Showing 39001 words to 42000 words out of 300844 words

Chapter 14 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2042

yace "Baba, yanzu misali in aka samu wani kasuwanci haka aka baka, zaka iya hakura da aikin nan?" Baba yace "to Hassan, ni dai ban taba yin kasuwanci ba, ni abinda na sani shine aikin karfi shi nake yi nake ciyar da iyali na har yanzu. Dan haka ba lallai ne in na fara kasuwancin ya dore ba tunda ban san kan abun ba, aikin dai shine, nasan abinda kake tunani kuma ina so ka cire komai daga zuciyarka ka gwada ni idan naci ka bani, wannan shine taimako mafi girman da zaka yi min".

Hassan yayi ajjiyar zuciya yace "Baba ba zan so in ke ganin ka kana wahala ba, nafi so inke ganin ka kana hutawarka" Baba yace "amma zaka ji dadi in ka ganni ina neman halak dina ko? Hutu kuma ai da saura na tunda da karfi na ba wai shekaru na ne suka ja ba, in lokacin hutawar yayi zan huta ne".

Haka suka yi ta ja in ja, a karshe dai a dole Hassan ya buga offer ya bawa Baba ya sallame shi saboda wadanda suke kan layi suna jira. Amma a ransa ya kudurce abinda ya kamata yayi akan lamarin.

Baba yana zuwa gida da murnar sa ya fara bawa iyalinsa labari "alhamdulillah, aiki ya samu, aikin gadin nan dai da nake ta buri gashi nan Allah ya kawo shi" ya bude takardar yana nuna musu ita upside down. Inna ta karba tana dubawa duk da ba gane wa take yi ba fuskarta lullube da farin ciki. "Masha Allah baban biyu, Allahu ya sa albarka a ciki, Allah yasa ka fara a Sa'a. Amma na dauka ba yanzu za'a baku ba sai an gama tantancewa" ya zauna yana cewa "haka ya kamata, amma yaron nan Hassan kinsan shine mai abin, a take ya buga min takarda a matsayin mai gadi ya bani".

Ruqayyah data fito daga toilet da buta a hannunta ta saki butar "mai gadi?" Ta fada, fuskarta tana nuna bacin ranta "wanne irin maigadi kuma? Yanzu Hassan din ne da kansa ya baka aikin maigadi a kamfanin sa? Wannan ai cin fuska ne"

Inna Ade tace "haba Ruqayyah, in ba'a gode masa ba ai kuwa ba za'a zage shi ba. Aikin gadin bashi baban naku yake nema ba? Ba dan shi ba kuma aikin gadin ma zai iya rasawa ya koma ya cigaba da leburanci da dako" cikin bacin rai Ruqayyah tace "amma wannan lokacin ai ya wuce, wannan sabuwar rayuwa ce, a matsayin sa na wanda zai zama surikinsa ba kamata yayi ya bashi babban office a kamfaninsa ba?" Baba ya fara fada "bana son diban albarka Hassana, da wanne takardun zai bani aikin office din? Me zanyi a office din? Shi cewa yayi ma in hakura da aikin ya bani jari inyi sana'a nace a'a, saboda ni bana son dogara da wani. In ba zaki yi murna da abinda Allah ya bamu ba ki wuce ki bani guri".

Bata kuma cewa komai ba ta wuce daki tana kunan zuci. Tabbas sai ta takawa Hassan burki, in dai yana sonta sai ya chanja wannan aikin, wannan ai ita zai zubarwa da kima a idon yan'uwansa da sauran jama'ar sa, shikenan kuma sai ace babanta shine mai gadin kamfanin mijinta? Ina! Ai sam ba zata sabu ba.

Da daddare dan halak din yazo zance.

