Showing 138001 words to 141000 words out of 300844 words

Chapter 47 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2068

Taimakon me?" Ruqayyah tace "ina neman wanda zan aika kano, a sirri, wanda zan aika din bana son ya san ni zan aike" Minal tayi dariyar "me kika kulla wa?" Ruqayyah tace "ke dai bari, ina ganin na samo hanyar da zan kori wannan yaron daga gidan nan, kuma in raba shi da Sumayya" Minal tace "wanne yaron fa?" Ruqayyah tace "Adam. So nake ki samu wani ki aika shi kano on my behalf, yaje unguwar badawa layout gida mai number 49 ya gaya wa masu gida cewa dansu da suke nema yana kaduna, ya basu address din gidan nan ya gaya musu cewa yana nan ynaa aikin driver".

Minal tace "ke Ruqayyah! Ji nake kin ce min iyayensa christians ne. In kuma suka tafi dashi suka mayar dashi Christian fa?" Ruqayyah tace "in haka ta faru to na tabbatar dama musuluncin nasa bana gaskiya bane ba, ai in dai da gaske yake to ba zai koma ba. Ni dai ina son in daina ganinsa anan gidan ne kawai, yadda ya gudu daga can ya taho nan haka in suka zo nemansa nan ma zai gudu ya kara gaba" Minal tayi shiru tana tunani, Ruqayyah tace "ni in ba zaki yi min ba ki gaya min in samu wanda zai yi min" Minal tace "babu komai, akwai wani yaron Alhaji Kabiru da nake dan saka wa aiyuka, zan tura shi Kanon" Ruqayyah tayi murmushi "shi yasa nake son ki Aminiya" Minal tace "babu wani Aminiya, yaudhe rabon ki da gida na? Ni kuma kullum ina kan hanyar zuwa gidan ki. Ina son ma zanzo ki raka ni in karasa siyayyar haihuwar nan" daga nan suka cigaba da hirarrakin su.

And so it happened....

Sanda cikin Fatima ya shiga watan haihuwa, a lokacin ne kuma sako ya samu Hussain na dawowar abokin sa Sadiq zuwa garin Abuja tare da balarabiyar matarsa da kuma dan su da suka haifa. Sai Hussain ya shirya da niyyar tafiya yaje ya gano abokinsa da kuma sabon family dinsa, sannan kuma yana son ya ga likitansa daga nan. Tunda yayi maganar tafiyar Fatima take kuka, ita bata so ya tafi, ita so take ta bishi amma kuma cikinta yayi nauyi sosai. "kiyi hakuri Fatima, Abuja ne fa ba wani guri ba, a yau zanje in dawo" amma ta tubure dole ya hakura da tafiyar sai gobe, goben ma ya kuma daga wa sai wata goben a haka har sati, dan haka ya yakice ya tafi da kyar ba wai dan ya damu da ganin abokinsa ba sai dai dan ya damu da zuwa gurin likita, ciwo ya dame shi sosai, ga kuma jini da yake fitarws sosai. Sau da takai shi har bakin mota yayi kissing dinta sannan ya sunkuya yayi kissing cikin sannan ya shiga mota shida Hassan Adam yana tukawa suka tafi.

A hanya suka yi hira sosai da Hassan, hira mai dadi duk da cewa baya jin dadin jikinsa, Adam ma kuma suna sako shi a cikin hirar yana jin labaran irin yarintarsu da kuma abubuwan da suka faru lokacin tasowarsu. A haka har suka iso garin Abuja suka shiga har cikin palace, sai dai kuma fitowa daga mota ya gagari Hussain. Nan take hankalin Hassan ya tashi ainun ya kuma umarci Adam daya juya motar zuwa asibiti, kafin su karasa asibitin jikin Hussain ya rikice gabaki daya dan sai tura shi akayi zuwa dakin likita kuma take aka saka masa oxygen dan numfashin sa sama sama yake fita. In hankalin Hassan yayi dubu to ya tashi gaba ki daya, amma a dole aka cire hannunsa daga na Hussain aka shiga da Hussain ciki shi kuma aka barshi a waje yana jira.

