Showing 276001 words to 279000 words out of 300844 words
gama sannan ya zauna ya dauko phone dinsa, sai yanzu ya tuna da ita dan he is not a phone person, tsakanin sa da ita ya dauka yayi waya kawai, wannan yasa mostly in yana gida kasheta yake yi in ba haka ba clients zasu yi ta damunsa ne da zancen aiki, shi kuma in yana gida yafi son yayi dedicating time din to his family, aiki kuma sai yayi shi a work hours.
Yana kwance a kan kujera da Afnan akan kirjinsa ya kunna wayar sannan ya ajiye ta a gefe yana sauraron hirar da Aysha take masa, duk a kokarin ta na ganin ya hakura da laifin da tayi masa, an jima kadan ya dauki wayar yana duba sakonnin da suka shigo masa, a lokacin ne yaga missed call din Madam Merry, shugabar gidan marayu na kasa, ya shafa fuskarsa yana tunanin dalilin da zai saka ta kira shi a wannan lokacin, last week yaje ya kai musu abinda ya ke kai musu duk wata a tallafin kula da marayun, to ko wani urgent issue ne ya taso kuma? Ko dai.......
Yayi sauri ya kawar da maganar daga ransa tare da ajiye wayar a gefe amma sai ya kasa ture maganar gefen, ya kalli Sultan daya kwanta akan carpet yana bacci sannan ya mayar da dubansa kan Aysha yace "wannan yarinyar, Afny, farin nan nata kina ganin maybe ko ta same shi ne daga family dina? Ina nufin biological family dina" Aysha ta dora hannunta akan nasa, ba zata iya tunawa da ranar da yayi mata magana irin wannan ba, sai tayi murmushi tana rike hannunsa a cikin nata tace "haka ne fa, kasan nima nayi wannan tunanin kawai gaya maka ne ban yi ba" ya gyada kai kawai yana jin ina ma bai furta maganar ba, maganar iyayensa ta na saka masa wani irin longing for them.
Sai ya chanja topic din hirar yana bata labarin Aisha, da kuma decision din daya yanke na yanke alakar sa da ita. Yaga alamar hankalin ta ya kwanta sosai akan maganar, musamman data fahimci cewa ba wata soyayya mai zurfi ce a tsakanin su ba.
Bai kira Madam Merry ba saboda dare yayi, amma sai yayi wa kansa alkawarin zai kira ga first thing in the morning dan yaji kiran da tayi masa, "ba zai wuce wani emergency taimako ne suke nema ba". Da safen ma bai kira ta ba sai da yaje office ya gama da abubuwan da suke buƙatar immediate attention din sa sannan ya dauko waya ya kira ta. Haka kawai yaji zuciyarsa tana bugawa da karfi, ko dan mafarkin da yayi ne? Bugu daya ta dauka, yana kokarin gaishe ta tace "nayi ta kiran ka jiya, you didn't pick up and you didn't return my call" ya dan bata rai, shi ya tsani ace za'a yi masa fada, yace "ban gani da wuri ba, hope everything is okay" tace "basu neme ka ba? I thought they should have contacted you by now" yawun bakinsa ya kafe yace "su wa ye" "your siblings" ta fada excitedly.
