Showing 15001 words to 18000 words out of 300844 words
ake kira da pistol, bakin bindigar a rufe da silencer. Zai iya cewa bai taba ganinta a zahiri ba sai yau ballantana ya taba ta amma yana ji a finafinai cewa karfenta sanyi ne dashi sai gashi yau ya tabbatar, sai dai abinda basu fada a films din ba shine yadda sanyin yake wucewa har cikin zuciyar mutum. Ya runtse idonsa ya bude, yana tunanin Hussain, ko yaya zaiyi copping da labarin mutuwarsa?
Murya yaji dai dai kunnen sa, cikin rada amma kuma da kakkausan amo "take your hand of the ignition and place it on your head" a hankali yabi umarnin da aka bashi, ta gefen idonsa yaga wani ya bude kofar gefen driver ya shigo, bai juya ya kalleshi ba amma daga yadda motar ta amsa zaman nasa yasan cewa katon gaske ne, yasan ba zai iya tarar sa da fada ba ballantana kuma gashi su biyu ne da wanda ya saka masa bindiga a wuya. Amma yasan da Hussain ne da zai gwada, zai gwada ko da kuwa chances dinsa na winning is 1% in yayi failing ma zai sake gwada wa, amma shi ba zai gwada ba, shi yana analysing situation dinsa ne kafin ya gwada sa'ar sa kuma wannan karon baya jin akwai Sa'a.
Yaji alamar wani ma ya bude baya ya shiga, su uku kenan, yayi shiru yana jiran yaji instructions din da zasu bashi amma basu ce komai ba sai kawai ji yayi wani hannu rike da wani tsumma ya zagayo ta baya ya rufe masa hanci da bakinsa. A jikin tsumman ya shaki kamshin wani abu, kamshin da yayi bringing back memory din lokacin da suka je South Africa shi da Hussain, lokacin da suka je kallon namun daji a reserve dinsu, lokacin da wani tiger ya tsallake shingen da aka yi masa yana kisan sauran dabbobi sai aka watsa masa wani abu mai irin wannan kamshin. Ya tuno sanda ya tambayi mutumin game da abin sai yace masa dashi suke amfani dan suyi knocking down dangerous animals, sai ya gaya musu cewa "masu satar mutane ma dashi suke amfani su fitar da mutum daga hayyacin sa dan suji dadin satarsa" ya tuno sunan da mutumin ya gaya musu "sunan sa chloroform".
Da sauri Hassan ya dauke numfashin sa yaki shakar abin ya kuma fara amfani da hannayen sa dan ganin ya cire tsumman daga fuskarsa amma sai mutumin ya kara danna masa shi wanda ya zauna a gaban kuma ya fara kokarin rike hannayen sa, tunanin Hassan daya a lokacin, tsoron sa daya a lokacin shine kar su sace shi suyi amfani dashi gurin cutar da Hussain. Shi farko ya dauka robbers ne sai yanzu ya fahimci kidnappers ne. Yaji sunyi magana a tsakanin su amma bai fahimci mai suka ce ba sai dai kuma yaji muryar wanda yake bayan tamkar muryar wanda ya sani, wanda ya sani sosai amma ya kasa placing.
Sai yaga sun dauke hanky din daga fuskarsa sannan na bayan ya saka hannayen sa biyu yayi amfani da duk karfinsa ya shake wa Hassan wuya yana toshe masa hanyar wucewar iska zuwa huhunsa, Hassan yaji kamar zai mutu, kwakwalwar sa ta totse kirjinsa kamar ana hura wuta a ciki babu abinda yake so illa ya shaki iska amma sun hana masa, ya yi tunanin this is what suffocating feels like, this is the end of him. Regret dinsa daya a rayuwa shine baiyi aure ya bar yaya ba kamar yadda yake da buri, sai yaji cewa ashe Hussain is right akan kayi komai a lokacin da ka samu dama kar ka jira sai wani lokacin, sannan yayi wa kansa alkawarin indai har yayi surviving the first thing da zaiyi shine aure, duk yarinyar data fara kwanta masa a rai ita zai aura.