Yaune zuwansa zance officially na farko. Yayi mata kwalliya sosai ya kuma gama shiryo kalaman da zai yi mata. Yayi packing sannan ya aika kiranta. Ita ma kuma a nata bangaren ta saka ran zai zo kuma ta shirya nata kalaman. Dan haka ana cewa ana sallama da ita ta saka hijab ta fesa daya daga cikin turaren da suke cikin kayan Hussain. A bakin kofar gidan ta tsaya ta gyara expression din fuskarta zuwa irin wanda tasan yana so, na yarinya mai kunya da nutsuwa

A jikin mota ta ganshi a tsaye ya rungume hannunsa. Farin yadi ne a jikinsa mai taushi wanda ya karbi kafar jikinsa sosai ya kuma fito da kyawun gyararriyar sumar kansa wadda ta sha gyara kuma take a bude. Bakin takalmi, bakin agogo da bakin tabarau, sai kuma kyakkyawan murmushi a fuskarsa. Zuciyarsa kuma cike da soyayyar hassanar sa.

Tayi masa murmushi itama. Sannan ta tako sannu a hankali tazo inda yake ta dan durkusa kadan ta gaishe shi. Ya amsa yana kara fadada murmushin sa. "Barka da fitowa uwar yayan Hassan" ta rufe fuska da hannunta. Yayi dariya yana karewa siraran dogayen yatsun hannunta kallo ya gyara tsayuwarsa yace "kinyi kyau sosai. Sai dai matsalar daya ce" ta bude fuskarta amma idanuwanta a kasa tace "wacce matsala kenan fa?" yace "wannan kunyar nake rokon alfarmar a rage ta ko yaya ne a bani dama inga cikin idanuwanki. Kullum su nake gani cikin baccina amma kuma a zahiri an hana mini ganin su" ta fara kokarin sake rufe fuskar ya hade hannayensa a guri daya yace "dan Allah, a tausayawa marayan Allah".

Tace "maraya?" Ya cire glass din idonsa Yace "eh. Baki sani bako?" Tace "Allah yaji kansa" yace "Allah yaji kansu zaki ce. Duk su biyun babu" tace "ohhh, ya Salam, na dauka ai....." Yace "Aunty? Ba ita ta haife mu ba, amma uwa ce a gare mu, haihuwar mu ne kawai baya yi ba".

Ko cikin abokan sa ba kowa ne yasan cewa ba Aunty ce ta haife su ba amma wannan ai Hassana ce, wannan aurenta zaiyi kuma aure akan gaskiya ake gina shi.

Tayi masa gaisuwa sai ya bata brief labarin asalinsu da kuma cikakkiyar dangantakar su da Aunty, ya kuma lissafa mata sunayen kannensa mata sannan ya gaya mata irin soyayyar da yake wa yan'uwansa.

Itama kuma sai ga bashi labarin nata asalin da sunayen nata family members din da stage din karatun kowanne. A lokacin ne ta ga time din shigar da maganar Baba yayi. Tace "ammm akan maganar Baba" sai ta dago kai kamar yadda tayi plan cewa zata saka idonta cikin nasa ta gaya masa ya chanja wa baban ta aiki. Amma the moment da suka hada ido sai komai nata ya ruguje, wannan mutumin ba wannan mutumin bane daya same ta a toilet yace mata "help me Please" wannan wani mutumin ne daban. Wannan is so strong and so sure of himself. Wannan mutumin will not be controlled, not by her, not by anyone.

Ta sauke idonta kasa tana jin komai yana rushe mata, plan dinta duk ya ruguje, yace "uhum, ina jinki, me zaki ce min a game da Baba?"cikin sanyin murya tace "cewa zanyi dama an gode madallah da aikin da ka bashi" yace "noo. Babu godiya ai a tsakanin mu. Baba ai babanane, tunda nawa baban ya mutu kinga ai yanzu na samu Baba ko?"

