Showing 294001 words to 297000 words out of 300844 words
visas, siyan tickets kawai ya rage musu sai kuma shiri. Wannan ya sa washegari suka tashi da shiri, kowa yana haka kayansa manyansu da yaransu. Amir kam ji yaje kamar ya jawo jibi ta dawo gobe wanda shine ranar da jirgin su zai tashi. Ya kosa ya ga mahaifiyar sa, ya kuma kosa yaga Suna cikin shirye shiryen ne kuma sai mota guda na yanuwan Fatima daga kano dan tun ranar da Amir yazo gida aka gaya musu aka kuma roke su akan kar su gaya wa Fatima su bari yaje har can ya same ta.
"Ba zamu iya jira ba, gwara mu zo mu ganshi dan ba lallai bane in Fatimah ta ganshi ta kuma barinsa ya dawo Nigeria"
A ranar sake wuni akayi gidan a cike da mutane. Amir kuma ya wuni yana karbar gata ta ko'ina.
Sai kuma Amir ya bawa kamfanin Moon Construction kwangilar renovating gidansa kafin ya dawo daga Dubai.
Kwana biyu bayan nan suka tashi zuwa UAE bayan Hassan ya kira Adam ya ya masa cewa gasu nan zuwa surprise visit, har Adam din yake masa dariya cewa tunda ta riga ya fada kuma ai ya tashi daga surprise. Sai kuma ya gaya wa Fatima labarin zuwan bakin nasu, nan da nan ita da yammatan ta suka tashi suka fara shirin taryar baki. Sai kuma ga Fatiman Hussain ita ma tazo zasu yi aikin tare, amma fatima a jikinta sai take jin zuwan nasu Hassan yana da dangantaka da wayoyin da take ta receiving kwanan nan daga yanuwanta, kuma kowa sai ya tambaye ta sunyi waya da Hassan? Ko kuma dai wata tambaya data danganci yanuwan Hussain. Ita ji take ma kamar bata da lafiya, wani irin feeling mai wuyar fassara. A ranta sai take kwatanta feeling din da irin wanda taji ranar da Hussain ya tafi Abuja, ranar da tayi sallama dashi sallama kuma ta har abada, ranar da tayi sallama da abinda yake cikin ta.
Duk da cewa duk tsahon shekarun nan bata mantawa da wannan ranar ba, bata taba kuma daina kokarin tunowa da abinda ya faru a ranar ba, amma abinda take ji a cikin kwana biyun nan yafi wanda take ji da, har ji take yi a kunnenta kamar ana kiranta a waje kuma da irin muryar Hussain sai ta duba sai taga babu kowa. Ga kuma Hussain karami daya tafi Nigeria yayi zamansa, ta lura kuma duk sanda suka yi waya kamar yana boye mata wani abu ne sannan kuma lokuta da dama takan ji shi kamar a cikin mutane, kamar ana hayaniya haka.
Farko tayi tunanin ko jikin mahaifiyar sa ne yayi tsanani shi yasa yake zaune gurinta kuma bai gaya mata ba saboda basa maganar ta ita da shi, sai kuma daga baya ta lura babu damuwa a muryarsa, duk da tasan babu shakuwa tsakanin sa da mahaifiyar sa amma ta san ya damu da wellbeing dinta. Wannan, coupled with wayar da ake tayi mata daga gida ya saka ta zama kamar marar lafiya. Dan haka ranar ma kasa aikin tayi sai ta barwa su Islam suyi aikin ita kuma ta koma daki ta kwanta ta lulluba. A haka Adam ya shigo ya same ta, ya yaye rufar yana taba wuyanta yace "what's wrong?" Ta bude ido tana kallon sa tace "bana jin dadi" yace "menene yake damunki?" Tace "nima ban sani ba, kawai dai bana jin dadin jikina da kuma zuciyata" ya kama ta ya tayar da ita zaune, im da sabo ya saba da wadannan mood swings din nata kuma sam basa damunsa saboda shi yafi kowa sanin what she went through.
