Showing 45001 words to 48000 words out of 300844 words

Chapter 16 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2041

Hassan ya yarda da hakan, gwara yaje ya gani da idonsa kar ya sayi abinda bashi yake so ba.

Washegari da sassafe kafin yaje office agent din yazo ya dauke shi suka je ganin gidan. Madaidaici ne kamar yadda ya bukata. Cikin gidan akwai dakunan bacci guda uku da kuma madaidaicin falo kowanne daki kuma da bandaki a ciki. Sai tsakar gidan da aka rufe kasan sa da interlocks, sai kitchen da bandaki a tsakar gidan. Akwai kuma dan siririn soro, a cikin soron akwai daki wanda yake da kofa guda biyu daya ta soro daya ta tsakar. Ya gyada kai cikin gamsuwa, komai yayi yadda yake so kawai dai yaso a samu shago a kofar gida inda yayi niyyar zubawa sulaiman kayan provisions ya ringa siyarwa inya dawo daga school. With that and salary din daya yi doubling ya bawa Baba, da kuma shi a matsayin sirikin gidan, yana ganin they are set for life.

A take ya saka hannu a takardar siyan gidan sannan kuma ya tura kudin, duk da cewa yayi tunanin cewa gidan yayi tsada da yawa but for Hassana it is worth it. Yayi tunanin irin farin cikin da gidan zai saka ta, ya tuno irin farin cikin da ya gani a idobta ranar daya ke kunna mata wayar da Hussain ya siya mata.

Briefly ya sa akayi furnishing gidan, light furnitures irin wanda yasan ko shi zai iya amfani dasu sannan wadanda yasan su din zasu yi murna dasu sosai.

Daga nan kuwa sai ya sake ware wasu kudin masu kauri ya kaiwa Aunty "Aunty maganar lefe, nace kina ganin wannan kudin zai isa?" Ta duba kudin tace "zai isa mana, in dai ba irin na Hussain kake son kayi ba" ta karasa tana dariya, shima yayi dariya yace "Allah ya kiyaye, wadannan barsu kawai, Hussain shi kudi kamar mintsinin sa suke yi" sai kuma ya kara da cewa "kuma shi saboda irin gidan da ya debo wa kansa aure ya saka banyi masa maganar ya rage kayan ba, abu ne na manya da manya" ya fada sarcastically.

Aunty ta girgiza kanta tace "kasan halin Hussain ko ba gimbiya Fatima bace bama irin abinda zai yi kenan. Ballantana kamar yadda ka fada ai shi tuwon girma miyarsa nama ce" Hassan ya mike yana cewa "ai shikenan. Sai yaje yayi ta cin naman" Aunty ta sake daukan kudin ta juya tace "amma fa in bai isa ba zamu ce maka ka karo" yana dariya yace "manage it aunty, bafa gimbiya Fatima ba ce ba".

An sanar da Baba maganar zuwa neman aure amma sai ya umarce su dasu hadu a Zaria gidan yayansa Malam Isyaku. Haka akayi kuwa suka hadu acan suka tambayar wa Hassan auren Hassana , a take aka ce an bashi, sai suka nemi a saka musu ranar da zata hadu da ta yan uwansa nan da wata uku da yan kwanaki. Malam Isyaku yace "anya kuwa? Wata uku ai yayi mana kadan ace mun shirya aurar da ya a cikin su. Kuyi dai wancan din wannan kuma sai a shirya a tsanake sannan ayi shi daga baya.

Baba Mustapha, ganin baban su Hassan yace "haba malam, wacce shiryawa zakuyi kuma? Mu ai ƴa kawai muka zo nema gurin ku bama bukatar komai daga gare ku. A yadda Hassan ya a bani labarin yarinyar nan ai nasan idan ma bashi zata aura ba shi zai yi mata kayan daki ballantana shi zata aura. Babu wani abu. Ita kawai zaku bamu. Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya da zuriya mai albarka". Anan jayayya ta kare, date fixed.

