Showing 63001 words to 66000 words out of 300844 words

Chapter 22 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2063

H and H?" Ruqayyah ta juyo tana kallonta amma bata ce komai ba, ita bata taba tunanin me yake nufi ba. Sumayya tace "ni ma ban sani ba, but ina tunanin Hassan da Hussain yake nufi" Ruqayyah tayi saurin cewa "meaning nasu ne su biyu right?" Sumayya tace "maybe, maybe not, but you will soon find out tunda kin auri daya daga cikin su. Am sure zai gaya miki koma na waye a cikin su. But Please Ruqayyah ki kwantar da hankalin ki, dan Allah kar ki nuna masa cewa hakan wani abu ne"

Ruqayyah ta rike hannunta tana hawaye "dan Allah Sumayya ki kwana anan. Ni goben nan tsoron zuwa Kanon nan nake ji, ban san me zan gani ba acan. Dan Allah ki zo muje tare" Sumayya ta goge mata hawayenta tace "tare zamu tafi, na taho da kayana ma jakata can a mota, tare zamu tafi ba zan tafi in barki ba. We are going to get through this together" ta samu ta lallabata ta kwanta sannan ta fita neman Adam ta karbi jakarta. Sai kuma ta sanarwa da kawayensu na kasa cewa Ruqayyah bata jin dadi ta kwanta bacci. Amma sai suka bita da tambayar "nan ne gidan Ruqayyah? Can kuma gidan waye? Ko gidan dan'uwan mijinta ne da ake bikin su tare? Waye mai Companyn ne wai a cikin su? Ruqayyah tace mana mijinta ne CEO haka ne?"

Da sauri Sumayya tayi excusing kanta tace bako ne da ita a waje ta fita, a ranta tana tunanin tabbas baki shine yake yanka wuya, Ruqayyah ta saka igiya ta daure wuyanta ta mika wa mutane bakin igiyar.

Bayan saukar Sumayya ne wayar Ruqayyah tayi kara, ta daga kai da kyar tana kallon sunan Hassan a jikin screen din "mijina" kamar yadda tayi saving. Tayi tsaki tana jin wutar data kwanta a kirjinta tana dada ruruwa. "Munafiki" ta fada a fili sannan ta kife wayar ta juya bayanta. Can kuma sai ta juyi ta daga wayar ta saka a kunnen ta "hello" ta fada da murya mai sanyi. "Hassana" ya fada da murya mai cike da conceri. "Yanzu Aunty ta kira ni tace kina ta kuka wai ko zan zo in rarrashe ki. Me ya faru? Waye ya taba min ke inzo in nuna masa matsayin sa?" Ruqayyah tayi shiru, a ranta tace "kamar gaske" yace "Please kiyi min magana mana inji dadi, in baki magana ba yanzu zan ajiye duk abinda nake yi in taho" a hankali tace "kana ina?" Yayi murmushi yace "gidan yafi karfin mu, baki sunyi yawa shine muka kama hotel mu da friends din mu. Kin gansu ma duk suna ta tsokana ta wai na kasa rufe baki saboda an kawo min amarya ta" bata ce komai ba saboda bata jin zata iya gaya masa magana mai dadi, dan haka shirun yafi. Yace "ba zaki gaya min abinda ya saka ki kuka ba? Ko sai nazo na gani da idona? Inji kuma da kunne na?"

Ta gyara kwanciyar ta tan jin cewa bata son ganinsa kwata kwata, at least not today, tace "na dauka a can zakuyi zamanku? Tunda nan din akwai mutane da zasu kwana saboda tafiyar da za'ayi kano gobe ko?" Ta shafa kansa yana runtse idonsa yace "yeah, right. Haka ne. But what about siyan baki and other traditional stuff?" Tace "it can wait ai......jibi in akayi dinner din kowa kaga zai watse ai, sai ku zo kuyi ta siyan bakin ku" yace "hakane......but ni kuma fa? Shikenan ba zanga matata ba? Ni fa yanzu ba gwauro bane ba fa" tace "ko? You will see me tomorrow ai in ka shigo da wuri kafin mu tafi" yace "ni ba wannan ganin nake nufi ba ai....." Tayi shiru, yace "ko abinda kike wa kuka kenan dazu?" Tace "good night" yayi ajjiyar zuciya yace "to ya zanyi da raina, ba haka dai aka so ba" tace "kanin miji ya fi miji kyau ba".


