Showing 210001 words to 213000 words out of 300844 words
su basu da ja cewa ita din ce, in dai har Fatima tana da rai to wa aka binne? Ko wacece har yanzu ana neman ta kenan ba'a same ta ba, His mind raced, putting two and two together. Tsohon ciki, kayan baby, Ruqayyah.
Ya ajiye Abdullahi dake hannunsa sannan ya dafe kansa da hannayensa biyu "oh my God. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" aunty da sauran yan'uwa duk suka juyo suna kallonsa, Sumayya ta mike da sauri tana kokarin rike shi dan gani tayi kamar zai fadi, ya bude idonsa yana kallon ta. Aunty tace "Hassan lafiya? Mai ka tuna?" Bai kalle ta ba sai Sumayya yake kallo, yana tunawa da yadda Ruqayyah taki kallon idon mahaifiyar Minal a asibiti sanda taje dubata tare da tambayarta ko ta san inda Minal take, ya tuna da karyar da tayi masa, ya tuna da yadda ta chanja magana tace sun hadu da Minal amma sun ajiye ta a hanya ta hau taxi zuwa gida. Gidan da har yau bata je ba kenan.
Yana kallon cikin idon Sumayya yace "bayan driver da Fatima da Ruqayyah a cikin motar ranar da suka yi accident akwai wata, akwai Minal kawar ku, ita ce a gaba, ita ce ta mutu ranar nan, ita ce aka binne ba Fatima ba".
Labarin dawowar Fatima ba karamin tayar da mikin mutuwar Hussain yayi a zuciyoyin yan uwansa ba, musamman Hassan, ga kuma wannan sabon al'amari wanda bai gane kansa ba na cewa ba'a san inda yaron Hussain yake ba. Ta yaya? Sannan kuma ga dawowar Adam tare da Fatima, me ya hada Adam da Fatima da har zai dauke ta su tafi garin su tsahon shekaru biyar? Me ya faru dasu.
A dole ya tafi ya sallami mutanen da suke gurin taron da excuse din cewa something emergency ya taso masa tare da bada hakuri, amma baya bukatar ya badu hakuri dan duk wanda ya ganshi zai lura ba'a cikin nutsuwar sa yake ba. Wani bari na zuciyarsa gaya masa yake yi kawai duk ya bar wannan bata lokacin ya shiga mota ya tafi gidan Hussain ya shake Ruqayyah yayi ta dukanta sai ta warware masa zare da abawa na duk wannan rikicin, gani yake itace answer to everything.
For starters, ta yi karya, muguwar karya, akan mutuwar kawarta, what kind of himan being is Ruqayyah? Shin idan Ruqayyah zata iya yiwa friend dinta haka me nene abinda zata yi wa makiyin ta? Ya tuno Fatima, Ruqayyah ta rike Fatima a matsayin makiyiyar ta, dan haka tabbas, yana da 90% assurance cewa Ruqayyah tana da hannu a cikin abinda ya faru da Fatima. Amma babyn Fatima fa? Ita Fatima ai ita zata san duk abinda ya faru da babyn ta. Sai yaji ba zai iya jira zuwa goben da aunty tace su bari tayi sannan su tafi Kano ba. Yana so yaga Fatima a yau, yana son ya ji inda ɗan Hussain yake a yau.
Sai dai baya son ya ki bin maganar Aunty, tace dare yayi yau su bari gobe da assuba sai su dauki hanyar kano kafin gari ya gama wayewa sunje. Sai daya gama sallamar mutanen roughly sannan ya dawo inda Sumayya take zaune har lokacin tana kuka, babu abinda take tunowa sai fuskar Minal da irin yarintar su tare a matsayin makota, in dai sun fita wasa gidan su Minal zasuje Kamar yadda itama take yawan zuwa gurin su wasa duk kuwa da cewa su Minal din sun fi su abin hannu, wannan ya sa basuyi makaranta tare ba amma duk da haka suna kawance a unguwa, bayan haduwar Hassan da Ruqayyah ne kuma kawancen Minal din ya kara karfi da Ruqayyah saboda ra'ayin su na karya da son kudi yazo kusan daya.