Bayan dawowar Baba daga Zariya ne yan uwa suka yi ta tururuwar zuwa gar gida suna yi musu murna shi da Inna Ade. Fatsar su tayi babban kamu. Ruqayyah kuwa kullum bata iya rufe bakinta dan murna, lissafi take tayi na irin shagalin bikin da za'a sha, irin wanda aka jima ba ayi irinsa a Kaduna ba. "I can't wait to see the reaction on my friends faces. Ruqayyah a ina kika hadu da mai H & H? Ko yanuwanku ne dama?" Ita kuma will be like "gani na kawai yayi a hanya ya like min. Yaga irin zubin matar manya" ta lissafa adadin parties din da za'a yi, dinner, luncheon, Arabian night, mother's day, sisters eve. Irin kayan da zata ke sakawa zuwa kowanne event da kuma irin kawayen da zata je dasu "ba kowa za'a gayyata ba, kar suje su ba ni kunya a cikin dangin miji".

Bayan Hussain ya dawo ne ya aiko wa da Ruqayyah tsaraba. Wani set din mayukan gyaran gashi ne, ya kira ta yace "gimbiya ta ce ta bani sako in siyo mata, shine kema na siyo miki ban sani ba ko zaki so shi. Kayan ku ne na mata, ni ban san kyansu ba" Ruqayyah ta bude dan akawatin kayan tana dubawa, ita duk bata san ma ya akeyin amfani dasu ba. Tayi tsaki ta mayar ta rufe. "Wannan Fatimah daga dukkan alamu ta fiya iyayi".

Hussain yana dawowa ya tarar an gama saka rana, dan haka shi kuma sai ya mayar da hankalinsa kan ginin gidajensu. Shi Hussain a nasa tsarin so yayi yayi mudu ginin iri daya, komai daya, amma Hassan yana ganin plan din ya girgiza kai yace "wadanna dakunan duk me za'a yi dasu? Ni gaskiya bana son wannan plan din sai kace ba za'a bar duniya ba" Hussain yayi kamar zaiyi kuka yace "dan girman Allah kar ka bata mana tsarin nan, mun riga mun gama shirya komai na gama magana da engineers din nan sun gama fitar da plan dinsu....." Hassan yace " sai ayi maka naka plan din daban ayi min nawa daban. Ni I won't be feeling comfortable a irin wadannan gidajen" haka Hussain a dolensa ya hakura saboda babu yadda zaiyi amma shi a son ransa yaso ace iri daya suka yi, komai iri daya.

A karshe sai da Hussain ya hada baki da engineers din sannan suka shawo kan Hassan ya bari aka dora masa bene, amma shi da cewa yayi shi baya son bene "ni bana jin zan iya rayuwa a sama kamar wani tsuntsu" sai engineer yace "amma oga Hassan tunda an riga an dora wa Hussain in ba'ayi a naka ba gidajen ba zasuyi kyau, zasu zama dogo da gajere kenan. Sannan kuma ginin oga Hussain zai toshe maka iska a naka gidan". Da wannan aka samu Hassan ya yarda, amma shi ya tsara kayansa. "Two bedrooms a sama three bedrooms a ƙasa. Shikenan sun ishe mu. Ni plan dina na rayuwa da mace daya ne ni Hassana ta ishe ni har abada. Tunda muna kusa da gida nasan ba wasu baƙin kwana zamu ke samu ba sai dai daga nata bangaren, suma in sunzo dakunan kasa guda uku sun ishe su" Hussain yayi ajjiyar zuciya yace "wannan Hassana, ina tausaya muku kai da ita".

Haka aka yi ginin part din Hassan aka gama, kullum yana gurin yan tabbatar wa cewa anyi masa yadda ya tsara abinsa. Ssi da aka gam ak koma kan na Hussain anan aka kure adakar gayu. Part dinsa daban na gimbiya daban na bakinta daban na bakinsa daban. Faluka iri-iri, ga gym ga swimming pool, irin kofofi da fitulun da aka saka a gidan ma kadai abin kallo ne. Amma Hassan ko a jikinsa bai ji cewa gidan Hussain ya burge shi ba. Shi tsarin nasa yafi yi masa kyau sosai dan har yana tunanin in ya fara gini irin wannan tsarin zaiyi sai dai maybe ya dan fi wannan girma saboda lokacin an fara tara iyali. He just can't wait yayi rayuwa da hassanar sa a wannan gidan.