Bayan tsahon lokacin da Hassan ba zai iya tunawa ba sai doctors din suka fito sannan suka bashi damar ya shiga ciki gurin dan uwansa. Yana shiga Hussain ya dago hannunsa yana masa alamar yazo, ya tako a hankali ya zo ya jawo kujera ya zauna tare da kamo hannun Hussain ya rike a cikin nasa. Hassan yace "Hussain " Hussain yace "don't talk. Just hold me. Let me talk" Hassan yace "a'a kayi shiru ka rufe idonka ka huta kaji? Ka samu kayi bacci in ka tashi zaka ji ka warke" Hussain yayi murmushi, sai Hassan ya jinjina masa cewa duk da halin da yake ciki amma still yana iya yin murmushi. Ya bude baki a hankali yace "take care of our kids bro. All of them" Hassan ya maimaita "all of them" Hussain ya sake cewa "take care of everyone at home" sai kawai Hassan yaji yana so ya karanta masa kalmar shahada, sai ya karanta masa sau uku sannan ya maimaita sau daya. And then he is gone. A hankali Hassan yaji hannunsa yana zamewa daga cikin nasa, sai ya kara rike hannun hopping yaji ya rike amma bai rike ba sai kara saki da yayi, sai Hassan yaji tamkar wani bangare na ruhinsa ya fita ya barshi, tamkar ya zama rabi ne shi ba cikakken mutum ba. Tamkar ruhin Hussain ya fita ne tare da wani sashe na daga nasa ruhin.


*********. ************. **********


Tunda su Hussain suka fita Fatima bata koma cikin gida ba, sai ma ta samu kujera ta kafa a bakin kofar ta zauna tana jiran dawowar sa, kowa ya yi mata magana amma taki shiga ciki, gani take yi bata da wani sauran abinyi a cikin gidan, gani take yi kamar rayuwar ta ta kare a cikin gidan. Bayan awa biyu da tafiyar su ta dauki wayarta ta kira Hussain, tana so taji ko sun sauka lafiya amma wayar shiru ba'a dauka ba, ta kuma kira still shiru, sai ta kira ta Hassan shima bai dauka ba. Ta mike tana dosar part din aunty, a lokacin ne Ruqayyah ta shigo a mita tare da Minal sun dawo daga soyayyar zasu dauki wasu kayan sannan ta kai Minal gida. Suka tsaya a gefen Fatima, Ruqayyah tace "Fatima ya dai nag kamar hankalin ki a tashe? Wani abu ya faru ne" Fatima tace "yauwa Ruqayyah ki gwada kira Hassan da Allah muji ko sun sauka lafiya" Ruqayyah tace "sun je wani guri ne? Ni tun safe bana gida" Fatima tace "sun tafi Abuja, shi da Hussain, na kira Hussain bai dauka ba, ina so ne kawai in san ko sun sauka lafiya. Ruqayyah da Minal suka kalli juna suna tabe baki. Sannan Ruqayyah ta dauko wayarta ta kira Hassan amma bai dauka ba tace "bai dauka ba" Fatima ta fra yarfe hannu, "na shiga uku, ni gaba na faduwa yake yi. Ji nake yi kamar babu lafiya, kamar wani abu ya sami mijina" Ruqayyah ta tabe baki tace "kin san dai halin su in suna tare, na tabbatar da cewa hira ce ta saka basu ga kiran ki ba" Fatima ta sake girgiza kanta, sannan ta hango wani driver lawan ta kira shi "lawan dan Allah dauko mota ka kaini Abuja yanzu" Ruqayyah ta saki baki "for real? Wai bin sa zakiyi dan bai dauki wayarki ba? Fatima tace "ba rashin daukan waya bane ba, it is something else" sai ta juya ta nufi inda lawan yake fito da motar.