Wannan littafin na siyarwa ne, duk wanda yake so ya neme ni through WhatsApp ta wannan number din 08067081020

Episode Twenty Two: Envious

Thank you so much for the birthday wishes. I had a great day, and you guys contributed a lot to that.

Nayi mistake din numbering, na shekaran jiya twenty ne na jiya twenty one na yau kuma twenty two.

Muna ta Allah wadai da halayen Ruqayyah, ina fatan muna tsintar pieces of halayyar mu a cikin nata.
Idan kina jin haushi a yayin da wani ya samu daukaka kina jin ina ma ke ce ba shi bane ba.
Idan kina kallon saurayin kawarki kina jin ina ma dai naki ne ba nata ba.
Idan kina jin bacin rai idan kika ga business din wata ya bunkasa ba naki ba, ko wata ta chanja kayan dakinta ke bami chanja ba, ko wata ta sayi kaya ke kuma baki da kudin siya.
Idan kina jin dadi a ranki idan wani ya samu wata matsala.
Wadannan duk kadan ne daga cikin siffofin hassada.

Hassada daban kishin kai daban, kishin kai shine ki nemi na kanki a lokaci guda kuma kina yiwa sauran masu neman kansu wadanda suke sama da ke da wadanda suke kasa dake fatan alkhairi.

Yar uwa, a duk lokacin da kike kallon na sama dake a samun abin duniya to zai toshe miki idanuwanki ki daina ganin kyawun abinda yake gabanki, abinda kike dashi, wannan kuma shi zai sa ki zamanto marar godiyar ubangiji.

Yar uwa ki kalli na kasa dake, ki duba dubunnan mutanen da suke fatan su samu daukaka irin taki, wannan zai saka ki samu wadatar zuci.

Irin wadannan halayen baka sanin kana dasu har sai kayi nisa a cikin su. A lokacin kuma sun riga sun bi jini da tsokar jikin ka.

Yes, akwai mutane irin Ruqayyah and they walk amongst us

*******************


Da kyar Sumayya ta samu ta lallaba kawayen da mostly Ruqayyah hayar su tayo, ta gaya musu babu siyan baki yau sai ranar lahadi, farko suka ki tafiya suka ce ai dare yayi sai dai su kwana da safe sa tafi, ita kuma tasan indai suka kwana din to kuwa cewa zasuyi sai anje dasu kano kuma Allah kadai yasan abinda zasu aikata acan din. Ba zata dauki wannan chance din ba, dan haka ta koma sama ta samu kudi a gurin Ruqayyah ta kuma lallabasu dashi, sannan ta fita waje ta samu Adam "Adam da Allah a cikin drivers din gidan nan ka samu wani ya mayar da mutanen Ruqayyah gida" yace "ohhh okay, gani ai, kim manta nima drivern gidan ne?" Ta nuna shi tace "banda kai, someone else" yana murmushi yace "why? Ba kya so insha wahala?" ta juya kamar zata bar gurin sannan ta juyo tace "saboda yammata ne" ta shige da sauri tana jin sa yana mata dariya.

