Showing 288001 words to 291000 words out of 300844 words

Chapter 97 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2066

su" Aunty tace "gobe goben nan a aika a dauko min jikokin Hussain in gansu" Hassan yace "insha Allah Aunty" ya kalli Amir yace "ka kira su yau kace gobe da safe su biyo jirgin safe zuwa Kaduna. Suzo mu gansu kafin daga baya mu shirya gaba-daya muje abujan mu yi godiya a gurin sarki Sadiq. Amma kasan Sadiq abokin Hussain ne?" Amir ya girgiza kai cikin mamaki, sai Hassan yace "a can wani guri suka hadu kuma sukayi abota amma mostly through social media, a ranar da Allah ya dauki ran Hussain mun tafi ne dan su sada zumunci ga juna kuma muga dan da akace balarabiyar matar Sadiq din ta haifa masa" Amir ya bude baki yace "Sultan ne, shine abokina da nake gaya muku yanzu" Hassan yace "tun kana labarin na fahimta, ina nuna mana hikimar ubangiji ne na yadda yake gudanar da dukkan al'amuran sa yadda yaso".

Daga nan suka cigaba da hira, wacce mostly take akan marigayi Hussain da irin tarin soyayyar da suke yi masa, kowa yana bada nasa version din, babu wanda ya ko kalli dakinda Ruqayyah take kwance tana jan numfashi da kyar, for a moment, ita kanta Sumayya hankalin ta ya dauke daga kan yaruwar tata. A haka har dare ya ja sosai sai manyan ciki suka tafi suka kwanta su kuma yaran suka bude sabuwar hira, har ma da kawo tea, coffee da snacks suka jibge a gefe suka yi daira suna taking turns gurin bawa Amir nasu stories din...

Wannan ranar ita ce best day of Amir's life...... So far



*Episode Finale*

Till down suka yi a ranar, Amir kam ya san ko da ya je ya kwanta ma ba zai iya yin bacci ba dan babu alamar bacci a idonsa ko kadan, sannan kuma wani part na zuciyar sa yana gaya masa kamar idan yaje ya kwanta zai farka ya ga cewa mafarki yake yi ashe. Sai da sukayi sallar asubar su a jam'i a cikin masallacin gidan sannan kowa ya fara tafiya neman gurin kwanciya bacci, ma'aikatan cikin su kam yau sun san zasu yi fashi a office.

Amir yana fitowa daga masjid yaga Hassan shima ya fito ta daya kofar, ana ta zuwa ana gaishe shi sai shima ya je ya gaishe shi din, sai a lokacin Hassan yake tsokanar sa "Fatima ce ta shafa maka rashin tsaho, ni dai dan uwana dogo ne nima kuma haka" Amir ya danyi dariya sai kuma ya tambaya "ba ta da tsaho ne?" Ya ji a ransa yana son sanin as much about his mother as possible, sai hassan yayi murmushi yace "ba wai bata da tsaho ba, for a lady tana da tsaho dai dai misali, ina nufin dai kawai baka yi tsaho irin namu ba" sai Amir ya dan bata fuska yana cewa "ni ban yi komai irin nasa ba, naso ace komai irin nasa nayi" sai Hassan ya dan jashi suka fara tafiya suna fita daga gidan yace "kayi kama dashi mana, sosai ma, dan ba kayo fatarsa ba ko tsahon sa ba ba yana nufin baka yo shi ba. In na kalli idon ka sai inga kamar dashi nake magana. Amma kuma duk wannan ba shine abu mai muhimmanci ba, abu mai muhimmanci shine kayo halayensa, shine kuma abinda nake so inyi maka magana akai, ka cigaba daga inda ya tsaya, ka zamanto masa cikakken magajin da yayi ta fatan samu kafin ya bar duniya yadda sakon nin aiyukan alkhairan ka zasu riske shi har cikin kabarinsa. Yadda shima zai san cewa ya haihu yabar magaji a duniya. Ban san adadin lokacin da Allah ya rubuta min zan yi tare da kai ba nima kafin in bi danuwana amma ina so inyi amfani da wannan lokacin gurin dora ka akan turbar da mahaifinka yafi, gurin baka labarai na irin rayuwar da mahaifinka a yayi" suka bude gate din gidan auntu suka shiga, Hassan ya cigaba da cewa "nan shine gidan mu, anan aka haife mu anan muka tashi anan muka yi komai kuma har yau anan Aunty take da zama, sannan anan na binne mahaifinka" Amir ya tsaya ya kasa cigaba da tafiya sai Hassan ya ja hannunsa yace "come, lets go and meet him" yana binshi a baya har suka shiga garden din gidan wanda har yanzu take cike ya yayan itatuwa irin su mango, ayaba, guiva, lemon zaki dana tsami, da sauransu. A can tsakiyar sane kuma Amir ya hango kabarin. Ya tsaya ya kasa cigaba da tafiya kuma ya kasa dauke idonsa daga kan kabarin sai Hassan ma ya tsaya a kusa dashi yace "kafin ya rasu ya sa ka nayi masa alkawarin cewa zanke kai masa ziyara kullum" ya danyi murmushi yace "mako ne dashi baya son rabuwa dani, wannan ne ya saka na binne shi anan kuma nake iyakacin kokari na na ganin cewa na cika alkawarin dana dauka masa duk da dai ba kullum din nake zuwa ba. Amma kuma babu sallar da zanyi in tashi ba tare da nayi masa addu'a ba, ina fatan duk ranar da nima na tafi zaka dora daga inda na tsaya" Amir da har yanzu idonsa yake kan kabarin babansa ya gyada kai da sauri ba tare da yace komai ba dan yana ganin kamar in ya bude baki kuka ne zai fito.