Minal ta kalli Ruqayyah tace "wai ke ma ba da mijin ki akayi tafiyar nan ba? Ke ba kya jin wani iri a jikin ki?" Ruqayyah ta tabe baki tace "ni lafiya nake jin jikina" Minal tace "dalla tashi ki bita, kema ki nuna kin damu da naki mijin" Ruqayyah tace "Abuja? Na bar fa dan jariri na tun safe a gurin Aunty" Minal tace "ba zai mutu ba ai, ki tashi ki bita ki ce kema naki jikin babu dadi mijinki kike so ki gani" Ruqayyah ta karasa packing sannan ta fito, Minal ma ta fito sai kuma lokaci daya tayi tunanin to in taje gida ma me zata yi? Ai gwara kawai ta bisu ta ga yadda dramar zata kare, sai kawai ta tafi itama ta bude gaban mota ta shiga ba tare da tayi tunanin bata tambayi mijinta ba ko kuma tunanin abinda zai je ya zo, Fatima kuma tare da Ruqayyah suka shiga baya sannan lawan driver ya ja suka dauki hanyar Abuja.



Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani wajen na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020.


*The Accident 2*


Kafin mu dora.
Sanda zamu fara banyi wa kowa alkawarin smiles and laughter a lokacin karatun tagwaye ba, besides, ni ban taba yin rubutu da niyyar in saka readers nishadi ba, a koda yaushe dalilin rubutu na shine dan in yi sharing abinda ni na fahimta akan bangarorin rayuwa tare da sauran mutane, fahimta ta ce, bance lallai ita ce dai dai ba, kawai dai ina fatan wani zai iya ya dauki wani abu da zai amfane shi a ciki.
And yes,
Duk wadda take son refund na kudinta tayi existing paid group sannan tayi min magana ta private.
But the story will continue as it is..............

Hassan ya sake kamo hannun Hussain ya kankame a kirjinsa yana jin hucin da zuciyarsa take yi yana huda kirjinsa yana dukan hannayensu, kuka yake so yayi amma ya kasa, tabbas wani tashin hankalin yafi gaban kuka. Ya jawo hannun zuwa bakinsa yayi kissing, baya bukatar likitoci suzo suyi masa bayani ya riga ya sani cewa Hussain baya tare da shi ya tafi gurin mahaliccin mu baki daya, ya tafi inda Maman su ta tafi, babansu ma ya tafi, yanzu shima ya tafi, sai Hassan yaji a ransa bai san me yake zaune yake yi a duniyar ba, zai iya bayar da komai da yake dashi dan ya bi bayan dan uwansa. Ya kalli fuskarsa fes da ita kamar yana bacci, dai yaga yayi masa wani irin kyawun da bai taba ganin yayi irin sa ba. Fuskarsa da hancinsa sun kara yin tsaho tamkar ba nasa ba. Sai yaji a lokacin babu abinda yake so kamar shima ya zama tamkar Hussain, shima ya zama gawa ko ruhinsa zai tafi gurin mutane mafiya soyuwa a gurinsa.

Yaji wani irin kadaici ya rufe shi tamkar shi kadai ne dan Adam din daya rage a duniya. Sai rufe idonsa ya kwantar da kansa a kirjin Hussain yana lura da yadda baya jin motsin bugun zuciya a kirjin. Ina ma dai shima tasa zata daina bugawar? Ina ma dai zata daina yi masa zafi da radadin da take yi masa yanzu.

Sun jima a haka sannan yaji an bude kofar dakin an shigo, bai motsa ba dan baya son motsawar, so yake ya cigaba da kwanciya a haka har tasa zuciyar ta daina bugawa shima ya tafi inda Hussain ya tafi. Inda mahaifan su suka tafi.