Ya cire wayar daga kunnensa ya kalla dan ya tabbatar da gaske waya yake yi ba daydreaming ba, ya ga sunan ta baro baro a screen din sannan kuma ga seconds suna tafiya, ya mayar da wayar kunnen sa yace "am sorry, banji me kika ce last ba, network yana cutting" tace "your siblings were here yesterday, three of them, suna neman ka" ya girgiza kansa da sauri yace "nooo, you are wrong, ni bani da siblings kuma kin san da haka" tace "not anymore Amir, yanuwanka sun zo suna neman ka" yace "maybe yan uwan wani sunzo suna nemansa, ba lallai ni suke nema ba, how can you be sure cewa ni suke nema? Akwai wata shaida da suka kawo? As far as I know babu wata shaida da aka barni da ita sanda aka yar dani" ya fada maganar tana kuna a ransa, Tace, muryar ta tana karyewa kamar zata yi kuka "basu kawo shaidar komai ba Amir, sun dai fadi date da time da kuma ranar da aka yar da kai. Ni ban san date din ba amma baba Asabe tayi confirming time din, kuma ....." Yace "10th of January. Shine birth date dina" sai yaji ta fara kuka "haka suka ce, haka suka ce Amir, yan uwan ka ne. Basu bamu shaidar komai ba sai ta kamannin fuskokin su, gabaki dayan su suna kama da kai, musamman ma farin, kamar ku daya banbancin hasken fata ne kadai dan Baba Asabe ta dauka kaine sanda ta ganshi" zuciyarsa ta tafi kan yarr jaririyar da ya baro a gida
Siblings? Shi wai shi yana da siblings kenan? Kuma har wai sunzo nemansa? Kenan sun san dashi sun kuma san inda yake, that's in the gaske yan uwan nasa ne ba tsufa ne ya kama Baba Asabe ba. Abinda ya fara fado masa masa a rai shine mahaifiyar sa, itace ta yar da shi kuma ita ce yanzu ta gaya musu inda ta yar da shi din. He threw him away and kept his siblings.
Why?
A cikin wayar yaji har yanzu Madam Merry magana take yi, "...........shine na basu e-mail address dinka, na ce su neme ka su tambayi iznin ganin ka daga gurin ka. Check your email yanzu haka sunyi maka magana dan they were so eager to meet you"
Ya cire wayar daga kunnensa sannan ya koma da baya ya zauna akan kujerar da take bayansa, maganganun suna harhaduwa da junansu a cikin kansa, Siblings, mother, eager to see him, suna kama dashi, e-mail. Sai ya ajiye wayar ba tare da yayi checking ko ya katse kiran ba ya jawo system dinsa ya kunna, sannan ya shiga e-mails dinsa roughly yana checking recent mails dinsa and then he saw it, daga wani address din da bai sani ba, yayi clicking ya bude zuciyarsa tana bugawa da sauri.
"Assalamu alaikum wa rahmatullah. I may be wrong but I think you are the person am looking for. Ina da labarin da zan baka, a story concerning your parents"
Sai address a kasa, "a story" ya maimaita a ransa, story za'a bashi? Shi answers yake so, so yake yaji dalilin da yasa aka yar dashi tsirara a kofar gidan marayu. Maimakon yaji dadin cewa zai ga family dinsa sai yaji wani irin bacin rai da kunan zuci a kasancewar mahaifiyarsa data yar dashi tana sane dashi all these years bata neme shi ba sai yanzu, maybe ma siblings din ne suka matsa mata ba wai dan ita ta damu da shi ba. Ya fahimci cewa ita ce ta aiko masa da sakon bayan yayanta sun koma gida ba tare da shi ba, me take tunani? Cewa zai fita a guje ya tafi gurin ta? Cewa yana bukatar ta a cikin rayuwarsa baya ita ta wofantar dashi a lokacin da yake tsananin buƙatar tata?
Ranar bai koma gida ba bayan ya tashi daga office, a zaman office din ma bai iya aikata komai ba, ya ga kiran Sultan abokinsa yana ta shigowa amma yakasa dagawa dan baya son ya fahimci komai a tare dashi, baya son ya gaya wa kowa komai, not even his wife. Da farko shawara ya fara yi da zuciyarsa akan yaje kiran da akayi masa ko kar yaje? Amma mostly amsar da zuciyar ta sa take bashi shine yaje din, dan in bai je ba ba zai famu answers din sa ba, answers din kuma suna zasuyi determining next action din da zaiyi taking.
