Showing 84001 words to 87000 words out of 300844 words

Chapter 29 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2090

dai wani barin na zuciyarsa yana gaya masa wannan shune dai dai, musamman in zuciyarsa ta hango masa Adam da Ruqayyah a mota yana kokarin tabata sai ya kara karfafa guiwarsa wajen ganin ya kori Adam din. Ya dauko wata ya kira shi. "Kazo ina neman ka" sai ya ajiye.

Tunda Adam yaga kiran yaji gabansa ya fadi, kawai Ruqayyah ce ta fado masa a rai dan yaga irin kallon da tayi masa ranar ban uma yasan dole ba zata so zamansa a gidan ba matsayinsa na wanda yasan the bad side of her. Ya runtse idonsa yana karanta hasbiyallahu wa nieemal wakeel, yana neman Allah ya kawo masa dauki. Tabbas yana son wannan aikin nasa kuma yana jin dadin zama a wannan gidan yana kuma son mutanen gidan including Hassan, baya son rabuwa dashi, baya son abinda zai saka shi ya sake sabon zibi a rayuwa. To ina zai dosa ne ma?

A haka ya tashi jiki ba kwari ya tafi part din Hassan, yayi sallama a bakin kofa yaji muryarsa a palo ya amsa masa yace "come in" ya shigo, half expecting to see Ruqayyah amma sai yaga Hassan din shi kadai a zaune, ya he gabansa ya zauna tare da gaishe shi, Hassan ya sake jinjina korar yaron a ransa amma dai sai ya daure ya mika masa takardar daya rubuta ta sallamar sa tare da check din kudin daya rubuta masa yace "am sorry Adam, na dauka cewa binciken da nayi a kanka ya bayyana min komai a game da kai amma ban sani ba ashe akwai wani hidden part da ban sani ba. Kayi hakuri Adam amma ba zamu iya cigaba da zama da kai a gidan nan ba" Adam ya dago kai yana kallonsa, maganar tana taba masa zuciya more than yadda yayi tunanin zata taba shi din" ya kalli takardar hannun Hassan sannan ya sake kallon Hassan din, mutumin kirki, shi kuwa menene wannan da Ruqayyah ta gaya masa da har zai kore shi irin haka? Bai karbi takardar ba yace "Ruqayyah ce ko? Me tace maka? Wanne sharri tayi min haka?" Hassan yace "matata ce fa, ka iya bakinka. Na tabbatar ai kasan abinda ya hada ku" Adam yace "nasan abinda ya hadamu amma a gurina abinda ya kamata ayi min kyauta ne ba wai a kore ni daga aiki a kansa ba" Hassan ya ajiye takardun a hannun kujerar da yake zaune yace "did you or didn't you try to touch her ranar nan a motar ka?" Adam ya runtse idonsa yana kokarin control zuciyarsa, wato sharrin da Ruqayyah tayi masa kenan ko? Sai da Hassan ya maimaita tambayar sannan Adam yace "yes, I acted kamar zan taba ta amma ban taba ta dinba. Nayi haka ne kuma saboda in koya mata darasi dan kada watarana ta hadu da wanda zaiyi abinda yafi taba ta" Hassan ya dan bata rai yace "ban gane ba, wani abin tayi da har zaka koya mata darasi ta wannan hanyar?" Adam ya mike tsaye yace "like you said, she is your wife and it is your job to find out who she really is" Hassan yaji zuciya ta taso masa amma sai ya danne ta tana gaya wa kansa cewa bacin ran korar da akayi masa ne ya saka Adam fadar haka, ya mika masa takardar yace "karbi" Adam ya girgiza i "I don't need it" Hassan ya mika masa check din "ga wannan ka fitar ka rage wani abu" ya sake girgiza kansa "I don't need it. Gwara ka ajiye abinka dan duk ranar da Ruqayyah ta gama da kai you are going to need it more than me" ya juya ya fita. Hassan ya mike kamar zai bishi sai ga Ruqayyah, bai ma san tana jin su ba tace "ka rabu dashi, ba girman ka bane ba, ba sa'an rigimar ka bane ba" yayi ajjiyar zuciya ya koma ya zauna itama ta zauna a hannunkujerar da yake kai tace "you did the right thing" ya lumshe idonsa ya bude yace "did I?" Sai ya mike ya hau sama. And for the first time in his life sai yaji insecurities, yaji he is no longer in control.

