Showing 135001 words to 138000 words out of 300844 words

Chapter 46 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2100

ko zamu shiga ku gaisa?" A ransa yana fatan hakan zai farantawa Hussain rai, Hussain yayi murmushi yace "baya nan, ya bata" Hassan ya danyi dariya, "ya bata fa kace? Ya bata kamar yaya?" Hussain yace "wata yarinya yake so balarabiya, babansa sarkin Abuja yaki zuwa ya nema masa aurenta shine na bashi shawarar yaje ya nema da kansa, he went there kuma suka hana shi. Tun daga nan ba'a kuma jin labarin sa ba yayi cutting off ties da gida gaba ki daya har mu abokan sa babu wanda yasan inda yake. Rumors have it that ya sace yarinyar ne yaje ya aure ta, but babu wanda yasan a wacce kasar suke yanzu" Hassan ya bude baki yana mamakin wannan irin karfin hali na wannan bawan Allah, amma ya sani dole duk inda suka tafi ma watarana da kafafuwan su zasu dawo gida kuma yana guje musu abinda zasu tarar a gidan musamman saboda kasancewar su yan sarauta.

Hussain yaji dadin magungunan sa sosai, dan da suka kare shi da kansa ya kira Doctor din ya sake bashi wasu. Sun rage masa ciwon da yake ji a cikinsa sosai kuma yanzu yakan ita zama yaci abinci ya koshi, yaji dadin hakan dan hakan ya kara taimaka masa wajen kara boyewa Fatima halin da yake ciki. Cikin Fatima yana ta girma abinsa, cikin lafiya ita kuma cikin kwanciyar hankali dan babu abinda yake damunta, ga Hussain yanzu da yake kara makale mata kamar cingam dan office din ma yanzu ba fita yake yi ba in ma ya fita da wuri yake dawowa, yawon kasashen duniyar ma duk ya daina kullum yana tare da ita yana yi wa babyn cikinta hira, haka zai ta bawa cikin labarai yana dariya shi kadai ita kuma tana yi masa dariyar wautar sa "ba fa ta jinka" yace "injiwa? Haka ya gaya miki?" Tace "wai kai wa yace maka namiji ne? Na gaya maka mace ce" yace "ke wa yagaya miki macece? Ni na gaya miki namiji ne" tace "ai a cikina take ko? Muna communicating through placenta" yayi dariya "gori zaki yi min ko? Nima ai muna communicating through you, kuma ya gaya min shi namiji ne" tace "to aje a duba mana, sai a kure musu" yace "anki wayon. Ni bana so a kure ni".

Sai dai ba wai rashin son a kure shine ya hana shi zuwa a duba gender din abinda yake cikin Fatima ba, damuwarsa shine yadda rabon gadonsa zai kasance idan ya mutu, dan haka ya yanke wani hukunci kuma ya gama tsara duk plans dinsa gabadaya sannan yaje ya samu Hassan a office dinsa ya ajiye masa takardu a gabansa yace "I need to sign these" Hassan ya dauki takardar yana jujjuya ta yana karantawa briefly, ya dago kai yana kankance idonsa yace "what is this? Me kake yi haka?" Hussain ya daga kafada yace "I am giving you half of h and h and all it's assets. Dama sunan sa H and H ma'ana Hassan da Hussain, it is yours as much as it mine, ka sani kuma" Hassan ya girgiza kansa yana dawo masa da takardun gabansa yace "bazan karba ba kuma kaima ka sani, ba tun yau ba ka nuna kana son bani nace bana so saboda ni nafi son inyi working in kuma yi earning kudi na da kaina. Wannan naka ne, H and H naka ne ba namu bane ba kuma kai ma kasan wannan" Hussain yace "shikenan, in baka karba ba ya zama na lawyers dina dan already na riga na fitar dashi kuma sun saka hannu, yanzu saka hannun ka kawai ya rage" suka yi shiru suna kallon juna. Hussain yace "look Hassan, ba wai na baka bane dan baka dashi ko dan in taimaka maka ba a'a na baka ne as security for our family, ban san abinda Fatima zata haifa ba, in ta haifi namiji yayi muku katanga da duk wani abu dana mallaka ni kuma ba zan so haka ba, zanso ace kun gaje ni kai da kannen mu saboda dama dan in kula damu na fara business din nan. Gidan mu da wannan kamfanonin aka dogara gabaki daya, idan Fatima da danta suka karbe komai kai da Aunty da sauran yan'uwa zaku koma a karkashin ta kenan, you will be working under my son and wife abinda ni kuma ba zai min dadi ba duk da nasan Fatima kuma ina saka ran abinda zata haifa zai samu tarbiyya mai kyau daga gurinta da kuma gurinka. But zan so ace kun zama partners ne. Yadda ko ma me ta haifa you still have your share, wadda nasan zaka yi amfani da ita ne gurin kula da kanka da Aunty da yan uwan mu da yayan mu, all of them".

