Showing 48001 words to 51000 words out of 300844 words

Chapter 17 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2061

ku lallaba min Baba ya yarda ya karbi gidan nan. Ku hada kanku ku nuna masa kuna so ya karba. Kunji"

Duk suka amince, ya juya yana kallon Ruqayyah da take ta zabga murmushi yace a hankali "do you like it" tace "sooo much. Yayi kyau sosai. Mungode Allah ya saka da alkhairi" yace "bana hana ki yi min godiya ba? Duk abinda nake dashi naki ne, to menene in mutum yayi amfani da abinsa?" Taji wani irin dadi a ranta, duk abinsa nata ne, tabbas bata da sauran wata damuwa a duniya.

Bayan ya ajiye su ne yace musu, "bayan gida kuma, akwai Napep da Hussain ya bashi shima saboda transport da kuma ko zai kezagayawa dashi, na san Baba baya son zaman banza" ya karasa maganar yana fadada murmushin sa. Sumayya ta taya shi murmushin "lallai kasan Baba. Ai kuwa Hussain ya kyauta sosai ayiwa Baba Godiya"

Sama sama Ruqayyah take jinsu. Tunda kalmar Napep ta shiga kunnuwan ta taji kunnen ya toshe. what? Baban nata ne zaike yin hayar Napep bayan ya taso daga aikin gadi? Ta juya ba tare da tace da kowa komai ba ta shige gida. Hassan yana sallama da yaran vai lura da shigar ta ba sai daya waigo yaga bata nan. Ya ji babu dadi, ya so su dan taba hira kadan amma kuma sai ya bata uzuri da maybe ta gaji ne, gashi kuma dama tace kafarta tana ciwo.
.
Ruqayyah tana shiga gida ta fara masifa "Napep fa yace, wannan wanne irin cin mutunci ne da cin fuska. Me nayi wa Hassan da zai ke wulakanta ni irin haka? Wannan ce sakayyar da zai yi wa taimakon da nayi masa?" Sumayya data biyo bayan ta tace " ke baiwar Allah! Yanzu menene laifin Napep din? Menene laifin wanda yaso mahaifin ki da arziki?" Tace "arziki? Ina arzikin yake? Napep din ne arziki? Mutumin da na tseratar da rayuwar sa shine zai jefi ubana da keke Napep? Ji nake a sanadiya ta ne ya samu ransa, kuma ya samu dukiyar sa daga hannun wadanda suka sace shi. Ji nake naira billion daya aka xe an karba daga hannun barayin kuma an bashi kayarsa? Me ya bani a ciki? Me ya taba bani? Sim card din?"

Sumayya tace "wannan ra'ayin sa ne ya baki ko ya hana ki, ganin damarsa ce. Amma ya kamata ace abinda kika samu daga gare shi ki gode Allah. Yaushe rabon da kinkwana da yunwa? Yaushe rabon da kici mai da yaji? Ji nake duk a dalilin haduwarki dashi ne? Yanzu kayan da suke jikinki ta dalilin wa kika samu. Ina laifi? Ina laifin wanda ya bawa mahaifinki aiki ya daina leburanci da turin baro? Ina laifin wanda ya bawa mahaifinki Napep yace yayi sana'a dashi? Gidan daya siya mana kuma fa? Mai tilesda ac da ban dakin water system? Shima duk bai kyauta ba?"