Yace "kina so muje asibiti ne?" Ta girgiza kai tana jin kamar hawaye zai zubo mata. Yace "ko zuwan bakin nan ne ba kya so?" Ta sake girgiza kai duk da tasan abinda take ji din yana da dangantaka da zuwan nasu. Amma ta yaya zata ce bata son su zo gidanta bayan sun dauko hanya tun daga wata uwa duniya sun taho domin ita. Ta danyi murmushi, dole ta taushi zuciyarta ta karbe su ko da kuwa zuwan nasu zai tayar mata da tabon da yake cikin zuciyarta. Tace "inaso su zo mana, sosai. Zan dan kwanta ne kawai watakila kafin su karaso in danji dadin jikina sai in ji dadin karbar su" ya gyada kai yace "hakan yayi, ki kwanta ni sai mu tafi da Muhammad mu taho dasu".
Sai da ya tabbatar babu sauran wani abu da ake bukata a gidan sannan airport tare da dan autan sa Muhammad wanda yake fifteen years a lokacin kuma yake carbon copy na babansa har gayun. Basu wani dade suna jira ba tunda yayi timing zuwan nasu sai gasu sun karaso. Sai da yaga suna fitowa daya bayan daya sannan ya tabbatar da gaske suke da yawansu suka taho dan family din Hassan gabakidaya Sumayya ce kadai babu sai matar Yusuf amma har matar Aminu da akwai da kuma yayansu duka. Sai kuma kuma kannen Hassan tun daga kan Hassana har kan Zulaihat, sai dai su duk basu taho da yara ba tunda yaran duk an girma. Babu Aunty kuma, girma ba zai barta tayi tafiya irin wannan ba.
A take Adam ya fara mental calculation na gurin da zai sauke su dan yana ganin gidan sa yayi musu kadan, ya yanke shawarar sai dai ya kama musu hotel sai mazan su sauka a can matan kuma wasu gidan sa wasu kuma gidan Hussain. Saboda yawansu ya saka ya kasa fahimtar akwai bakuwar fuskar da bai sani ba, ya fara yin hannu da su daya bayan daya fuskarsa da faffadan murmushi da kuma Muhammad a gefen sa yana gaishe da duk wanda yaga babansa ya gaisar, har yazo kan Amir. Ya mika masa hannu sai Amir yaki bashi hannu ya rissina zai gaishe shi yana jin girmansa a zuciyarsa. Sai a lokacin Adam din ya kalli Amir sosai sannan yayi sauri ya dago kai suka hada ido da Hussain da yake kusa da Amir din da alamar tambaya a idon Adam, sai Hussain ya gyada masa kai yace "Amir sunansa. Abdullahi Hussain Aminu Abdullahi".
Adam ya saki key din hannun sa harshen sa yana sarkewa, kwakwalwar sa ta dauke ballantana bakin sa ya samu kalmomin da zai furta dan ya rasa wacce kalma ce ta dace ya fada din, sai ya tuno da ubangiji, ya tuna cewa babu abinda ya gagare shi sai ya fahimci kalmar da zai yi amfani da ita ita ce tasbihi ga ubangiji dan iyawarsa ce kadai iyawa babu wani wanda ya iya sai dai shi ya iya wa mutum.
"Subhanallah. Hasbiyallahu wa nieemal wakeel. Lallai tsarki ya tabbata ga Ubangiji mai yin yadda yaso a sanda yaso ga kuma wanda yaso" sai yanzu ya fahimci dalilin wannan ziyara da da ya dauka ta sada zumunci ce, ashe tsuntsu biyu ne aka jefa da dutse daya. "Amir!" Ya fada yana rike kafadunsa yana kallon fuskar sa. Bashi da tantama kamar yadda babu bukatar ta sake tambaya dan yasan wannan dan oga Hussain ne. Sai ya rungume shi yana tuno da mahaufinsa da kuma tarin kyautatawar sa gare shi, sai yaji kaunar da yake yiwa Hussain a duk shekarun can na baya ta dawo ta sauka akan dansa, sannan kuma ga matsayin sa na dan Fatima Zahra, tauraruwar da take haske zuciya da gangar jiki sa har yanzu bata dusashe ba.