Sai Hassan ya dan dafa kafadar sa yace "go and talk to him, kayi masa addu'a. In ka fito ka same ni a cikin gidan Aunty" sai ya juya ya ta fi ya bar shi.

Amir ya jima a tsaye sannan ya taka a hankali ya karasa gaban kabarin ya durkusa, sai da yaga hawayen sa yana diga akan kabarin sannan ya fahimci kuka yake yi, bai goge hawayen ba yace "Assalamu alaika father. Am here. Finally"

Sai da rana ta fito sosai sannan Amir ya baro kabarin Hussain, shima kuma saboda ya tuna bai yi waya da Aysha ba, bai gaya mata duk abinda ake ciki ba ballantana yayi mata maganar tahowa kamar yadda Hassan ya umarce shi. A cikin garden din ya samu kujera ya zauna sannan ya dauko wayarsa da tun jiya bai duba ta ba ya kunna da niyyar kiran Aysha amma kafin ma ta gama budewa har kiran ta ya shigo, sai yaji bai ji dadi ba a ransa dan yasan kwana tayi tana tunanin halin da yake ciki tunda bai taba tafiya ya wuni ya kwana basu yi waya ba.

Ya dauka yana kokarin gyaran murya amma muryar tasa ta daskare sosai, cikin saurin magana take cewa "Amir, honey are you okay? Ka kashe phone tun jiya bamu ji ya kake ba" muryar ta kamar zata yi kuka, sai ya kara gyaran murya yace "am sorry sweetheart, nayi laifi kiyi hakuri" sai tace "lafiya kuwa? Naji muryar ka wani iri" yayi shiru yana tunanin ta inda zai fara yi mata bayani sai yace "daga ziyara nake Aysha, daga ziyarar kabarin mahaifina nake" ta danyi shiru kamar bata fahimci me yace ba sannan tace "mahaifinka fa kace?" Yace "eh Aysha, abinda ya kawo ni Kaduna kenan,ban gaya miki ba saboda ban tabbatar ba, amma yanzu na tabbatar, a gidan mu na kwana jiya Aysha, a cikin yanuwa na" muryar sa ta karye kamar zaiyi kuka yace "I have a family Aysha, and they love me so much"..........

Sun jima suna magana da Aysha kafin ya baro garden din, shi sai yaji ma kamar ta fishi murna dan kamar zata shide masa a cikin wayar, yana jin Sultan yana tambayarta menene take kuka, tun kafin yayi mata zancen tahowa ita tafara yi masa kuma yadda yaji tana dokin abun ya tabbatar a yanzu haka ta fara hada musu kayan su ita da yara. Bayan sun gama ne kuma ya kira wayar abokinsa Sultan shima ya gaya masa abinda ya faru, shima kuma daga muryar sa ya san ba karamin dadi labarin yayi masa ba kuma nan take yace masa zai taho tare da iyalinsa zasu biya su dauko Aysha su taho tare, bayan sun gama wayar sai ya sake kiran Aysha yace ta shirya Sultan da Moon zasu dauko ta su taho tare.