A ranar bayan ya koma gida Aysha ta fahimci cewa hankalin sa baya tare dashi amma kuma duk iyakacin kokarin ta sai yaki gaya mata, ita kuma sai tayi fushi thinking dannyayi breaking up da budurwar sa ne ya saka yake cikin wannan yanayin, da safe ma daya fita bai je office ba zuwa yayi park ya zauna yana cooking kwakwalwar sa, yana getting ready for abinda zai tarar idan yaje Kaduna din, babu abinda zuciyarsa bata yi masa imagining.
Yana gurin Aisha ta kira shi, yayi tunanin maganar dauko ta daga school ne amma sai ta gaya masa cewa wannan malamin nata, Nura, yayi accident tana asibiti gurin sa, sai kawai ya tashi ya tafi gurinta dan dama yana neman abinda zaiyi distracting dinsa daga tunanin da yake ciki, ba ya kuma son yin magana da wanda zai takura masa sai ya gaya masa abinda yake damunsa kamar Sultan ko Aysha matarsa. A can asibitin ya same ta, ya duba nuran sannan ya dauko ta suka tafi zai kaita gida. A hanya ta gaya masa cewa komai ya warware mata na maneman ta. Finally ta yi deciding cewa Nuran dai shine ta tsayar.
Bayan yayi packing ne ya gaya mata "something came up, something related to my parents" ta juyo tana kallonsa ido a bude, ya dan kirkiri murmushi, "ba wani abu bane ba, It maybe nothing and it may be something, babu wanda na fada wa, not even Sultan" ta gyada kai tana jinjina irin yardar da yayi da ita, tana kuma jin farin cikin maganar daya gaya mata, yace "I want to go and investigate first, zan danyi tafiya zanje Kaduna, in na dawo duk abinda ake ciki I will let you know" ta guada kai da sauri idonta yana kawo kwallar da bata san ta menene ba. Yace "adious *A'isha Humairah*" ta fita ta rufo masa kofa tace "adious my friend".
Washegari da sassafe ya dauki hanyar Kaduna, bayan ya gaya wa Aysha cewa wani harkar gini ce zata kai shi can, bata damu ba saboda tasan babu inda baya zuwa akan aikinsa. Sultan ma abinda ya gaya masa kenan kuma tunda yanzu ba sosai yake kula harkar kamfanin ba dan haka bai fahimci babu wani aiki a Kaduna ba. Yana shiga Kaduna hotel ya tafi ya kama, daga nan ba tare da ko da jakarsa ya sauke daga mota ba sai ya dauki hanyar address din da aka bashi a email din. Zuciyarsa kamar zata fado daga kirjinsa.
A kofar gidan ya tsaya yana karewa layin da kuma gidan kallo, katon gida ne wanda za'a iya cewa duk layin babu gidan da ya kai shi girma amma alamu suna nuna kamar yana lacking maintenance, kamar mutanen gidan basa cikin gidan, amma wani abu mai karfi yana jan sa zuwa cikin gidan. Ya daga kai yana kallon manyan balconies din da suke ta two sides of the house, amma sai a idon sa yaga kamar an dade ba'a yi amfani da su ba. Bai san me yasa kallon gidan yake kokarin kawo hawaye cikin idonsa ba. Ya girgiza kansa yana so ya dawo cikin hayyacin sa.
Ba irin wannan gidan ya saka ran zai gani ba, ba irin wannan gidan zuciyarsa take kwatanta masa a matsayin inda mahaifiyar sa take ba, gidan kamar yafi karfin wacce ta haihu ta yarda dan ta zauna a ciki. Yayi horn mai gadi ya leko yayi masa tambayoyi sannan ya koma, jimawa kadan, already har Amir ya fara kawowa wuya sai gashi ya dawo ya bude masa kofar. Ya shiga yana karewa compound din gidan kallo, it definitely lack maintenance kamar yadda ya fada, amma kuma a matsayin sa na engineer yasan cewa duk wanda ya gina gidan nan tabbas yana da taste, dan duk da shekarun gidan amma ko a zamanin nan ba ko ina ne za'a yi wannan aikin ba. Mai gidan, ba karamin mai kudi bane ba.