A lokacin daya gama saddakar da tafiya lahira a lokacin ne kuma suka cika masa makogwaron sa sannan suka yi placing wannan jikakken hanky din a kofar hanci da bakinsa. Farkon abinda ya fara kokarin yi shine shakar iska zuwa huhunsa da yake ji on fire, wannan yasa ya shaka da karfi, ya kuma shaki abinda baya so din har cikin huhunsa. Ya jima yana shaka, a kokarin sa na dawo da numfashin sa dai dai, a lokacin da numfashin nasa ya fara dawowa dai dai a lokacin ne kuma hankalin sa ya fara gushewa, a lokacin ya fahimci cewa ya shaki chloroform din.
Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741
Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020
Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.
Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only
Episode Seven : Lost
Free Episode
Sai da suka tabbatar jikinsa ya gama saki, suka mammare shi a fuska suka tabbatar babu alamar motsi a tare dashi sannan suka cika shi, suka bude booth din motar suka jefa shi a ciki roughly sannan suka shiga motar suka bar gurin. Babu wanda ya gani, kasancewar babu kowa a cikin building din sai masu gadi guda biyu da sun tafi sallah basu dawo ba, dan haka basu samu matsala ba suka yi tafiyarsu.
Bayan sun hau kan titi sosai ne katon wanda yake gaba yace cikin budaddiyar murya "ina dan uwan nasa yake?" Wanda yake zaune a baya yace "yayi tafiya, ina jin ma ƙasar ya bari" mai tuka motar yace "what? To a gurin uban wa zamu karbi kudin tunda baya nan? Tunda kasan bayanan ba sai ka gaya mana ba mu bari sai ya dawo sannan mu dauki wannan ɗin? Yanzu anything can happen kafin ya dawo din, kuma bamu da number din da zamu same shi a can ɗin" na bayan ya gyara zamansa yana murmushi yace "kun san kuwa yadda yake son dan uwan nan nasa? Da zai san mun dauki dan uwansa a yanzu, da zai iya biyan ko nawa ne dan jirgin da yake ciki ya juyo ya dawo dashi Nigeria" ya karasa maganar yana dariya, na gaban duk babu wanda ya taya shi dariyar har ya gama sannan katon yace "to yanzu ta yaya zamu gaya masa mun dauki wannan ɗin" na bayan yace "Hassan ba zai rasa wayar sa a jikinsa ba, Hussain yana sauka wanda zai fara kira ya gaya wa ya sauka shine Hassan, mu kuma sai mu dauki wayar.....ina tabbatar muku da cewa next jirgin da zai dawo Nigeria da Hussain a cikin sa" ya sake yin wata dariyar "nasan mutanen nan kamar yadda nasan tafin hannuna".
Babu wanda ya kula shi a na gaban amma kuma duk sun yarda da abinda yace, a hankali suke tafiya da motar da normal speed dan gudun jan hankalin mutane zuwa gare su, har suka yi nisa sannan suka sauka daga titi suka fara shiga cikin unguwa, unguwar rimi, suka ringa wuce gida je har suka zo wani incomplete gida, suka shigar da motar cikin kofar da ba'a saka wa gate ba suka yi packing, na bayan motar ne ya fita ya tsaya yana yi musu gadi su kuma biyun suka bude booth suka fito da Hassan suka shiga dashi cikin gidan zuwa wani daki sannan suka bude kofar bandakin da suka riga suka yiwa aiki suka saka mata lock suka jefar dashi akan simintin toilet din, sannan suka dauko igiyar su da suka riga suka tanada suka daure masa hannayensa a bayansa suka kuma hada ƙafafuwan sa guri daya suma suka daure sannan suka dauko masking tape suka nannade masa bakin sa. Sai da suka gama sannan suka lalube jikinsa sula cire wayoyinsa da ID cards dinsa da duk abinda yake jikinsa, suka dauke shi hoto da wayarsa sannan suka fita suka rufe kofar dakin da key.
