Showing 60001 words to 63000 words out of 300844 words

Chapter 21 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2052

a samu shiga aljanna, ita ce kuma abinda idan an ƙi yi sai a halaka a fada wuta Allah ya kiyaye, wannan kadai ya nuna miki darajar abinda kika yi, aure. Aure sunna ne, amma abinda ake yi a cikinsa farilla ne, dole ne ki bi mijinki Ruqayyah indai kina son lahirar ki tayi kyau, dole ki sauke wannan bakar zuciyar taki da wannan saurin fushin naki kiyi masa biyayya Hassana idan ba haka ba ina tausaya miki, ina tausayawa duniyar ki da lahirar ki baki daya"

Baba ya jima yana ta yiwa Ruqayyah fada, fadan daya saka Sumayya kuka amma ba Ruqayyah ba. Bayan ya gama yayi mata adduoi na fatan zaman lafiya a gidan mijinta sannan yayi musu sallama ya fita.

Bayan ya fita ne Inna da yanuwanta da suka zo daga zamfara suka dora da nasu, suka yi mata doguwar nasiha akan zaman aure da kuma hanyoyin da za'a kyautatawa miji ta hanyar magana mai dadi, godiya, ladabi da biyayya, nuna soyayya da kulawa "ki mayar da duk abinda ya shafe shi ya zama top priority dinki, yan uwansa su zama naki, shimfidar ki ta zama abinda kullum yake muradin komawa ga, abincin ki ya zamanto shi kadai yake iya ci yaji dadi, wadannan sune manyan abinda namiji yake bukata. In dai har kin rike wadannan to kuwa ba kya bukatar boka ko Malam akan mijinki. Zaki juya kayan ki yadda kika ga dama musamman idan yana sonki" Daga nan kuma sai suka dauko nata tsarabar da suka taho mata da ita suka fara bata, dake dake ne da kulle kulle iri iri, wasu a leda wasu a robobi da kwalabe ko wanne an rubuta yadda za'a yi amfani dashi. Gwoggo Habibah tace "bamu baki su bane ba saboda bamu san kalar halittar ki ba kema kuma baki san ta mijin ki ba, dan haka sai kinje gidan kin kwana biyu kin fara gane yadda abin yake sannan zan kira ki in kara miki bayanin abinda kike bukata da kuma yadda zaki yi amfani da shi sosai. Ko wacce mace da irin halittar ta haka suma mazan, in akaje akayi ta bawa yarinya abubuwan da suka fi karfinta sai azo a zamu matsala kuma. "

Bayan sun gama nasu sannan sauran yanuwa kowa yazo ya dora da nasa, hakuri, biyayya, girmama wa, soyayya, su akayi ta maimaita wa Ruqayyah har sai data ji ta haddace kalaman tsaf a kwakwalwar ta. Abinda Ya rage mata shine yin amfani na kalmomin.

Bayan magrib akazo daukan amarya. Aunty ce da kanta tare da hajiyan Kano, kanwar baban su Hassan su suka jagoranci sauran mata zuwa dauko Ruqayyah, Ruqayyah har tayi wankan ta ta shirya cikin wata green atamfa mai adon pink wadda tayi matukar karbar ta, dinkin yayi kyau sosai a jikin ta, sai a lokacin taga Sumayya tana kuka sannan nata jikin ya fara sanyi, sannan ta fara tunanin zata yi missing Sumayya da sauran yan gidansu, sai kuma tayi saurin kawar da maganar ta hanyar gayawa kanta cewa ai zata ke yawan zuwa tana ganinsu, suma kuma haka musamman in suka je gidan nata suka ga daular da taje ciki. Kuma zata saka Hassan yazo ya roki Baba ya bar Sumayya ta koma can da zama.

Sai a lokacin taga ana fito kayan gararta, ita bata san ma cewa anyi mata garar ba kuma bata da idea a inda Baba ya samo kudin yin garar. Ta daiji Aunty tana cewa "haba malama Sa'adatu, dan me zaku takura kanku kuce lallai sai kunyi gara? Ai da kun barta kawai" Inna Ade tace "aa auntyn yara, ai babu wani takura kai wallahi, kayan dakin ma dan dai an saka lokacin ne gajere Amma da babansu duk zaiyi dai dai iyawarsa".

