Showing 108001 words to 111000 words out of 300844 words

Chapter 37 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2070

hada dana farkon ta rungume a jikinta tana jin hawayen dadi yana taruwa a idonta, ganin jariran sai ya tuna mata da ranar da aka haifi Hassan da Hussain, sai ta tuno da yar uwarta, take taji son yaran ya shiga ranta kamar yadda taji tana son Hassan da Hussain lokacin da aka haife su. Ta juya tana kallon Ruqayyah wadda take ta mazar kwalla ana yi mata dinki, tabbas ta jinjina wa kokarin yarinyar yadda ta haifi yan biyu da kanta duk da karancin shekarun ta. Sai dai fa tabbas ita kanta auntyn ta san ta sha wahala ba kadan ba. Duk da azabar da take sha amma bai hana ta tambayar Aunty ba "aunty me na haifa?" Aunty ta shafa kanta tana murmushi tace "duk maza ne Ruqayyah"

Ruqayyah ta sauke ajjiyar zuciya, deep down tana jin dadi saboda hakan yana nufin sauran maganar mai duban nan itama gaskiya ce, zata yi kudi fiye da wanda take saka rai. And she just can't wait. Ko ma menene option din tasan zata yi decision mai kyau wanda zai amfane ta ya amfani ahlinta baki daya, ya amfani twins dinta.

Ta fita da yaran a hannunta zuwa waiting room inda Hassan yake ta faman safa da marwa dan kunyar Aunty ce kawai ta hana shi shiga ayi labor din tare dashi. Yana ganin ta da yaran ya tafi gurin ta da sauri yana mika hannu sai kuma ya janye hannun yana murmushi, tayi dariya "karbi abinka, ai kayi kokari, da wancan marar kunyar ne da har ciki zai bini yace in fito in basu guri" yayi murmushi yana mika hannayensa duk biyun ita kuma ta saka masa yaran a kowanne side, ba zai iya misalta farin cikin da zuciyarsa take ciki a lokacin ba, ba zai iya misalta soyayyar yaran da yaji a cikin zuciyarsa ba tun daya dora idanuwan sa akan su. Sumayya ta leko da kanta ta gefensa tana kallon babies din tana murmushi, hannunta yana yi mata kaikayi tana so ta dauke su, ta miko hannu amma sai ya maze yayi kamar bai ganta ba. Dole ta hakura ta cigaba da leken su ta gefensa. Ya dago kai yana kallonta yace "suna da kyau ko?" Ta gyada kai da sauri tace "suna da kyau sosai ma. Kama suke yi da kai" ya girgiza kansa yace "no, da Hussain suke kama" tayi dariya, "da Hussain da kai ai duk kamar ku daya" shima sai yayi dariya yace "da yana nan da kunyi fada yanzu, zai ce ya fini kyau ai" ita ma tayi dariya tana shafa hannun daya daga cikin babies din, sai kuma ya bata daya ya zauna da dayan a hannunsa yana yi masa kiran sallah a kunnuwan sa. Ya gama ya miko mata shi ya karbi na hannun nata shima yayi masa.