Ta kuma cewa "an kawo mana sako kuma, mungode" ya dan bata fuska yace "sako kuma? Tace "eh" a ranta tana tunanin bashi din bane ba kenan, sai ta kara da cewa "Hussain yazo jiya, da dare kuma sai ya aiko mana da wayoyi ni da Sumayya da kuma kaya"

Hassan yayi dariya yana bayyana farin cikin sa yace "ya kyauta sosai. Ko gaya min bai yi ba. Hussain yana da kirki sosai yana kuma da kyauta sosai. Kinga ya rigani, ina ta lissafin siyan wayar amma bana so inyi laifi a gurin Baba tunda ban sani ba ko ba ya son kuyi waya yanzu"

Ta harare shi ta gefe yadda ba zai gani ba sannan tace "ai kuwa yayi fadan, sai da kyar ya bari" yace "to Alhamdulillah tunda ya bari ɗin, yanzu an kunna ta kenan a bani number in samu ta rage dare? Kinsan abinka da gwauro" tace "bamu bude bama, sai mun siyo sim card" yace "gobe zan aiko, da sassafe ma kuwa"

Sun dan jima suna hira, ita kanta Ruqayyah tasan taji dadin hirar Hassan yadda yake komai a nitse, sai kuma yace "naga alamar akwai sauro, gwara in barki ki koma gida kar ya cizar min ke ko?" Da haka suka yi sallama ya raka ta bakin kofa ta shiga sannan ya juyo.

A lokacin ne wata taxi ta shigo layin, mai taxin ya dan wuce motar Hassan kadan sannan yayi packing. Ya fito a dai dai lokacin da Hassan yake kokarin bude kofar motar sa. Ya mika masa hannu, sai da Hassan ya kare masa kallo ya ganshi dan karamin saurayi da ba zai wuce ashirin zuwa ashirin da biyar ba, ya mika masa nasa hannun suka gaisasai ya nuna gidan su Ruqayyah yace "dan Allah nan ne gidan su wasu twins masu kama daya?" Hassan ya gyara tsayuwarsa yana studying saurayin yace "eh nan ne ya akayi?" Saurayin yace "Okay dama gidan nake nema shikenan na gode" Hassan ya kuma cewa "me yasa kake neman gidan su?" Saurayin yace "ohhh, dama muna haduwa ne dasu yawanci a school dinsu, to kwana biyu ban gansu ba shine nazo in duba su kuma mu gaisa" Hassan yace "really? Da wa zaka gaisa a cikin su?" Saurayin yace "Ruqayyah nasan ba zata kula ni bama, so.....da Sumayya zamu gaisa" Hassan yayi murmushi ya nuna masa kofar gidan yace "bismillah" sannan ya shiga motarsa ya bar unguwar zuciyarsa fara kal. Hassanar sa mai kamun kai ce ita, Hassanar sa mutuniyar kirki ce.

Wannan littafi na siyarwa ne, in kina son siya ki nemi wannan number din 08067081020

Episode Fifteen : The New Driver

Adam ya bi motar da kallo har ta kule, shi dai bai ga alamar wannan mutumin daga wannan gidan ya fito ba dan bai ma yi kama da unguwar ba ballantana gidan. Waye shi? Kwalliyar da yayi da kamshin da yake yafi kama dana wanda yazo zance, amma zance gurin wa? Ya kalli nashi kayan jikin, basu mutu ba amma kuma ba zasu tsaya a jere dana wanda ya bar gurin ba.

Ya dan tsafa kansa yana kallon gidan, shi bai taba zuwa zance ba, sai kuma ya tambayi kansa in da gaske zancen yazo. Shi dai yasan yaran sun tsaya masa a rai, kamannin halittar su da bambancin halayyar su yana bashi mamaki kuma yana kara sawa yaji tsoron Allah a zuciyarsa. Wannan ya sa ya kasa cire su a ransa, sai ya mayar da makarantar su gurin zuwan sa kullum idan lokacin daukan dalibai yayi, a haka watarana ya gansu wata rana kuma sai dai yayi ta rarraba ido ba tare daya gansu ba, haka zai hakura ya koma gida.

