Showing 144001 words to 147000 words out of 300844 words
mamakin sa sai yaji wayar tana kara a cikin mota, sai ya katse ya fara neman ta Hussain, sai dai kafin ta shiga yaji tsayawar mota a bayansu, ya juya da sauri, abinda ya gani shi ya saka shi sakin wayar ya juya kamar zai fita a guje sai kuma ya tuna da Fatima sai ya dawo ya tsaya a gabanta yana kare ta daga wandanda suke tahowa.
Babansa ne mahaifi, tare da wasu maza karfafa su biyu. Ya dauke kansa yana kallon gefe a ransa yana tsananin mamakin yadda aka yi suka iya biyo shi har nan. Uban yace "Joseph? Wannan shine taryen da zaka yiwa babanka? Ka gama guje gujen?" Adam ya girgiza kansa yace "sunana ba Joseph ba, sunana Adam, Joseph din da kuka sani ba shine wannan ba" uban yace "say whatever you want to say, call your self whoever you want to call your self amma ni nasan you are my son, my responsibility, and I am taking you home" Adam ya girgiza kansa, "ni ba danka bane ba, kuka babu inda zanje" sai ya juya ya kalli wadanda ya taho dasu yace "ku dauko min shi" Adam ya sake yin kamar zai gudu amma kumaba zai iya barin Fatima ba wadda duk abinda suke yi take binsu da ido. Ya kalle ta sai ya daga hannunsa yace "zan bika, ka barni in taimaka mata please, in ka barni na taimake ta bazan kuma guduwa ba" mutumin ya kalli Fatima yace "wacece ita? Your girlfriend?" Adam ya gyada kansa yace "yes. She is injured, let me help her please"
Uban yayi murmushi, a ransa yana ganin ya samu weakness din dan, ya dauki wayar adam da ta fadi a hannunsa ya yi jifa da ita cikin ciyayi sannan yace ya dauko Fatima ya shigo da ita cikin mota su tafi, sai da suka shiga motar sannan yace "say bye bye to the north. You are never coming back here".
*This is the Intermission of the Story*
Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020
*Broken*
Tunda Hassan ya tura Adam yabi bayan su Fatima hankalin sa bai kwanta ba, magana likitan yake yi masa amma shi hankalin sa ya kan kofa, yana ta kallon hanya yana jin kamar ya bi bayan Adam din dan ya tabbatar ta samu su Fatima ya mayar da su gida lafiya lau. Amma kuma baya sin ya tafi ya bar gawar Hussain tare da mutanen da bai yarda dasu ba duk kuwa da cewa yanzu police sun zo asibitin kuma su zadu raka gawar Hussain har Kaduna. Sama sama yake jin abinda suke cewa, aka miko masa takarda yayi signing duk da bai san signing din me yayi ba but yasan ba zai wuce ta sallamar su ba. Sannan aka dora Hussain akan gado mai taya aka turo shi zuwa waje, inda by now mutane sun fara tsatstsayawa a waje suna kallo, wasu da wayoyi a hannunsu suna daukan hoto, Hassan ya kara tabbatar da cewa duk jikin Hussain a rufe yake babu abinda ake gani sannan ya sa aka kawo bakin ambulance din dai dai kofa yadda suna fitowa kawai shiga ciki sukayi shi da police guda biyu da kuma maaikacin lafiya guda daya, sannan aka rufe kofa. Daya police din kuma ya zauna a gaba tare da driver suka dauki hanyar kaduna.
Hassan yana zaune kawai hannunsa daya a dafe da gawar Hussain ya zubawa farin matafin da aka rufe shi dashi ido amma ba zai ce ga abinda yake tunani ba, tabbas kukan da yayi dazu a jikin Adam yaji dadin yinsa dan yaji nauyin da yake ji a kirjinsa ya ragu sosai amma duk da haka tunanin sa bai dawo dai dai ba. Suna kokarin barin gari ne wayar Hussain da take hannunsa tayi kara, ya duba yaga sunan Adam. Gaban sa ya fadi sai ya dauka da sauri "Hello, hello" amma baya jin magana clearly sai dai yan maganganu a can nesa, a cikin maganganun akwai muryar adam din amma baya fahimtar me suke cewa amma kamar shi da wani namiji suke magana. Ya katse kiran sannan ya sake kira amma har ta gama ringing ba'a daga ba, ya sake kira shima shiru. Sai ya kuma jin hankalin sa ya kara tashi. Ya dan daga labulen da aka rufe tagar motar yana lekawa yana jin a ransa yana so yake kallon hanya. Amma kuma babu abinda yake gani din.