Hassan yace "stop talking as if mutuwa zaka yi Please, idan da kasan yadda maganganunka suke taba zuciyata da ka daina yin irin su Hussain. You are getting well, ba ka ganin yadda jikin ka yayi kyau?" Hussain ya mike yanakara tura masa takardun gabansa yace "sign this please, and try to get some sleep dan ka rame da yawa".

Daga nan ya fice ya barshi a zaune, ya jawo takardun yana duba signature din Hussain baro baro a jiki cewa ya bashi rabin duk abinda ya mallaka a duniya. Sai ya jawo drawer ya saka takardun sannan ya mayar ya rufe. Ya koma ya kife kansa akan table din gabansa yana jin kansa yana sarawa sosai. Shi kansa yasan ya rame ya kara baki ya bushe, mutane da yawa suna tambayarsa "lafiyar ka kalau kuwa?" Yakan amsa da eh amma shi kansa ya san bashi da lafiya, ciwon nan na Hussain yana damunsa sosai kullum hankalinsa ba a kwance yake ba, ko magana yaji anyi da karfi ko kuma yaji hayaniya sai gabansa ya fadi, sai ya dauka za'a ce masa wani abu ya samu Hussain din sa.

Ga kuma problem din Ruqayyah. Duk da wani bangare na zuciyarsa wanda yake cike da sonta kullum yana yi mata uzuri amma kaso mafi yawa na tunanin sa yafi karkatuwa ga karbar gaskiyar magana. Gaskiyar magana kuma shine bai yi dace da mace ta gari ba. Lokuta da dama yakan samu kansa da tambayar kansa shin ina wannan Hassanar daya aura take? Anya ba'a chanja masa da wata ba kuwa? Ina wannan karamar yarinyar nan data dora rayuwarsa a saman tata ta ceto shi daga bakin bindiga take, ina yarinyar nan yar gidan malamai mai cike da tarbiyya, kunya da ilimin addini? Ina yarinyar da bata saba da kyale kyalen duniya ba? Dan yasan ba ita bace wannan wadda last week ta hana masa sakat a gidan sa da mitar Hussain ya sake wa Fatima mota ita banda ita ba, dan waccan yarinyar babanta ko keke bashi dashi.

Yanzu gidan sa ya koma abin gudu a gurinsa, wannan yasa kullum yana office, har weekend zuwa yake yi yayi ta aiki shi kadai musamman tunda yanzu Hussain ya tattara harkar kamfanin yayi watsi da ita. Shi kuma sai ya dauki aikin yake tayi da iya kacin karfinsa dan yana so ya rage wa kansa tunani kuma ya nesanta kansa da fada da kuma mitar Ruqayyah. Yau ma kafin ya fito sai data saka shi a gaba da zancen tana son ya bata kudi ta tafi Dubai siyayyar haihuwa.

Hussain yana komawa gida yayi wa Fatima alkawarin ta lissafa masa dream countries din da take son zuwa a rayuwarta shi kuma zai kaita. Ta bude baki cikin murna "lah! Na dauka yanzu baka son fita" yace "yanzu ina so, so nake mu fita mu samu good quality time daga ni sai ke sai baby" ai kuwa nan take ta fara lissafa masa duk inda take son zuwa, shi kuma ya ware wasu kudade masu kyau daga cikin personal kudinsa ya fara shirya musu tafiyar. Kafin wani lokaci komai ya kammala, suka shirya suka tafi and they spent the best days of their lives together. A lokacin ne ciwon Hussain yafi karfin drugs din da ya ke sha har Fatima ta fara fahimtar bashi da lafiya, amma sai ya gaya mata cewa ulcer ce take damunsa, ta nemi suje asibiti sai ya shiga drug store kawai ya siyi magani ba tare da ya bari an wani do ba shi sosai ba. A lokacin ne labarin haihuwar Ruqayyah ya same su, ta haifi danta namiji kuma kowa ya kira sai ya gaya musu irin tsananin kamar da yaron yake yi da Hussain. Kuma Hassan ya rada masa suna Hussain duk da cewa bashi da abokin tagwaitaka. Wannan yasa hankalinsu kuma yayo gida dan itama Fatima nata cikin ya kai wata bakwai kenan, tace "naga alama dai gidan nan sai maza ake ta haifa, ni kam nafi son mace dan ta zama kawata amma ko namijin nema ina sonsa shima".