To yanzu kuma kusan sati uku kenan kullum in yaje school din baya ganinsu, sai kawai yaji zuciyarsa babu dadi, haka kawai yaji shi lallai yana so ya gansu duk da cewa bashi da wani dalilin ganin nasu. Wannan yasa yanzu yana tashi daga aiki ya taho unguwar su yazo dai dai inda yake sauke su ya fara tambayar ko akwai wanda ya san su. Bai sha wahala ba "ohh Sumayya da Ruqayyah kake nufi? A can layin suke amma bansan gidan su ba, sai dai in kaje can din ka tambaya" yana shiga layin ya tambaya sai aka nuno masa gidan, sai kuma yaga wannan hadadden saurayin yana kokarin barin gurin.

Yayi ajjiyar zuciya yana tattaro duk courage dinsa. Bai san me zai ce musu ba, bai san kuma yadda zasu karbe shi ba. In sun tambaye shi dalilin zuwansa bai san me zai ce musu ba. But he is going to try, ko Ruqayyah zata wulakanta shi yasan Sumayya ba zata wulakanta shi ba, kuma shi bai damu da wulakanci ba, in da sabo ya saba, babu abinda bai gani ba. Ya ci dubu sai ceto.

Ya kira yaro ya tura shi, "kaje kace wai Sumayya tazo inji Adam" sai yaji abin odd, sai yayi murmushi sannan ya jingina da jikin motar taxi dinsa.

Yaron yana shiga ya bude muryarsa ya kwada sallama sannan ya fadi sakonsa "kutumelesi! Wannan dan rainin hankalin me ya kawo shi gidan mu? Uban waye ya nuna masa gidan mu" Inna Ade tace "ke Ruqayyah! Menene haka? Ban hana ki irin wannan maganganun ba?" Ta juya kan Sumayya "waye kuma Adam? A ina kika samo shi shi kuma?"

Sumayya ita ma data cika da mamakin jin adam din a gidan su tace "Inna ban san yadda akayi yasan gidan mu ba, mai taxi ne kawai da wani lokaci yakan kawo mu gida daga makaranta" Inna tace "dan taxi? Dan taxi fa kika ce min Sumayya, menene hadin ki da dan taxi?" Sumayya tayi kamar zata sa kuka tace "wallahi inna babu komai a tsakanin mu, kawai......" "Babu komai a tsakanin ku yasan sunan ki?"

Yaron da yake tsaye a gefe yace "me zance masa?" Sumayya ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta, Inna tace "ki fita, ki tambaye shi me ya kawo shi, in bai gaya miki dalili mai kyau ba ki ce kar ya kara zuwa gurinki, bana son jaye jayen mutane kina ji ko?"

Sumayya ta mike da sauri ta shiga daki, Ruqayyah ta mike ta bita "ki bar ni inje in korar miki shi, irin wadannan mutanen in ba korar kare aka yi musu ba ba hakura suke yi ba" Sumayya ta saka hijab dinta tace "thank you, but I don't need your help. Zan iya yi masa Magana da kaina".

A jikin taxi dinsa ta same shi kansa a kasa yana daddanna wayar sa, fuskarsa da murmushi. Sai da tayi sallama sannan ya dago yana kallon ta yana kara fadin murmushin sa yace "ameen wa alaikumus salam Sumayya. Nice to see you a cikin kayan da ba uniform ba" sai ta samu kanta da yin murmushi "it is nice to see you too" sai kuma ta tuna da abinda tazo gaya masa "ya akayi kazo gidan mu Adam? Me kuma ya kawo ka gidan mu?" Ya mayar da wayarsa aljihu yace "laifi ne kenan dan na nemo gidan ku? In laifi nayi kiyi hakuri. Nazo ne kawai dan in ganki, ko shima laifi ne?" Ta girgiza kanta "wannan ba dalili bane ba, babata da kyar ta barni na fito kuma cewa tayi inzo in sallame ka, idan kuma Baba yazo ya ganni anan tare da kai inajin sai ya targada ni, dan haka dan Allah Adam ka tafi kafin yazo ya ganmu"

Yayi ajjiyar zuciya, fuskarsa tana nuna rashin jin dadi yace "lucky you. Yar gidan inna da Baba. Inna zata ce miki bari Baba kuma zai yi fada, kinji dadinki. Shikenan bara in tafi. Dama kwana biyu bana ganin ku a school ne shine nace bara inzo in duba ku ko lafiya?"