Suna fita katon ya jefa wa wanda ya zauna a bayan motar key din motar yace masa "discard the car, kafin safiya nasan police zasu fara neman ta".
************************************
Washegari Saturday, babu school, dan haka kamar yadda yake alada a gidan Inna Ade tunda suka tashi sukayi sallar asuba sai suka zauna suna tilawar karatun Alqur'ani har gari ya waye, sannan suka fara ayyukan gida. Yammatan suna gyaran gidan wanda kusan kullum kalkal yake cikin tsafta, ita kuma inna Ade ta hada wuta ta dora musu dumamen tuwo ta kuma kunu. Tana saukewa kuma ta dora musu ruwan wanka. A lokacin ne Baba ya fito daga daki da radiyo a hannunsa, Sumayya ta shimfida masa tabarma ta saka masa pillow ya zauna, duk suka gaishe shi. A lokacin samarin suma suka shigo duk suka gaishe shi ya amsa.
Inna Ade tace "Baban biyu yau ba zaka fita bane ba? Naga ka dauko radiyo" yace "zan fita, labarai dai nake so inji ko zanji sanarwar sunayen wadanda aka dauka aikin nan da muka je nema jiya" Sumayya tayi dariya tace "Baba jiya fa kuka yi interview din, daga jiya zuwa yau har a sanar da wadanda suka ci?" Yace "ahau, ba aikin kamfani bane ba, ai su basu da bata lokaci sha yanzu ne magani yanzu ba kamar aikin gwamnati ba da za'a yi ta fama kamar cin kwan makauniya. Su kuwa wadannan tunda sunyi mana intabiyu shikenan" yaran duk suka kwashe da dariyar yadda yayi pronouncing interview din, yayi musu dakuwa yace "ku ungo ku raba, ni kuke wa dariya" Ruqayyah tace "Baba interview ake cewa ba intabiyu ba" yace "ko ma inta uku ne ku kuka sani,ni dai abinda na sani shine a bani aiki kawai, kunga inna samu aikin gadin nan sai innar ku take yi min abin siyarwa ina tafiya dashi ina siyar mata a bakin gate" Zunnur yace "baba ni zan taya ka dauka" Baba yace "makarantar kuma fa?" Sumayya tace "Baba ni zan daukar maka tunda kaga mu mun kusa gamawa, kafin ka fara aikin mun gama sai in ke kai maka" yayi murmushi yace "Husaina in dai har ina da rai kuma ina da lafiya ai ba zaki yi talla ba. Har kar neman kudin da zaki yi idan ba sana'a a gidan mijinki ba to sai dai aikin office" Inna Ade tace "allahumma ameen Baban biyu, Allah ya nuna mana wannan rana ya Allah" yace "ameen. Kinga yaron da yayi mana intabiyu din nan, wallahi ya burge ni sosai yaron nan, sai naji ya kwanta min a rai ina kallon sa nace Allah ameen, Allah ka muna min Suleiman dina watarana kamar haka. Dan saurayi dashi fa wai amma shine mai gurin gabaki daya" Suleiman yace "Baba ba H & H ba? Ai yanzu su suke tashen kudi a garin nan, wannan kamfanin da za'a bude na goma kenan fa kuma ance ogan ko aure bai yi ba" Ruqayyah tace "kai Suleiman banda kari, yanzu har sunyi goma?" Sai kuma ta langwabe kai gefe tace "sunji dadin su, wasu mutanen da sa'ar su suke zuwa duniya" Baba yana kallonta yace "Hassana ni banji kin ce zaki tayani daukan kayan abinci mu siyar a bakin gate ba" ta sunkuyar da kanta tana zuba kunu a cup tace "Baba in nace ma cewa zakayi a'a shi yasa ban ce ba" ya dauke kansa yana maida hankalinsa kan tuwon da Inna Ade ta ajiye masa a gabansa yace "insha Allahu ina samun aikin nan zan fara tara kudin da zan biya muku kudin jami'a. Insha Allahu ba zan kasa biya muku ba kamar yadda na kasa biya muku kudin wannan jarabawar".
