Showing 297001 words to 300000 words out of 300844 words

Chapter 100 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2046

buƙatar ganinta har abada." Sai kuma ta juya da sauri tana kallon sa tace "kar dai so kake ka ce min ka yafe mata?" Ya girgiza kai yace "ban sami ba, ban san ko na yafe mata ko kuma a'a ba. Na san dai cewa abinda ya faru dani, rayuwar da nayi a baya duk kaddara tace haka Allah ya rubuta zai kasance dani ko da ita ko babu ita kuma sai hakan ya same ni. Allah bai yi xan rayi a tare da iyaye na ba, ita din kawai sila ce ta kasance war hakan, kuma nasan ko da babu ita dole za'a haife ni a gurin kuma a barni, maybe wani ya tsince ni ya kaini gidan marayu, maybe kuma wani ne daban zai sace ni saboda wata a kida ta daban ya kaini can, maybe kuma in bata da kaina in na fara wayo a tsince ni a kaini can, whatever the case dole sai ya rayu a can, wannan shine kaddara ta. Kuma ni bana regretting rayuwar da nayi a baya mommy, saboda it is what made me who I am today. Badan nayi waccan rayuwar ba da ba lallai ne in hadu da amazing mutanen dana hadu dasu ba" ya karada yana kallon Aysha ita kuma ta sunkuyar da kanta kasa.

Adam yace "amma naji dadin maganar ka Amir, tabbas you are your father's son dan kalaman ka sai naji tamkar shine yake furta su" Amir yayi murmushi yace "nagode" sai kuma ya juya gurin Fatima ya rike hannunta a cikin nasa yace "mommy, abinda ya faru dani kaddara ta ce, ke kuma a gurin ki jarabawa ce" sai ta dago kai da sauri tana kallon sa tare da tuna cewa Hussain ya taba fada mata magana exactly irin wannan. Sai kawai ta dora kanta a kafadar sa tana kuka. Ya fahimci ita saurin kuka ne da ita kuma ya fahimci cewa hakan yana da alaka da halin da ta shiga a baya, a saboda rashinsa da kuma rashin Mahaifin sa. Sai ya dora hannunsa a kafadar ta yace "it is over mommy. I am here".

Sati daya Hassan da family suka yi a Dubai. Dama kuma duk sun shirya enjoying kansu a garin Dubai, mata sun ciko jakankunan su da niyyar shopping dan haka satin nan guda suna enjoying rayuwarsu sannan suka yi shirin komawa Nigeria amma Amir da family dinsa anan zasu bar su. A cikin satin kullum sai Amir ya dauki Aysha da kannensa sannan sun biya sun dauki Amatullah sai su tafi yawon bude ido. Islam ta tambaye shi dalilin da yasa suke zuwa daukan Amatullah bayan daga can ma suna fita sai yace "ita kadai ai ba zata ji dadin yawo a cikin maza ba" Iman tace "akwai mata ai, akwai aunties dinta da matan yayyenta" sai yace "sunyi mata girma" a dole suka rabu dashi. Kuma sai suka lura ita ma Amatullah din kamar tafi son fita dasu din tunda sune kusan sa'annin ta, sannan kuma gata yar gayu irin su da haa shopping interest dinsu yake zuwa kusan iri daya.

Kullum kuma sai ta tsokani Amir akan gashin daya tara a fuskarsa. Har suma sisters din suka fara takura masa shi kuma yace tunda matarsa bata nuna ta damu ba ba zai aske ba. Sai ana gobe su Amatullah zasu koma Nigeria, sunzo gidan Fatimah gabakidaya zasu yi musu sallama sai ya dauke ta ita kadai yayi mata siyayya ta musamman yace tsaraba ce. Tayi godiya sai kuma yace "in zan taho me kike so in taho miki dashi kuma?" Tayi shiru tana kallon sa sannan tace "hmmm. Da dai zaka yi aski, maybe da ka burge ni" yayi murmushi, "shine abinda kike so kadai?" Tace "zaka yi ne?" Yace "in dai kina so zanyi" ta bude ido "Allah da gaske?" Yace "kin dauka wasa nake yi?" Tace "yaushe to zakayi?" Yace "yau. Gobe in nazo rakiyar ku zaki ga nayi"

