Showing 243001 words to 246000 words out of 300844 words
ranta bata son ya dawo Nigeria din. Kasancewar gidan dayake zaune a ciki a can din gidan mai martaba sarki ne ba wai a gidan Aunty Maryam yake ba, ya saka ya cigaba da zamansa hankali kwance ba tare da yana tunanin ya takura wa wani ba, kyawun takardun sa ya saka ya nemi aiki yake yi tun kafin ya samu sabon admission na PhD din, wannan ya fara supplying dinsa da kudi, duk da cewa dama duk wata ana aika masa da pocket money amma yaga lokaci yayi da zai fara standing up for himself tunda yanzu har ya bawa talatin baya.
Duk wanda yake tare da Adam, ko Fatima, ko kuma yake tare da Adam da Fatima to kuwa ko makaho ne in dai har zai saurara yaji yadda suke magana a tsakanin su yasan akwai soyayya a ciki, amma babu wanda ya taba furtawa a cikin su kuma babu wani wanda yayi musu magana akan hakan. In dai har kanason kaga dariyar Fatima to ka kira wo Adam gurin, amma in baya nan to little Hussain ne kawai yake ganin hakoranta. In Adam yana guri ta kanji ta manta da duk bakin cikin ta da stress dinta suna tafiya ne taji kamar babu su, ko mai yayi, ko me yace, tana jinsa ne har cikin ranta, komai nasa is valuable a gurinta. Wannan yasa ta ke supporting dinsa akan kokarin sa na ganin ya jawo hankalin real iyayensa zuwa addinin musulunci.
She befriended kannensa mata, tana supporting dinsu tana badu shawarwari tana kuma nuna musu good behavoirs na islamic teachings. Sanda tazo Nigeria ma unexpectedly taje gidansu ta gaishe da Maman sa, tunda yanzu sunyi breaking up da uban ta dawo kano kuma yayan sun biyo ta. Daga Fatima har Adam sun sani cewa kadan ya rage su karbi shahada, kawai dai basa so suyi forcing dinsu ne sai dai su idan sunyi ra'ayi da kansu. Babu takura wa a addini.
A shekara ta uku ne Sumayya ta kuma haihuwar Abdulrahim, wanda aka hada taron sunan sa da bikin bude estate ta uku wadda ita ce his biggest so far. A yanzu, in ana maganar masu kudi a garin kaduna, tabbas za'a saka da sunan Hassan Aminu Abdullahi. Sumayya kuma ta mori ladan biyayya dan a yanzu idan da za'a dawo mata da baya ace ta kuma zaben miji da Hassan zata kuma zaba ko da kuwa sau goma ne. Bata da wani problem wanda ya wuce lafiyar yaruwarta da har yanzu take cigaba da lalacewa dan last zuwanta ma Ruqayyah nuna wa tayi kamar bata santa ba, sai daga baya kuma sai ta fara yiata kuka tana tambayarta ina yayan ta. Babu irin rokon da bata yiwa Hassan akan ya barta ta tafi da yaran Ruqayyah ta gansu amma ya shafa wa idonsa toka yace bai san wannan maganar ba, "in sun ganta kuma sai kice musu wacece? Ta yaya zaki musu bayanin dalilin da yasa kuke kama?" Tace "sai ince yaruwa tace, saboda yar uwa tace, kuma banajin ma zasu ga kamannin da muke yi, dan yanzu babu wata sauran kama a tsakanin mu" ta fada tana share hawayen fuskarta.
Tasan yanada soft spot for her, balle yaga tana kuka, sai ya dawo ya zauna a kusa da ita ya rike hannunta "Sumayya! Yaran nan are not ready for Ruqayyah and her drama. What if kuka je ta gaya musu ita ta haife su? Ta yaya zaki fara yi musu bayani? Kinsan yaran nan fa sunyi wayo yanzu sosai, suna lura da komai. Nasan dole zasu santa watarana amma not now please, dan Allah kar ki tayar min da hankalin ki akan wannan maganar" ta share hawayenta, tana kallon sa, yayi kokarin yi mata murmushi da fatan ko zai samu ta mayar masa amma sai ta kasa mayarwa, fuskar Ruqayyah kawai take gani a ganin da tayi mata. Tace "dan Allah, ka samu lokaci kaje ka ganta, na tabbatar in kaga halin da take ciki zaka shiga cikin maganar".
Haka tayi ta lallaba shi amma yaki yarda. Ta koma tayi ta bin su Baba amma suma duk babu abinda zasu iya yi akai tunda suna ganin case din Ruqayyah a hannun police yake ballantana suje suce zadu dauke ta ko su chanja mata asibitin, Hassan din ne dai tunda yana da masu gidan rana zai iya jan wasu zarurruka ya fitar da ita, shi kuma Baba ya kasa yi masa maganar tunda ya san cewa in yayi masa magana ba zaiyi masa musu ba amma zai zama kamar ya takura masa ne.