Kasa kasa Ruqayyah tace "hmmm. Allah yasa. Necon ma dam gwamnati ce take biya da cewa za'a yi ita ma mu hakura babu kudi" Inna Ade tace "me kike cewa ne Ruqayyah?" Ta dago kai tace "cewa nayi Allah yasa, Allah yayi jagora" duk suka amsa da ameen.
A bangaren su Aunty kuwa da safe, Aunty ta sauko daga samanta idanun ta akan dining table tana lura da cewa ba'a taba abincin gurin ba, tasan kuma Hassan kullum shine na farkon tashi a gidan dan kusan kullum akan dining take samunsa. Ta karaso tana bude warmers din taga babu alamar an taba abincin. Ta ja kujera tana kwalla wa Safiyyah kira amma maimakon taji ta amsa daga san su sai taji ta tana amsawa daga bakin kofa, da alama daga waje take, Aunty tabi fuskarta da kallo har tazo ta zauna a kusa da ita tace "wai har yanzu baki samu number din Hassan ba?" Safiyyah ta ce "ban samu ba Aunty. Da daddare wayar tana shiga amma yanzu da safe a kashe take" Aunty tace "je ki duba mim dakinsa, tashi da sauri" Safiyyah bata motsa ba fuskarta kamar zata yi kuka tace "daga can nake aunty. Yaya Hassan bai kwana a gidan nan ba, motar daya fita da ita ma bata nan. Tun daya fita kafin magriba mai gadi yace bai dawo ba".
Aunty tayi shiru tana kallon gefe daya, sannan kuma sai tayi saurin dauko wayarta tana kiran Hassan, switch off taji, ta katse kiran ta ajiye wayar tana jin yunwar data sauko da ita tana guduwa tana barinta. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ta ringa fada tana maimaita wa "ina yaron nan ya tafi? A ina ya kwana?" Tunda take da Hassan bai taba kwana ba'a gida basao lokacin da yana makaranta kuma shima dan a hostel ya zauna. Ta juya tana kallon Safiyyah wadda idanunta suka cicciko da kwalla tace mata "maza ki kirawo min Jabir" Jabir shine babban abokin Hassan wanda kuma za'a iya cewa shine kadai abokin sa bayan Hussain, shine kuma saurayin Safiyyah.
Ta dauko wayarta ta nemo number din Jabir da kyar saboda hawayen da ya lullube mata idanunta ya rage mata gani. Ta kira ta saka a handsfree, yana dauka tace "yaya Jabir ina kwana? Aunty ce take tambayar ko kuna tare da yaya Hassan, bai kwana gida ba" shirun da Jabir din yayi shi ya tabbatar musu da amsar sa, basa tare, Safiyyah ta fara kuka sosai, Aunty ta karbi wayar daga hannunta tace "Jabir ba kwa tare ko?" Ya danyi gyaran murya yana kokarin boye tashin hankalin sa yace "bama tare Aunty, tun jiya da safe dana raka shi yayi interviewing kananan ma'aikatan kamfanin su ban kuma ganin sa ba, na kira wayarsa dai da daddare bai dauka ba sai nayi tunanin ko har yayi bacci lokacin, da wacce motar ya fita?" Aunty ta gaya masa sai yace " bara in zo gidan, amma ku kwantar da hankalin ku, bara in kira Khalid, maybe gidan su ya kwana kuma maybe bashi da charge" ya fada cikin kokarin sa na ganin ya kwantar musu da hankali amma tabbas shi nashi hankalin ya kai kololuwar tashi. Aunty tace "Khalid? In kwana yayi a gidan su Khalid din kuma bashi da charge mai yasa ba zai karbi wayar Khalid din ya kira mu ya gaya mana ba? Wannan ba halin Hassan ba ne ba. Hassan zaiyi tunanin cewa ya kamata ya kira ya fada. In Hussain ne ba zan damu ba" ta danyi shiru sannan ta dora da tambayar "waye ma Khalid din?"
