dafe kansa yana ambaton innalillahi wa inna ilaihir rajiun, daga neman kafa kuma yanzu shikenan sai a rasa kunne kuma? Kunne fa, shi fa a gurinsa yana ganin kunne duk yafi muhimmanci a cikin sense organs na jikin mutum, saboda shine yake responsible for balance in baka da kunne kana rasa balance ne yadda ko tafiya ma wahala take zamar maka, wani rashin kunnen ma ya kan taba har da kwakwalwar mutum sai mutum ya zama kamar mai mental problem, shi yana ganin anya ma kuwa kunne bai fi ido muhimmanci a jiki ba?
Ya dago kansa yana kallon likitan da yake kallonsa seriously, sai ya mika masa hannu yace "kawo takardar inyi signing" ya mika masa ya saka hannu yace "yaushe za'a yi mata aikin?" Doctor yace "as soon as possible, kamar tomorrow morning insha Allah" Hassan yace "tomorrow morning? Ba za'a iya yi mata yau ba? I mean ba za'a iya yi mata yanzu kafin ta farka ba?" Doctor ya girgiza kai yace "noo, ba za'a iya ba. Muna bukatar preparation ita ma kuma muna bukatar preparing dinta. Dan ma kune, kuna da kudi, idan babu kudi wani ya kan dauki weeks ba'a yi masa aiki ba wani ma months, wani ma har abada ba za'a yi masa ba haka yana ji yana gani zai zama kurma" Hassan ya gyada kai a ransa yan godiya ga Allah, there is always something to be grateful for. Sai kuma yaji ya samu idea akan wani abu daya kamata yayi da kudin Hussain.
Sai dai kuma he is not looking forward to seeing Ruqayyah, dan bai san me zai ce mata ba kuma ko ya fada din ma ba jinsa zata yi ba. Yaji hawaye ya taru a idonsa, yana matukar tausayin ta a ransa, wannan shine ana kukan targade ga karaya ta samu. Ya fita ya tafi dakin da aka kwantar da ita, ya tarar tana bacci, fuskarta duk jirwayen hawaye, tana ta zabura alamar tsorata take yi a cikin baccon nata, Sumayya tana zaune a gefenta tana rera kuka a hankali, ga Hussain a hannunta. Yana shiga Sumayya ta mike tana kallonsa, tana jin kamar wani babban solution yazo da zaiyi maganin problem dinsu, sai dai abinda ta karanto a fuskarsa yasa ta koma ta zauna tana sake wani sabon lalen a kuka. Ya zauna a bakin gadon yana dora hannayensa akan goshin Ruqayyah, ya fara shafa gashinta a hankali sai yaji ta sauke ajjiyar zuciya. A ransa yace ina ma dai zata cigaba da baccin nan har zuwa sanda za'a yi mata aikin? Baya son tayi experiencing total deafness yafi son in akayi aikin ko yaya ne tana ji hankalin ta ba zai tashi kamar yadda zai tashi in taji dif ba.
A bangaren Ruqayyah kuma mafarki take yi, mafarki take yi wai gata a cikin daki tana karbar haihuwar Fatima sai Fatima ta miko mata babyn "in go shi ki kaishi gurin Hussain. Ki kaiwa Hussain shima ya ganshi" sai ta barta a gurin ta juya ta kama hanya tana tafiya da sauri tana waige, sai kawai taga orphanage a gabanta, ba tare da tunanin komai ba ta ajiye babyn a kofar orphanage din yana ta kuka ta juya da sauri amma bata fi taku biyar ba sai kafarta ta makale, tayi tayi ta kasa tafiya ga kukan babyn ya cika mata kunnuwan ta tana kokarin ya fasa mata dodon kunne, sai kuma kafafuwan ta suka fara motsewa a hankali suna komawa kanana, a hankali har suka komawa irin na jarirai, har ta fadi kasa tana birgima tana kuka irin na jarirai, sai kuma taga jaririn data ajiye shi kuma yana girma yana girma har ya zama katoton namiji mai cikar kamala da kwarjini, sai ya taso ya taho inda take ya tsaya a kanta yana kare mata kallo, kamannin sa sak irin na Hassan sai kuma ya rikide ya koma Hussain sannan ya daga kafarsa wadda take sanye ta wani kafcecen takalmi ya sai ta tada niyyar talitse ta.