Bayan anyi duk abubuwan da akeyi na al'ada cikin barkwanci da wasa da dariya tsakanin bangarorin biyu sai aka bayar da Ruqayyah Aunty ta rungumo ta ta fito da ita ta saka ta a motar da tazo a cikinta ita da hajiyan kano da gwoggo Habibah sauran motocin da suka zo daukan yan uwan amarya suka mara musu baya.

Sumayya ta tambayi inna ta hada yan kayanta a karamar jaka, tana so zata raka Ruqayyah kano, so take sai an gama bikin gaba-daya sannan zata dawo gida. Tun da ta fito kofar gidan ta samu gefe daya ta tsaya hannunta rike da jakarta tana ta sharar hawayen ta tana bin mutanen da suke ta turereniyar shiga motoci da kallo, sai kuma taji tana jin haushin kanta na damuwar da tayi, ita me auren ma ko a jikinta dan ko digon kwalla bata gani a idanuwan ta ba amma ita har nata idanuwan sun kumbura saboda kuka.

Tana tsaye taji mutum a kusa da ita, ta gefen idonta ta gane namiji ne dan haka ta yi saurin juyowa side dinsa a tsorace, ya jefe ta da best smile dinsa, ta ji half of damuwarta ta tafi amma sai ta kara bata rai "har da kai aka zo za'a dauke min yar uwa ta ko Adam?" Yayi dariya "mu menene laifin mu? Gidan miji fa zamu kaita, at least ai yanzu zata daina runton kudin mota" Sumayya ta harare shi "be careful, matar ogan ka ce dai yanzu, or else you get fired" ya saka hannu ya kama bakinsa ya ce nayi shiru, ba zan kara cewa komai ba" Sumayya ta nuna shi tace "you better, kasan Hassan baya wasa da yara" yace "yeah, ba sai kin tuna min ba na sani, Hussain ne mai wasa da dariya, dadinta kuma shi na ke yiwa aiki ba Hassan ba" tace "amma Hassan din ne ya dauke ka aikin kuma he can fire you" yace "to mai mijin sister, naji, can we go now" yayi kasa kasa da murya yace "daga ni sai ke, na boye motar da nazo da ita" ya kashe mata ido.

Yayi gaba, da kamar ba zata bishi ba sai kuma ta juya tana waige waige sai data tabbatar babu wanda hankalin sa yake kanta sannan ta bishi inda taga yayi, tana zuwa ya zagayo ya bude mata kofar front seat ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga gurin driver ya tayar da motar. Sai kuma ta juyo tana kallonsa da budaddun idanunta tace "gidan amaryar zaka kaini ai ko?" Bai kalle ta ba yace "yeah, sure" ta kuma cewa "ba wani gurin zaka kaini ba ko?" Ya juyo yana kallonta da guntun murmushi a bakinsa yace "babu inda zan kaiki, daga nan straight zuwa gidan oga Hassan" tace "ka rantse" yace "I cross my heart and hope to die" ta bata rai tace "da Allah ai nace ka rantse" seriously yace "na rantse da Allah ba sace ki zanyi ba. Can we go now?"

Dogon convoy aka hada ana ta sharara gudu akan titinan garin Kaduna, manyan mata suna ta rangada guda yayinda samari da yammata kuma suke kara volume din kida suna rausaya a cikin motoci, amarya kuwa motarta na tsakiya tana jinta kamar a cikin gajimare take tafiya ba wai a cikin mota ba. Ta lullube fuskarta da mayafinta amma da yake ba mai duhu bane ba tana hango gabanta, a haka har suka isa low cost, har suka shiga jerin gidajen da a cikin films da kuma social media ne kawai take ganin irin su. Ta bude ido sosai zuciyarta tana bugawa da karfi tana son ganin wanne ne nata a ciki, a haka taga anzo kofar gidan tun daga wajensa zata iya cewa kaf jerin gidajen babu wanda ya kaishi kyau da tsari. Aka bude gate, mutane da yawa a ciki mata suna ta guda, wannan ya tabbatar mata da cewa wannan shine gidan nata, sai da motar taje gaban gidan sannan ta lura gidajen guda biyu ne a jere amma ko kusa basu yi kama da junan su ba, na farkon yayi ukun na biyun, tayi murmushi a ranta, maybe na biyun na Hussain ne, ko daga nan wannan so call gimbiyar zata gane tayi mata zarra.