Ya sake shi ya juya yana kallon Muhammad yace "Muhammad kaga brother dinka, brother dinku da muka ce ba'a san inda yake ba shekara da shekaru ka ganshi ya dawo gare mu" ya fada yana hada hannyensu a guri daya. Amir yana kallon Muhammad kamar yadda shima yake kallon sa cike da shock, shi dai bai taba tunanin yana da kani ba, ballantana as cute as this one.
Sai a lokacin Adam ya fahimci dalilin Hassan na boye maganar dawowar Amir ga Fatima, gar yanzu ba lafiya ce ta ishe ta ba da taji maganar da yanzu anxiety yayi mata yawa, da Allah kadai yasan yadda zata yi spending days din nan kafin suzo. Duk da haka sai ya nemi alfarmar Hassan cewa zasu yi gaba daga shi sai Amir, su kuma in sun gama karbar kaya sai su biyo su a baya tare da Hussain. Ya fi son sanda Fatima zata ga danta ya kasance babu hayaniya abin zai zo mata a nutse.
Su biyu kadai suka shiga motar sa suna tafiya, yana ta so yayi wa Amir hira amma ya rasa abin cewa sai Amir yace " how is she?" Adam ya dan kalle shi yana concentrating a tukin sa yace "okay. She is okay. But she has never been her best tun ranar da aka rabata da kai. Har yanzu da akwai rami a zuciyarta wanda ni da yayana duk bamu iya mun cike mata shi ba" ya danyi shiru sannan ya cigaba da cewa "yanzu ma da zan fito a kwance na barta bata jin dadi kuma nasan zuwan su oga Hassan ne ya tayar mata da hankali ta san sai sun taso mata da mikin rashin ka a tare da ita. Har yau in dai tayi sallah sai tayi addu'ar in dai kana raye Allah ya nuna mata kai, kuma sai tayi addu'ar Allah ya saka muku akan wanda ya raba ku" sai Amir ta tuno da fuskar Ruqayyah. Tabbas addu'ar uwar da aka rabata da danta tsahon shekara talatin da biyar zata mayar da mutum haka ko ma fiye da haka. But with him back, yasan adduar mahaifiyarsa zata tsaya kuma hopefully suffering din Ruqayyah zai ragu.
Sai yaji a ransa yana tunanin ko da akwai wamda ya taba zalunta? Tabbas in dai ka zalinci mutane kuma ba wai cikin rashin sami ba to kayi gaggawar zuwa neman yafiyar su dan ko basu daga hannu sunyi maka addu'a ba kamar yadda Fatima take yi to tabbas hakkin su yana nan yana binka har cikin kabarin ba.
Har suka isa gida babu su Hassan babu labarin su, kuma Adam ya tabbatar zasu dauki lokaci a can din dan suna da yawa, kafin su gama hada kayan su ma aikine sannan sai sun nemi karin motocin da zasu kawo su gidan, but in ya gama da Fatima zai koma ya rago wadansu. Ya shigo da Amir har cikin palo, yana jin hayaniyar yan matan gidan a dining section amma baya son su zo suma suyi hayaniya. Sai ya dakatar da Amir a palo shi kuma ya shiga corridor din da zai sada ka da Bedroom dinsu. Zuciyarsa fal da farin ciki, yana jin dadi sosai daya kasance shine zai numa wa Fatima danta.