Washegari da sassafe aka aiko su bayar da kayansu, wai kayan duk a mota za'a hada su tare da motar da zata dauki kayan lefe, su kuma in sun shirya sai su bi jirgi. Ruqayyah ko hada kayan bata yi ba, sai a lokacin Sumayya ta taimaka mata suka debi wadanda ta saka da bikinta tunda bata dinka lefe ba kuma kayanta na gida duk ta barsu a gida saboda bata bukatar su. Suka hada akan kayan Sumayya a yar karamar jakarta suka bayar. Sai a lokacin sannan Sumayya ta jawo Ruqayyah da kyar suka fito zasu zagaya gida. Tun daga kan Bedroom din da suka kwana a ciki, daya Bedroom din wanda suke tunanin na Hassan ne amma daga alama shima bai tare ba tunda babu kayansa komai a ciki sai dai set din furniture shigen nata sai banbancin design da color. Suka zagaya katon palon da yake sama mai hade da dining room, su kansu set din dining din abin kallo ne, sannan suka sauko kasa suka duba three bedrooms din da suke kasan kowanne in suka shiga sai Sumayya taga kamar yafi ba baya kyau, Ruqayyah kawai binta take yi fuskarta babu yabo babu fallasa, suka dawo falon farko komai Sumayya ta gani sai tayi ta kambamawa dan ta jawo hankalin Ruqayyah har ta samu ta dan fara yabawa da kalmomi irin " eh, yayi kyau" duk kuwa da cewa bata bata ganin makamancin shi ba ballantana wanda ya fishi.

Suka shiga kitchen Sumayya tana ta santin kitchen din da duk kayan da suke ciki, sannan suka fita waje ta kofar baya Sumayya tana yaba shuke shuken da akayi a surrounding area din, flowers masu kyau da kamshi aka zagaye backyard din gidan dasu, gidan Hassan mai kyau ne, mai matukar kyau ne, sai dai ace masa karami, kankantar ma za'a fada ne in akayi comparing da gidan Hussain. Amma sai Ruqayyah ta daga kanta kana kallon gidan Hussain, ita so take ta shiga ciki taga menene a cikin wannan katoton gidan, tasan anyi wa gimbiya jere so take taga dame dame aka saka mata, so take taga sun kai nata kyau ko kuma sunfi nata? Sumayya ta kama hannun ta suka koma, tanata yi mata hirar yadda mutane suka yi ta santin gidan har suka koma dakin ta sannan Sumayya ta cire kayanta ta shiga bandaki zata yi wanka. Kayan bandakin ma sai data yi ta gwadawa kafin ta iya gane yadda zata yi amfani dasu. Bayan ta shiga toilet din ne sai Ruqayyah taga kofa a tsakanin windows, ta saka hannu ta bude ta shiga. Nan take taji farin ciki ya kamata "a balcony!" Madaidaicin balcony ne mai kyau da tsari, railers din sa kawai abin kallo ne ga set din kujerun hutawa da dan karamin teburin su. Ta zauna akan kujera daya tana murmushi, sai ta juya da niyyar ganin gari, da niyyar ganin Kaduna a kasan ta amma sai taga gidan Hussain yayi bakevake ya tare mata hanya. Ta daga kanta tana hango karshen gidan sai taga balcony a can karshe, meaning idan matar Hussain ta fito ita ma ta fito to matar Hussain zata ke hango ta a kasanta. Taji zuciyarta ta buga, ranta ya baci, hankalin ta ya tashi. Ita gidan Hussain take so, wancan balcony na sama shi take so ba wannan ba. Ta mike da sauri ta shige ciki ta rufe kofar ta murda key sannan tazo ta wuce Sumayya da take ta santin closet din data bude duk da babu kaya a cikin ta, ta shiga toilet, ta jefa key din a toilet tayi flushing dinsa.