Jabir yayi saurin kashe wayar,shima baisan wani Khalid ba kawai sunan ne ya fado masa kuma yana son kwantar mata da hankali ko da ta hanyar karya ne. Ya zauna a bakin gado yana dafe kai. Tabbas babu lafiya, Hassan ba zai taba tafiya wani gurin ya kwana ba sannan ya kwashe wayarsa. Ko wanka baiyi ba ya fita, duk inda yasan suna zuwa da Hassan ko wanda yasan suna harka da Hassan sai da ya nema amma babu wanda ya gan shi. A karshe dai ta tafi police station ya sanar wa yan sanda ya kuma basu description din Hassan da kuma motar da ya fita da ita. Anan ya bata lokaci da yawa, saboda police suna fahimtar waye Hassan din suka daukaki maganar kuma abinda suka fara kawowa shine kidnapping. Sai wajen azahar sannan yaje gidan Aunty ya same ta ita da yara sunyi kuka har gode Allah. Ya yi musu bayanin duk abinda yayi sannan yace "ku kwantar da hankalin ku dan Allah. Police sun riga sun shiga maganar nan kuma sun bazu gurin nemansa a lunguna da saƙunan jahar nan, an bada cigiya gidajen rediyo da talabijin duk an baza hotunan sa. An aika asibitoci suma da mortuary duk za'a duba" Zulaihat ta saka kuka tace "mortuary kuma Yaya Jabir?" Ya dafe kansa yace "baya can Zulaihat, dubawa kawai za'a yi amma baya can" tace "to in baya can me yasa za'a neme shi a can?"
Yayi kokarin kawar da maganar ta hanyar tambayar "ina Hussain. Aunty ta dago kai daga kallon charbin hannunta tace "Hussain ya tafi China Jabir. Har yanzu kuma bai kira mu yace mana ya sauka lfy ba, shima bamu san halin da yake ciki ba" ta karasa tana goge hawayen idanunta.
Da yamma a gidan Inna Ade. Inna Ade tana yiwa Ruqayyah kitso Sumayya kuma tana tsefe nata kan. Suleiman da Zunnur suna gefe suna dorawa wasu yara karatu sai ga Baba ya fito daga daki fuskarsa dauke da tashin hankali, hannunsa rike da radiyo. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Maman biyu kinji wai an sace shi. Yanzu shikenan ya bata sai kace ba mutum ba? Sai kace wata jaka?" Inna Ade ta saki kitson da take yi tana dafe kirji tace "wa aka sace baban biyu? Waye ya bata?" yace "yaron nan da na ce miki na jishi a raina kamar Suleiman, yaron da muka je neman aiki gurin sa, mai sabon kamfanin nan, yan zu ake sanarwa a gidan radiyo wai tun jiya ba'a ganshi ba ana tunanin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa dashi".
Gabaki daya suka dauki salati. Inna Ade tace " wannan wacce irin rayuwa ce muke ciki a yanzu? Dan adam ba'a bakin komai yake ba, talaka bai tsira ba mai kudin ma bai tsira ba. Ubangiji Allah ka bayyanar dashi, Allah ka hana azzalumai yin zaluncin su a kansa, Allah ka kare shi ka kare mu baki daya. Allah sarki iyayensa, har naji tausayin su wallahi. Allah ka bayyanar musu dashi in kuma ya mutu Allah ka sa su ga gawarsa" gabaki daya suka ce ameen.
Ruqayyah tace "at least