Ana tsakiyar shirye shiryen ne ya dauki Hussain ya kai shi gidan daya siyawa Baba ya gani, yayi masa bayanin aikin daya dauke shi da irin albashin daya bashi. Hussain ya gyada kai yace "ka kyauta sosai, yayi kyau sosai. Ni kuma a tawa gudun mawar zan siya masa napep yake zuwa dashi gurin aiki, ranar kuma da bashi ne da duty ba sai ya zagaya ya samu karin kudin cefane"

Hassan yayi masa godiya suka bar gidan. A hanya Hussain yake cewa Hassan "amma sai yaushe zaka bashi?" Hassan ya yi murmushi yana shafa kansa yace "sai satin bikin mu, sai su tare a sabon gida suyi bikinsu acan" Hussain yace "why? Hassan the planner. Da nine a ranar da na siya, maybe ma kafin inga gidan shi zan dauka muje mu gani tare. To me zan jira kuma? Yanxu in kai ka mutu kafin biki ko kuma shi ya mutu kaga ai siyan gidan bai yi serving amfaninsa ba".


Seventeen: Ungrateful

Hassan ya dauke kai tana bata fuska "kai dai baka da zance sai na mutuwa, kullum sai ka ambaci mutuwa kake jin dadi, at the same time kuma kana gina rayuwa kamar ba zaka mutu din ba. Sometimes I find you confusing wallahi" Hussain yayi dariya "to mutuwa ai dole ce, kullum saka rai nake cewa ba zan kai gobe ba shi yasa bana taba barin abinda zan iya yi yau ince sai gobe, at the same time kuma ina living rayuwata the fullest tunda nasan in na mutun bani da second chance, ina kashewa kaina da mutanen da suke tare dani kuɗi saboda ina ganin basu da wani amfani banda a kashe su din, to inna ajiye me zasu yi min? In na mutu sai dai dangi suyi fada akan su to ba gwara in basu ba sanda nake raye? Ni fa kullum ina addu'ar ka da Allah ya bani kudin da ba zan iya kashewa ba".


Hassan ya jinjina maganar Hussain a ransa, to ko dai ya bawa Baba gidan nan ne yanzu? Yana tunanin rikicin da zasu yi akan gidan kafin ya karba amma kuma sai ya yanke wata shawara. A iya kacin saninsa da Baba yasan babu abinda yake so sama da iyalinsa, dan haka dasu zaiyi amfani. Ya gama shirinsa tsaf sannan ya yiwa Ruqayyah waya "hello sweetie. Ya gida" ta gyara kwanciyarta tace "lafiya kalau. Ya office?" Yace "na dawo ai tun dazu. Baba yana gida kuwa?" Tace "eh, ya dawo" yace "Okay, ko zaku tambayeshi dake da Sumayya da su Zunnur ku shirya zan zo in dauke ku mu tafi unguwa" ta mike zaune daga kwanciyar da take tace "ina zamu je?" Yayi murmushi "it is going to be a surprise" tace "ina ne dan Allah" yace "to in na gaya miki kuma ai bai zama surprise din ba kenan"

Tayi rolling idonta cikin takaici, ita bata taba ganin mai zurfin ciki irin Hassan ba, baya taba gaya mata komai, shi hirar sa kawai ta kalaman soyayya ce wanda dasu da kuma kwarjinin sa yake amfani gurin kashe mata baki ta kasa challenging dinsa, amma sam bata jin dadin yadda alakar su take tafiya, sam bata jin dadin abubuwan da take fahimta a tare dashi sai dai ba zata yi magana, ko da zata iya challenging din nasa ma ba zata yi ba saboda kar ya fahimci true color dinta yace ya fasa. Target dinta daya shine a daura auren dai, in ta riga ta shiga gidan sa a matsayin matarsa kuma ai shikenan tana da control over duk wani abu da yake nasa.