Daga part din Hassan Adam dakin sa ya zarce, ta jawo akwatin sa ya fara jawo kayansa babu ko ninki yana zubawa a ciki. This is one of the times da wani voice a ransa yake gaya masa cewa ya koma gida, inda babu wanda zai kuma wulakanta shi ballantana yayi masa sharri, bai san takamaiman abinda Ruqayyah ta gayawa Hassan ba amma yasan sharri tayi masa, bakin cikinsa kuma shine Ruqayyah yaruwar Sumayya ce, wannan shine dalilin da yasa bai gaya wa Hassan actual a binda ya faru ba saboda kar ya bata wa Sumayya inya lalata auren yar uwarta, zata ga kuma kamar yaci amanar maganganun data gaya masa akan Ruqayyah. Zai tafi, yasan Allah yana tare dashi a duk inda zaije. Yayi ta zuba kaya har akwatin ya cika sannan ya jawo jaka yana tuna ranar da Hussain ya bashi jakar a cike da kayn sawa masu kyau, sai ya kara jin ransa ya baci, yaji mafarkinsa ya komawa karatu yana rushewa a gaban idonsa. Ruqayyah bata san me ta aikata ba amma yasan tabbas wata rana sai tayi dana sani, sai tayi nadama a ranar da nadama ba zata amfane ta da komai ba.

Ya gama hada kayan sa kaf ya ajiye a gefe, baya jin zai sake kwana a gidan nan. Sai dai kuma yana gama shiryawa ana kiran sallar magrib, sai kawai ya shiga toilet ya yi alwala sannan ya fita zuwa masallacin gidan akayi sallah dashi. Yana fitowa yaga oga Hussain shima tare akayi sallar dashi, ya kura shi."Adam ka shirya gobe da sassafe zamu fita, akwai gurin da zamu je mai muhimmanci" Adam ya dan shafa kansa kadan yana jin rashin kyautawar sa ta niyyar tafiya ba tare daya gaywa Hussain ba, sai dai kuma baya son ya zamanto kamar ya hada tsakanin yan uwan ne yafi son sai ya tafi sannan Hussain ya sani. Ya dan shafa kansa bai ce komai ba sai Hussain ya kankance ido yana kallonsa "akwai problem ne?" Adam tayi saurin girgiza kai yace "babu komai oga Hussain. Allah ya kaimu goben" Hussain ya bishi da kallo har ya wuce sannan shima ya tafi, amma sai ya samu kansa da kasa shiga part dinsa sai ya sa aka kawo masa kujera ya zauna a waje. Bai jima da zama ba yaga shigowar taxi gidan, ya dauka baki sukayi sai yaga Adam ya fito daga bq da akwati a hannun sa ya kai motar ya koma ya dawo da jaka, sai ya mike ya bishi a baya zuwa wajen motar yace "are we going somewhere?" Adam yabdan tsorata dan bai san yana ganin sa ba, sai kuma ya shafa kansa yana kokarin ƙirƙirar murmushi amma yaƙi zuwa, Hussain ya sake cewa "ina zaka je da kaya haka Adam?" Adam ya fahimci an kama shi sannan yace "I got fired" mamaki ya bayyana a fuskar Hussain yace "what? Fired? By who? The last time I checked I am your boss, waye kuma ya kore ka bani ba?" Adam yace "it doesn't matter oga, just let me go, bana son ku yi jayayya a sanadiya ta. Kuma kona cigaba da zama ba zamu daidaita da ita ba" Hussain yace "Ita? Wacece ita? Fatima ko wa?" Adam yace "noo, Ruqayyah" Hussain yayi murmushin takaici yana bubbuga hannunsa a jikin motar, "Ruqayyah, Ruqayyah ce ta kore ka? Menene dalilin ta? Huh? Me kayi mata?" Adam yace "it doesn't matter oga" Hussain yace "no it does matter, kai ne na farko kuma bani da tabbas din kai zaka zamo na karshe, ba zan barta tana korar min ma'aikata ba anyhow. Zaka zauna har sai naji dalilin ta idan yayi min sannan zan barka ka tafi idan kuma bai yi min ba you are going no where. Kana ji na?" Adam yace "yes sir" Hussain yace "ka mayar da kayan ka zanje in ganta".

