Showing 207001 words to 210000 words out of 300844 words
kadai ya saka ta fahimtar cewa yaudarar kanta take yi, Hussain ya mutu, shekaru biyar da suka wuce, ita da Hussain sai a Darussalam.
Sai ta sake shi sannan ta zame zuwa kan kafafuwan sa, idanuwan ta a kasa amma hawaye ya tsaya a cikin su, Kamar yadda duk tunani ya tsaya a zuciyarta fuskar Hussain kawai take gani.
Ta tuno da maganar sa
"wannan ciwon da yake damuna jarabawa ta ce, abinda zai same ni kuma jarabawar ki ne"
Ta girgiza kanta kamar ta girgiza lokacin daya gaya mata maganar "no, no, no, Hussain, babu abinda zai same ka, please babu abinda zai same ka, ba zan iya ba Hussain, ba zan iya rayuwa babu kai ba" Hajiya ta zo gurinta tana kuka ita ma, tana cewa "zaki iya Fatima, Allah ya san zaki iya shi yasa ya dora miki, sai ki karba kuma ki gode masa bisa ga sauran ni'imomin da yayi miki" ta dago tana kallon ta, her mind racing, sauran ni'imomin da Allah yayi mata? Hajiya tana nufin dan ta kenan? Danta da suka haifa ita da Hussain? Mai kama da Hussain?
Ta mike da sauri ta fara waige waige tana neman sa, tana neman yaro dan shekara biyar mai kama da Hussain ko da Hassan, yaron da tasan zata yi dedicating duk kan sauran rayuwarta a gun tabbatar da cewa ya samu kyakykyawar rayuwa ba tare da yayi kukan maraici ba, yaron da tasan zai goge mata dukkanin kewa da kadaicin Hussain.
"Ina yake?" Tace tana bin mutanen gurin da kallo, "Allah sarki, ya dauka bashi da uwa bashi da uba ko?" Ta share hawayen ta "it must have been so hard on him, it must have been so hard on all of you" amma sai ta ga duk suna binta da kallon rashin fahimta, wa take nema? Wa take nufin ya tashi ba uwa ba uba?
Ganin kallon da suke yi mata ya sake tsinka zuciyarta, God please no, not her son please. Bata son tayi musu tambayar dan bata shirya jin amsar da zasu bata ba, zuciyarta ba zata iya dauka ba. Sai ta tambayi kanta "me ya saka ta dawo gida, me nene yayi mata saura a gida? Ina ma dai da gaske ne abinda suke tunani, ina ma dai ta mutu a ranar nan kamar yadda suka yi zargi.
Duk da haka tana so taji me ya faru da dan nata, ta kama hannun umma "ina Da na?" Ta tambaya da wata irin murya data huda zuciyoyin duk wadanda suke gurin "ko yana gurin Hassan ne? Ku kawo min mota in tafi Kaduna in ganshi, ku gaya min inda yake don Allah".
Ummah tace "Fatima ke zamu tambaya ai inda yake, mu gawar da aka bamu muka binne da ciki a jikinta dan haka bamu nemi inda abinda yake cikin ki yake ba, mu duk mun dauka tare muka binne ku. Kin haihu ne dama kafin kuyi accident din? A ina kika haihu? A ina kika bar babyn?" Fatima ta dafe kanta da hannayenta biyu tana jin yadda kan ta yake juyawa, "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ta ringa fada cikin muryar ban tausayi. Duk iyayenta suka yi kanta kowa yana kokarin rarrashin ta
Maman Adam ce tazo itama tace "ku barta dan Allah ta huta, kar ku gaya mata abinda zai bata ranta Please" duk suka juyo suna kallonta, suna lissafin inda zasuyi placing dinta. An enamy or a friend? Amma sai aka dauki shawarar ta aka shigar da Fatima cikin gida, nan da nan kuma aka guda da shewa da murnar dawowar Fatima gida, labari ya bazu ko'ina cewa gawar da aka binne ba ta Fatima bace ba. Sai dai kowa aka gayawa labarin sai ya tambaya "how comes?" Lallai akwai zare cikin nadi.