Amma sai me, sai taga an wuce katon an tafi ga an karamin, sai a lokacin ta lura cewa kofofin katon a rufe suke fitulun sa a kashe karamin kum komai a bude yake tana iya hango mutane a ciki ma. Ta juya side din Aunty, zuciyarta tan agaya mata t tunawa Aunty cewa anyi mistake ba nan ne gidan Hassan ba nan gidan Hussain ne. Amma sai taji aunty tana cewa "alhamdulillah Ruqayyah Allah y kawo ki gidan ki lafiya, sai kiyi masa godiya sannan ki fito da kafar dama tare da bismillah" sai wata zuciyar ta gaya mata to ko nan part din Aunty da yara ne aka kawo ta ayi mata fada sannan a kaita part dinta? Yes, that must be it.

Ta fito da bismillah kamar yadda Aunty tace, sannan Hajiyan Kano ta kama hannayenta tana tafiya da ita yan uwanta ta suka rako ta suna take musu baya. A palo ne taga hoton su ita da Hassan wanda suka dauka last week yace enlargement za'a yi musu a kafe musu a palon su. Kafafuwanta taji sun kasa daukan ta, jikinta yayi sanyi kwakwalwar ta tana neman toshewa. Ta tafi kamar zata fadi, Aunty tayi saurin riketa "subhanallah. Ruqayyah lafiya? Sai ta taba wuyanta, wuyan da lokaci daya da dauki mugun zafi ta ce "ya salam, jikinta zafi, dama bata jin dadi?" Goggo Habibah yayar Inna Ade tace "anya kuwa, kamar lafiyar ta kalau" Ruqayyah ta fara kuka a hankali irin wanda sheshsheka ce kawai take fitowa, tana jin tamkar duniya ce gabaki daya take ruguzo mata aka, tana jin kamar duk mafarkanta suna tarwatsewa a gaban idonta. Zuciyarta tana rada mata wata magana, wata mummunar magana.

Hussain shine CEO na H and H ba Hassan ba.

And that explains alot of things. Tayi saurin tana girgiza kanta kamar mai fada fa zuciyar tata. No, no, no. Ta ringa maimaitawa

She felt her dreams shattering. Ta sake girgiza kanta trying to comport herself, wani barin na zuciyarta yana gaya mata "ba haka bane ba, kinsan Hassan da makale aljihu, shine zai zabi gina karamin gida ba wai dan ba shine mai Company ba" sai daya barin yace "kuma sai yabar kaninsa ya gina babban gidan da ya fi nashi?" Nan take sautin kukanta ya karu

Kuka take yi kamar ranta zai fita, Hassan ya yaudareta yaci amanar ta, yayi mata karya dan ya aureta. Zuciyarta zafi take mata, zuciyarta ciwo take yi mata, anya kuwa ba ciwon zuciya ne zai kama ta ba?

Tana jin maganganun mutane a kusa da ita, yawancin su hakuri suke bata, sama sama kuma tana jin dariyar wasu. Sai ta fahimci sun dauka kukan barin gida take yi. "Kaji yarinyar nan, har muna yabonta muna cewa yarinya karama amma bata yi kuka ba ashe kukan zuci take yi sai yanzu zata yi na fili" "kiyi hakuri Ruqayyah, muma duk da haka muka sossoma wai kuturu yaga mai kyasbi" suka kwashe da dariya wasu daga ciki suka yi guda, "ni sanda za'a kaini gidan nawa mijin ma guduwa nayi, sai da akayi ta nema na aka rasa har aka hakura sannan na dawo, ina dawowa kuwa aka kama ni aka kaini" aka sake wata dariyar.