A yadda ya barta a haka ya same ta. A bude rufar da tayi yana murmushi. Ta bude idonta a hankali tana jin bata ji dadin dawowarsu da wuri ba dan har yanzu bata jin dadi sai ma faduwar gabanta data karu. Sai dai yanayin da taga fuskarsa a saka ta mike zaune da sauri. Ya kama hannun ta ya mikar da ita tsaye yana murmushi mai hade da dariya yace "Fatima Zahra, gaya min, duk duniya menene burinki" taji hawaye yana bin fuskarta tace "ka sani ai, kafi kowa sanin burina a duniya. In dai yana da rai ina son ganinsa" sai ya ja ta kirjinsa ya rungume ta a hankali yace "Allah ya karbi addu'ar mu Zahra, ya dawo mana dashi" ta ture shi tana kallon sa dan bata tabbatar da abinda yake cewa ba, sai ya gyada mata kai yace "shi su Hassan suka taho kawo wa. Allah ya bayyana mana shi Zahra"
Tayi sauri ta kalli hanyar waje, sai taji yace "he is waiting for you"
Bata kuma jiran sauran wata magana ba, bata kuma san sanda ta fita daga dakin ta fita daga corridor din ba sai ganinta tayi a palo a tsaye tana mayar da numfashi da sauri tana zagaye palon da idonta. Sai idonta ya sauka a kansa, yana tsaye ya juya mata bayansa yana kallon family picture dinsu da yake rataye a palon, ita da Adam, Islam, Iman, Ilham da Muhammad. Yana yin tsayuwarsa sak na babansa, yanayin zubin bayansa sak na babansa sai tsaho da bai kai babansa ba.
Bata san da wanne suna zata kira shi ya juyo ba saboda bata san sunan sa ba, a matsayin ta na mutum da yafi kowa kusanci da shi a duniya amma bata san sunanshi ba, sai kawai ta saki kukan da take ta rikewa, ya juyo da sauri yana sauke jan idonsa akanta. Ta tafi kamar zata fadi, "mother" ya fada da sauri tare da zuwa ya tare ta ta fado jikinsa sannan suka fada kan kujera tare, ta bude ido ta sauke a kansa tana kare wa fuskarsa kallo tace "you are here" yace "yes mother, I am here".
Duk abinda Amir yayi ta mafarkin yadda haduwarsa da mahaifiyar sa zata kasance to abinda ya faru ya wuce nan saboda Fatima ta wuce duk yadda yake kwatanta mahaifiyarsa zata kasance. Haka beautiful beautiful sisters dinsa da little brother dinsa. Haka suka zagaye shi duka makalkale shi ta koina suka hana shi ko motsin kirki. Aysha kuwa da su Sultan nan da nan suka mayar dasu nasu ko ganin su ma bayayi, dan shi sai yaga ma Fatima kamar tafi son Aysha din ma akan sa dan suka zo tana daki a gurin ta shi kuma an barshi palo tare da sisters dinsa da suka hana kowa taba shi.
Lissafin da Adam yayi na inda zasu zauna sai ya tashi a banza dan already tun kafin su taho Hussain ya kama musu wani apartment anan kusa da gidan sai yadda in suka hada da gidan sa ya ishe su, yayi hakan ne dan abar Amir yayi bonding da family dinsa ba tare da takurawa ba, kuma sai Adam ya amince da haka, dan haka gidan Amir kawai aka bari da family dinsa su kuma suka tafi can.
Sanda bakin zasu tafi har da Amir a rakiya, ya dauki motar Fatima ya debi Amatullah, Suhaima matar Aminu yaranta da yaran Yusuf ya tafi dasu gidan Hussain bayan an saka masa address din a Google map, suna tafiya suna hirar kyawun garin har suka iso gidan a dai dai lokacin da sauran motocin ma suke karaso wa. Yana sane ya ja Amatullah da zance dan ya fahimci mai magana ce ita har saida sauran jama'ar motar suka fita sannan ta lura saura su kadai a gurin, ta fara neman jakarta zata fita sai ya dauke jakar ya dora akan cinyarsa.