A lokacin ne aka turo Ruqayyah daga labor room zuwa dakin hutu, idanunta a rufe aka wuce da ita, sai kuma duk hankulan su ya koma kanta suka bita a baya sai Aunty ta dakatar dasu tace "anyi mata allurar bacci ne saboda ta huta sosai, kar ku shiga kuma ku dame ta" Hassan ya dan shafa kansa yana kara leka inda aka shiga da ita sai aunty ta karbi babyn hannunsa tace "shiga ka ganta, kar ka tashe ta amma ka barta ta hutawar ta Please, yarinyar nan ta sha wahala wallahi" ba musu ya mika mata shi da sauri ya shiga ya rufo kofa su kuma suka zauna a kujerun gurin Sumayya tana shafawa babies din dabinon data tauna suna ta lashewa tana dariya, sai kuma ta dan basu zam zam kadan, Aunty kuma ta dauko waya ta fara kiran yin albishir, Inna Ade ta fara kira ta gayawa, daga inda Sumayya take zaune tana jiyo muryar Inna tana hamdala sai tayi murmushi, Allah sarki uwa. Ko dazu da rana sai data kirawo su ta tambayi lafiyar Ruqayyah. Daga nan kuma sai Aunty ta kira Hussain, bata sami wayarsa ba sai ta kira ta Fatima ta gaya mata tace ta gaya masa. Ita ma tayi ta murna kamar ita aka ce ta haihu, sauran kuma Aunty tace sai gari ya waye tukunna tunda yanzu dare ne. Sumayya kuwa bata bari sai gari ya waye ba tuni ta dauki hoton babies din ta saka a social media. A lokacin nurses suka zo suka karbe su aka tafi dasu aka yi musu duk gwaje gwajen da za'a yi musu sannan aka yi musu wanka aka shirya su cikin kayan da aka taho dasu daga gida.

Hassan yana shiga dakin ya ja kujera kusa da Ruqayyah ta zauna ya zuba mata ido, da ace zai iya hadiye ta dan kauna to kuwa da tabbas ya hadiye tan, ya rike hannunta a cikin nasa, yayi kissing hannun, still yaji hakan bai yi masa ba sai ya sunkuya yayi kissing goshinta, ta dan bude ido kadan tana kallonsa dusu dusu sai yayi mata murmushi yace "sannu Hassana. Allah ya baki lafiya kinji" cikin magagin bacci tace "bana so" yace "menene ba kya so? Gaya min menene ba kya so?" Tace "suna Hassana, bana so" sai ta koma baccin ta. Yayi shiru yana kallonta ammaya kasa judging komai a cikin maganar ta, maybe abinda yake ranta kenan, maybe kuma magagin allura ne.

Bata tashi ba sai da gari ya waye, har Inna da Baba dasu Sulaiman sunzo, yammatan Aunty ma kaf dinsu sun zo kowa yana ta daukan babies ana yabawa. Hassan kuwa baki har kunne ya kasa boye farin cikin sa. Ganin ta farka yasa hankalinsu ya dawo kanta suka yi ta mata sannu tana amsawa sai dai ko yaya ta motsa sai taji gurin dinkin da aka yi mata yana damunta, ganin bata da wani problem ya saka Aunty ta nemo musu sallama kuma a take aka sallame ta suka dawo gida.

Part din aunty suka sauka, anan Aunty ta hada ruwa mai dumi da isasshen detol ta saka ta shiga ciki, "ba za'a saka miki ruwa mai zafi sosai ba saboda dinkin zai iya budewa, zafin ruwan yana iya lalata zaren da akayi dinkin dashi" sannan kuma ta gasa mata jikinta sosai da towel tana fitowa kuma aka kawo mata tuwon kanwa miyar kukar da Inna Ade ta tashi tun asuba ta tuka mata shi ta taho mata dashi, sannan kuma aka kawo mata dahuwar nama mai romon da Aunty tayi mata, sai ta zauna ta ci naman tuwon kuma taki ci.