Sai kuma tace "babu ruwana, ban sani ba ko matar ka tafi son ganinka haka" yace "sai in aske rabi naki sai in bar mata rabi nata" sai suka yi dariya ta sake cewa "babu ruwana fa. Kayi zamanka da abinka" ta juya da sauri ta koma cikin gida gurin mutane.

A ranar ne suna hira a cikin gidan Fatimah sai Safiyya take cewa "kamata yayi idan kun dawo Nigeria a shirya wata dinner haka ta musamman dan celebrating dawowar Amir" sai Adam yace "ni kuma sai nayi tunanin ba dinner ya kamata muyi ba, Umrah ya kamata mu shirya muje kamar yadda muka je lokacin rashin lafiyar oga Hussain muyi godiya ga Allah sannan kuma muyi wa Hussain addu'a kamar yadda muka yi masa a wancan lokacin" sai duk suka amince da wannan shawarar.

Bayan sun tafi da dare sai Amir ya dauko diary din Hussain ya nunawa Fatima "kin tuna wannan?" Ta rufe baki da mamaki tana kallon diary din, a take kuma idonta ya kawo kwalla, ta karba tana jujjuya shi Amir kuma yana kallon ta yana murmushi, tace "yayi min alkawarin cewa zaka karanta min abinda yake ciki watarana" sai ya karba yace "to ga ranar tazo. Are you ready?" Sai sisters dinsa ma duk suka taho suka jeru, ya bude page din farko, wanda shine page din daya iya budewa har yau ya fara karantawa

Dear baby....

Sai duk suka kwashe da dariya har da Aysha da Sultan saboda sun fahimci shine babyn, ya bata rai "an fasa karantawa ma tunda dariya zakuyi min" sai ya mayar da kayansa cikin aljihu, dama ba niyyar karanta wa yayi ba dan har yanzu he is not emotionally ready.

Sai da suka gama dariyar sannan ya mike yace "mommy zan fita, zanje ayi min gyaran fuska" Ilham tace "ahh, finally". Fatima tace "da kafi kyau kuwa idan kayi" ya shafa fuskarsa yace "tunda kina so yanzu zanje inyi" ya juya ya fita Aysha kuma ta bishi da kallo. Sai da ya je gurin askin sannan ya kira Amatullah. "Duk gashin fuskar kike so a cire ko kuma kina so a gyara shine irin na 2pac?" Tayi dariya "a tambayi yaya Aysha, duk abinda take so shi zaka yi" yace "ai na gaya miki bari daya ne nata daya barin naki, yanzu side dinki nake tambayar me kike so ayi" sai tayi shiru kamar mai tunani sannan tace "duk sides biyun nata ne, ni dai babu ruwana" sai ta kashe wayarta.

Sai kuma ya nemi number din Aysha ya kira "Finally dai burinki ya cika zanyi gyaran fuska" tace "burina ko burinta? Tun yaushe nayi ta nacin ka gyara kaki har na hakura na daina magana, sai yanzu kuma?" Yace "yanzun ai mommy ce tace....." Tace "babu ruwan mommy fa, dama kayi niyya tun kafin mommy tayi magana" sai ta kashe wayarta itama.

Ya zauna hannu ruje da yawa ya rasa me zaiyi sai kuma yayi tsaki ya fita ya shiga shagon askin. Sanda ta fito ba zaka dauka shine wanda ya shiga ba, shi kansa yasan yayi kyau ba kadan ba. Compliments din kuma da ya samu daga mommyn sa da kannensa shi ya kara tabbatar masa da cewa yayi kyau, hatta Aysha da take fushi sai data sauko dan kanta kuma ta yaba tace yayi kyau har ta bashi tukuici a dakin da aka sauke shi.