Ya sake gwada number din Adam amma ba'a dauka ba still, ya kira wayar Ruqayyah bata shiga sai ya nemo number din Fatima ya kira itama not reachable, ya sake gwadawa sai taji ta shiga kuma lokaci daya aka daga "Hello" yaji muryar Ruqayyah, da alamar tashin hankali a tare da ita, yace "Hassana ina kuke ne ya akayi har yanzu baku je gida ba?" Cikin dimauta yaji tana magana da sauri "Hassan mun shiga uku, kuzo ku taimaka min, accident muka yi, duk sun mutu, duk sun mutu Hassan na shiga uku".
Ya girgiza kansa da sauri sannan ya kalli wayar hannun sa yana so ya tabbatar daga ita ne maganar take fitowa, ganin seconds suna reading ya tabbatar masa da tabbas daga ciki ne kuma abinda ya ji gaskiya ne dan ta muryar Ruqayyah kadai yasan babu maganar masa a cikin bayanin ta. Sunyi accident, duk sun mutu saura ita kadai, su waye duk din? Fatimah? Abinda yake cikin Fatima? Dan Hussain? Is only link to Hussain? Ji yayi wayar ta zame daga hannunsa ta fadi a kasan motar. Kwakwalwar sa ta tsaya chak sannan kuma a hankali jikinsa ya zame daga kan kejerar ya fadi kasa.
Mutanen cikin motar ne suka fara salati, ma'aikatan lafiyar yayi sauri ya kai hannun sa wuyan Hassan yana feeling heart beat dinsa kuma ya tabbatar da akwai sannan ya fara bashi taimakon gaggawa yayinda daya daga cikin police din ya dauki wayar wadda suka tabbatar ta cikin ta aka gaya masa abind ya sumar dashi ya kara a kunnensa "hello" Ruqayyah tace "hello waye? ina Hassan?" Yace "wacece? Hassan gashi muna tare dashi, wacece ke?"
Duk da Ruqayyah taji wani iri kuma taji a jikinta wani abu ya faru da Hassan amma itama a yanzu taimakon take bukata ido rufe, tace "sunana Ruqayyah, ni ce matar Hassan Aminu Abdullahi. Ina cikin daji munyi accident tare da gimbiya Fatima matar Hussain Aminu Abdullahi da kuma drivern mu, motar mu ta kama da wuta, Allah yayi musu rasuwa, ni kadai na rage yanzu. Ina neman taimako dan bansan a inda nake ba" san sandan ya juya yana kallon yanuwan sa, sai kuma ya kalli gawar Hussain yana jinjina hikima ta ubangiji daya dauki ran mata da miji a lokaci daya ba tare d kowannen su yasan da mutuwar dan uwansa ba. Tabbas wannan labari ne da zai iya saka Hassan yayi abinda yafi suma ma ba suma ba, briefly ya fada wa sauran abinda matar tace, sai wani a cikin su ya karbi wayar yayi setting dinta ta yadda zasu ke tracking wayar hannun Ruqayyah suka ga inda take sannan suka sanar mata da cewa gasu nan zuwa, sai kuma suka yi waya station aka turo musu da wata motar suka hadu a hanya suka rabu biyu wadansu suka tafi gurin Ruqayyah wadansu kuma suka wuce da gawar Hussain da kuma unconscious Hassan.
Ruqayyah kam tsoro take ji, ta bar gurin motar tayi hanyar da zata mayar da ita kan titi dan ji take kamar gawawwakin da suke cikin mota suna miko hannu zasu jata zuwa cikin sauran wutar da bata karasa mutuwa ba. Sannan kuma tana jin tamkar Fatima tana binta a baya, tamkar nemanta da tayi ra rasa ta zama fatalwa ne zata galaka ta saboda yar mata da yaron ta da tayi. A idonta take ganin kamar wulkawar Fatima ta gefenta, in kuma ta rufe idon ko da da niyyar kifta shi ne sai taga idanun Minal suna kallonta kamar yadda ta ganta a cikin mota a mace. Ga kafa ta rike, sam taki lankwasuwa sai janta takeyi ta sandare kamar wani ita ce. Duk kuma wannan da sauki akan abinda take ji a zuciyarta, wani irin feeling wanda ba zata iya misalta shi ba.
Ta fara tuno masoyan ta, ƴaƴan ta guda uku, Sumayya, inna Ade da Baba, suleiman da Zunnur dan duk abinda take yi, duk wannan fadi tashin da take yi da wannan dakakkiyar zuciyar tata amma ita kanta ta san tana son su sosai sai dai kawai ita bata iya nuna soyayya ba, ga kuma Hassan , da kin ta da sonta he have come to be part of her, ba zata ce tana masa so na soyayya ba amma ta damu dashi. Ta runtse idonta tana matse hawayen daya taru a idonta yake disashe mata ganin ta amma kuma hoton fuskar Minal data gani shi ya saka ta yi saurin bude idon tana kokarin kara sauri ama kafa taki bada hadin kai. Gani take kamar gawawwakin ne suka rike mata kafar. A kunnuwan ta har ji taje yi kamar ana maganganu kasa kasa. Sai kuma taji kukan jaririn data ajiye yana amsa kuwwa a kunnuwan ta.