A palon Aunty ya samu uncle dinsa Hassan kamar yadda ya gaya masa ya same shi a can, ya gaishe da Aunty da kuma aunties dinsa da duk ya same su tare da auntyn, suna ta tsokanar sa wai sai ya fadi sunan kowa a a cikin su shi kuma duk ya gane fuskokin amma ba zai iya hada fuska da suna ba musanman saboda duk suna yanayi, sai ya juya yana waigen neman Amatullah, Hassan yace "bata nan ai interpreter din taka" sai yayi murmushi, Aunty tace "ina kallon ta ai tun jiya ita ce mai gaya masa sunan kowa da kuma alakar sa da kowa, fatan dai ta gaya maka cewa yar riko ce ita?" Amir yayi dariya "haba dai Aunty, ko makaho ne ya shafa fuskarta ya shafa tawa ai yasan kanwa ta ce" Aunty ta rike baki "la ha ila, zasu nuna min yanubanci ina a gaba na, har ina sakin sauran mazaje na saboda nayi sabo ashe sabon shima kasa zai watsa min a ido" duk suka yi dariya sannan Aunty tace "ina kishiyar ta wa?" Yace "munyi waya, nasan yanzu suna shirin tahowa in sha Allah" ya kalli Hassan yace "tare zasu taho da abokina Sultan" Hassan ya gyada kai yace "ya kyauta sosai, muma yanzu muke lissafin sanda ya kamata muje abujan dan ina so muje kafin mu tafi Dubai, kuma ina so muje dubai da wuri preparably cikin satin nan dan yadda labarin dawowar ka yake bazuwa a gari, duk da an fada wa duk yanuwan Fatima cewa karsu gaya mata so ake kawai akai mata kai, amma bana jin labarin zai rufu for long, bana so kuma taji a wani guri" yayi murmushi, "I just can't imagine yadda zata yi reacting idan ta ganka, it is unimaginable" Amir yayi murmushi, shima kansa ba zai iya imagining yadda zai yi reacting to ganin mahaifiyarsa ba.

Jin sa yake yi kamar a mafarkin da har yanzu ya kasa farkawa daga cikin sa, bayan yayi wanka ya shirya ne cikin kayan Hussain sai suka fito suka yi breakfast gabakidayan su a gidan Aunty, sai a lokacin yaga Amatullah, ya jata gefe ya ce ta banbance masa sunayen aunties dinsu, tana ta yi masa dariya ta sake yi masa bayanin kowa da kuma yayanta, tana yi tana nuna su a boye, Khadijah ta hango su tace "duk dai mai gulma dai yasan matsayin sa, ballantana wanda yake gulmar iyayensa" sai suka yi dariya kawai amma basu daina hirar su ba har sai da Hassan ya taso ya kira Amir yace yazo ya raka shi waje, sai ya bishi suka fita su biyu, suka fita daga gate din gidan Aunty sannan suka tsaya a gaban wata bishiya suna facing gidajen Hassan da Hussain.

Hassan yace "Hussain ne ya gina gidajen nan guda biyu" yayi murmushi yace "so yayi yayi su iri daya amma naki yarda, I can remember rigimar da muka yi dashi a lokacin yace zan bata masa tsari wai ba zasu yi kyau ba in akayi daban daban ni kuma nace bana son irin nasa" Amir yayi murmushi shima, Hassan ya cigaba "farko gate daya ne kuma babu katanga a tsakani, burinsa shine mu zauna tare da matayen mu a guri daya dan mu karfafa zumuncin tsakanin mu, so yayi ace yayan mu sun taso tare babu bambanci kamar yadda babu bambanci muma a tsakanin mu" ya danyi murmushi yace "it was even one of his dreams wai watarana yayanmu zasu yi aure da junansu" Amir yayi sauri ya kalle shi amma sai yaga shi hankalin sa bama ya tare dashi, it was deep in his thoughts, ya cigaba da cewa "kasan dan Adam da buri, amma duk kokarin ka na cika burikanka dole sai ka mutu cike da wasu burikan. Amma wannan duk da shine abinda na fito da kai nan in gaya maka ba, abinda na ke so in gaya maka shine wannan gidan a yanzu naka ne kamar yadda ya kasance na mahaifinka before you. Yana daga cikin abinda na gada daga gare shi, kuma tunda kana da rai hakan yana nufin bani da gadon sa kenan daga ni har yanuwana, dan haka dole zamu dawo maka da duk abinda muka gada daga gare shi as soon as possible dan mu guje wa cin dukiyar maraya. Ni abinda na gada shine gidan nan a kuma share a cikin H and H. Wadanda sune abinda na bawa Ruqayyah kamar yadda ta nema dan kar ta bata sunan mahaifin ka kamar yadda tayi iƙrarin yi. Dan haka a yanzu duk wani abu na dukiya da yake dauke da sunan Ruqayyah naka ne, ma'ana gidan nan da duk abinda yake cikinsa da kuma rabin H and H da kuma duk wasu kudi da suke account dinta. For the fast thirty five years babu abinda tayi sai gadin dukiya ita kuma dukiyar tayi ta ninkuwa tana habaka saboda Allah ya san cewa kana nan dawowa zuwa gare ta, ba tare da ita kuma Ruqayyah Allah ya bata ikon jin dadin dukiyar koda kuwa na rana daya ne ba"