Ruqayyah taji tamkar ta samu bindiga Ak47 duk ta bi su da bullet goma goma. Dan dai tasan sun fi ta karfi ne da babu Abinda zai hana ta tashi ta rufe duk mutanen gurin da duka. But bata son ta bata rawar ta da tsalle, zargi ne ai kawai take yi, bata tabbatar ba lokacin taji muryar Nafisa a kusa da ita, "kiyi hakuri kiyi shiru kinji yayata kar kanki yazo yana yi miki ciwo, kinga duk su Aunty tsokanar ki suke yi" sai itama tayi dariyar sannan kuma ta juya tana waigen neman Sumayya tace "ina Sumayya? Wata kila ita zata iya rarrashinta"

"Kaga Adam kazo ka mayar dani inda ka dauko ni ko kuma ka kaini inda zaka kaini, ka daina yawo dani a titi" yace "sai kinyi dariya tukunna. Haka kawai dan Ruqayyah tayi aure sai ki zauna kiyi ta kuka har idonki yayi wannan kumburin? Kinga fuskarki kuwa?" ta kuma hade rai "ni bana cikin mood din dariya, dan Allah ka rabu dani" yace "in rabu dake fa kika ce? Kamar fa kina nufin in rabu da wani sashe na jikina in daina amfani dashi kenan fa? Kina ganin haka zai yiwu?" Ta kara hade rai "kaga fa za'a neme ni a can, in aka fahimci yawo na tafi kuma za'a yi min fada. Dan Allah ka kaini, ni jikina bani yake yi kamar Ruqayyah tana nema na" yace "Ruqayyah da aka kai dakin miji, maybe ma suna can suna zuba soyayya ita da mijin ta ke kina nan kin hana ni ganin hakorinki" tace " koma dai me take yi ni ka kaini in ganta, dan Allah" yace "sai kin yi dariya" ta sake hade rai yace "Please, pretty please!" Ta dauke kanta gefe daya sai ya saki stirring ya hade hannayensa alamar roko "Please Please Please" da sauri tace "Adam zaka yar da mu fa?" Yace "kiyi dariya to" ba shiri ta yangare baki daga gani kasan dariyar karya ce, ya kama stirring yana dariya yace "bara dai in kaiki, ba dan halinki ba" sannan ya juya kan motar zuwa gidan su Hussain.

Suna shiga idanunta suka sauka a kan gidan Hussain, ta saki baki tana kallo sai taga kuma gidan Hassan, sannan sai taga sunyi packing a kofar Hassan, ta juya tana kallon gidan Hussain sai kuma ta sake dawowa ta kalli gidan Hassan, tagan shi a bude mutane suna ta hada hada, daga ciki ta jiyo an rangada guda.

Gabanta ya fadi, ta juyo da budaddun idanuwa tana kallon Adam fuskarta da alamun tambaya. Yace "can gidan oga Hussain ne, he Calls himself "dangoten Kaduna" . Nan shine gidan Ruqayyah, gidan oga Hassan kenan. Nan zaki shiga". Sumayya bata jira sauran wani karin bayani ba ta bude kofar mota ta fita da sauri, ko rufewa bata tsaya tayi ba, yace "hey, babu thank you balle goodnight? Kin bar jakarki a ciki" bata ko kalle shi ba ta shige gidan da sauri.