Ruqayyah tace "wannan kuturun gidan kike magana akai? Ai wannan gidan is nothing in aka duba irin dukiyar sa, wannan gidan ai bai kai gidan da a za'a nuna ace ga gidan surukan mutumin daya mallaki kamfanoni ba. Ban taba lissafin cewa zan auri mai kudi ba sai da na hadu dashi, ban kuma san cewa marowacin mai kudi zan aura ba sai yau. Wallahi yayi da yar halak, ba dai za'a yi bikin ba? Ba dai zan shiga gidan sa a matsayin matarsa ba, wallahi sai na chanza masa takunsa tunda dai ace duk motocin da yake ta shiga yana fita dasu ya rasa wadda zai bawa mahaifina sai ya bashi Napep. Wallahi har wannan gidan sai ya chanza in dai yana son zaman lafiya"

Ta wuce Sumayya kamar kububuwa. Duk maganganun su Inna Ade tana tsaye akan baranda tana jinsu. Sai da Ruqayyah ta zo zata wuce ta sannan tace "zo nan Hassana" ta dakata da tafiyar da take yi amma bata juyo ba ballantana Inna Ade ta saka ran amsawa. Inna Ade tace "yanzu rashin godiyar Allahn naki har ya kai haka Ruqayyah?" Ruqayyah tayi magana kasa kasa sannan ta juya zata shige daki. Inna ta saka hannun ta na hagu ta finciko ta baya sannan ta saka na dama ta wanke ta da mari tace "watakila wannan ya dawo dake cikin hayyacin ki".

Hussain yana ta shirye shiryen sa. Gida ya kammala, an gama finishing touches da komai. Takanas aka yo masa yawa daga masarautar kano akan cewa kar ya saka wa Fatima komai a dakunan ta. Bai so haka ba, amma sai ya bar musu ya fara zuba kaya a nasa dakunan, the best of the latest of komai yake sakawa. Hassan ya fada tuntuni cewa shi zai yiwa da Ruqayyah kayan daki. Amma kuma Hussain ya ga shiru, kullum in yayi masa magana ko kuma yayi masa tayin wani design na kaya sai yace ai zaiyi ne "tunda nace maka zanyi ka bar ni mana, ina ta planning irin wadanda zan saka da wanda zan saka mata, ba lallai ta so irin naka ba kasan taste dinta ba irin na gimbiya bane ba" Hussain yace "ka tambaye ta ne kaji wanne taste ne da ita? Ko kuma dan sunan ta Hassana sai ya zamanto tana da ra'ayi irin na Hassan?"

Daga nan bai kuma bi ta kan Hassan yakira kamfanin daya bawa kwangilar nasa aikin yace su shiga gidan Hassan su saka komai "kaya masu kyau zaku saka a ko'ina, karku gaya masa, in kuma yazo ya same ku kuna aikin kuce masa ni na saka ku" ai kuwa kamfani suka zage dantse suka fara kure adakar su a gidan Hassan. Gashi dai gidan ba za'a kira shi da katon gida ba amma kuma sanda suka gama aikinsu sai ya zamanto kyan da gidan yayi ba karami bane ba. Babu abinda zaka kalla ba tare da ka kuma kallo ba.

Sanda Hassan ya samu Hussain da fadan me yasa ya taba masa gidan sa sai yace "ba kai na sakawa ba, Ruqayyah na saka wa. It is my wedding gift to her, it is just my little way of saying thank you for saving my brother".



Kuyi hakuri in kunga typos......

Wannan littafin na siyarwa ne, duk mai so tayi min magana ta wannan number din 08067081020.

No calls please, WhatsApp only.


Eighteen : His Religion

Ranar da Hassan ya bawa Adam complimentary card dinsa, a hanyar sa ta komawa gida yana ta bitar hirar su da Sumayya yana murmushi, yana mamakim kansa yadda har ya iya ce mata he likes her. He saw the look in her eyes kuma ya fahimci abinda take tunani, alaka tsakanin su zata yi wahala gaskiya, bazai ce impossible ba saboda yasan babu wani abu da yake impossible agurin ubangiji, idan Allah yayi zasu kasance tare to ko sama da kasa zasu hadu tabbas sai sun kasance din.

Rayuwar sa kadai ta isa misali a gurinsa na cewa nothing is impossible indai aka saka Allah a ciki. Bai taba tunanin zai yi wannan rayuwar ba, sanda ya fara ta kuma bai taba tunanin zai yi surviving ba amma gashi nan yanzu har ya saba. Da dadi ba dadi he still prefers wannan rayuwar akan wacce ya baro a baya.