Duk wannan murnar da ake yi Fatima bata tare da murna, bata kuka kuma bata dariya, tana dai zaune kawai tana kuma yin duk abinda aka umarce ta tayi batare da musu ko doki ba.
Kafin wani lokaci maganar ta zagaye ko ina, duk yan uwan Fatima sun samu labari kuma da yawadaga cikin su wadanda basa gida sun kamo hanyar gida, hatta wadanda basa kasar sun nemi next flight to Nigeria sun yi booking, Asma'u kuma da take gida already ta dauki hotunan Fatima ta tura wa yan uwadan su tabbatar da gaskiyar magana.
An sauki Adam a gurin saukar baki maza a waje, an kuma sauki Mama a kebantaccen guri a cikin gida har sai anji labari daga bakin Fatima tukunna kafin ayi tunanin matsayin ta a cikin maganar, sai dai ba Fatima ba kadai duk wanda aka gaya wa dawowar Fatima sai ya tambaya "har babyn suka dawo tare?" Amsar, ita take saka su cikin jimami da kuma tunanin ya akayi aka kwana a ragaya?
Bayan anyi sallar magrib ne maimaita sarki ya kira iyalinsa gabaki daya, immediate family dinsa, wadanda da yawa daga cikin su sun iso gidan kuma duk suna son suji inda maganar ta kwana.
Bayan sun zauna ne, fuskokin su dauke da mixed feelings na farin ciki da kuma jimami, Fatima a kusa da baban ta, fuskarta unreadable, sai aka gabatar da addu'a tare da godiya ga ubangiji akan wannan abin farin cikin daya same su tare da kuma neman jagorar sa akan duk hukuncin da zasu yanke.
Tambayar da tafi damun kowa a gurin ita Takawa ya fara yiwa Fatima. "Fatima Zahra, ina kike tsahon shekarun nan kuma mai ya hanaki dawowa gida? Ko kuma neman munki sanar mana a inda kike mu muje mu taho dake?" Ta dago kanta tana kallon sa, sannan cikin karamar murya tace "ina imo, bani da lafiya, kuma an rufe ni ba'a barina na fito ko da kofar gida, ban san yadda zanyi in neme ku ba" suka fara kallon juna cikin mamaki sannan Hajiya Ummah tace "imo? Ya akayi kika je imo?" Duk suka dawo da hankalin su kanta suna jiran amsa, amma ga mamakin su sai suka ga ta juya hannayenta, alamun bata sani ba.
Umar ya gyara zamansa yace "Fatima abinda ke cikin ki a lokacin fa? Kin san yadda akayi kika rabu dashi?" Idonta ya ciko da kwalla, ta dora hannunta akan cikinta sannan tace "ban sani ba Yaya, ni bansan komai ba, ni dai na ganni acan baninda lafiya, Adam ya gaya min accident mukayi ni bansan ma munyi accident din ba, ya gaya min tsinta ta yayi a daji sai kuma babansa ya hada mu gaba daya ya tafi damu can, ya gaya min shima bai ganni da ciki ba, yace sanda ya ganni babu ciki a jikina amma da alamar na haihu ne a lokacin, ni na dauka a inda muka yi hatsarin na haihu, na dauka an kawo muku babyn kuma kuna ta nemana, na dauka...." Muryarta ta makale saboda kukan da ya ci karfin ta, Hajiya, Ummah tare da yan uwan Fatima mata suna taya ta kukan.