Ta bata rai "bani jaka ta" shima ya bata rai "sai kin tsaya na ga wani abu" tace "menene zaka gani a cikin jakar, ba'a bude jakar mata fa" ya danyi murmushi, "ba'a jakar ki zan gani ba, a fuskar ki zan gani" ta dan bata fuska cikin rashin fahimta tace "menene a fuskar tawa?" Yace "wai da gaske muna kama? Ni dai ba gani ba" tace "nima ban gani ba. Nafi ka kyau nesa ba kusa ba" yayi dariya tare da daga mata gira "Allah ko? To gaya min menene a fuska ta da bashi da kyau" sai ta juyo tana kare masa kallo har da karkata kai sannan tace "to ni dai ba gane kamannin ka nake sosai ba da wannan tarin gashin a fuska. Dama zaka aske ne watakila inga kamar tamu da ake fada. Ni a haka ma sai naga kana min kama da Davido" ya bude ido "what?" Sai ta kyalkyale da dariya, "wallahi kunyi kama sosai ma kuwa" sai ta bude motar da sauri ta fita sannan ta leko tayi masa gwalo. "Ka kaiwa matarka jakar na bar mata"
Ya jima a zaune a motar yana murmushi sannan ya fita ya yi knocking gidan ya mika jakar ya koma mota ya koma gidan Adam. A palon ya tarar da Islam ya zunduma Sultan a cinya tana bashi abinci a baki, yace "wannan katon yaron kike dorawa a chinya? Sai ya ji miki ciwo?" Tace "aiya, nawa yake ja ganshi fa bai fi in saka zani in goya shi ba" yana kallon Sultan har da kara narkewa wai shi ana shagwaba shi. Amir yayi dariya yace "zaka yi bayani ne, kasan mamanka ba zata dauki wannan shirmen ba" sai ga maman nan kuwa ta fito tana masa murmushi ta zauna a hannun kujerar da yake zaune tana shafa cikinta tare da yin katuwar gyatsa. Yace "yayi miki kyau, wato an kaiki daki an cika miki ciki kin manta da mijinki ko" ta zagaye hannun ta a wuyansa tace "ni na isa in manta da mijina? Duk abinda naci na ajiye maka ai, ka taho muje in baka" ta mike tana jan hannunsa zuwa dining.
Tana cikin serving dinsa abinci sai ga Adam da Fatima sun shigo, sai kuma taji kunya ta juya zata tafi amma sai Amir ya riko hannun ta ya dawo da ita ta zauna a kujerar kusa da shi. Adam ya zauna a gefensa Fatima tana zuba masa abinci tace "Aysha matar kirki ce, matar rufin asiri ce, tayi mana abinda ba zamu taba mantawa ba, tayi mana abinda mata da yawa ba zasu iya ba" Amir yayi murmushi yana jin dadin an yabi matarsa, ita kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta. Yace "hakane, she gave me a home, a family and stability when I needed them the most. And I will never forget that"
Sai Adam yace "naji oga Hassan yayi mentioning abuja's palace, but bamu san abinda ya faru a can din ba. Zaka iya bamu labarin yadda abin ya kasance?"
Sai Amir ya basu labarin, labarin wahalhalun da yasha da kuma dadin da yaji, labarin ups da downs din da yayi ta samu a rayuwa har karshe kamar yadda ya bawa Hassan tare da sauran yan'uwa. Fatima tana ta kuka "ba zan taba yafewa Ruqayyah ba. Ko na yafe mata halin da ta saka ni a ciki ba zan iya yafe mata halin da ta saka ka a ciki ba. And Hussain will never forgive her too." Sai Amir ya dawo kujerar kusa da ita yace "have you seen her lately?" Ta girgiza kanta "ban ganta ba kuma bana son in ganta. Bana