Tana cikin ci Sumayya ta shigo da babies din ta kwantar dasu akan gado tana cewa "ni fa Ruqayyah banga kin dauki yaran nan ba, ya kamata ki dauke su suji dumin jikin ki suji dadi suma" Ruqayyah ta harari inda babies din suke tace "bayan sun gama bani wahalar? Ai dole duk dan da bai bi uwarsa ba ya hadu da bala'i" Sumayya tace "am glad kin fara fahimtar haka" Ruqayyah ta daga kafada tace "me kuma nayi?" Sumayya ta nuna mata tuwon Inna Ade tace "baki ci tuwo ba, dan ke ta zauna ta tuka shi sannan tayo dakonsa tun daga gida har asibiti har nan gidan amma still baki ci ba" Ruqayyah ta tura baki "ni baki na babu taste ai, ya za'a yi mutum ya haihu a kawo masa wannan bakin tuwon fisabilillahi" Sumayya ta jawo robar yajin daddawan da Inna ta taho dashi tace "saboda tasan bakin ki babu taste shi yasa ta hado miki da yaji dan ki zuba kiji taste din, ga kuma man shanu ta kullo a leda duk dan saboda tasan halinki kar ki ƙi ci. Ki tuna, irin wannan wahalar da kika sha irinta itama ta sha lokacin da zata kawo mu duniya" Ruqayyah ta sake hararar yaran da suka fara mutsu mutsu tace "irin wancan harbe harben fa suke min a cikina, duk sunbi sun duba min fatar ciki na" Sumayya tayi dariya tana zuba mata tuwon tace "kin san fa naji ance tuwon kanwa yana taimakawa wajen samar da ruwan nono ga mai jego, ki samu ki ci ko suma sa samu abinda zasu saka a cikin su" Ruqayyah tace "chafdi, ai kuwa dai babansu dole ya bude bakin aljihu ya siyo madara dan bazan iya shayar da su duk su biyun ba wallahi. Sai an siyo madara an hada musu da ita" Sumayya tace "wannan kuma tsakanin ku ne, ni dai abinda nake so shine ki ci tuwon nan sai ki dauki yaran nan ki basu nono su sha. Kim san kuwa cewa wannan ruwan nonon na farko yellow marar kauri yafi komai amfani a gurin jariri? A cikin sa anti bodies suke, suna sha shi zai zama kariya gare su daga dukkan wani abu da zasu saka a bakinsu nan gaba. Dan haka ko ma ba zaki basu nonon ba kwata kwata ki daure ki basu na farkon su sha"

Da kyar da lallabawa Ruqayyah ta dan ci tuwon Inna kadan, sannan Sumayya ta dauko mata Hassan dinta tace "wannan shine babba, a fara bashi tunda ya riga dayan zuwa duniya" Ruqayyah takarbe shi tana kallon sa fuskarta da murmushi "da babansa yake kama" ta fada tana lakuce masa hanci" saura kuma kayo halin babanka" Sumayya ta zauna kusa da ita hannunta rike da dayan tana kallon yadda Hassan din yake ta kokarin kama abincin sa, tace "mene halin baban nasa? Kirki?" Ruqayyah ta harare ta "so kike yi inyi magana ki fara yi min wa'azi, kin san halin nasa ai"

Sumayya tace "hmmm Ruqayyah kenan. Ruqayyah ki gode wa ubangijin ki. Babu abinda bai yi miki ba a rayuwa. Kin san kuwa akwai matan da babu abinda ba zasu yi ba dan su samu miji irin Hassan? Amma ke kina korafi? Ubangiji bayan ya yi ki mutum mai daraja a cikin halittun sa sai yayi ki musulma wadda aka haifa a gidan ilimi, sai kuma ya baki lafiya, hankali, ya baki iyaye da mu yan uwa masu tsananin sonki, sai kuma ya dauki miji one in a million ya baki, miji kuma mai tsananin sonki sannan yanzu kuma ya baki haihuwa, da kika tashi haifa bai baki daya ba sai ya baki biyu, biyun ma sai ya baki su duk maza, zaman da shi da kansa yace sune zugabanni akan mata. Ko gaya min, which among the favors of your God do you deny?"

Ruqayyah ta saki baki tace "ni yanzu da kike min wannan lissafin me kika ji nace ne?" Sumayya tace "baki ce komai ba, na fada ne dai tun kafin ki ce din" ta mike tana ajiye haririn hannunta sannan ta tattara kayan abincin ta fita dasu.