Suna gama wanka Aunty ta sake aikowa tace su tafi can main house din suyi breakfast, suka shirya sama sama sannan suka fita tare da yar aiken data ce musu ita cousin din su Hassan ce. "Mamana ita ce Hussainar Maman su yaya H1" ta fada proudly, kawai sai Ruqayyah taji yarinyar bata yi mata ba duk kuwa da cewa bata yi mata komai ba. Sumayya tace "hmmm. Lallai kice akwai twins da yawa a wannan family din" ai kuwa kamar ta tsokano Magana sai ta fara lissafa mata su, gidan Aunty wance gidan gwoggo wance gidan auncle wane, Sumayya tace "haka kuke da yawa ashe? Lallai Ruqayyah kina da aiki a gaban ki. Duk sai kinyi kokari kin gane su saboda gaba" yarinyar tace "au wai ba ke ce yayar tamu ba? Ni fa ba gane ku nake yi ba" Ruqayyah tace "in dai kika yi magana kika ji an cika miki kunne da surutu to ba ni bace ba" Sumayya tace "in dai kika yi magana kika ji an baki amsa gida daya an dauke kai to ita ce yayar taki" duk sukayi dariya. Suka wuce ta gaban gidan Hussain sannan suka shiga wani dan karamin gate da akayi a tsakanin gidajen guda niyu yadda ba sai an zagaya ta babban gate ba, suka shiga main gidan su Hassan, inda Aunty take.

Suna shiga suka tarar gidan a cike da yan uwa, ana ta hayaniya. Nan da nan aka fara drama din banbance Ruqayyah da Sumayya, a karshe har sai da aka kira Hassan a waya aka ce ya fadi bambanci guda biyar. Nan ya fara jero musu "nutsuwa, kunya......" Suka katse shi, physical banbanci muke so kafada mana ba abstract ba" yayi dariya yace "let me close my eyes and think. Kunga na farko fuskar Ruqayyah tafi ta Sumayya tsaho, idanuwan Ruqayyah kwantattu ne na Sumayya kuma zagayayyu ne, lips dinsu ma ba iri daya bane, na Ruqayyah sunfi siranta na Sumayya sunfi kauri. Sannan Sumayya ta danfi Ruqayyah kiba kadanita kuma Ruqayyah tadan fi ta tsaho kadan. Hassana ta bata da yawan magana sosai, tana dai da yawan murmushi, Sumayya kuma tana dariya as much as she talks".

Duk mutanen gurin suka kwashe da dariya. "Wallahi to kowa ya jika a gurin nan har su Aunty" ya kashe wayar yana dariya. Kowa a gurin jan su yake a jiki, ana ta nan nan dasu, aunty tayi wa Sumayya godiya data zauna a tare da Ruqayyah. "In kina nan zata fi sakin jikin ta, tunda ita ba mai magana ba ce ba sosai"

Suka yi breakfast tare da family ga baki daya, sannan aka fara shirye shiryen tafiya, aka kai su Ruqayyah dakin yaya Hassana akace su shirya a can. Suna ta tunanin wadanna kayan zasu saka, su a niyyar si na jikinsu da shi zasu tafi dan a cikin sababbin kayansu suka dauko, amma sai sukaji ance suje su canja kaya su shirya. Ma'ana na jikin nasu basu yi ba. Suna cikin tunani sai ga kaya an kawo wa Ruqayyah, iri daya Aunty tayi musu ita da Hassana tunda sune amare, Ruqayyah ta saka doguwar rigar jan lace din mai kwalli tana kallon kanta a mudubi, tana noticing yadda shape din jikinta mai kyau ya fito sosai a jikin rigar, ashe duk tailors din da suke yi mata dinki bata mata kaya suke yi?

Ita kanta tasan tayi kyau sosai duk da bata yi kwalliya ba, amma kuma sai taji a ranta tana tunanin ko gimbiya fatima zata fita kyau? Ta dai ga tana da kyan fuska a hoto, ko tana da kyan jiki irin nata? Sai kuma taji tana fatan ya kasance bata da shi din da at least ya kasance ta fita da wani abu. "Ai babu wanda yake perfect" ta gaya wa kanta. Bayan ta gama shiryawa ne sai akace tazo ayi mata kwalliya, mai kwalliya ce aka dauko ta Musamman zata yiwa amare sannan da wata wadda zata yi wa sauran mutane duk mai so. Aka yiwa Hassana sannan aka yiwa Ruqayyah aka daura mata head, Ruqayyah ita kanta data kalli kanta a madubi bata gane kanta ba. "Dama haka take da kyau amma tsumma ya boye mata shi?" Tayi murmushi, tabbas tasan tafi gimbiya Fatima kyau.