Kuka take yi sosai, tana kokarin yin sauri iyakacin iyawarta amma in ta waiga sai taga babu inda taje, still bata wani yi nisa da motar ba. Sai data kwashe lokacin da a gurinta kamar ya kai tsahon shekara guda sannan taji gunjin mota tana shigowa gurin, sai kuma taji hayaniyar mutane sannan taga an haske ta da fitila. Hasken da ta ji shi har cikin zuciyarta, ta sauke ajjiyar zuciya tana tunanin karshen wahalar ta yazo. But that is just the beginning.
Tana ji suka karaso inda take suka kamata suka sakata a motar da suka zo da ita sannan wasu suka tafi gurin accident din suna kokarin karasa kashe sauran wutar da take ci, tana jin su suna ta yawa suna fadar abinda ta gani, sun dan fara yi mata tambaya amma ganin yadda take a rikice yasa wani wanda take tunanin shine babban su yace su rabu da ita kawai, a lokacin wata motar ta karaso kamar ta fite service da kuma wata karamar mota again, taji suna ta maganar abin taji kuma sun ambaci mutuwar Hussain, sun kuma fahimci abinda take so su fahimta na cewa Fatima matar Hussain ce a cikin motar, sun kuma fahimci wacece Fatima dan take taji wani yana waya Kano cewa a sanar da gidan sarautar kano sunyi rashin yarsu, gimbiya Fatima.
Ta lumshe idonta tana jingina da jikin kujerar motar, the dead is now complete, ta haka ta binne sirrinta babu gudu babu ja da baya, amma kuma ina Fatima take? In kuma bata mutu ba fa? In kuma tashi tayi ta tafi fa? In kuma yanzu already tana hanyar Kaduna kuma fa? In ta fada tace ta haihu ta bawa Ruqayyah dan ya zata yi kenan? Me zata ce?
Ta girgiza kanta da sauri tana cewa "uhm uhm" a fili kamar wata zararriya. It is going to be her words against fatima's. Zata musa ne da duk iyakacin iyawarta tace ita bata karbi da ba, tace Fatima sharri take yi mata. To amma kuma in aka tambayeta game da gawar da take cikin mota wadda ta riga ta furta cewa ta Fatima ce fa? Me zata ce akan hakan? Tabbas bata haƙa ta binne sirrinta ba, tabbas yana nan a bude kuma yana tare da Fatima a duk inda take. But What if ta mutu da gaske wani ne ya dauke gawarta, ko matsafa, ko naman daji? There is still hope for her amma bata da tabbas, kuma tasan wannan rashin tabbas din tabbas zai ke hana ta bacci. A koda yaushe, Fatima zata iya bayyana kuma bayyanar ta yana nufin bankaduwar sirrinta.
Wannan kuma yana nufin rasa komai nata.........
Including iyayenta, dan tasan direct Baba zai tsine mata inna Ade kuma tace babu ita babu ita har abada
But for now, shin gawar Minal tayi konewar da ba za'a Iya gane ta ba? Ta tambayi kanta tana lekawa ta taga, kamar amsar tanbayarta taji wani a gurin yana cewa. "Ayi wa yanuwansu waya, sai dai a binne su anan dan ba zasu dauku ba, sun zama gawayi" ta lumshe idonta da niyyar yin ajjiyar zuciya amma fuskar Minal data gani ya saka ta bude idon da sauri.
Motar da take ciki aka bawa umarnin ta tafi, a kaita Kaduna gidan mijinta, wannan yasa taji hankalin ta ya kwanta, sai dai suna barin gurin ta juya tana kallon gurin. A nan ne rayuwarta ta kare, anan ne kuma rayuwarta ta fara. Su Kusan rai shida suka bar Kaduna a mota, amma a cikin su ita kadai zata koma garin Kaduna.
***************. **********. **********
Da taimakon maaikacin lafiyar da yake cikin ambulance din Hassan ya fara dawowa hayyacin sa, amma sai dai shi har cikin zuciyarsa bai so dawowar tasa ba, so yake ya tafi shima, so yake yabi Hussain, baya so ya cigaba da rayuwa. Wannan wacce irin jarabawa ce uban giji yake yi masa?