Da kyar Inna Ade ta lallaba Aunty ta bar ta ta tafi da Ruqayyah gida wankan jego, sai dai ita Ruqayyan ce gaba ki daya ba haka taso ba ita so tayi a barta tayi zamanta a gidanta, ta fara mita "to yanzu in na tafi can Inna kuma wadanda zasu zo min barka kamar sababbin kawayena da matan abokan sa ya zasu yi kenan?" Inna Ade tace "shi ai yasan gidan, sai yayi musu kwatance su je, ke ma kuma sai kiyi wa kawayen naki. Ba kuna waya ba?" Ta kara bata rai "Ni yanzu can din ne Inna ban san inda zanke ajiye baki ba, kuma dakin Sumayya yayi mana kadan ni da yaran da ita, kuma....."

Inna tace "Sumayya sai ta dawo dakina ke kuma ki zauna a nata, in yaso in yaran sun tashi kukan dare ke sai kiyi ta rarrashin su ke kadai. Ke da ba a miki abin arziki har zaki nuna ke ba kya son zuwa gida wanka. To kuma da a wancan daya gidan muke kuma fa? Da ya zaki yi? Dolen ki dai can din shine tushen ki shine tutiyarki, nan gidan mijin ki ne ba gidan ki bane ba* Ruqayyah tayi shiru a ranta tana jero istigfari dan bama zata iya imagining komawa wancan gidan ba. A ina zata kwanta?

Ita kuwa inna a ranta taji zafin abinda Ruqayyah tayi, godiyar ta ga Allah da babu kowa a gurin sai su kadai dan da ta basu kunya a cikin dangin mijin ta. Wannan kuma shi yasa Baba ya dage sai ta taho da ita "in dai har mijinta ya bari ki taho da ita gida tayi wankan ta anan, ayi taron suna anan, dan a tuna mata cewa nan ne gidan su ba can ba".

Sosai Ruqayyah take samun kulawa, ko juyi tayi Sumayya ko Inna zasu tambayeta abind take so. Ita kuma sai iko take zubawa da iyayi son ranta. Duk baya kwana biyu kuwa sai Aunty tazo ta ganta sannan kullum sai tayi abinci ta turo wata a cikin yayanta takawo mata. Hassan sau biyu yake zuwa, safe da yamma, kuma bashi da shamaki da har dakin yake shiga gurin matarsa da yayansa. Kullum kuma yazo sai tayi masa mita, "jiya sauro ya ciji Hassan" "yau Hussain ya kasa bacci da safe sabida hayaniyar mutane" ita dai kawai so take yace tazo su koma gida shi kuma ya toshe kunnuwan sa yayi mata kamar bai san me take yi ba saboda duk da cewa shima yana son su zauna tare amma ba zai iya taka maganar Baba ba..

Ranar suna ta zagayo aka sakawa yaran sunan mahaifin su Hassan "Aminullah" da kuma sunan Baba "Yusuf" ko wanne kuma aka bar masa sunan sa ba'a boye musu ba.

Ruqayyah an sha hidima, a shiga wadannan kayan a fita wadannan, kawayenta suna kara zuga ta na kara kumbura kai duk dama dai ba haka taso ba, taso ayi a gidan ta ne ko gidan aunty tunda sunfi girma da kaya masu tsada. A ranar sunan ne kuma Hussain da Fatima suka zo, ba a ranar ya shirya zasu dawo ba sai dai yadda Fatima ta matsa tana son ganin babies din ya saka a dole yayi squeezing ya gama abinda yake da wuri suka taho, duk kuwa da cewa taga babies din a waya. Suna sauka direct gidan sunan suka taho, suna zuwa gaba ki daya idanuwa suka koma kansu, yan tsegumi suka fara, Hussain har cikin palo ya shiga duk da mutanen da suke ciki ya dauki babies din aka yi musu hotuna sannan yayi wa mutanen gurin ruwan kudi ya tafi, tafima kuma ya barta a gidan.