Daga nan bai shiga part dinsa ba duk da yasan Fatima tana jiransa su ci abinci sai ya wuce part din Hassan. Ya zauna a palo ya kira shi a waya sai gasu sun sauko tare shida Ruqayyah. Ta gaishe shi ya amsa sannan ta zauna kusa da mijinta. Yace "Ruqayyah driver na Adam yace min kin kore shi. Menene dalilin ki?" Ta dafe kirji ta fito da ido "ni? Ni ina nagan shi ma ballantana in kore shi?" Hassan yace "nine na kore shi ba ita ba" Hussain ya gyara zamansa akan kujera yace "can I know why please?" Hassan yace da Ruqayyah tashi ki shiga ciki. Sannan ya juyo yayi wa Hussain bayanin abinda Ruqayyah ta gaya masa akan Adam, da kuma yadda suka yi da Adam din, ya kara da cewa "bai yi denying ba, ya dai yi wa maganar data fada kwaskwarima" Hussain yayi dariya yace "wannan shine dalilin? Saboda yayi kokarin taba matarka a tun kafin ka hadu da ita?" Hassan yace "ba da wannan nayi judging dinsa ba, wannan abinda ya faru tsakanin su ya nuna mana wata character dinsa wadda nayi judging dinsa da ita. Muna da kanne mata a gidan nan, zai iya daukan su zuwa unguwa wata rana. What if he tries them? Yana da kyau wanda zai iya amfani dashi a kansu" Hussain ya daga kafada yace "Ruqayyah bata barshi ya taba ta ba saboda tana da tarbiyya, haka kannen mu suma suna da tarbiyya. Besides, personal driver na ne, bashi da hadi da kanne na ballantana matarka" Hassan ya girgiza kai yana jin ramsa yana baci yace "na riga na kore shi, and that's final" Hussain ya mike yace "ni kuma na sake renewing contact dina dashi, he works for me and that's final" daga nan ya juya ya fita.

Hassan yaji ransa ya baci sosai. Hussain ya jima bai bata masa rai irin na yau ba. Ruqayyah ta kuma saukowa ta zauna a kusa dashi tace "shikenan ai yanzu kaga ya zubar maka da girman ka a gurin Adamun, ya zubar maka da girman ka a gurin duk sauran ma'aikatan gidan nan dan nasan duk sai Adamu ya gaya musu abinda ya faru" Hassan ya mike yana jin haushin Hussain yana karuwa a ransa, sai kuma yaji haushin Ruqayyah data saka yaji haushin dan uwansa har haka. Ba tare daya ce mata komai ba ya hau sama ya shiga dakinsa ya rufe kofa.

Da sassafe Hussain ya fito ya tarar Adam har ya fito da mota, ya bude masa baya ya shiga shi kuma ya shiga seat din driver ya kunna ta suka fita. Suna fita Hussain yace "tell me about Ruqayyah, me ya hada ka da ita? Da gaske kayi kokarin taba ta a motar ka" Adam yace "yes sir, amma nayi haka ne saboda in ja mata kunne akan abinda tayi" Hussain yace "menene abinda tayi din?" Adam ya girgiza kansa yace "matar yayanka ce oga, kuma yayar Sumayya" Hussain yayi murmushi yace "Sumayya ce tauraruwar ka kenan" Adam yayi murmushi shima bai ce komai ba. Hussain yace "this means kasan abubuwa da yawa akanta ko?" Adam yace "yes sir" Hussain yace "yanzu dai ba zaka gaya min ba kenan" Adam ya sake murmushi kawai. Hussain ya kwanta a corner din motar yana taping hannunsa a kan cinyarsa, fuskarta tana nuna zurfin tunani yace "tell me one thing, should I be worried about Ruqayyah?" Adam yayi jim sannan yace "you should be very worried sir"

Wannan littafin na siyarwa ne, in kina so kiyi min magana through WhatsApp 08067081020

Har suka gama abinda zasu yi suka dawo gida Hussain hankalin sa yana kan maganar Adam. Yaron yaki ya gaya masa gaskiyar abindaya faru maybe daya gaya masa da yasan abinda ya kamata yayi. Shi tun farko hankalin sa bai kwanta da Ruqayyah ba, sai dai kuma a yanzu matar dan uwansa ce dan haka bibiyarta da kuma saka ido a kanta ba zai yiwa dan uwan nasa dadi ba. Dole sai yabi a hankali, dole sai ya nemi dabara yadda zai bullowa lamarin ta lumana ba tare daya taba zuciyar dan uwan sa ba.