Sai yaji kalmar mai gidan ta tsaya masa a ransa...
Sama sama yaji mai gadin yana yi masa magana, yana nuna masa ta inda zai shiga cikin gidan. Ya bishi zuwa bakin kofar, amma sai yaji ya kasa shiga, har sai da ya sake masa magana sannan ya taka kafarsa ya shiga, yana jin zuciyarsa tamkar ta koma cikin hanjinsa. Ya zagaya palon da idonsa, babu kowa a ciki, ya daga ido yana kallon tafkeken benen da yayi sama sannan kuma ya rabu gida biyu ya sake yin sama. Ya dawo da idonsa kan kujerun gurin yana kokarin nema wa kansa gurin zama, a lokacin ne idonsa ya sauka akan hoton.
A nutse yake taka ƙafafuwan sa yana nufar katon hoton da yake rataye a bangon parlon amma a cikin jikinsa ji yake tamkar wata maganadisu ce take jansa zuwa ga abinda idanuwansa suka gane masa. Wani iri yake ji a kirjinsa, ya kasa tantance wa cewa zuciyarsa ce ta tsaya daga aikinta na buga jini zuwa sassan jikinsa ko kuma huhunsa ne ya daina nasa aikin na zukar oxygen, amma ko ma menene dai yasan wani abu, abinda bai taba tabuwa a jikinsa ba yau ya tabu.
Ya karasa gaban hoton, sannan ya daga hannayensa da suke karkarwa tamkar na wanda yake cikin matsanancin zazzaɓi ya dora akan hoton yana karewa halittun cikin hoton kallo.
Daga ganin hoton zaka gane cewa ya kwana biyu a duniya, daga ganin camerar da akayi hoton kasan bata yanzu bace ba. Sai dai shekarun hoton basu saka yayi komai ba dan mutanen ciki tamkar zaka kirasu su amsa.
Su biyu ne, daya a zaune akan kujerar alfarma daya kuma a tsaye a bayansa ya dora gwuiwar hannunsa akan kafadar na zaunen. Kallo daya zakayi musu kasan cewa yan'uwa ne, kallo daya zakayi musu kasan cewa ciki daga suka fito, sannan inka kalli fuskar su zaka tabbatar cewa ba wai jini da iyaye kawai sukayi sharing ba har da mahaifa. Tare suka rayu a ciki, tare kuma aka haife su. *Tagwaye* ne.
Komai nasu iri daya ne, tsahon su, yanayin jikinsu, shape din fuskarsu, abubuwan da suke cikin fuskar, abinda ya bambanta su guda daya shine kalar fatar su. Na zaunen fari ne tas, na tsayen kuma baki ne irin fatar Amir da yake kallonsu.
Ko digon alkalami na doubt babu a zuciyarsa, yasan cewa ta jikin daya daga cikin wadannan bayin Allan ya fito yazo duniya. Abinda bai taba tsammanin gani ba, ya saka ran ganin mahaifiyar sa a yau amma bai yi tunanin samun wani abu daya danganci mahaifin sa ba.
Amma wanne daga ciki? Farin ko bakin? Na zaunen ko na tsayen?
Ya dora tafin hannunsa na dama akan fuskar wanda yake zaune, farin, sannan ya saka idonsa cikin nasa yana jin wani abu mai girma yana ratsa zuciyarsa yana kawo kwalla cikin idonsa. Murmushi ne a kwance akan kyakkyawar fuskarsa, murmushi exactly irin wanda kullum yake kwance akan tasa fuskar.
Ya hadiye wani abu da yaki tafiya a makogwaron sa.
Sannan ya mayar da idanunsa kan na tsayen, Baƙin, and he felt as if yana kallon kansa a madubi ne. Ya tabbatar da cewa, da ace a yanzu zai shiga shagon aski a aske masa gashin da yake fuskarsa da tabbas za'a iya cewa shine a cikin hoton. Dan daga dukkan alama an dauki hoton ne a lokacin da shekarun su suke kusan nasa na yanzu.