Ta farka a firgice tare kwalla kara "Hussain" amma kuma sai taji bata ji muryar tata ba, bata ji komai ba sai wani irin duumm marar dadi mai shiga har cikin kwakwalwar mutum. Ta bude idanuwan ta tana numfashi sama sama, sai ta ga Sumayya a zaune kamar kuka take yi tunda ga hawaye nan a idonta amma kuma bata jin karar kukan nata, ta ji an taba ta sai ta zabura ta waiga taga Hassan, me Hassan yake yi a nan? Ita dai a saninta sun bar shi a kaduna su sun tafi Germany inda zata ga likitan kafa. Ina ne kuma nan? Mai suke yi anan tare da Hassan?
Tayi kokarin tambaya "me muke yi anan? Ina ne nan?" Amma sai taji bata jin maganar tata. Sai ta tuna da abinda ya faru da ita a jirgi, the pain, the blood, sai ta saka hannayenta biyu tana dukan kunnuwan ta dasu "menene ya samu kunne na? Wayyo Allah na na shiga uku, menene a kunne na? Hassan, mijina ka taimaka min wani abu ya shigar min kunne na" Hassan ya fara kokarin kamata, yana yi mata magana, tana ganin bakinsa yana motsawa amma sam bata jin abinda yake fada, tana ganin Sumayya tana kuka tana magana amma ita ma bata jin abinda take fada. Ta kara rikicewa, ta mirgino ta fado daga kan gadon, ta fara kokarin tashi amma kafa taki cooperating. Hassan yayi sauri ya daga ta yana kokarin rungume ta ya lallashe ta amma taki barin shi, kuka take yi tana magana da karfi tamkar zata tsaga masa nasa dodon kunnen, babu shiri Sumayya ta kwantar da Hussain shima da hayaniyar uwar ta sa ta tashe shi ya fara kuka ta fita waje da sauri ta samo nurse, haka suka hadu da kyar suka rirrike Ruqayyah sannan suka sake yi mata wata allurar baccin ta koma.
Kafin dare labari ya iske gida, Aunty ta hada Nafisa da Zulaihat sannan suka biya suka dauko Inna da sassafe suka taho Abuja, lokacin da suka isa har an shiga da Ruqayyah dakin da za'a yi mata aiki dan haka sai suka hadu da Sumayya suka zauna zaman jira kawai da addu'a a bakin ta na samun nasarar yin aikin. Nafisa tace "ni ban taba ji ba, ko a labarai ban taba jin wanda ya samu irin wannan problem din ba kawai dan ya hau jirgi. Kuma jirgin nan ba yau ta fara hawansa ba da duk bai sa mata ciwon ba sai yau?" Sumayya tace "doctor din yace ana samu but it is very very rear. Amma yana saka ran success a surgery din sai dai kuma babu sake shiga jirgi a gun Ruqayyah" Zulaihat tace "to wa yake ta shiga jirgi kuma? Ana maganar lafiya? Fatan mu dai kawai ta samu lafiya dan itace tafi komai muhimmanci yanzu a gare ta" Sumayya ta gyada kai, amma a ranta tasan maganar shiga jirgin nan ba karamin taba zuciyar Ruqayyah zata yi ba. She is not going to like the news.