Ta tuna yadda ta kan yi wa Ruqayyah nasiha akan kula Minal saboda tana gudun kar ta jata ga halaka, bata san cewa bakar zuciyar Ruqayyah tafi ta Minal baki ba. Bata san cewa da ace Minal zata san yadda karshenta zai kasance da ko hanyar da Ruqayyah ta ke bi ba zata bi ba.
Ta goge hawayen ta da bayan hannunta tana kallon yaran da suka zauna a layi suna kallon ta, Hussain shima yana ta sheshshekar kuka duk da bai san abinda Sumayya take yiwa kukan ba. Kaicho, dan Adam baya zaben iyayen da zasu haife shi, tabbas wadannan yaran basu yi sa'ar uwa ba. Tabbas inna da Baba badu yi sa'ar Ruqayyah a matsayin ya ba.
Ita bata san ma ta yadda zata yi musu breaking wannan mummunan labarin ba, musamman Inna da har yau kullum sai tayi addu'ar Allah ya bayyana Minal dan har yau suna mutunci sosai da iyayen Minal din. Baba kuwa dashi aka yi ta yawo gidajen rediyo yana raka Baban Minal ana bada cigiyar ta, har hoton ta ya lika a gurin aikin gadinsa da cikin Napep dinsa wai ko Allah zai saka wani da ya ganta ya gani yayi magana.
Ga maganar Adam, menene role dinsa in all of this?
Hassan yazo yana daukan Abdullahi daga cinyar ta sannan ya juya yana kallon yaran da suka jeru suna kallon ta suna hawaye yace "ku tafi ku shiga motar Aunty ku tafi gida, gamu nan zamu taho muma" suka mike ba tare da musu ba sai dai har suka yi nisa suna waigen mommyn su suna son sanin menene ya saka ta kuka, sun san dai akan wata Fatima ne da wata Ruqayyah ne, sai dai basu san me Fatima da Ruqayyah suka yiwa mommyn su ba.
Ta mike tana kallonsa tana goge hawayenta tana jinjinawa jarimtarsa, tana mamakin inda yake samun kwarin gwiwar facing abubuwa in suka same shi. Ita bata taba ganin mutumin da yake karbar kaddararsa hannu bibbiyu irin Hassan ba. Hannun ta ya kama ba tare da yace komai ba sannan yafara tafiya da ita zuwa motarsa, sai data shiga ya dora mata Abdullahi a cinyar ta ya zagaya ya zauna shima sannan yace "let's go home" yaayin muryar sa kamar zai saka ta kuka. Menene rayuwa bata jefo wa Hassan ba?
Matarsa matar daya zaba ya so kamar rai duk da banbanci mai girma da yake tsakanin su ya kuma taimaka mata in ways that ita kanta ba zata iya lissafawa ba ita ce tayi sanadiyar destroying family dinsa, ta yadda matar kaninsa tayi shekaru biyar ba tare da an san ma tana raye ba, ta yadda da daya tilo da kanin nasa ya mallaka yake kuma so fiye da ransa ba'a ma san inda yake ba a halin yanzu, ba'a san ma ko yana da rai ko bashi da rai ba.
She can't even imagine the heartbreak......
Duk da cews basu san menene ya faru da Fatima da babyn ta ba amma duk su biyun sun san cewa akwai hannun Ruqayyah a ciki. Me yasa tayi karya akan mutuwar Minal?