Sulaiman ne yayi kokarin neman Lukman akan maganar, ya tuntube shi kan batun fito da Ruqayyah kamar yadda yayi alƙawarin zaiyi tun farko amma kuma sai Lukman din ya nuna masa cewa yana yin iyakacin kokarin sa akan hakan abin ne yafi karfin sa, ya dauko masa takardun bogi ya nuna masa yana masa bayanin irin kokarin da yake yi akan maganar Ruqayyah. Amma sai Sulaiman ya nemi cewa zai ke shiga cikin duk fafutukar da Lukman din yace yana yi, ma'ana zasu ke yi tare da ya tabbatar da cewa anayi din.
Farko Lukman ya tsorata da cika ido da hargagin Sulaiman, amma ganin bai yi masa maganar kudin Ruqayyah dake hannunsa ba sai ya sauke ajjiyar zuciya, amma shi Sulaiman babu abinda ya dame shi da kudin Ruqayyah, shi Ruqayyah din yake so. Amma maganar kudin Ruqayyah dake hannun Lukman, duk da bushashar da Lukman yake yi dasu amma kullum karuwa suke yi suna kuma ninkuwa, H and H group of companies kullum cigaba yake samu da kuma karin samun karɓuwa a gurin mutane a ciki har ma da wajen kasarnan.
Shekara ta hudu tazo ta wuce, a cikin tane kuma akayi bikin Sulaiman wanda Hassan ya bashi gida a cikin phase 1, ya kuma tare da matarsa Ummulkhairi, bayan bikin ne kuma Sumayya ta same shi da magana akan Ruqayyah inda ta nemi su hada kudi a tsakanin su, tunda yanzu shima yana aiki yana daukan albashi, Zunnur kuma tunda ya gama jami'a ya kama business, ya bude boutique yake siyar da kayayyakin maza dana mata na zamani. Shawarar da suka yanke shine zasu hada kudi, shi Sulaiman zaije gurin police yayi following case din Ruqayyah yaji menene options dinsu akan ta, suka kuma yanke shawarar kar su saka Lukman a ciki dan sun fara fahimtar inda ya dosa akan maganar. Daga nan suka fara fafutuka, daga waccan station din zuwa wannan, daga waccan court din zuwa wannan, police suna ta cin rabon su daga hannayensu, alkalai suma suna cin nasu, amma shiru babu Ruqayyah babu labarin ta.
A shekara ta biyar bayan an rufe Ruqayyah ne Sumayya ta kuma haihuwa, ta haifi mace this time around, a cikin murna ne Hassan yace ta fadi duk abinda take so ya bata shi kuma zai bata, ko kuma in akwai abinda take so yayi mata ta fada ko menene shi zaiyi mata. Ita kuma anan ta yi amfani da damar ta ta shigar masa da maganar Ruqayyah, ta fara kuka "dan Allah Habibi ka shiga maganar nan, munyi iya kokarin mu mun kasa, she is dying slowly, dan Allah" ta dauko wayar ta tana kokarin nuna masa hoton Ruqayyah amma sai ya daga mata hannu "bana son ganinta. Kina so in fito da ita?" Ta gyada kai da sauri, yace "to zan fito da ita, saboda ke, saboda bana son ganin wannan a idon ki" ya fada yana goge mata hawayenta.
And, anan kudi da power suka yi aiki. Within a week akayi komai aka gama. Ranar sunan babyn Sumayya wadda aka saka wa Amatullah, a ranar ne kuma aka sallamo Ruqayyah daga gidan mahaukata, Sulaiman ne yaje dauko ta amma da yake sunan Lukman ne a matsayin care taker din ta dan haka dole asibitin suka kira shi shima yazo, sai dai daga nan Sulaiman bai taho da ita gida ba sai ya zarce da ita private hospital sannan ya kira gida ya gaya musu inda suke da halin da suke ciki.
Dubai, United Arab Emirates
Ranar da aka fito da Ruqayyah ta zamo dai dai da ranar zagayowar haihuwar little Hussain, shekara goma, meaning wata daya da kwanaki ne kadai suka rage Hussain yayi shekara goma a kasa. Fatima ta shirya masa Birthday party, ta kuma yiwa su Hassan video call sun gani suma kuma sun nuna musu kwalliyar su ta suna sun kuma nuna musu baby, little Hussain yana ta murna yayi kanwa mace atlast.