Hannu yaji an dora akan kafadar sa, ya dan bude ido kadan yana kallon likitan a cikin Scrubs dinsa, Doctor din yace "I am very sorry Hassan. Allah yayi wa Hussain cikawa. Allah yaji kansa da rahama" sai Hassan ya mayar da idonsa ya rufe, yana so yace Ameen amma bakinsa ya kasa motsawa, zuciyarsa ma ta kasa amsawa. He just can't accept cewa gaisuwar Hussain ake yi masa. Sai doctor din ya cire wa Hussain duk machines din da suka jojjona masa, ya kuma cire masa abin oxygen din da suka saka masa dan baya bukatar oxygen a yanzu, sannan sai ya jiya ya fita dan ya lura Hassan yana bukatar karin lokaci tare da Hussain. Bayan fitarsa ce wata nurse ta shigo ta dauki takardu ta fita, sannan wani ya shigo shima ya dauki wani abu da Hassan bai san menene ba, ya kuma rufe idonsa yaji shigowar wani, shi bai dauki komai ba ma ya fita. Sai Hassan ya fahimci wani abu, ya dago kansa yana kallon bakin kofa yana tunanin abinda ya faru a lokacin da akayi wa Hussain aiki a India ballantana yanzu da suke Nigeria, yadda Hussain yake public icon kowa zai so ace shi ya fara sanar da labarin mutuwarsa. Ya mike yaje ya rufe kofar dakin ya dawo ya ja abin rufa ya lullube Hussain har fuskarsa. Har yanzu kwakwalwar sa bata aiki sosai dan haka ya kasa tunanin mai zai yi. Ya jingina bayan sa da jikin kofar ya rufe idonsa yana sauraron bugun da zuciyarsa take yi, sai kuma yayi sauri ya bude idonsa ya fara laluben aljihunsa yana neman wayarsa, sai yaji bata jikinsa, ya barta a mota.

Hankalin sa a tashe ya bude kofar ya fita tare da yin amfani da key din daya gani a jikin kofar ya rufe ta ta waje, babban abinda ba zai so ba shine yaga hotunan gawar Hussain tana yawo a social media. Yes, people are that cruel, wasu tamkar jira suke yi abu ya same ka su fara yadawa babu ruwansu d halin da kake ciki ko abinda yadawar tasu zai iya janyowa. Ya tabbatar da yawa daga staff din asibitin by now sun san cewa Hussain Aminu Abdullahi ya mutu a cikin asibitin su, wani ya gaya wa wani wanin shima ya gaya wa wani, ya tabbatar kafin nan kafin minti biyu wani zaiyi posting a social media sannan wasu suyi sharing suma kuma ayi sharing nasu post din. Yasan kannensa gabaki daya suna social media haka ma Fatima, tashin hankalin sa kadai shine Fatima taji wannan labarin a media kamar yadda taji na rashin lafiyar Hussain. Musamman duba da halin da take ciki. Shi kuma a yanzu ba ya jin akwai wani abu da yake so fiye da abinda yake cikin Fatima, hatta yayan da ya haifa a cikinsa kuwa.

Adam yana ganin ya fito ya taso da sauri ya taho gurinsa, kallo daya zakayi masa kasan cewa hankalin sa a matukar tace yake dan yanzu a duniyar sa bayan Sumayya da iyayenta da suka karbe shi irin karbar da akeyi wa family member baya jin yana da kamar Hussain a duniya, shine gatan sa, shine tutiyarsa, a makaranta har kallon dan masu kudi ake yi masa saboda irin suturar da yake sakawa kuma duk na Hussain ne, babu wanda zai gansu tare yace drivern sa ne shi sai dai a dauka ko kaninsa ne.