Yanzu gashi cikin ikon Allah da kudirarsa sai gashi ya fada hannun ogan h and h, gashi har yace yaje ya same shi a office zai bashi aiki, wai aiki a matsayin driver. Still yana feeling excitement in ya tuno da yadda aka tsara masa aikin, irin benefits din gaskiya abin ya burge shi sosai. Dan haka monday da sassafe yana tunanin shi kansa Hassan din sai dai yaje office ya same shi yana jiran sa. Fatan sa kawai kar ya ganshi cikin hasken rana ya fahimci ko wanene shi yace ya fasa bashi aikin. Kamar yadda yake tsoron ranar da baban Sumayya zai kama shi yace kar ya sake dawo masa gidan sa.

Haka ya karar da weekend din nan cikin saka da warwara, sai dai ko sau daya tunanin sa bai bashi cewa ya fasa zuwa ba dan shi mutum ne da yakan doshi abu ko da kuwa yasan da illarsa ballantana wannan da bai tabbatar ba, dan haka monday nayi ya shirya ya tafi, sai ya zamanto har ma ya riga shi kanshi Hassan din zuwa office din. Ya zauna ya jira har aka ce masa yazo, sannan aka sanar da Hassan zuwan Adam sai yace ya jira shi. Daga nan Adam ya zauna jira, shiru shiru shi dai yana zaune yana jira yana kuma lissafa yadda rayuwarsa zata kasance a matsayin drivern gidan masu kudi, yayi murmushi yana girgiza kansa yana tuna drivers din da suke gidansu yana kuma zaben wanne daga ciki zaiyi koyi da, but sai dai duk cikin su babu yaro karami kamarsa, babu mai background irin nasa dan haka babu wanda rayuwarsu zata zo daya.

Ba zaiyi koyi da kowa ba he is going to live as himself.

A haka aka leko aka kira shi. Ya shiga yana kallon fuskar mutumin da suka gaisa ranar nan amma da yake ranar da daddare ne sai yanzu ya samu ya ga cikar halittar sa da kwarjinin sa. A ina Ruqayyah ta samu wannan? Me yasa ya zabi Ruqayyah a matsayin matar aure? When? Where? How? Why Ruqayyah bayan duk yammatan da suke gari babu wadda zai ce yana so tace a'a? Sai kuma yayi saurin kawar da tunanin sa daga kan maganar, zuciyarsa tana kwabarsa da cewa "ina ruwanka? Kai da kazo neman aiki ina kai ina bin diddigin insa ogan ka ya samo budurwar sa?

Ya zauna akan kujerar da Hassan ya nuna masa sannan ya gaishe shi, ya amsa yana rubutu a takardar da take gabansa, sai Adam yaga kamar he is not as nice as he was ranar nan. Sai da ya gama rubutun sa ya dago kai sannan yace "barka da zuwa. Sorry I kept you waiting. Ban dauka zaka zo yau ba ban kuma dauka zaka zo da wuri ba, already akwai masu appointment so I have to see them first. Ina fatan ka gane" Adam ya gyada kai da sauri. Sannan Hassan ya tambaye shi full name dinsa. "Adam......." Hassan "Adam who? Adam ya dauke kansa gefe yace "Adam Clement Young" ya fada yana studying Hassan yana so yaga yadda zaiyi reacting to the name amma sai yaga ya rubuta ba tare da yanayin fuskarsa ya chanja ba. Daga nan ya cigaba da jero masa tambayoyi, "age" "23" "tribe" "igbo" "state of origin" "imo" "religion" "islam" haka suka yi tayi yana jero masa tambayoyi akansa shi kuma yana amsawa, ya tambaye shi contact address dinsa sai ya bashi adireshin dakin da yake haya sai kuma ya tambayeshi permanent home address sai ya kuma bayar da same address. Hassan ya dago yana kallonsa sai shi kuma ya sunkuyar da kai, Hassan ya ajiye biron hannunsa yace "for this, you have to give me address din inda mahaifanka suke, gidan ku nake son sanin a ina yake" Adam yace "Kano" Hassan yace "kano wacce unguwa, wanne layi wanne number din gida?" Adam ya dago kai yace "that's a very private question" Hassan ya bude baki cikin mamaki yace "you think so? I am about to give you a very private job na entrusting rayuwar only brother dina a hannunka, and you are telling me address din gidan ku is a private thing? I have to know as many things as possible akan ka kafin in iya baka wannan aikin".