Hussain shima ba wai ya damu da lallai sai namiji ba, kawai dai yana ganin kamar namijin zai fi jan nasabarsa sosai akan mace, tunda ita mace in tayi aure ta haihu yayanta da gidan baban su zasu yi tutiya ba da shi ba, amma a yanzu yadda yake jin ya matsu yaga abinda zai haifa ko macen cema yana so sosai. Sai suka shirya dawowa Nigeria dan ayi sunan takwaran Hussain dasu, kafin su taho sai Hussain ya dauke ta zuwa asibiti inda ya nemi ayi musu 4d scan na babyn cikinta. Tayi ta mamakin dalilinsa nayin hakan bayan da yace ko gender baya son sani, ta tambayeshi dalili sai yace "I changed my mind, ina tsananin son ganin abinda yake cikin ki ko da a hoto ne" ita bata taba sanin cewa 4d pregnancy scan is possible ba sai yau, lallai technology babu abinda ya bari rai ne kawai Allah bai bawa turawa ikon hurawa jiki ba, babyn da yake kwance a cikinta sai gashi suna ganinsa clearly a jikin screen a kwance a cikin amniotic fluid yana ta tsotsar hannunsa, idanuwan sa tar a bude. Ba sai Doctor ya gaya musu ba su da kansu suka gani cewa namiji ne, ta juyo da sauri ta kalli Hussain sai taga hankalinsa yana kan screen din yana kallon babyn, and she saw a tear in his eyes but sai yayi sauri ya mayar da ita a hankali yace "bai yi miki kara ba, kamar mu daya" ta turo baki "ai dama hada baki kuke yi kullum in kana yi masa hira, a lokacin kukayi meeting kuka ware ni" ya danyi dariya, tace "amma ai kalar fata ta ce dashi, bai kai ka haske ba" yace "waya gaya miki? ai hoton black and white ne kuma yayi duhu ba zaki gane kalar fata ba".

Sun jima suma kallon babyn su for 30 minutes wanda shine medically advisable sannan aka kashe, Hussain yaji kamar an kashe wani part na zuciyarsa ya daina amfani, sai dai kawai jin dadin sa shine an musu record na scan din a CD aka basu. At least ya samu abin gani kafin babyn yazo, that's in babyn zai zo ya tarar da shi.

Kwana biyu bayan nan suka dauki hanyar Nigeria. Suna sauka suka je suka ga jaririn Ruqayyah, Fatima tana jin kamar ta sace shi saboda kamannin da taga yana yi da Hussain.

Bayan an kammala suna ne Hussain ya koma Abuja gurin Doctor din da yake dubashi yayi requesting ya bashi wasu magungunan da suka fi wadancan karfi, amma sai Doctor din ya nuna masa cewa babu sama da wadannan, from kallon da Doctor din yake yi masa yasan cewa lokacin da ya rage masa bashi da yawa, amma sai yaji har cikin zuciyarsa baya jin tsoro kawai dai yana bakin cikin rabuwa da masoyansa ne. A ranar bayan ya koma gida ya dauko diary dinsa wanda har ya kusa cika shi da rubutu ya rubuta..

Dear baby

Duk rubutun da zan yi maka daga yanzu zai iya zama abu na karshe da zan gaya maka. Rayuwa ta kadai ta isa nasiha a gare ka akan cewa babu wani abu da yake da tabbas, lokaci ne kawai yake da tabbas sai dai mu bamu da tabbas din kaiwa zuwa lokacin, an rigaan kayyade wa kowa iya kacin adadin seconds da zai yi a duniya kuma duk yawan kudin daka tara, duk kyawun fuskarka, duk yawan masoyanka da makiyanka, duk martabar ka, duk yawan ibadarka da rokon Allahn da zana yi akan ya kara maka kwanaki a duniya ba zaka wuce wadannan seconds din ba. Kowanne dan Adam yana tafiya ne akan nasa lokacin, dan wani yayi kudi da wuri ya sayi katon gida da manyan motoci ya auri kyakykyawar mace yar nasaba ba lallai ne shine successful man a duniya ba, maybe shi kwanaki kadan aka kayyade masa da kuma arziki da yawa, wannan shi yasa yayi arziki da wuri dan ya cinye arzikin sa kafin lokacin sa ya cika.

Wani kuma sai yayi ta neman kudin da karfin sa da kwakwalwar sa amma sai ya dauki dogon lokaci bai samu ba kuma zata iya yiwuwa shi mai tsahon rai ne, dan haka yake cin arzikin sa kadan kadan. Wani kuma a wahala zai fara kuma a wahala zai kare saboda tasa kaddarar kenan. Babu wanda yake sauri babu kuma wanda yake lakaki, kowa yana tafiya ne akan lokacin sa.