Motsi yaji a bayansa, hakan ya saka shi saurin waigawa a dan tsorace saboda baisan da shigowar mutum parlon ba. Idanunsa ya sauke a kanta.
Baka ce kamar shi, bata da tsaho sosai kamar shi, kuma tana da manyan idanuwa irin nasa. Shekarunta zasu yi anywhere between 20-25. Ya girgiza kansa da sauri tare da dafe shi da hannu daya. Ba ita ya saka ran gani ba, a lokacin da yaga hoton mahaifinsa for the first time a rayuwar shi mahaifiyarsa yake saka ran gani tare da hoton. Ko ba dan komai ba dan ya samu yayi mata tambayar da ta jima tana cin zuciyarsa. Tambayar daya taho takanas dan yayi mata.
"Why?"
Tun yana yaro babu abinda yake son yaji irin dalilin da yasa mahaifiyar sa ta jefar dashi a kofar gidan marayu ba tare da ko cibiya ta tsaya ta yanke masa ba.
"Excuse me" matashiyar matar ta fada tana kallon sa cike da zargi da rashin fahimta. Ya dafe goshinsa yana kokarin tattaro hankalin sa guri daya dan ya samu muryarsa ta fito amma sai yaga yanayin fuskarta ya chanja daga kallon rashin yarda da take masa zuwa kallon mamaki hade da excitement. Ta dauke idonta daga fuskarsa ta mayar kan hoton da yake bayansa sannan ta kuma dawo wa da shi fuskar tasa.
Sai kuma ta saki keys din motar da suke hannunta ta rufe bakinta da hannayenta duk biyun amma ta kasa cewa komai.
Cikin tuhuma yace mata "sunana Amir. Ke kika aika min da email cewa kina nemana?"
Ta girgiza kanta cikin sauri, sannan tace "mahaifiya ta ce". Then there is hope, then she is here within these walls. Dan ya tabbatar ba tare da doubt ba cewa wannan yarinyar ta gabansa kanwar sa ce, then mahaifiyarta mahaifiyarsa ce kenan.
"Where is she" ya fada cikin budaddiyar muryar da tayi amsa kuwwa a cikin gidan. Muryar da Amatullah taji tamkar ta daddyn ta idan yana fada, ta ja baya, yanayin Amir yana tsorata ta, Amir ya tabbatar ta jiyo shi indai tana cikin gidan. Cikin gaggawa Amatullah ta juya tana cewa "bara in gaya mata kazo" sannan ta bude wata kofa a can karshen parlon ta shige.
Yabi kofar da kallo, jikinsa yana bashi cewa tana ciki, mahaifiyarsa tana cikin dakin da yake hade da parlon da yake tsaye a gaban hoton mahaifinsa. "Wannan wanne irin mafarki ne" ya fada yana dukan goshinsa da tafin hannunsa na hagu.
Mintina suka yi ta wucewa, wannan ya saka shi ya fara sintiri a parlon yana kaiwa yana komowa ba tare daya dauke idonsa daga kan kofar da yarinyar ta shiga ba. "What is taking her so long?"
Finally kofar ta bude, ya tsaya chak a tsakiyar taku yana son ganin fuskar ta amma sai yaga fuskar yarinyar data shiga ta dawo ita kadai.
Me ya faru? Ko ta fasa ganin na shi ne?
Ta tsaya a gabansa sannan ta mika masa wani littafi wanda sai a lokacin ya lura cewa ta fito dashi a hannun ta. "Gashi tace a baka" ta fada cikin muryar da tayi kama da na wadda tayi kuka. Yabi littafin da kallo sannan ya kalle ta, wani barin na zuciyarsa yana gaya masa cewa ya makure ta har sai ta daina numfashi.
"Littafi? What the fuck am I supposed to do with a book?"