Showing 300001 words to 300844 words out of 300844 words
cinyarsa tace "kaima ka dana, duk munyi iyayin mu taki yin shiru, ya ajire diary din a gefe ya daga babyn, "Fatima Zahra, waye ya taba min ke duk garin nan yanzu mu mai ruwa rana ni da shi" Amatullah ta shigo hannun ta rike da afnan ta zauna a gefensa tana hamma "wa ya tabata kuwa in banda rikici?" Sultan ya shigo ya zauna a gaban babansa yace "a cigaba da karanta mana diary din grandfa" Amir yace "yauwa dan albarka, itama Fatima abinda take so kenan, tana son jin kalmomin mijinta yanzu zakuga tayi shiru" Aysha ta zauna itama a daya side din nasa tace "to a karanta mana muji" sai ya bude page din da yake ya cigaba da karanta wa daga inda ya tsaya.
Dear baby
Duk rubutun da zan yi maka daga yanzu zai iya zama abu na karshe da zan gaya maka. Rayuwa ta kadai ta isa nasiha a gare ka akan cewa babu wani abu da yake da tabbas, lokaci ne kawai yake da tabbas sai dai mu bamu da tabbas din kaiwa zuwa lokacin, an rigaan kayyade wa kowa iya kacin adadin seconds da zai yi a duniya kuma duk yawan kudin daka tara, duk kyawun fuskarka, duk yawan masoyanka da makiyanka, duk martabar ka, duk yawan ibadarka da rokon Allahn da zana yi akan ya kara maka kwanaki a duniya ba zaka wuce wadannan seconds din ba. Kowanne dan Adam yana tafiya ne akan nasa lokacin, dan wani yayi kudi da wuri ya sayi katon gida da manyan motoci ya auri kyakykyawar mace yar nasaba ba lallai ne shine successful man a duniya ba, maybe shi kwanaki kadan aka kayyade masa da kuma arziki da yawa, wannan shi yasa yayi arziki da wuri dan ya cinye arzikin sa kafin lokacin sa ya cika.
Wani kuma sai yayi ta neman kudin da karfin sa da kwakwalwar sa amma sai ya dauki dogon lokaci bai samu ba kuma zata iya yiwuwa shi mai tsahon rai ne, dan haka yake cin arzikin sa kadan kadan. Wani kuma a wahala zai fara kuma a wahala zai kare saboda tasa kaddarar kenan. Babu wanda yake sauri babu kuma wanda yake lakaki, kowa yana tafiya ne akan lokacin sa.
Shi arziki ba komai bane ba illa wata hanya da ubangiji yake jarabtar bayinsa, sai ya baka kudi yaga abinda zaka yi dashi ko kuma ya hana ka yaga abinda zaka yi. Ida har ka nemi kudi ka samu to Allah ne ya baka, idan kuma baka samu ba to shine ya hanaka. Idan ka samu dama ka nemi kudi ta hanyar halak, idan zaka kashe su ka kashe su ta halak. Idan kana dashi ka taimaka wa wanda bashi dashi, idan baka dashi ka nemi na kanka ta hanyar halak kar ka zama mai matacciyar zuciya ko mai roko a gurin mutane.
A duk lokacin da dama ta same ka tayin wani abu to kayi shi a lokacin kar ka jira sai wani lokaci, dan ba kai kake da lokacin ba. Duk abinda kaji kana son yi to kayi abinka, as long as bai sabawa ubangijin ka ba kuma ba zai zamanto cutarwa ga wani abin halitta ba ba to kayi abinka kar ka damu da abinda mutane zasu ce dan su mutane ba'a taba iya musu, in kabi ta tasu ba zaka yi achieving komai ba.
Ka zauna da clean heart, kar ka nufi kowa da sharri kar kuma ka rike kowa a ranka, always think positive dan shi negativity yana huda zuciya ne ya kuma hana ka ganin alkhairi ko da yana gabanka
Bana tunanin halin da zan barka saboda nasan na barka da best mother in the world da kuma best father in the world. Na san ko ban bar maka ko kwandala ba Hassan zai iya yin dako ya ciyar da kai. Dan haka indai a kan wannan ne bani da damuwa"
*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*
Anan na kawo karshen wannan littafin mai taken TAGWAYE. Alkharin da na rubuta Allah ya hada mu a ladan ni da ku bakiɗaya. Kurakuran da suke ciki Allah ya yafe min ni da na rubuta da kuma ku da kuka karanta.
Godiya mai tarin yawa da masoyan rubutu na a duk inda suke. Musamman wadanda Allah ya bawa ikon siyan wannan littafin, it really means a lot to me, Allah ya bar kauna.
Zuwa ga wadanda suka fara biyana da niyyar zasu karasa kafin in gama littafin, na yafe muku sauran.
Zuwa ga wadanda suka karanta littafin tagwaye ba tare da sun biya ba, na yafe muku, amma ku sani wannan ba shine hanyar nuna kaunar ku gare ni ba. Like I always say, it is not about the money, it is about loyalty.
Zuwa ga wadanda suka sayi littafin nan bisa amana kuma suka fitar dashi zuwa groups. Ku da Allah.
Sai mun hadu a sabon littafi na mai suna *Jidda* in Allah ya kai mu da rai da lafiya.
Nagode. Taku har kullum.
*Maman Maama*
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020