Shi arziki ba komai bane ba illa wata hanya da ubangiji yake jarabtar bayinsa, sai ya baka kudi yaga abinda zaka yi dashi ko kuma ya hana ka yaga abinda zaka yi. Ida har ka nemi kudi ka samu to Allah ne ya baka, idan kuma baka samu ba to shine ya hanaka. Idan ka samu dama ka nemi kudi ta hanyar halak, idan zaka kashe su ka kashe su ta halak. Idan kana dashi ka taimaka wa wanda bashi dashi, idan baka dashi ka nemi na kanka ta hanyar halak kar ka zama mai matacciyar zuciya ko mai roko a gurin mutane.

A duk lokacin da dama ta same ka tayin wani abu to kayi shi a lokacin kar ka jira sai wani lokaci, dan ba kai kake da lokacin ba. Duk abinda kaji kana son yi to kayi abinka, as long as bai sabawa ubangijin ka ba kuma ba zai zamanto cutarwa ga wani abin halitta ba ba to kayi abinka kar ka damu da abinda mutane zasu ce dan su mutane ba'a taba iya musu, in kabi ta tasu ba zaka yi achieving komai ba.

Ka zauna da clean heart, kar ka nufi kowa da sharri kar kuma ka rike kowa a ranka, always think positive dan shi negativity yana huda zuciya ne ya kuma hana ka ganin alkhairi ko da yana gabanka

Bana tunanin halin da zan barka saboda nasan na barka da best mother in the world da kuma best father in the world. Na san ko ban bar maka ko kwandala ba Hassan zai iya yin dako ya ciyar da kai. Dan haka indai a kan wannan ne bani da damuwa"

Shigowar Fatima tasa yayi saurin rufe wa, ta tsaya tana kallon sa "wannan diary, ina jin kwanan nan a karkashin pillown ka zaka ke sakawa saboda tsabar baka so a karanta" yace "kar ki damu, shi wanda nake rubutawa da kansa xai karanta miki wata rana. Have patience" ta zauna da kyar tana cewa "Allah y kaimu, a gabanka zai karanta min ai, sai inji in ka rubuta abinda ya shafe ni a ciki" ya taso yana rungume ta ta gefe yace "a duk page da akwai sunan ki Fatima. Idan babu ke babu ni Princess" ta shafa fuskarsa tana murmushi tace "kaima in babu kai babu Fatima " sai ya dora kansa a kafadar ta ya lumshe idonsa.

Hajiya Ruqayyah an haihu, da namiji na uku kenan data haifawa Hassan kuma tana tutiya a ranta cewa ko a haka ta barshi ta riga ta zamar masa karfen kafa, ta zamar masa kadangaren bakin tulu duk kuwa da cewa a yanzu ta fara fitar da ranta daga dukiyar Hussain musamman bayan ganin tulelen cikin Fatima da tayi duk da bata san me nene a ciki ba amma tana ganin haihuwar Fatima zata kara nesanta ta da H and H. Duk da cewa Hassan yayi signing takardun da Hussain ya bashi amma bai gaya wa kowa ba hatta Aunty, and definitely not Ruqayyah dan yasan in ta sani to kuwa ba zata haihu a Nigeria ba cewa zata yi ya fita da ita waje ta haihu a can. Amma duk da haka sai data matsa masa ya bata uban kudi kawai tayi ta siyan kaya wai na fitar suna, kayan babu kuwa haka tayi su daki guda duk dacewa akwai kayan twins wadansu ko amfani dasu basu yi ba, wadansu kuma kudin data karba kawai a account ta zuba su ta ajiye.

Sai dai duk wannan abin da take dasu bai saka saka farin ciki a zuciyarta ba, kullum ranta babu dadi zuciyarta bakikkirin musamman inta lissafa taga plans dinta duk babu su, Adam din ma da take ta kokarin ganin ta raba shi da yar uwarta har yanzu abin ya gagara sai kara samun karbuwa yake yi a gurin iyayensu da kuma a gurin Hussain, hatta Hassan din data juya wa ra'ayi akan Adam yanzu ya fara chanjawa dan kwana biyun nan har hira taga suna zama suyi su kuma yi dariya. Ta saka ta warware ta kuma saka wa ta kuma warwarewa amma har yanzu ta kasa samun mafita. Then one day, bayan Hussain din ta yayi wata daya a duniya sai taga Hassan yana aiyukan files din staff din da suke dasu a gidan, kowa da file dinsa tun daga kan masu gadi har zuwa masu ban ruwan fulawa. Ta zauna tana taya shi sorting, yana ware wasu wadanda yake so zai yiwa karin albashi a ciki har da Adam, ta miko masa file din ya bude yana going through, anan ne idonta ya sauka akan sunan Adam na gaskiya da kuma address din gidan iyayen sa mahaifa. Anan wani plan ya fara forming kansa a zuciyarta. Bata ce komai ba har suka gama aikin sannan ta tafi dakin ta. Ta kira Minal a waya "Minal ya kike ya nauyi? Dan Allah taimako nake so" Minal tace "taimako?


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login