Adam ya gyada kai, ya yarda da abinda yake cewa but it is just that bai fiya magana akan parents dinsa ba sai in ta kure, kamar yadda ta kure yanzu dan gaskiya yana son wannan aikin sosai saboda chance din da ya gani a cikin aikin na komawa makaranta. Yana son karatu sosai. Dan haka ya fada "house number 14, badawa layout, Nassarawa local government, kano state"

Daga nan tambayoyin suka ci-gaba kamar ba zasu kare ba, "wannan mutumin da bin kwakwkwafi yake" Adam ya fada a zuciyarsa. Sai kuma ya yi kokari wajen ganin cewa ya fadi gaskiya to the best of his knowledge. Sai da suka gama sannan Hassan ya rufe file din gabansa and for the first time tunda ya shigo yayi masa murmushi yace "that will be all. Kayi kokari sosai, but I will have to run a background check on all what you said, ba zai dauki lokaci ba zan gama within this week next week insha Allah zan kira ka in gaya maka yadda ake ciki" Adam yaji gabansa ya fadi, ya dago da budaddun idanuwa yana kallon Hassan, Hassan ya daga kafada yace "yes now, ta haka ne zan tabbatar da gaskiya, ko akwai wani abu da kake boyewa ne?" Adam ya sunkuyar da kansa yana girgiza kansa, wani bari na zuciyarsa yana gaya masa cewa yace ya fasa neman aikin amma kuma ita magana ai kamar zarar bunu ce inta fita bata komawa. There is no going back. Fatan sa kawai in Hassan ya samu abinda yake fatan kar ya samu to kar ya gayawa Sumayya. Idan zai gaya mata to shi zai gaya mata da kansa.

Adam yana fita Hassan ya dauko wayarsa yayi kira "Hello. Kanawan dabo. Kana lafiya? Ya iyalin? Dan Allah dan wani taimako nake nema, zan turo maka info din wani yaro ina son kadan bincika min shi. Eh nan kano yace min unguwar badawa. Okay, just find out if there is anything that I should know about. Thank you." Ya kashe wayar yana murmushi, rami ya gina wa Adam kuma ya fada ciki.

Tun sanda ya ganshi yana zagaya gidan Baba kuma ya fahimci gurin Sumayya yake zuwa kuma ya fahimci cewa ita ma Sumayyan kamar tana da interest akansa sai ya kudurce a ransa yana so yayi bincike akansa amma ya san ba zai bashi hadin kai ba shine ya yaudare shi da aiki dan yaga alamar yana bukatar aikin, yanzu sai yayi binciken sa sosai akansa, in ya samu alkhairi zai bashi aikin kuma yayi masa jagora zuwa ga Sumayya in kuma ya samu sharri sai yayi warning Sumayya kuma aikin ma ya bi ruwa.