"Abu na gaba da zamu dawo maka dashi shine abinda yanuwana mata duka gada, wanda su kuma ni suka bawa nayi amfani dashi tare da sauran abubuwan da nake dashi a lokacin da kuma wasu abubuwan da Aunty ta bani wanda sune na hada na juya har suka zama abinda nake dashi a yanzu. Na san in na duba cikin tsofaffin takarduna ba zan rasa wancan tsohon lissafin ba, sai a zauna a fitar da percentage na abinda zai zama riba na kason da yake naka sai a hada a baka gabaki daya daga uwar har ribar" ya danyi murmushi "zaka iya tashi da estate guda koma fiye da haka"

Amir da yake ta girgiza kai yace "kayi min afuwa Daddy amma ba zan iya karbar komai daga hannun ka ba, na yafe har abada. Abinda zan karba shine wanda yake hannun Ruqayyah saboda in cigaba da rike legacy din Hussain Aminu Abdullahi kamar yadda ka fada min cewa yana daga cikin biririkan sa cewa sunan sa ya jima a duniya bayan mutuwarsa. Zan cika masa wannan burin insha Allah, tare kuma da sauran wasu daga cikin burikansa"

Hassan yace "to sai ka fara cika masa burin ta hanyar tarewa a gidan sa" yayi murmushi, "you have no idea how much yake son wannan gidan" ya fara tafiya zuwa cikin gidan yace "come, let me show you something" Amir ya bishi a baya da sauri yana tunanin abinda za'a nuna masa, the last time da aka ce masa "let me show you something" sai a aka nuna masa kabarin babansa.

Cikin gidan Hussain, or rather gidan Amir suka shiga, sannan suka hau stairs suka yi sama sannan suka yi bangaren dama na inda stairs din suka rabu, sai Hassan ya dauko keys a hannunsa yana juyawa yace "na iya ajjiya, amma ban sani ba ko zasu bude kofar ma?" ya mikawa Amir "gwada mu gani" Amir ya karba ya saka a lock din ya dan yi fama for some seconds sai komar ta bude amma sai ya kasa shiga ya tsaya yana kallon katon palon da duk aka yi amfani da yadi aka rufe furnitures din ciki. Hassan ya wuce shi ya shiga yace "nan ne bangaren Hussain. Anan yayi rayuwar sa a gidan nan ta shekara biyu" Amir yabi gurin da duk yasha kura da yana da kallo, Hassan ya cigaba da cewa "na rufe shi tun sanda na barwa Ruqayyah gidan, saboda akwai abubuwa masu muhimmanci sosai a ciki wadanda ba zan so maci amana kamarta tayi amfani da su ba, na dauka zata yi kokarin balla kofar ta shigo ko something amma bata yi ba. Maybe ko dan dakunan gidan sunyi mata yawa ne already? Though ita kanta ma bata jima a saman ba ta koma kasa gabaki daya saboda Allah ya dauke kafar da zata hau benen da ita".

Amir jinsa kawai yake yi amma hankalin sa yana kan kallon gurin, tun daga kan yanayin ginin zuwa hotunan da akayi wa gurin ado dasu. Sai Hassan ya wuce shi ya bude kofar da take can karshen palon, zuwa mintuna ya fito ya dawo ya tarar da Amir har yanzu a tsaye a inda ya barshi, sai ya bude hannun sa ya saka masa wani abu a ciki. Amir ya dawo da hankalin sa kanshi sannan ya kalli abinda aka saka masa a hannu, wani madaidaicin diary ne mai hardcover, ya maida idanunsa kan Hassan, sai Hassan yace "he spent almost a year writing this to you. Tun kafin ma a samu cikin ka. I almost burn it sanda na dauka ka mutu but cikin ikon Allah I kept it. Gashinan kuma yau na baka. Maybe zai debe maka kewar sa kadan" sai kuma ya bude daya hannun na Amir ya saka masa keys din gidan a motocin da suke cikin garage din gidan wadanda tun ranar da twins din Ruqayyah suka mutu ba wanda ya kuma amfani dasu. Yace "am telling you all of this and giving all this to you saboda kamar yadda mahaifinka yake yawan fada, today is what we have, tomorrow is never promised"

Sai kuma ya juya zai bai gurin yana cewa "ba zan iya zagayawa da kai gidan nan ba, shekaru sun ja" Amir ya saka diary din a aljihun sa yana cewa "haka ne Daddy, Nagode sosai, hakan ma kayi kokari Allah ya kara lafiya. Bara in kira Amatullah sai mu zagaya tare" Hassan ya juyo yana kallon sa yace "Amatullah? Wannan mai shegen son jikin? In na fita zan turo maka Hussain da Abdulrahman sai su taya ka tsara komai. Duk abinda kake bukata zasu yi maka ko su hada ka da wanda zaiyi maka. Amaty babu abinda zata yi maka sai surutu da iyayi" yayi murmushi "halin su daya da baban ta" sai ya juya ya fita ya bar Amir a tsaye yana murmushi saboda ya san wanne baban yake nufi.

Bayan fitar Hassan ne Amir ya cigaba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login