Ta tashi ta fita tsakar gida in da sauran yan gidan suke, Baba ya a magana "Zunnur in na dauki albashin wannan watan keke zan siya maka. Saboda ka rage wahalar zuwa makaranta" Zunnur ya tashi da murna yan uwansa suna taya shi, Ruqayyah ta tabe baki, su keke manya.

Ta durkusa a gaban Baba "Baba dama Hassan ne yayo waya yace mu shirya ni da sauran yara zai zo ya dauke mu zamu je unguwa" Baba ya bata fuska "unguwa kuma? Wacce unguwa?" Ta tabe Baki "nima bai gaya min ba fa, ya dai ce wai wani mamaki zai bamu. Ba zai wuce shopping ne zai kai mu ba" a ranta ta karasa da cewa "it is about time daya kamata ya bude wannan matsatstsen aljihun nasa"

Baba yayi shiru bai ce komai ba, Inna Ade tace "tunda da sauran yara zasu je ai ina ganin babu komai ko Baban biyu? Kaga bikin ya fara matsowa sosai yanzu haka wani abu ne daya shafi bikin nasu" Sumayya cikin doki tace "baba mu shirya, yanzu haka gidan da zasu zauna zai kai mu mu gani" Inna Ade tace "haka ne kuwa, shi din nema yanzu haka" Baba yace "sai ku tashi ku shirya ai, ku bi a hankali, banda rawar kai banda kwadayi".

Ai kuwa cikin murna suka mike da sauri suka shirya, su Ruqayyah suka yi dressing daga cikin sababbin kayan su suka yi wa juna kwalliy mai kyau, sunyi kuma matukar kyau da yanayin su mai daukan hankali. Sun gama shiryawa kenan Hassan yayo waya cewa gashi nan ya kara so, suka yi wa Inna sallama suka fita tana yi musu fatan alkhairi.

Suna fita ya bude musu mota suka shiga. Ruqayyah ta zauna a gaba kusa dashi su kuma duk suka shiga baya suna hada baƙi gurin gaishe shi. Ya amsa musu individually kowa yana tambayarshi makaranta, sai da suka nutsu suna kus kus a tsakanin su suna santin motar sannan ya juya side din Ruqayyah yace "ranki ya dade" tayi murmushi tana sunkuyar da kanta tace "tare da naka" daga nan bata kuma cewa komai ba, hankalin ta yana kan titinan da suke bi tana lissafin wanne mall zasu je, wanne nema wanda yake tashe yanzu?

Sama sama Hassan yaje hira da kannen Ruqayyah, lokaci zuwa lokaci kuma yana juyo wa ya kalle ta yayi mata murmushi itama ta mayar masa, shi shirun ta da nutsuwarta suna burge shi sosai, wannan yana nuna cewa bata da hayaniya kamar yadda yake so sannan kuma bata da mita.

A kofar gidan ya tsaya, duk suka juya suna kallon gidan with different thought a zuciyoyin su.
Ruqayyah "wait! What? Ba dai nanne gidan da zamu zauna din ba"
Sumayya "kai!!!, Ji wani gida mai kyau"
Sulaiman "duk sanda na tashi yin gidana irin wannan kofar zan saka"
Zunnur "me muke yi anan?"

Hassan ya bude motar yana cewa "okay, we are here, kowa ya fito" suka fara fitowa daya bayan daya duk idon su akan gidan, Ruqayyah trying so hard not to scream. Ya dauko key ya bude gidan fuskarsa cike da farin ciki yace "ku shigo, kowa ya zagaya ya gaya min view dinsa akan gidan nan".