Sai taji kuma babu dadi, taji something a tone din da yayi magana dashi ya taba ta tace "lafiya lau Adam. Mun gode sosai. Mun gama exams ne dama neco kadai zamuyi. Mun gode sosai da kulawa" ya gyada kai yana cewa "I understand. Allah ya bada Sa'a. Allah kuma yasa kuyi amfani da result din ku. Ni ga nawa nan a ajjiye suna ta kura" ya dan huri iska ta bakinsa, trying to hide his emotions ya sake cewa "bara in tafi nasan zaku je islamiyya ko?"

Ta girgiza kanta "mu bama zuwa islamiyya ai. Inna Ade ce islamiyya mu, a gurinta muka koyi komai na ilimin addini da kuma duk wata tarbiyya ta musulunci" yayi murmushi "yan gata, kunji dadi. Lemme go kafin Baba yazo yayi fadan ganin ki tare da ni" sai taji tana son jin dalili chanjawar fuskarsa, amma kuma tana tsoron jan maganar kar tayi kaifi a gurin Inna Ade ko Kuma kar Baba yazo ya same su.

Ta tsaya tana kallon sa har ya bude motar ya shiga sannan tazo kusa da motar ta sunkuyo tace "thank you Adam for the visit. I relly appreciate it" yayi murmushi yace "thank you for seeing me" ya ja motarss yana daga mata hannu ya tafi. Ta bi motar da kallo har ta kule, sai taji a ranta tana son ta ji abinda yake zuciyarsa, tana son taji menene labarin sa, kuma taji tana son su sake haduwa watarana.

Da safe kafin Hassan ya tafi office ya biyo ya kawo wa Ruqayyah sim card dinta. Tana fitowa ta gashi a mota ta gaishe shi tace "na dauka aikowa zaka yi ashe da kanka zaka zo? Ko Hussain ai da sai ka aiko?" Yayi dariya sosai yace "Hussain? Hussain baya min ladabi ai, yace da minti biyar kawai na girme shi, baya ma kasar nan ya tafi China jiya. Akwai yara dai da zan iya aikowa amma I didn't want to miss the chance to see you, ina so inga wannan early morning look din naki" tayi murmushi tana dan juya masa baya tace "bayan ko wanka banyi ba" yace "and yet, you look like a model".

Ta dauko kwalin wayar da har yanzu bata ko farke ta ba, amma bai kar ba ba sai ya sa hannu ya bude mata daya side din motar yayi mata alama da hannu cewa ta zagaya ta shiga. Ta zagaya ta danyi jim tana kallon motar kafin ta shiga, ita bata taba shiga cikin private car ba sai yau, kuma tasan wannan motar ko a cikin motoci sunanta mota. Ta zauna tana zagaye idonta a cikin motar sai suka hada ido da Hassan yana mata murmushi, sai ta nuna alamar jin kunya, cikin kwantar da murya yace "you like it?" Ta gyada kanta tace "tayi kyau, sosai" yace "thank you. Sai anyi bikin mu zan koya miki mota, kinga in zaki je unguwa sai ki dauki mota a gida kawai ki fita abinki ba sai kin nemi driver ba" tayi murmushi, fuskarta cike da annashuwa sai kuma ta girgiza kanta tace "ni me zanyi da mota. Ni babu inda ma zan ke zuwa" yace "dan dai baki saba yawo babe ba, ba dan kar Baba yayi fada ba da sai in kaiki yawo yanzu kiga gari" ta mika masa wayar hannunta tace "ni dai hada min wannan wayar, ni babu yawon da zanje, ni ba inda nake zuwa".

Ya karba ya bude ya fito da ita yana nuna mata, yana jin dadin excitement din fuskarta kuma ya fahimci a matsayin ta na wadda bata taba yin waya ko raka ni kashi ba dole ta zana excited idan tayi irin wannan wayar. Ya kunna ya saka mata komai yayi mata duk setting din


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login