Sai da suka yi nisa a tafiyar su sannan yace "bansan ta yadda zan gaya wa Alhaji Kabiru wannan maganar ba" ta dora hannunta akan nasada yake kan gear tace "you don't have to, ba alhakin ka bane ba, kar ka dorawa kanka wannan nauyin bayan already wanda yake kanka, ka bari in munje kano munji details din maganar sai a sanar wa da police din da aka gayawa zancen baran ta, su sai su kira shi su gaya masa"
ya girgiza kansa "dile in gaya masa Sumayya, dole in gaya masa da kaina, tunda abin nan ya faru nake keeping in contact da shi Saboda haka kawai nake jin kamar I am responsible for something da bansan menene ba, ko last week sai daya kira ni ya gaya min matarsa, uwar gidan sa ta haihu bayan kusan shekara goma sha biyar tana neman haihuwa. First child dinsa kenan wannan. I have to tell him da kaina dan in rage feeling guilty"
Sumayya tace "quilt? Habibi you are not guilty of anything. Babu laifin ka ko kadan a cikin wannan maganar" ya girgiza kansa, "akwai laifi na Sumayya, laifi na kuma shine auren yaruwarki. Da ban aure ta ba da duk wannan bata faru ba"
Suka shiga layin gidan su, suka zo dai dai kofar gidan Hussain sai Hassan ya tsaya da mota yana kallon gidan , Sumayya ta kamo hannayensa duk biyun tana cewa "no, no, please. Violence baya taba solving problem sai dai yayi adding. Kar ka shiga dan Allah. Kar ka bata abinda zata fake dashi. Kan taba ta yanzu sharia ta hau kanka. Kar ka taba ta dan Allah" ya sauko da idonsa kanta sannan ya kuma kallon gidan, babu abinda yake so, babu abinda zai sanyaya masa ransa a yanzu irin ya kama Ruqayyah yayi ta duka kamar Allah ya aiko shi.
Sai kuma ya taka motar suka karasa nasu gidan. Sumayya ta sauke ajjiyar zuciya tana hoping ya hakura kenan ba ajiye ta zai yi ya koma ba. Sai da yayi packing sannan ya juyo yana kallonta yace "you are right, in na taba ta na bata abinda zata fake dashi, ninkuma bana son ta samu abinda zai zamar mata madafa, ba zan shiga gidan ba sai da yan sanda, sanda zan fito kuma zan fito ne da ita a cikin sarka. Amma kafin nan ina son ganin Fatima, ina son jin gaskiyar magana ina kuma son inji abinda ya faru da ɗan Hussain" daga yadda ya fadi maganar tasan zuciyarsa kuna take yi. Tana son ta bashi hakuri ta rarrashe shi amma bata san ta yadda zata fara ba.
A haka suka shiga gida, kamar yadda tayi tunani haka yayi ta pacing, yayi ta safa da marwa ya kasa zama ma ballantana kwanciya, a karshe sai taga ya cire kayan jikin sa yayi wanka ya saka jallabiya ya fita, sai dai bata tambayeshi inda zashi ba dan jikinta ya riga ya bata amsar, kabarin Hussain zaije.
Daren ranar haka ta ringa bacci tana tsorata, tana ta tunowa da Minal, tana kuma lissafin yadda zata gayawa iyayensu, yan uwansu da kuma kawayensu abinda Ruqayyah ta aikata. Jin dadin ta daya shine yaran duk suna gidan aunty ba dan haka ba da tasan zasu saka ta a gaba ne da tambayoyi su kuma karamata tension tare da tuna mata cews Ruqayyah ce mahaifiyarsu ba ita ba, no matter how much she pretend, b aita ta haife su ba.
Assubar fari suka dauki hanya, gabaki dayansu banda yara, dan sai da suka je Zaria sannan suka yi sallar asuba suka cigaba da tafiya. Mota biyu sukayi, da motar Hassan wadda Jabir yake tukawa Hassan yana gaba, Aunty da Sumayya da Zulaihat suna baya, sai motar Aunty wadda drivern ta yake tukawa Hassana tana gaba, Safiyya, Khadijah da Nafisa suna baya. Karfe bakwai da yan mintuna suna kofar fadar Kano. Dama tun dare Aunty ta gayawa Hajiya Ummah yadda tafiyar tasu zata kasance dan haka already an san da zuwansu.