Tun a bakin kofa ta jiyo gunjin kulan Ruqayyah, gabanta ya fadi. Innalillahi, wannan wanne irin rashin ta ido Ruqayyah take nuna wa? Ba tare da tunanin komai ba ta ratsa mutanen da suke palon har zuwa gaban Ruqayyah da har yanzu take durkushe a kasa tana ta risgar kuka da iyakacin karfin ta. Nafisa tace "alhamdulillah, ga Sumayyan nan ma, zo ki yi mata magana ko zata yi shiru" Sumayya ta durkusa a gaban Ruqayyah sannan ta tallafi fuskarta a hannayenta tana jin yadda fatarta tayi zafi, ba tare data ce mata komai ba sai ta kama ta ta mikar da ita tsaye ta rungume ta a jikinta ta fara tafiya tace "ina za'a kaita?" Nan take aka yi mata jagora zuwa Bedroom din Ruqayyah da yake sama. Ta zaunar da ita a bakin gado kamar yadda ake zaunar da ko wacce amarya sannan ta goge mata hawayen fuskarta ta ja mayafi ta rufe mata fuskarta ta kuma zauna a kusa da ita ta rike hannun ta a cikin nata, a hankali Ruqayyah tace "Sumayya, Hassan ya yaudare ni" Sumayya tayi shiru bata bata amsa ba saboda mutane da suka fara shigowa, suna ta tsokanar Ruqayyah da sunan amarya mai kuka, yan uwansu da suka kawo ta suka yi mata sallama abokan wasa suna tsokanar ta, kusan kuma duk wanda yazo yi mata sallama sai ya yabi gidanta "Ruqayyah ki godewa Allah, kinga kyawun gidan ki kuwa? Masha Allah. Wannan miji naki ba karamin sonki yake ba, ki rike kayan ki hannu bibbiyu Allah kuma ya baku zaman lafiya" Sumayya ce mai amsawa da ameen.

Sai da aka ragu saura kawayensu da suke palon kasa suna ta dauke dauken hotuna dan a samu na burga sannan Sumayya ta rufe kofar dakin ta dawo kusa da Ruqayyah ta zauna tace "Ruqayyah me nene hakan kika so ki aikata? Wannan wanne irin abin kunya kika so ki jawo wa kanki ki jawo mana?" Ruqayyah ta bude fuskarta data kumbura cikin dasashshiyar murya tace "abin kunya? Abin kunya kike magana akai? Shin baki kalli gidan can ba? Kin tambayi kanki gidan waye kuwa?" Sumayya tace "ba kaina na tambaya ba, mai motar daya kawo ni na tambaya kuma ya gaya min cewa gidan Hussain ne and so what? Me yasa za ki juya ki kalli gidan Hussain bayan ga gidan Hassan kina cikin sa? Me yasa ba zaki kalli abinda yake hannun kin a matsayin mallakin ki ba sai kike juyawa kina kallon abin hannun wani? Ba ki ji abinda yanuwan mu suke fada ba? Cewa badu taba ganin gidan da yake da kyawun naki ba? Ni ma kuma haka, ban taba shiga gida mai kyan wannan ba, ban taba zama a kan gadon mai kyan wannan ba. Which of the favors of your God do you deny?"

Ruqayyah tace "amma ba kya ganin kasancewar gidan Hussain yafi na Hassan yana nufin ba Hassan ne mai Company ba?" Sumayya tace "and so what? Hassan kika aura ko kuma Company kika aura? Ni I don't get you Ruqayyah. Na kasa gane kanki. Me kike so ne? Hassan mutum ne mai nagarta da kamala da sanin ya kamata, mai addini mai asali mai kyawun sura, mai lafiya mai aikin yi da rufin asiri, no ba rufin asiri ba, mai arziki. What more do you want" Ruqayyah ta mike kamar an mintsine ta tace cikin daga murya "but he made me believe cewa Companyn sa ne. He made a fool of me" Sumayya tayi saurin yi mata alama da tayi shiru, ta na leqa window sannan tace "yaushe? Ban sani ba ko kunyi maganar sanda bana tare daku amma ni ban taba jin ya jingina kansa da H and H ba, ni ban ma taba jin ya ambaci sunan kamfanin ba" Ruqayyah ta dafe kanta tan zama a bakin gado tare da cigaba da kuka tana jin kanta kamar zai tsage, Sumayya ta dawo ta zauna kusa da ita tace "kin taba zama kinyi tunanin ma'anar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login