Washegari suka tafi rakiya. Kowa ya ganshi sai ya yaba da kyan da yayi amma Amatullah sai ta nuna kamar bata gani ba. Shi kuma ya kasa daurewa yayi ta binta wai sai tace yayi kyau ita kuma taki fada a karshe ma sai ta gudu ta buya inda ba zai ganta ba har sai da aka kira jirginsu, yana ta sallama da mutane yana tambayarsu ina Amaty, kusan kowa a gurin sai da ya fahimci halin da yake ciki yayin da ita kuma Amaty din ta rufe fuskarta ta shige cikin mutane ta wuce ba tare da ya ganta ba.

Bayan sun tafi ya dauko Aysha suna dawowa gida yana ta kokarin yi mata hira ita kuma ta cika tayi fam. Sai da ya gaji da zance shi kadai sannan ya tambaye ta "wai sweetheart nayi wani laifin ne?" Ta juyo da sauri tana kallonsa "sweetheart? Kake cemin sweetheart?" Ya bude ido "miji ya cewa matarsa sweetheart kuma ya zama laifi yanzu?" Tayi banza ta rabu dashi sai kuma tace "menene tsakanin ka da Amatullah?" Ya bude ido "Amaty? Menene kuwa hadi na da Amaty?" Tace "shine abinda na tambayeka ai yanzu. Ai ni ba makauniya bace ba kuma ba kurma bace ba na san duk abinda kake yi. So nake kayi admitting da bakin ka ka gaya min ka daina wasu kame kame da hanya hanya"

Sai taga yayi murmushi, ranta ya kara baci tace "au dariya ma na baka ko? Dariya ma kake yi min ko?" Sai ta fara kuka, ya sauke motar gefen titi tare da kokarin rike hannunta amma taki yarda "babu abinda zaka ce min Amir, kar ma kayi kokarin yi min dadin baki ko kokarin kare kanka. Kawai ka bani amsa direct ka gaya min menene a zuciyar ka" yace "I don't know. Okay. I am not sure menene a zuciyata ballantana in gaya miki. Kuma ni bansan ranki zai baci har haka har kiyi kuka akan abinda ni kaina ban tabbatar ba ballantana in tabbatar wa da wani. Ni ba son Amatullah nake yi ba idan haka kike tunani"

Yayi shiru yana kallon gefen titi sannan yace "I thought zan iya cika daya daga cikin unfulfilled dreams na mahaifina. Yana daga cikin burinsa cewa watarana a samu auratayya tsakanin yayansa dana Daddy. Ni kuma ni kadai ne dansa, Amatullah ce kadai yar Daddy. I just thought maybe zanyi wani abu da idan da zai gani zaiji dadi. Ba wai burina inyi abinda zai bata miki rai ba ne. Kuma ko a haka din ma banyi niyyar yin maganar yanzu ba saboda ke, saboda bana son abinda zai bata ranki. Kuma ko da nan gaban ne banyi niyyar yi ba sai da iznin ki, sai kin amince tukuna idan baki amince ba it will just be one of his dreams da basu cika ba. And from your reaction nasan ba zaki yarda din ba dan haka it is over before it even begins". Ya fada yana stirring motar zuwa kan titi.

Sun danyi tafiya kadan tace masa "ba sonta kake yi ba?" Ya girgiza kansa "uhm uhm" tace "ba baka ita suka yi a gida ba?" Ya sake girgiza kai "uhm uhm. Babu wanda yayi min zancenta" sai tayi shiru tana kallon gaban ta. It will be selfish idan taki amince masa, and from all indications watarana sai Amir ya kara aure ko tana so ko bata so kuma bata san wacce zai kuma jajibomata ba. Yes Amatullah yar uwarsa ce amma in dai har ba hada su akayi ba aurensu ba zai nufin cewa yanuwansa basa sonta ba. Kuma in tayi la'akari da yadda tarihi ya nuna yadda akayi auren ita kanta maman Amatullah din sai ta fahimci cewa suna da kara sosai. But ba zata bashi amsa ba har sai tayi addu'a akan lamarin. Tabbas itama tana bukatar zuwa Umrah tana bukatar ta gaya wa Allah kuma ta nemi zabinsa.