Suna shiga aka tafi dasu Hassan masaukin baki maza, anan ne suka hadu da Adam. Suka tsaya suna kallon juna Hassan yana kokarin kawar da batun Adam da Sumayya daga zuciyarsa, for years ya jima yana fatan ganin adam amma bai taba tsammanin haduwar tasu zata kasance a irin wannan yanayin ba. Sai dai hakan bai hana shi nunawa Adam din farin cikin ganin sa ba kamar yadda shima Adam din yake fatin cikin ganin Hassan.
"Oga Hassan!" Ya fada da murmushi mai kyau a fuskarsa. Hassan ya kirkiri murmushi shima "Adam! Oh my God. Har mun fitar da ran zamu sake ganin ka" ya bawa Adam din hannu amma sai adam ya rungume shi yana dariya "you have no idea how happy I am that you are alright" Hassan yace "it is good to see you too" sannan ya raba shi da jikinsa yana lura da yadda Adam din ya kara girma ga wani gyaran fuska na musamman da yayi wanda yayi matukar yi masa kyau. Sai yaji abinda tun kafin su taho yasan zaiji idan yaga Adam din. Kishi. Sai yaji a ransa ina ma dai bai taho da Sumayya ba? Baya so taga Adam especially when he is looking this good.
Sai kuma ya kama hannun Adam din suka tafi suka zauna a kujerun alfarmar da suke gidan bakin yace "come, tell me everything. A ina kuka hadu da Fatima kuma ina kuke tsahon wannan lokacin? Me ya hana ku dawowa?" Suka zauna, Adam yana kallon Hassan yana lura da yadda ya bashi dukkan attention dinsa sai yace
"bayan na rabu da kai a asibiti, kace in taho in duba su Fatima a hanya. Na bar Abuja kenan banyi nisa sosai ba sai na ganta, tana tafiya a gefen titi kayanta a yage jikinta da jini kanta babu dankwali. Sai na tsaya nayi mata magana, na fahimci accident suka yi, na kuma fahimci ba'a cikin hayyacin ta take ba dan ka.ar ma bata san inda tame ba tnaa ta ce min wai in kaita gurin Hussain. Kuma na lura babu ciki a jikinta, na lura kamar ta haihu ne..........."
Hassan ya daga masa hannu "wait wait wait.....wai kana nufin a inda suka yi accident din anan ta haihu?" Adam yace "possibly, but am not sure ko a exact gurin ne ko kuma a wani gurin ne daban amma ta haihu kafin in ganta" Hassan ya mike yana dafe kansa, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, shi duk hope dinsa shine Fatima a hannun Adam ta haihu,cewa yaron ya a gidan su Adam ne ko something. Ya dawo ya zaunaz idonsa yai ja yace "kuma bata gaya maka inda ta haihu ba? I mean ta san inda ta haihu right?" Adam ya girgiza kansa, zuciyarsa cike da tausayin Hassan dan yasan how much dan Fatimah means to him yace "Fatima bata sani ba. Fatima bata san komai ba. Ko sunan ta bata ba sai watanni kadan da suka wuce" Hassan ya bude ido cikin mamaki, Adam ya gyada kai yace masa "yes, she is suffered from memory lost, har yanzu akwai abubuwan da bata tuna ba. Har yanzu bata tuna sanda suka yi accident ba da kuma abinda ya faru bayan accident din da kuma sanda na dauke ta".
Hassan yaji kamar an kwada masa mari a duk sides din fuskarsa, sai kuma ya daure ya juyo yana kallon Adam yace "okay, tunda gaka ai, tell me yadda ka dauke ta da kuma dalilin da yasa ka tafi da ita shekara biyar ba tare daka neme mu ka gaya mana tana hannunka ba"
Adam yaji threat din da yake cikin maganar Hassan amma ya riga yayi expecting hakan dama, dan haka ya cigaba da bayani.