Mazan kuma suna ta kokarin amfani da kwakwalwar su wajen ganin sun fahimci menene ya faru. Abubakar yace "tunda ga Fatima anan a gaban mu, wacece kenan muka binne da tsohon ciki? Menene dalilin da yasa aka faya mana cewa Fatimah ce bayan ba ita bace ba?" Umar ya juya gurin Fatima yana tausayin yadda take kuka na rashin sanin inda danta yake ga kuma mikin mutuwar mijinta, yace "Fatima Zahra, ki daure, ki tuna, ranar da kuka yi accident din menene ya faru? Dake da waye a cikin motar? Shin kunyi accident din ma ko ba kuyi ba? Ko wani cover up aka shirya dan a salwantar da ke da kuma abinda yake cikin ki? Ki tuna Fatima, ki bamu labarin menene ya faru, wannan ne zai taimaka mana gurin gano inda yaron yake".
Ta goge hawayen idanunta, duk da cewa tana goge su wadansu suka yi replacing dinsu. Tun sanda ta dawo hayyacin ta, tun sanda ta fara tuna ko wacece ita tare da taimakon Adam, babban abinda take kokarin tunawa shine yadda akayi ta haihu, saboda tana so ta tuno koda fuskar danta ne, ta tuna feeling din nakuda da fitowarsa daga jikinta, ta tuna muryar sa sanda yayi kukan sa na farko amma ta kasa tunawa. Abu na biyu da take kokarin tunawa shine accident din da Adam yace sunyi, menene ya faru, amma abinda kawai take tunawa shine Hussain ya mutu, bata san ya akayi ta sani ba amma ta san ta san Hussain ya mutu kuna shine last abinda ta sani.
"Kiyi kokari ki tuna Fatima" Asma'u ta fada tana shafa kafadar ta, ki tuna a ranar tunda safe me kikayi har zuwa tafiyar ku Abuja, ke da waye a cikin motar? Me ya faru a cikin motar" tayi shiru tana kallon Asma'u, daga alama tunani take yi, sai ta runtse idanunwanta ta yare da dafe kanta da hannunta, ta jima a haka sannan tace "Hussain........ Hussain ya tafi Abuja shi da Hassan da Adam a mota, ni kuma bana son ya tafi, hankali na ya tashi da tafiyar sa. Bayan na lissafa lokacin daya kamata su sauka sai na kira wayarsa amma baya dauka, nayi ta kira amma baya dauka dai hankali na ya tashi, na kira driver nace yazo ya kaini Abuja gurin Hussain, sai muka tafi tare da ........tare da ........matar Hassan, Ruqayyah, tace ita ma tana son taje taga Hassan. Sai muka tafi, mun kusa shiga Abuja sai Hassan ya kira ta yace mata mu koma gasu nan sun gama abinda suke yi zasu taho, muna juya mota sai aka ce min Hussain ya mutu ......" Sai ta rufe fuskarta tana kuka "shikenan abinda na sani"
Umar yace "waye ya gaya miki Hussain ya mutu?" Ta bude idonta da suka juye saboda kuka tace "ban sani ba Yaya Umar, ba zan iya tunawa ba" ya matso kusa da ita "okay, just close your eyes ki tuna sanda kuke zaune a motar, a ina kika zauna?" Ta rufe idonta a tana tunani sannan tace "a baya nake, a side din driver"
Suka kalli juna suna tunawa cewa gawar da aka samu a gaban mota take, yace "good. Ruqayyah fa? A ina take?" Ta kara tunani Tace "a baya itama, tare muke da ita a baya" yace "waye a gaba, akwai mutum a gaba" tayi shiru, her eyes squeezing, tana jinta kamar a cikin motar take, tana jin tension din son taji halin da Hussain yake ciki, tana tuno maganganun su da Ruqayyah da kuma maganar da Ruqayyah suka yi da Hassan a waya da kuma umarnin da Hassan ya bayar, she remembered the driver, da yadda yake kokarin juya motar, and then.....then she remembered her face sanda ta juyo daga seat din gaba tana kallon su da budaddun idanu, she remembered her voice, kamar yanzu take mata maganar tace "Ruqayyah? Ba Hussain dinku ne Hussain Aminu Abdullahi ba? Ya mutu! Yanzu ake fada a twitter wai ya mutu a wani asibiti a abuja!" Fatima ta tuna yadda dan cikinta ya harba da karfi a lokacin. Ta dafe cikin ta tana tsananin missing dinsa.