Bayan ya tashi daga aiki ne ya koma gida ya tarar Aunty tana palo tana jiransa "kudin nan fa sai ka karo su Hassan. Kaya gasu an fara siya basu fi rabi ba amma kudi sun kusa karewa, ko boxes din ba'a siya ba. Ga sauran kayan al'ada da ake yi duk ba'a siya ba" ya shafa kai, "aunty, kayan nan wai me zata yi ne dasu? Ji nake dai sakawa zata yi a jikinta in tazo gidana ko? To ba gani ba muna tare? In tazo din duk abinda take so ai za'a siya mata" Aunty ta girgiza kai tace "ba shi kadai ne amfanin lefe ba, ai ana rabawa dangi, kusan rabin kayan ma rabarwa ake yi ballantana su da ba masu kudi ba ai kaga duk zasu so su rarrabawa dangi suma su samu albarkacin ta ko? Shi yasa nake siyan kayan kashi biyu akwai masu tsada sosai akwati daban za'a saka su a matsayin nata, masu dan saukin kudi kuma sai a siya da yawa a basu a ce a raba wa yan'uwa" yayi ajjiyar zuciya "mata dai da al'ada. Shikenan nawa za'a karo yanzu?" Ta gaya masa, ya bude baki yana mamaki tace "to boxes din ma set uku zan siya, biyu nata daya na rabo" ya rufe bakin yace "set daya ya ishe ta, set daya na rabon. Yarinyar nan ba sabawa tayi da irin wannan spending kudin ba, nafi so kuma ta cigaba a haka. In an siya da yawan ma sai dai tayi ta ajiiyar su sai a hankali zata saba da amfani da wasu abubuwan ma. Dan haka gwara a bari in tazo din ta fara sabawa a hankalin sai ake introducing dinta to sauran abubuwa" Aunty tace "in an siya mata a kayan lefen nata ai dole zata koya, in bata dasu ta yaya zata koya? Kuɗi fa sai ka fito dasu komai wayon ka" yayi dariya yace "shikenan Aunty, zan kawo gobe" tace "yauwa, kuma ina son inji yadda kuka yi da ita akan sauran hidimomin biki, nawa zaka bata?" Ya sake bude baki "bikin ai da saura ko" tace "sauran wata daya ba? Yanzu lokacin yadda yake gudu kafin ka gama lissafin ka wata dayan ya kare. Kaje ku zauna da ita ta fada maka shirye-shiryen ta sai ka lissafa ka bata abinda zai ishe ta" ya mike tsaye yana cewa "an gama Aunty" tayi dariya tace "zaka gudu ko? To ai ban gama da kai ba" yace "in na cigaba da zama sai kaina ya kunce saboda lissafin kudin da za ki cigaba da yi min".

A bangaren Ruqayyah ranar da ta sha mari a gurin Inna kusan kwana tayi ta kasa bacci, ba wai marin ne yayi mata zafi ba a'a yadda akayi mata marin a gaban kannenta sannan inna ta wanke ta tas da soso da sabulu shi yafi kona mata rai. Yanzu ai sai su raina ta su cigaba da kallon ta da sunan da Inna ta kira ta dashi "butulu".

Ita kuma Inna hankalinta gaba daya a tashe yake da jin kalaman Ruqayyah, ita da kanta wai take ikirarin saita wa mijin da zata aura zama idan anyi auren su. Wannan kadai ya nuna cewa ita ba ta rike alkhairi a ranta ba akan auren nata, Inna taji tana jin tsoro, tana jin tsoron abinda Ruqayyah zata aikata a gidan mijinta. Sai taji a ranta cewa kamar ta bawa Baban biyu shawarar cewa ya dakatar da auren baki daya, amma kuma tana jin tsoron abinda Ruqayyah zata aikata in akace an fasa wannan auren, zata iya yin komai koda kuwa abinda zai lalata mata rayuwa ne, tsoron wannan yasa Inna Ade ta kasa yiwa Baba maganar.

Ita dai tuntuni ta san cewa Ruqayyah jarabawa ce a gare su ita da Baba, iyakacin iyawarta tayi tarbiyyar, ta bada ilimin, ta kuma yi addu'ar. Ba dan Allah ya saka sauran ya'yan sunyi turning out good ba da sai taga kamar laifin sune su iyayen amma yanzu su sun sani, Allah ya sani, sannan duk wanda ya san su ya sani cewa sunyi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login