Yace "oga Hassan ya jikin oga Hussain? Sun hanani shiga ciki tun dazu" Hassan ya bude motar yana duba wayarsa a inda ya zauna bai ganta ba amma sai yaga ta Hussain. Ya dauka ya fito yana kallon Adam da fuskarsa take nuna cewa yana gab da fashewa da kuka, ya dafa kafadar sa yace masa "Adam, Allah ya karbi oga Hussain" sai Adam yaji kamar bai ji sosai ba, sai yaji kamar bai iya hausa ba kuma, yace "what? Ban gane ba oga Hassan" Hassan ya tsaya kawai yana kallon sa ya kasa furta kalmar mutuwa tare da sunan Hussain a tare. Sai daya hadiye wani abu sannan yace "Adam Hussain ya mutu, Hussain ya tafi ya barni" sai ya dora kansa a kafadar Adam ya fara wani irin kuka wanda babu maiji sai Adam din da yake yi a jikinsa.

Adam ya sandare a tsaye, oga Hussain, oga Hussain din da suka taho yanzu tare suna hira suna dariya suna nishadi shine za'a ce ya mutu? Me ya same shi? Sai ya dora hannunsa a kafadar Hassan, yana jin yadda jikinsa yake motsawa da kukan sa, yanajin yadda hawayensa yake jika rigarsa da kuma yadda zafin jikinsa yake ratso har nasa jikin yace "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ka ringa maimaita innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allah zai saka maka nutsuwa kuma zaka ji sanyi a zuciyarka. Kayi kukan kuma yana da kyau ga lafiyar ka, amma kar kayi mai kara dan yana kara azaba ga mamaci" Hassan ya cikashi ya koma ya zauna a cikin motar kafafuwansa a waje. Ya jingina kansa da head rest yana sauraron rarraunar muryar Hassan yana maimaita masa fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Shima sai ya fara fada har ya samu nutsuwa sannan ya bude wayar Hussain da take hannunsa. Missed calls din fatima ya gani har 30+, gabansa ya fadi, kar dai har taji? Amma in taji baya jin zata samu karfin zuciyar kiran Hussain. Amma baya so ya kirata dan vai san me zai ce mata ba, sai dai bai san wanda zai fara kira ba, Aunty? Ko kuma wani a cikin yaran gidan maza? Ko Gombe zai kira? Amma kafin suzo Kaduna fa?

A karshe ya yanke shawarar kiran Aunty yayi mata dabarar da zata kai Fatima part dinta sannan ta karbe wayarta. Sai dai bai san me zaice da auntyn ba. Amma kuma kafin ya kira sai ga kiran auntyn ya shigo wayar Hussain din. Ya runtse ido tare da gyaran murya ya dauka, kafin yayi magana ta fara magana ita "Hussain kuna ina? Kasan Fatima ta biyo ka Abuja kuwa? Yanxu na shiga gidan mai gadi yace min ai Lawan driver yace masa Fatima tace zai kawo ta Abuja. Me zata yi a nan din" Hassan ya rikice "Abuja? Fatiman?" Tace "Hassan? Ina Hussain din? Neme su a waya dan ance tare da Ruqayyah suka fito sun biyo bayan ku" Hassan yaji hankalin sa ya sake tashi, bai iya cewa da ita komai ba sai ya kashe wayar tare da dafe kansa yana digesting maganar, Fatima da Ruqayyah suna kan hanyar tahowa Abuja a mota saboda me? Kuma wai harda Ruqayyah, Ruqayyan da tun safe ta fita daga ce masa gata nan yanzu zata dawo amma har suka fito bata dawo ba kuma bata dauki duk kiran da yake mata da niyyar gaya mata zaiyi tafiyar ba. Yanzu kuma wai tabiyo Fatima sun taho Abuja.

Shi bai ma san ta inda zai fara ba, da abinda yake ji a zuciyarsa zai fara ko kuma da gawar Hussain da take kwance a daki tana jiran a shiryata ga magrib tana dosowa ko kuma da tracing Fatima da Ruqayyah a garin Abuja, ko kuma da rarrashin sisters dinsu da yasan labarin mutuwar Hussain yana gab da zuwa gurin su. Ya sake daukan wayar ta nemo number din Ruqayyah ya kira. Bugu daya ta dauka tana cewa da Fatima "ga mijin naki nan yana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login