"A lokacin na dauko wayata na kira ka, kiran ya shiga kenan sai ga motar Daddy na nan tazo gurin. Ban san yadda akayi yasan inda nake ba a lokacin bansan kuma yadda akayi har ya kama ni irin haka ba,ka riga kasan issues dina da gidan mu. Shi ya kwace wayar ya hanani kiranka sannan ya jefar da ita, nayi kokarin guduwa, kuma zan iya guduwa a lokacin amma ba zan iya guduwa in bar Fatima ba. Dole na hakura na tsaya saboda ita, na kuma hakura ya kama ni saboda ita, sannan nayi masa karyar cewa budurwa ta ce tare muke saboda ya dauke ta in ya dauke ni, tare da yi masa alkawarin bazan kuma guduwa daga gurin sa ba in har ya bari na taimaka mata"
"Nayi hakan ne saboda in tserar da ita dan baxan iya tafiya an barta a cikin dajin nan ita kadai ba ga ciwuwwuka duk a jikinta gashi bata cikin hayyacin ta, ban san hannun su wa zata fada ba dan zata iya rasa ranta a gurin. A lokacin nayi lissafin daga mun je gida zan dauke ta in kaita gidan iyayen ta, saboda na dauka kano zamu tafi a lokacin, sai da muka shiga mota sannan na fahimci ba Kano zamu dawo ba, na fahimci imo yake da niyyar ya kai mu"
"Babu irin magiyar da banyi masa ba a lokacin da muka shiga Abuja akan mu samu asibiti mu ajiye ta sai mu kira ku mu gaya muku inda take sai muyi tafiyar mu amma yaki yarda, sai a lokacin na fahimci dalilin da yasa ya yarda ya dauko ta, saboda ya fahimci na damu da ita ne shi kuma yana neman abinda zaiyi amfai dashi gurin rike ni. Tun a lokacin na kasa tantance cewa daukan Fatima da nayi shine dai dai ko kuma kuskure ne?"
"Sai da muka je lokoja sannan na roke shi da kyar ya yarda muka kaita asibiti, shima dan yana ganin in bai kai ta asibitin ba zata zamar masa gawa a cikin mota dan sosai take zubar da jini yadda daga ni har ita duk jinin ne a jikin mu. Idonta ya juye gabaki daya sai sumbatun kiran Hussain take yi. Asibitin ma kin karbar ta sukayi suka ce sai an dauko police, sai Allah ya taimake mu ya dan basu cin hanci sannan suka karbe ta suka tsayar da jinin suka kuma bata first aid treatment sannan suka kara mata jini leda daya, haka muka kuma daukan hanya duk da cewa jinin bai ishe ta ba amma dai ta dan samu kanta kadan".
"Daga nan bamu kara tsayawa ba sai a imo, ko sallah basu tsaya nayi ba duk da magiyar da nayi ta yi musu, tun a lokacin na fara dana sanin daukan Fatima, dana sani na nuna masa ban san ta ba maybe Allah zai hada ta da na gari su taimaka mata amma na fara tunanin wannan tafiyar tamu a kwai matsala babba a cikin ta. Na farko matsayin Fatima a kasar hausa, yar sarki, kuma matar prominent person kamar Hussain Aminu ba kowa ne zai fahimci gaskiyar magana ba. Musamman in aka yi la'akari da banbancin yare da addini da yake tsakanin yankin da take da yankin da aka kaita"
"Muna zuwa ya saka a ka rufe ta a daki, I had to sign some papers na agreement a tsakanin mu kafin ya bari likita yazo ya dubata sosai yayi treating dinta sannan kuma ya fahimci cewa haihuwa tayi, shi duk a tunaninsa sai ya dauka ni ta haifa wa Da, shi ya dauka da gaske budurwa tace kuma ina sonta sosai tunda har na aikata