Ya kamo hannun Hussain ya rike "Hussain! Ka tafi dani nima mana! Hussain Fatima ta bika ka roka min ubangiji nima ya dauke ni in biku! Hussain Fatima ta tafi , ta taho tare da abinda yake cikin ta. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" duk rarrashin duniya babu wanda ba'a yi masa ba amma ya kasa yin shiru. So yake wai maybe in ya ishe su da magana su gaya masa cewa ba gaskiya bane ba, su gaya masa Fatima da abinda yake cikinta suna raye, su gaya masa Ruqayyah ba gaskiya ta fada ba ko kuma anje an tarar basu mutu ba but instead of su ce haka sai yaji suna waya da yanuwansu na can akan a gaya masa gawar Fatima ba zata dauku ba sai dai a binne ta a can.
Girgiza kansa kawai yake yi, so yake yayi kukan amma ya kasa sai magana kawai yake yi da gawar Hussain kamar wani tababbe. Tabbas mutuwar Hussain ta taba shi amma bata yi masa dukan da wannan ta Fatima tayi masa ba. Saboda dama yasan Hussain bashi da lafiya, kuma a hannun sa ya mutu. Amma Fatima fa? Hussain yana mutuwa ba abinda yake so sama da abinda yake cikin Fatima amma ashe ko ganin sa ba zai yi ba, ashe ko numfashi ba zai shaka ba. Wannan wacce irin jarabawa ce? Anya zai iya ci kuwa? Ace a rana daya babu Hussain babu family dinsa? Babu komai sai memory dinsa?
Memory mai dadi.......
Memory mai zafi.......
Memory mai tsayawa a zuciya......
Yana jin wayar Hussain tanata ringing amma ya kasa kallon ta ma ballantana yayi tunanin dauka. Ba zai wuce mutanen gidan su ba, ba zai wuce aunty ko yan uwansu ba, sun kira shi suji da gaske ne? Da gaske Hussain dinsu ya tafi ya barsu? Da gaske Fatima tare da babyn su sun bi shi inda ba'a dawowa?
Ba zai iya amsa musu ba.....
Ba zai iya kallon wayar ba.....
Ba zai iya kallon hoton Fatima hannayenta a dafe akan cikin ta tayi shape din heart da yatsunta a kan cikin ba, wanda shine hoton da yake kan wayar.
Sai ya saka hannu ya kife wayar, baya jin zai iya magana da kowa.
Ya tuno da nasihar da Adam yayi masa dazu "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya fara fada yana maimaita wa hannunsa biyu rike dana Hussain "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" sauran mutanen motar suka cigaba da taya shi har suka iso Kaduna suka je gida.
********. *********** *****
Tun tafiyar su Hussain Aunty take zarya a falo, in ta hau sama sai ta sauko sai ta kuma komawa sama ta kwanta sai ta tashi ta dawo kasa ta zauna. Ta rasa me yake yi mata dadi. Su Zulaihat suna kallo a palo ta kora su daki ta kashe kallon, ji tayi bata son karar tvn, bata son karar komai.
Ta jima a nan sai kuma ta koma sama ta saka hijab dinta ta fita da niyyar shiga part din Hussain ta duba gimbiya Fatima, dama tunda cikinta ya girma kullum sai taje ta dubata. Sai dai a compound din gidan ta hadu da maigadi wanda yayi mata bayanin cewa ai Fatima bata nan yaji Lawan driver yace tace zai kaita Abuja "tare suka tafi da Aunty Ruqayyah"
Wannan yasa a take ta dauko wayarta ta kira Hussain dan taji dalilin da zaisa ya bar Fatima ta bi bayansa da tsohon ciki. Sai dai Hussain din bai dauka ba sai Hassan, ta gaya masa abinda ake ciki sannan ta koma gida ta cigaba da zaman jiran dawowarsu.
Har magrib tayi, sai ta kuma dauko waya ta kira Hassan amma bai dauka ba, ta kira Fatima not reachable Ruqayyah switched off. Ta kira Hussain shima ba'a dauka ba. Hankalin ta yayi dubu ya tashi, ta shiga dakin Khadijah ta tarar da ita a kwance wai zazzaɓi takeyi, ta dafa jikin ta taji zafi sosai, sai ta koma dakinta ta dauko mata magani ta taho da niyyar zata bata sai taga kira daga Bauchi. Babban yayan su Alhaji Lukman, tayi gyaran murya ta dauka tana gaishe shi, sai taji yayi shiru kafin ya amsa sannan yace mata "duk kuna gida tare da yara?" Tace "eh" tana mamakin tambayarsa, sai yace "shikenan ku zauna a gidan gamu nan tahowa komai dare insha Allah" sai ya kashe wayar ya barta da sakakken baki. Me zai zo yayi komai dare? Koma menene a barwa gobe