Ta bude idonta tana kallon Umar, ta gyada kai da sauri tace "na tuna ta, na tuna kamannin ta da komai, kawar Ruqayyah ce tare suka shigo gida sanda zan fita, ita ce a gaba, ita ce ta gaya min Hussain ya mutu" Abubakar yace "zaki iya tunawa ko da akwai ciki a jikin ta?" Ta gyada kanta ba tare da tayi wani tunani ba tace "tsoho ma kuwa".
*************. ************** *****
A yau, bayan shekara hudu da bude estate dinsa na farko, Hassan ya samu nasarar bude na biyu wanda kamar na farkon ya saka masa suna "Hussain Aminu Abdullahi memorial estate phase 2". Kamar na farkon, shima wannan block shida ne sai dai wannan hawa uku ne ba biyu ba, dan haka wannan gidaje goma sha takwas ne a ciki ba sha biyu ba.
Kamar wancan karon, yan uwa da abokan arziki sun taru sosai dan taya shi murnar wannan abin farin cikin. Aunty da family dinta, yaya da jikoki, dan yanzu Hassana da na uku take goyo, Safiyya daya, Khadijah tsohon ciki, Nafisa karami, Sumayya da one year old Abdullahin ta sai Zulaihat da take ta cin yammatancin ta har yanzu. Hassana ta kira Zulaihat "zo ki dauki Ilham ki tafi da ita gurin samarin, in sun baki kin kasa karba ita sai ta karbo ta kawo min mu raba" ta fada tana miƙa mata ikram da take ta tsalala kuka. Zulaihat ta bata rai "kai yaya Hassana! Ni ya zanyi da ita?" Sumayya ta miko mata abdullahi "hada da Abdul, sai ya taya ki renon ta" Abdul ya mika wa Zulaihat hannu yana murna za'a dauke shi. Zulaihat ta bata rai tana dungure masa kai sannan tace "Aunty kin gan su ko?" Aunty tace "ina ruwan Amina? In da kinyi aure ai da ba zasu ke hada ki da rainon yayan su ba. Ki dauki yaran, maybe in samarin ki suka ganki dasu suka fahimci cewa kin iya raino zasu fahimci cewa kin isa aure". Duk suka kwashe da dariya banda Zulaihat, ita ta gaji da wannan sa idon da suke mata suna cewa taki aure, ga Aunty tana tare mata amma tun da taga Sumayya ta haihu sai ta fara matsanta mata itama akan ta fitar da miji ayi mata aure.
Ta tura baki, "babu dan da zan dauka, ai duk kuna da yan aiki ku basu yaran mana su rike muku" ta tashi tana kokarin barin gurin wayar Aunty tayi kara. Ta fito da ita daga jaka tana duba sunan sai ta dafe kanta "innalillahi" Khadijah tace "waye?" Aunty tace "Hajiya Umma ce, wallahi shaf na manta ban aika musu maganar taron nan ba, yanzu haka labari suka ji zata kira tace min ban kyauta ba" Hassana tace "kash, walllahi an manta kuwa, amma kinga wancan ai an aika musu har suka zo ma" Aunty ta dauki wayar da kiran har ya riga ya katse tace "bara in kira in basu hakuri, ban kyauta ba wallahi"
Kafin ta kira sai wani kiran ya sake shigowa, ta tashi tsaye ta dauka yana matsawa inda babu hayaniya ta fara wayarta, bata jima da tashi ba sai sai Hassan yazo, yan samarin sa guda uku suna binsa kamar jela, ya saka hannu ya dauki Abdullahi da tun daya hango shi ya fara tsalle a cinyar maman sa, ya daga shi yana kissing forehead dinsa sannan yace "shine kika zo kika yi zamanki kika barni da mutane ko?" Ta mike tana murmushi tare da pretending hamma, ya harare ta, tayi murmushi "ba laifi na bane Habibi, laifin wannan katon yaron na hannunka ne" sai shima ya ja kujera ya zauna "nima zama zanyi, duk wanda yazo yanzu ke zaki zagaya dashi" ya zauna Sumayya ta fara zuba masa drink sannan ta zubawa boys din suma. Suna ta hada baki gurin bata labarin abubuwan da suka faru a gurin.