Adam ya cika little Hussain da gifts, dan shima ba kadan yake son yaron ba, kuma son nasa yana da nasaba da kamar dayake yi da oga Hussain da kuma son da Fatima take yi masa. Bayan sun gama ne Fatima ta tafi raka shi mota zai koma gidan sa, tana ta yi masa hira amma shi yau sam ba hirar yake ji ba. A mota ne ya bude baya ya dauka wani dan karamin akwati kamar na sarka ya mika mata yace "a beautiful gift to the most beautiful woman in the world" sai ta harare shi, "yau kuma wani abu ya hau kan ka haka?" Ya dan shafa kai yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa yace "open it mana"
Ta dauki box din tana kallo, tayi mata kyau sosai amma kuma zuciyar ta tana bigawa sosai akan abinda zata gani a ciki. Tana kallon Adam wanda shima ita yake kallo yace "open it" ta hadiye wani abu da yake neman kawo kwalla idonta ta bude, sai a lokacin ta lura da cewa music box ce, irin dan box din da kana bude shi zai yi kida,
"There are three words, that I have been dying to say to you"
"it burns in my heart, like a fire that ain't going out"
"there are three words and I want you to know they are true"
I need to let you know, I wanna say I Love You, and I wanna hold you tight, I want your arms around me and I want your lips on mine
I wanna say I Love You, but beb am terrified, my hands are shaking my heart is racing, but it is something that I can't hide, something I can't deny.
So here I go.........
Darling I love you
Sannan sai box din ya karasa budewa and a ring appears. A very beautiful ring.
*Rejection*
Tayi sauri ta rufe box din sannan ta rufe idonta, jin take yi a ranta tamkar ta rufe kunnuwan ta suma ko zata daina jin yadda kalmomin suke amsa kuwwa a cikin kanta. Siraran hawaye ne suka fito daga idanunwanta suka biyo ta kan kyakkyawan kuncinta sannan suka sauka akan kirjinta. Adam ya bi hawayen da kallo har suka iske destination dinsu yana jin tamkar digar dalma ne a cikin tashi zuciyar. Ya dafe goshinsa da hannu daya yana jin haushin kansa, how foolish of him to say these words to her, yana jin haushin zuciyarsa data zuga shi tana masa creating scene iri iri na yadda Fatima zata yi accepting proposal din sa and they will live happily ever after. "Stupid" ya fada wa kansa, "idiot" ya kara.
Ta bude idonta sannan ta juyo tana kallon sa, yana jin kukan ta yana soya zuciyarsa "Adam" ta fada a hankali, sai kuma ta kasa ci gaba da magana, ya hadiye abin da yake barazanar hanashi numfashi sannan ya gyada kai "am sorry Zahra. It was foolish of me" sai ta kara karfin kukan ta tana matse box din a tsakanin hannayenta. "Ba kai ne mai laifi ba Adam, ba kayi min laifin komai ba. Ni ce mai laifi to, zuciyata ce mai laifi Adam, ita ce take yi min zafi" ya gyada kai yana jin tamkar ya kamata ya share mata hawayen ta, yace "am sorry da na zama silar da yasa zuciyarki take yi miki zafi"
Ta juyo tana facing dinsa, dan box din still a hannunta, sai ta girgiza kanta tace "am sorry Adam, I can't do this" sannan sai ta kama hannun sa ta bude ta saka masa box dinsa a ciki sannan ta rufe tayi taku biyu baya sannan ta kuma cewa "am sorry". Sai kuma ta juya da sauri cikin gidan, duk da baya kallon fuskarta amma yasan cewa kukan take yi har yanzu, ya bude hannun sa yana kallon box din, yana jin ina ma dai bai kawo mata ba? Ima ma dai bai biye wa zuciyarsa ya fadi mata abinda yake dakon sa for over five years ba, but komai da limit dinsa, a hakan ma yana jinjinawa kokarin da yayi.
Sai dai kuma turning dinsa down da tayi yafi komai bata masa rai, da bai fada mata ba ba zata yi turning dinsa down ba, da ya cigaba da samun damar ganin ta kamar kullum suyi hira suyi dariya together, amma yanzu yasan wannan abin ya shiga tsakaninsu kenan, dole ba zasu koma kamar yadda suke before yayi fooling kansa ba. Sai yanzu yake ganin foolishness dinsa, waye shi? Shi a suwa da har zai gaya mata wannan three words din da yayi ta practicing yadda zai gaya mata su for a very long time. She is a princess, a widow of his former employer, how dare he even said that to her!
Yayi kicking tayar motarsa sai kuma ya rike kafar yana jin zafi, amma zafin da yake ji a zuciyarsa yafi yawa. Shi ba kowa bane ba face dan riko a gidan su, duk abinda yake takama dashi a yanzu, hatta wannan motar da yake shiga yake kira da tasa duk ya samu ne albarkacin babanta, duk mahaifin ta ne yayi masa komai, ilimin sa kuma dayake ji dashi a yanzu Marigayin mijinta ya taka muhimmiyar rawa wajen samar masa da shi.