Sati biyu bayan nan suka tafi Umrah kamar yadda suka shirya, su su Amir suka tafi daga Dubai su kuma yan Nigeria suka tafi daga can. Wannan ƙaron har da Sumayya tare da Jamila matar Yusuf, an mayar da Ruqayyah gidan Aminu kuma abin mamaki sai Sumayya ta asu labarin cewa Ruqayyah ta fara samun lafiya, tana iya motsawa yanzu kuma tana iya rubuta abinda take so ta fada.

Sunyi adduoi sosai musamman ga Hussain, sannan kuma sunyi wa kawunan su adduoi. Aysha ma tayi nata adduoin. Tana kuma lura da yadda Amir ya koma gidan jiya tunda ya kuma haduwa da Amatullah a can, duk da ta lura yarinyar tana ta share shi kuma da alama utatake yiwa alkunya dan ta sha kama shi suna waya suna dariya amma in a gaban tane sai Amatullah tayi kamar bata san abinda Amir yake yi ba. Ta kuma lura da yauwan su duk sunsan halin da suke ciki amma ko maganar babu wanda yake yi ba kuma su taba ko da kwatanta gaya mata magana akan hakan ba. A haka har suka gama two weeks din da suka je da niyyar yi, daga nan kuma Nigeria zasu dawo gabaki dayan su.

Ana gobe zasu dawo ne sai Amir yaga Sumayya tare da gabaki daya ƴaƴan ta har Amatullah sun shirya zadu fita, ya tambaye su inda zasu je sai suka gaya masa zasu je suyi wa Ruqayyah dawafi ne da niyyar nema mata lafiya. "Watakila in tana da rabo sai ta warke, harta samu damar neman gafarar ku da kanta" sai Amir yayi murmushi yace "na yafe mata ni ai. Da fatan Allah zai duba wannan ya yafe min nima tarin nawa zunuban, dan ina dasu da yawa"

Yasan wannan zai faranta ransu amma bai dauka farin cikin su zai kai wanda yaga suna yi ba. And he felt soo good inside and outside.

Suna komawa Nigeria suka tarar an gama renovating gidan Amir, farko ya kai Aysha Maiduguri ta ga danginta sun yi murnar abinda ya faru, sannan ya debi kudade masu yawa ya bata tayi shirin tariya a sabon gidan su duk kuwa da cewa an saka komai a gidan sai yan abinda ba'a rasa ba wadanda suke ra'ayin ta ne. Ita kuma saita shirya musu walimar tariya a sabon gidan su, inda ta gayyaci kowa da kowa dangin uwa da uban Amir, jama'ar gidan sarkin Abuja, abokan arzikin da aka zauna tare a abuja da kuma nata yanuwan. Kowa kuma yazo sai yayi san barka.

A lokacin ne kuma Fatima tayi masa kyautar rabin share dinta na H and H, rabin kuma ta bawa kannensa. Ma'ana shi yana da kaso 75% kenan yanzu, sauran kuma na kanensa ne.

Bayan an watse daga taron ne kuma taje har gida gurin Aunty ta shigar mata da maganar tana nemawa Amir auren Amatullah. Maganar da tashin farko Aunty tace bata yarda da ita ba, Hassan ma kuma ana fada masa yace a'a, wannan ai cin fuska ne, sai dai kuma dagewar da tayi akan taji ta gani ta amince, da kuma shima Amir din da ya nuna yana so, suka kuma iyayen dama ransu yana son abin sai suka karba.