Alhamdulillah anyi aiki lafiya an kuma gama lafiya, aka turo Ruqayyah aka fito da ita yan uwanta suna ta bin ta da addu'a kowa yana cikin alhini da tausayin ta. Inna kuma ta na tayi mata addu'ar Allah ya bata karfin zuciyar da zata karbi kaddarar ta da hannu bibbiyu. A haka har ta farka, ta gansu a zagaye da ita suna kallon ta, Sumayya ido ya kumbura saboda kuka, still tana jin wannan feeling din marar dadi a kunnenta. Ta saka hannu da niyyar bubbuga kunnen wai ko zai bude amma sai ta ji su a nannade da bandage, sai a lokacin tunani yazo mata, tunanin irin azabar da taji a kunnenta lokacin da jirgin su ya tashi da kuma yaddata taba taji jini yana fitowa daga kunnen. Bata bukatar tambaya tasan ta samu matsala a kunnenta, bata bukatar tambaya tasan tafiyarta zuwa Germany ganin likitan kafa bata yi ba, sai ta fara kuka a hankali ba irin na jiya ba, tana kallon yadda bakunan su suke motsawa tasan sannu suke yi mata da kuma kokarin bata hakuri amma sai ta mayar da idonta ta rufe tana cigaba da kukan ta dan ba jin abinda suke cewa take yi ba. Wannan wacce irin mummunar kaddara ce? Ita Ruqayyan ita ce ta kurumce bayan kuma kafar ta da har yanzu aka kasa gane menene matsalar ta?
Babu wanda bai tausayawa halin da Ruqayyah take ciki ba musanman Hassan wanda bayan ta tashi ya fahimci bata jin abinda suke cewa sai ya koma gurin doctor da complain, amma sai doctor din yace masa ai ba yanzu ne zata ji din ba sai aikin yayi healing an kunce bandage din. Sai nan da sati biyu masu zuwa tukunna sannan za'a tabbatar da success din surgery din ko akasin haka.
A cikin sati biyun nan Hassan da Sumayya sun kasance tare da Ruqayyah, supporting her, encouraging her tayi accepting duk abinda result din ya nuna amma ita ta tubure so take yi su bar asibitin, su bar Nigeria gabaki daya su tafi kasar waje tunda ita a ganinta acan ne zata samu lafiya, gani take nan kawai karasa lalata mata kunnen zasu yi ga kuma kafarta da take getting worst everyday. Sai dai har yanzu Hassan ya kasa samun courage din gaya mata abinda likita yace, tausayinta yake ji, ya kasa samun right time da zai ganta cikin mood mai kyau yayi mata bayani, kullum cikin kuka take, kullum cikin mita take. Ga magana da karfi in ya nuna mata ta rage Muryar ta sai ta fara kuka tana ganin kamar yana mocking dinta ne. In zasuyi mata magana a takarda suke rubuta mata, in zata basu amsa kuma sai ta fada, da karfi kamar zata tsaga dakin. Ta zama very edgy, abu kadan sai fada sai kuka shi har tsoron shiga dakin yake yi gurinta shi yasa yake jinjinawa kokarin Sumayya dan tunda suka zo tana tare da Ruqayyah ko nan da can bata zuwa tana ta hidima da Hussain ga kuma nata ciwon da yake cin zuciyarta na rashin sanin inda Adam yake. Amma bai taba jin tayi complain ba ko sau daya. Wannan yasa ya karbi Hussain daga hannunta ya mayar dashi Kaduna gurin Inna aka cigaba da bashi madara dan ga uwar tasa nan amma ba samun shan nonon yake yi ba madarar ake bashi.
Ranar da sati biyun suka cika a ranar ne aka budewa Ruqayyah bandage din kunnen ta, doctor din ya kunce tare da wanke kunnen a gaban Hassan da Sumayya sannan ya gwada yiwa Ruqayyah magana "Hajiya Ruqayyah, can you hear me?" Ta juyo tana kallon sa, tana ganin bakin sa yana motsawa sannan tana jiyo Maganar sa can nesa kamar irin ana hira a makota din nan. Bata fahimtar abinda yake cewa sai data tattara dukkan hankalin ta a guri daya