Sun jima a haka sannan Aunty ta dawo daga wayar da taje yi. Yanayin fuskarta ya saka kusan gaba ki dayansu suka mike tsaye, Nafisa tace "Aunty mutuwa akayi? Waye ya mutu kuma?" Aunty ta bisu da kallo daya bayan daya sannan tace "ba mutuwa akayi ba, the most strangest thing has happened, Fatima ta dawo gida, bata mutu ba"
*The Story*
Shirun daya biyo bayan maganar ta hatta kurma zai iya jinsa. Hassan ne ya fara cewa "what? Aunty menene kika ce yanzu? Fatima fa kika ce bata mutu ba" kallon sa take yi itama da alama shock din maganar bata gama hitting dinta ba har yanzu, cikin rawar murya tace "abinda Hajiya Ummah tace min kenan yanzu, wai ga Fatima a gida, wai bata mutu ba duk tsahon shekarun nan tana jihar imo tare da Adam, wannan drivern Hussain din".
Sumayya ta koma ta zauna, saboda kafafuwan ta da taji ba zasu dauki jikinta ba in bata zauna ba zata iya faduwa "Adam?" Ta fada a hankali, Hassan ya jiya ya kalle ta sannan ya kalli Aunty shima yace "Adam?".
Khadijah ta bude ido tace "in bata mutu ba kenan ta haihu, babyn yaya H2! Ina babyn yake? Suna tare a kanon?" Hassan ya kuma juyawa sharply yana kallon Khadija, zuciyar sa tana bugawada karfi kwakwalwar sa tana analysing maganar Khadija, tabbas in Fatima bata mutu da ciki ba to kuwa ta haife shi, shekaru biyar da suka wuce, meaning abinda ta haifa har yayi yawo ma kenan, meaning an haifa wa Hussain da a duniya.
Sai kuma yaji amsar Aunty ta daki kunnensa kamar yadda tambayar Khadijah ta daka "babu baby, ita kadai ta dawo, ba'a san inda babyn yake ba" ya dawo da idanuwan sa kan Aunty, this is too much to take a cikin mintuna kadan "what?" Ya sake cewa, "ban gane ba Aunty ban fahimta ba" tana kallonsa tace "nima ban gane ba Hassan, kai na ya toshe ban san ma wanne tunani zanyi ba, bana ma gane komai, abinda ta fada min kenan"
Hassana tace "a dauko mota mu tafi kanon, a xan ne zamu fahimci maganar nan dan ba maganar da za'a yi a waya bace ba, wannan fa ba karamar magana bace ba, ya za'a yi Fatima da tayi accident ta kone kurmus ita da abinda yake cikinta kuma aka binne su sannan bayan shekara biyar su dawo? Wannan ko a film, ko a Indian film bana jin zai iya faruwa" Safiyya tace "to ai yar su ce, ba zasu yi karya suce ta dawo ba indai ba dawowar tayi ba. Kuma ma in sunyi karya me zasu yi gaining?" Khadijah tace "amma ku dakata, in da gaske Fatima bata mutu ba, in ba gawar Fatima aka binne da ciki a cikin daji ba, wacece kenan? Wa aka binne?"
Duk suka kalli juna banda Sumayya data ke zaune ta dafe kanta da hannayenta biyu tana sauraron yadda zuciyarta take bugawa. Hassan ya kalli Khadijah yana lissafin amsar tambayar da tayi, tabbas bai ga gawar da aka binne dinba amma ance ba za'a gane kamannin ta ba except that macece mai tsohon ciki, in dai har iyayen Fatima da kansu sun tabbatar wadda ta koma gida Fatima ce then