Amma ita zuciya ai bata san wannan ba, not when dealing with a lady like Fatimah. Perfect in every way. Shekaru goma kenan da rasuwar mijinta, a cikin shekaru goman nan kullum sai ya ganta, sanda suna imo kullum suna tare for five years, su abinci tare suyi hira tare suyi sallah tare, kullum jam'i suke yi tunda bashi da masallacin da zai je yayi sallah a cikin mutane, ya tuno da yadda take saka masa rigima kullum sai ya bata labari zata yi bacci, she always calls him handsome. Shin ina laifin zuciyarsa dan ta fada cikin soyayyar ta?
Bayan sun dawo kuma bata taba nuna masa fifiko ko wani dagawa saboda title din ta ba, ta cigaba da treating dinsa kamar suna can dan sau da yawa yana jin comment daga gurin brothers ko sisters dinta cewa "in kana son ganin dariyar Fatima to ka kira mata Adam" duk sanda ta shiga cikin one of her moods shi suke kira, shi kadai yake iya soothing dinta ta saki ranta har kuma ya saka ta dariya. Ko bai kira ta ba ita sai ta kira shi a waya kullum, a can Nigeria da kuma nan Dubai, in suna makaranta suna tare in ya dawo da ita gida sai ta hana shi tafiya tace ya zauna tare da ita, sai ya bambare kansa da kyar yake guduwa, da daren ma kuma ko yana gidan sa sai sunyi waya,ta kan yi girki na musamman ta kai masa har gida a duk ranar da yaki zuwa gidan Aunty Maryam yaci abinci. Shin menene laifin zuciyarsa dan ta fada cikin soyayyar ta?
Ya bude motar ya shiga yana jin wani irin zafi a zuciyarsa, dama haka mutum yake ji in aka ce ba'a son sa? Dama wannan shi ake kira da real heartbreak? Kaji duniya tayi maka zafi, hatta yawun bakin ka yayi maka daci, kaji kana jin haushin kanka kuma kana jin haushin kowa da yake kusa da kai hatta wadanda basu yi maka laifin komai ba, amma no matter how much he tried ya kasa jin haushin ita wadda tayi rejecting din nasa. Sai dai yayi ta dorawa kansa laifi.
Karar wayarsa yaji a aljihun sa da ringtone din da yayi setting just For her, ringtone din da a rana ya kan yi kara kamar sau goma ko ma fiye da haka. Bai kula wayar ba ballantana ya dauka, ya cigaba da tukin sa a hankali dan yasan in yayi gudu to kuwa sai dai ya kuma ganin fuskar Fatima a lahira dan tabbas sai yayi accident. Bai tsaya ba sai a kofar gidan da yake a matsayin nasa, zuwa lokacin wayar tayi kara yakai sau biyar ko fiye da haka, ya kashe motar sannan ya dauki ring dinsa yana kallo, it is such a beautiful ring da ya jima yana zaba yana saka wa ana kara trimming dinsa, har sai da ya saci zobenta ranar nan ya kai aka gwada size din wai dan ya tabbatar yayi mata dai dai bai yi mata kadan ko yawa ba. In ya kalli yatsunta har imagining yadda ring din zaiyi mata kyau yake yi.
Ya adana shi a cikin motar sannan ya fita ya rufe ta ya shiga gida a lokacin da wayarsa take sake wani kidan.
"You make me wanna call you in the middle of the night, you make me wanna hold you till the morning light, you make me wanna love, you make me wanna fall, you make me wanna surrender my soul. I know this is a feeling that I just can't fight, you are the first and last thing on my mind, you make me wanna.............."
Ya dauko wayar ya katse kiran tare da tafiya gurin setting dan ya chanja mata ringtone, zuciyarsa ba zata iya dauka ba. Kafin ya chanja wani kiran ya kuma shigowa, da yake yana cikin danna wayar ne sai yayi rashin sa'a ya dauki kiran. Muryar Aunty Maryam "Adam kana ina? Me ya samu Fatima take ta kuka haka?" Ya shafa fuskar sa, wannan kukan yasan kwana zata yi tana yin sa yace "kuka take yi? Me akayi mata?" Tace "to ni dai ban sani ba, gashi ta saka shima Hussain ya zo ya saka ta a gaba suna tayi. In baka ita ko zata gaya maka?"
Yaji zuciyarsata so su, kullum indai akan Fatima ne a gurin mutane to shine solution, ammaita a gurin ta ashe ba shine ba. Bai bayar