Sumayya ma taje aka gyara mata tata fuskar akayi mata simple makeup, tayi kyawunta ita ma sosai da sosai. Ana ta hidimar shiryawa sai ga angwaye sun shigo tare da abokan su, suka je gurin su Aunty suka gaishe su aka yi ta saka musu albarka sannan akayi hotuna, Aunty ta aika aka kirawo su Ruqayyah, Ruqayyah ta taho idonta a kasa hannunta rike da jakarta, tana takawa a hankali yadda duk hankalin mutanen gurin ya dawo kanta. Hassan ya juyo ya kalle tavsai ya dauke kai, sai kuma ya sake juyowa da sauri yana kallon ta, wai Hassanar sa ce wannan, jinyake kamar ya rashi yaje gurinta ya gaya mata irin kyawun da tayi a idonsa amma yana jin nauyin iyayensa da suke gurin, sai ya bo ta da idanu kawai, a ransa yana jin dadin mayafin data saka ta rage bayyanar surarta. Nan akayi ta jera su ana daukan hotuna dasu, iyaye kowa ya shigo ayi dashi haka kanne ma da sauran yan'uwa. Anan Ruqayyah taga Hussain. Kaya iri daya suka saka shi da Hassan amma sai taga kamar tasa shaddar tafi haske ta Hassan tayi duhu, ko dan hasken fatarsa ne? Ko kuma a idonta ne taga hakan. Fuskarsa cike da annuri, idanunsa suna haske, dimple dinsa yaki komawa saboda murmushin da yaki daukewa daga fuskarsa. Kowa a gurin in ya gaishe shi sai ya ambaci sunansa kuma ya tambaye shi a game da wani abu daya shafe shi, ma'ana yasan kowa kenan, yasan affairs din kowa, kuma sai taga kamar yan uwan sunfi tafiya inda Hussain yake akan inda Hassan yake, ko ita ce take ganin haka?

Sai da aka shigo aka tuna musu da cewa lokaci fa yana tafiya sannan suka bar hotunan haka. Sai a lokacin Hassan ya samu magana da Ruqayyah. Yana kallon fuskarta yace "kinyi kyau sosai matata" tayi murmushi tace "kaima kayi kyau mijina" ya danyi gajeriyar dariya yace "maimaita in kara ji" ta saka hannu ta rufe fuskarta tare da dan juya bayanta kadan. Yayi dariya "zanji ne ai, one way or another. Kinsan wani abu?" Ta bude fuskar tana girgiza kai, yace "ji nake kamar in fasa zama in biku kanon nan" ta ji ranta ya fara baci "zaka bi mu kuma? Kai fa kace hutawa zaka yi" yace "yadda naga kwalliyar nan anya zan iya zama in sake kwana ina rungumar pillow" ta sake juya masa baya "kai dan Allah!" Sai kuma ta juyo tace "In ka bimu ma fa ba tare zamu zauna ba, ku kuma waje ko kuma kuna hotel mu muna cikin gida. Ni nafi si kayi zamanka anan kar kabi Hussain da abokansa su zo suyi ta wahalar da kai" yana murmushin gefen baki yace "really?" Tace "eh mana. Kaga gobe daurin aure biyu ne daku ga dinner da dare. You rest today" ya daga murya yana kiran Hussain "ka ga inda aka damu dani ake so in huta, kai kana mitar nace ba zan je ba ita tana cewa inyi zamana in huta" Hussain ya juyi yana kallon su sannan yace "soyayyar da muke yi maka ce daban daban, ni nafi sonka by my side through thick and thin, ita kuma ta fi son ta sha wahala ita kadai kai kuma ka huta" ya dauke kansa, Hassan yayi dariya yana ce mata "fushi yake yi wai nace ba zan je ba. I think zan je ɗin kawai, kar ransa ya kara baci" tayi shiru tana hararar bayan Hussain a fakaice, shine


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login