A take maganganu suka fara wayo "wannan waye haka?"
"Ai shine mai kamfanin nan na H and H"
"au ba mijin Ruqayyah bane ba dama mai H and H din ba?"
"Aa, wannan ne, mijin Ruqayyah dan uwansa ne"
"kun ga matarsa kuwa?"
"Ai Yar yar sarkin kano ce"
maganganu dai iri iri, a take marokan da Ruqayyah ta saka aka dauko mata hayar su dan suzo su koda ta a gaya wa mutane wanne irin suna akeyi sai suka juya kan Fatima suna yi mata kirari, ita kuma ta bude bakin jaka tayi ta musu barin kudi. Wannan ya saka Ruqayyah ta zare jikinta ta koma daki ta cire gwagwgwaron ta yi kwanciyar ta, sai ga Fatima ta shigo dakin ta tsaya tana kallonta tace "lafiya Ruqayyah kika kwanta ana tsakiyar taron sunan ki?" Ruqayyah ta juyo tana kallon ta tana yamutsa fuska tace "wallahi stitches din nan ne suke min ciwo, sun takura min. Kin san azabar zafi ne dasu. Ko da yake ashe fa ke baki sani ba ko?" Ta juya ta cigaba da kwanciyar ta.

Bayan Fatima ta koma gida tun da ta shiga babu labarin da take yi irin na taron sunan Ruqayyah. "Ruqayyah tayi kyau, twins din nan sunyi kyau sosai, sooo cute. Kamar in sako su a jaka ta in taho dasu in kawo mana su gida" Hussain yayi dariya "kar ki damu, in duka dawo gida zamu ke dauko su suna yi mana wuni anan" ya sunkuyar da kansa yace "kafin mu samu namu muma" sai tayi shiru tana breaking knuckles dinta, ya tsaya yana kallonta dan yasan wata magana take son fada, sai tace "Mi Amour, nace ko zamu fara zuwa asibiti ne?" Ya girgiza kansa da sauri yana rike hannunta yace "ko wata goma fa ba'a yi ba da bikin mu, let's not be inpatient please, mu jira ikon ubangiji kinji Princess. Our time will surely come kinji?" Ta gyada kai a hankali, ya jawo ta jikinta yace "nima ina so Fatima, ina son naga jinina a duniya ko ba biyu ba ko daya, ko mace ko namiji, ina so nima. But nasan cewa what ever will be will be".

Ta kwantar da kanta a kirjinsa tana sauraron bugun zuciyarsa, sun jima a haka sai wayar sa ta fara ruri ya dauko ta ya daga kiran ya saka a kunne. "Manya manya maganin kanana kanana. Ya akayi? Ya garin? Nayi fushi ai in dai har ka kuma barin kasar nan ba ka zo kaga gidana ba to nasan matsayi na" ya danyi shiru sannan yace "ai na gaya maka tun ranar nan da muka yi Magana, in har baka gwada ba babu ta yadda zaka yi ka tabbatar cewa zasu baka auren yarinyar nan ko kuma ba zasu baka ba? Fargaba fa asarar namiji ce" yayi dariya "ka sami takawan kawai ka gaya masa halin da ake ciki, shi zai tura a nemar maka auren ta" "oh haka yace? To shawara ta rage naka kuma, amma ni dai personally bana giving up without trying, ka shirya kaje Riyad din da kanka ka nemi auren yarinyar nan in an baka you come and thank me in ba'a baka ba kuma to kar kace ni na baka shawara" yayi dariya, "gata nan a kirjina. Kai dai tsaya wasa sai da kaga munayi" ya cire wayar daga kunnensa yana dariya, ya juya yana kallon Fatima "mutumin ki dai ya kusa zuwa karshen katanga. Babansa ya ki zuwa nema masa auren balarabiyar nan" ta gyara kwanciyar ta a kirjinsa tace "shine kai kuma kake zuga shi ya tafi shi kadai ko? Ba zasu bashi ita ba ko me zaiyi. Am sure" yayi ajjiyar zuciya yace "I know. But there is no harm in trying, right?"

A daddafe Ruqayyah tayi sati uku a gidan su, sai kawai ta shirya plan ta gaya wa Inna Ade cewa Hassan yace ta shirya zai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login