Ruqayyah a tsakar gida ta tsaya tana jin kamar kafafuwanta ba zasu iya kaita double door din da taga sun shiga ba, sai da Sumayya ta dawo da sauri ta ja hannun ta. "Zo ki gani, Ruqayyah, har furnitures an saka" Ruqayyah bata ce komai ba ta dai bita a baya kirjinta yana bugawa.

Ɗakunan guda uku duk an saka musu set din gado masu kyau da labulaye, falon ma an saka set din kujeru irin wadanda ita kanta Ruqayyah ta san cewa bata taba hawa irin wannan kujerar ba amma duk da haka ji tayi sam basu yi mata ba, sam basu dace da ceo na H and H ba. Ga set din kayan kallo, plasma tv ce amma Ruqayyah a idonta sai taga it is not big enough, ita katuwa ta ke so.

Hassan sai murmushi yake yi yadda yaga yaran suna zagaya gidan cikin murna, ko bai tambaya ba yasan cewa gidan yayi musu. Yaga Ruqayyah a tsaye a falo tana daddanna wayarta sai ya saka hannu ya karbe wayar yana cewa "I am here, ba sai kin kalli hotuna na ba" ta dan yi murmushi tace "to ai baka tsaya na kalle ka ba, kana ta zagaye" yace "ke ma ba sai ki zo muyi zagayen ba?"

Tace "bana jin dadi ne, kafafuwana suke ciwo" taga yanayinsa ya chanja, ya durkusa a gabanta yana kallon kafafuwanta da suke sanye da takalmi tace "subhanallah. Wacce ce daga ciki take yin ciwon?" ta kara jan skirt dinta kasa tana kuma rufe kafafuwanta tace "ba nan bane ai yake ciwon" ya dago kai yana kallon ta yace "ina ne yake ciwon?" Ta juya masa baya tana jin zuciyarta tana zafi, kamar zata yi kuka take ji.

A lokacin ne su Sumayya suka fito daga dakin da suka shiga na karshe, suka dawo palo, Zunnur yace "kai! Wannan tv da girma take, zata yi dadin kallon ball" Hassan yayi dariya yace "you like it?" Duk suka amsa da yes banda Ruqayyah data juya musu baya tana kokarin rike hawayen ta. Sumayya tace masa "nan ne gidan ka? Anan zaku zauna da Rukee?" Yace "yaya Ruqayyah, yaya Ruqayyah zaki ke ce mata ba Rukee ba, and no, ba gida na bane ba kuma ba anan zamu zauna ba" Ruqayyah ta juyo tana jin kamar an yaye mata wani abu a kirjinta. Yace " wannan sabon gidan ku ne dana siya muku , nan nake so ku dawo tare da Baba da Inna ku cigaba da rayuwar ku anan".

Yaran suka dauki sowa gaba ki daya, Ruqayyah ma ta rufe bakinta tana dariya, wannan ce dariya ta farko data yi tunda suka shigo gidan, Hassan yace da samarin "ga naku dakin can a soro, akwai tvn ku a ciki da zaku yi ta kallon ku a ciki. Ku zo muje in nuna muku" suka bishi a baya da sauri suna hada hanya.

Sai a lokacin Sumayya ta zagaya da Ruqayyah ta ga gidan, sai a lokacin taga kayan sunyi mata kyau amma da duk dusu dusu ta gan su. Sai a lokacin ta lura da cewa toilets din modern ne. Suka fito suka yi joining sauran a dakin soro inda aka yi masa tsarin samari da toilet dinsu. Sai da suka gama sannan suka fito, ya rufe gidan suka shiga mota suka juya suna barin gurin. Ruqayyah ta juya tana kallon gidan, sai taga baiyi mata kama da gidan su matar mamallakin H and H ba.

A hanya ne yake ce musu. "Ya kuka ga gidan? Yayi muku? Suka yi dariya, Sumayya tace "yayi mana, sosai ma kuwa. Mungode mungode Allah ya saka muka da alkhairi Allah ya biya ka da aljanna" yace "ameen na gode nima da addu'a. Yanzu abu daya nake nema daga gurinku shine ku taimaka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login