Cikin lokaci kadan aka tsayar da magana, aka kuma saka rana kusa ba tare da bata lokaci ba duk da Amaty taso a barta ta kammala masters dinta da take kokarin kammalawa yanzu. Aka sha biki babu bata lokaci amarya ta tare a gidan angonta tare da uwargidan ta. Mu dai namu sai muce Allah ya sanya alkhairi ya kuma kade fitina.

*Two year Later*

Tsakar gidan cike yake da yara yan makarantar allo kowa da allo a hannun sa yana biya karatun da aka dora masa, wasu kuma suna gefe suna yin rubutu a nasu allon yayinda a can kan barandar da take gaban falon da zaka shiga cikin gidan malamar su ce a zaune tana ɗorawa wasu daga cikin su karatun. Tana kuma yiwa wadanda suka kawo mata rubutun su gyara. A lokacin ne mazan su biyu suka shigo gidan tare da sallama. Ta dago kai tana kallon su tare da murmushi, ta fara kokarin mikewa tana neman crutches dinta. Aminu ya karasa da sauri ya taimaka mata ta mike tana cewa "mutanen Abuja, an shigo gari kenan" yace "dazu na shigo, nazo naga babyn Amaty" suka nufi cikin falon tana cewa "Sumayya ta gaya min haihuwar, yau nake shirin da dare in na sallami dalibai in kira Yusuf ya kaini in gani jaririyar" suka shiga falon Yusuf ya biyo su a baya, Aminu ya zaunar da ita a kujera sannan duk suka durkusa suka gaisheta, ta amsa tana gyara hearing aid dinta tare da saka musu albarka tana kuma tambayarsu lafiyar iyalan su.

Mai aikin ta ta zo ta kawo musu lemo da ruwa. Suka sha suna yi mata hirar abinda ya shafi iyalan su tana da murmushi, lokaci zuwa lokaci masu daukan karatun sukan leko tayi mudu gyara akan karatun su koma su cigaba da biyawa. A haka har suka gama sai Aminu ya dauko kudi masu yawa ya ajiye mata a gefenta "ko za'a bukaci wani abu wanda babu a gidan" sai tayi saurin girgiza kanta tare da dawo masa da su tace "ina da duk abinda nake bukata, ni a yanzu babu abinda bana son gani a rayuwata irin kudi, kudi masifa ne kudi bala'i ne" Yusuf yace "kudi Mama, bala'i ne idan aka neme su ta haram, amma kuma alkhairi ne idan aka same su ta halak kuma aka kashe su ta halak. Wannan kudin albashinsa ne, gumin sa ne dan haka halal dinsa ne"

Ta sake girgiza kai. "Duk da haka dai. Ni suna bani tsoro sosai. Bani da burin sake rike su. Burina a yanzu shine inci in sha yadda zan samu damar gabatar da ibada ta kuma in koyar da dalibai na sannan in cigaba da neman gafarar Allah data wadanda soyayya kudi ta saka ni na zalunta. Bani da damar zuwa inda Fatima take amma ba zan gaji da aika mata da yan aiken neman yafiya ba har sai ranar da na bar duniya ko kuma ita ta bari ko kuma ranar da ta furta cewa ta yafe min"

Ta karasa tana share hawayen idonta da hannunta da yake a karkace.

"Babban abinda zanyi muku nasiha dashi shine ku gode Allah, duk abinda ya baku ku karba ku gode masa saboda shi yafi ku sanin abinda yake shine mai alkhairi a gare ku, a kullum kuma kar ku kalli wanda yake sama daku dan hakan ne yake kawo rashin godiyar Allah. Kullum ku ringa duba wanda yake kasanku wannan shi zai kara muku godiyar Allah a zuciyoyin ku"

"Duk wanda bai godewa Allah ba to kuwa tabbas zai godewa azabarsa"
Ni shaida ce akan wannan

*********************†*********

A gidan Amir, yana zaune a palonsa da diary dinsa a hannun sa. Aysha ta shigo da yar jaririyar Amaty a hannun ta wadda take ta tsala kuka ta dora masa akan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login