Suna dawowa gida ya wuce part din Aunty ya gaishe ta, a can ya tarar da Hassan shima ya shiga gaisheta, Hassan ya dauke kansa yayi kamar bai ga shigowar Hussain ba shi kuma sai ya kama tsokanar sa wai yaga alamar har wani tumbi ya fara ajiyewa saboda jin dadin amarci. "Me Ruqayyah take baka ne? Zan ke aiko da kwano na nima ana sammin ko na kara kumari da kwarjini" Hassan ya kalle shi kawai ya dauke kai, Aunty tace "an kuma kenan, me ya hada ku?" Hussain yace "aunty driver na ya kora, ni kuma nace na mayar dashi bakin aikinsa shine yake fushi" Aunty tace "akan driver kuma? Hassan me yayi maka da zafi haka da har zaka yi fushi da dan uwanka?" Hassan ya mike yana daukan wayarsa yace "ya wuce aunty, laifi na ne dama, drivern sa ne shi yake biyan sa albashi, motar sa ce gidan sa ne, I should have know my place, yanzu kuma na sani dan haka zanyi minding business dina" aunty ta rike baki tana salati yayin da Hassan din ya juya ya bar gidan. Tabbas yan biyun nata suna fada, amma mostly fadan nasu yafi yi mata kama da wasa dan akan silly silly things suke yin fadan,but na yau is different. Na yau ba wasa bane ba.

Ta juya tana kallon Hussain tace "ka sallami drivern Hussain" ya girgiza kansa "Aunty ba zan iya ba. Kuma akwai dalilin da yasa ba zan iya din ba" ya dago yana murmushi yana kallonta. "Ki rabu dashi, yadda ya hau shi kadai haka zai sauko shi kadai"
Daga gidan aunty hassan gidan sa ya zarce, a palo ya tarar da Ruqayyah a kwance a kujera da packet din chewing gum a gaban ta tana kuma cin wani, tayi masa murmushi amma sai ya wuce ta ba tare daya mayar mata ba, ta bi bayansa da harara sannan ta cigaba da wayarta. "Wallahi ina gaya muki Rukee sai kin waye, in ba haka ba kina ji kina gani za'a mayar dake tsumman goge kashi" tace "to Minal me zanyi? Kin ga fa su Fatima ce tasu, sam basa ma shigo bangare na sai gurinta, saboda zata dauko abin duniya ta basu ni kuma bani dashi" Minal tace "nema zakiyi kema ai, in baki dashi ai mijinki yan dashi shine zai baki ai. Ki san me yafi so ki ringa yi masa, ki kwantar da kanki sosai kar ki sake ki nuna masa wannan zafin ran naki, ba dai shine babba ba? In dai kin kama babban yayansu ai kin kama su gabaki dayan su babu wanda zai isa yayi miki musu. Kuma suma ki shiga cikin su, ki nuna musu soyayya kamar ruwa, ai da haka ake jan ra'ayin mutane, ke yanzu ko yar kissar nan ma ashe baki iya ba? Ai nuna musu zaki yi duniya babu yasu. Ki kafa gwamnatin ki sosai sannan ki fara diban rabonki. Dakin samu kin tara ki sayi gida, in kin kuma tarawa ki kuma siyan wani. A haka in rabuwa ma tazo Allah ya kiyaye kin ga kin samu madafa, tunda dai ba wani sonsa kike yi ba nasan auren ba wani guri zaije ba" Ruqayyah ta bata rai tace "wannan ai mugun fata ne, kuma ni yaushe nace miki bana sonsa?" Minal tace "ko kima sonsa ma na tabbatar kinfi son kudinsa a kansa, ko ba haka bane ba?" Ruqayyah ta jiya ido tace "to waye bayan san kudi? Annabi ma da kansa yace mu nemi tsari da talauci dan talauci musiba ne. Duk wanda yace baya son kudi to munafiki ne" suka yi dariya tare. Minal tace "yanzu yana ina?" Ruqayyah tace "yana dakinsa ina jin. Yanzu muna wayar nan ya shigo ya haye sama, kin san fushi yake yi akan maganar drivern nan" Minal tace "amma lallai Ruqayyah sai na kai ki ina jin gurin Aunty Hafsa ta wanke min ke, yanzu mijin naki yana fushi shine kika barshi ya tafi daki shi kadai? Mijin ma kuma mai kudi irin wannan? Ai ko da baki yi laifi ba zuwa zakiyi ki ba shi hakuri. Ki lallaba kayanki in ma yaga laifin ki ya dawo yana ganin laifin wanda ya fadi laifin ki".

Da haka suka yi sallama Ruqayyah ta tashi ta hau saman itama, sai data fara shiga dakinta ta shafa turare saboda jin ta take yi kamar tana dan tashi kadan duk kuwa da cewa tayi wanka ta kuma saka turaruka iri iri, amma ta na jin kamar kalar turaren da ta saka ne bata so. Ta shiga dakinsa ta tarar ya fito daga wanka yana shafa mai, ta bi kirar jikinsa da kallo sannan ta danyi masa murmushi "yanzu ni shikenan sai mijina yazo ya wuce ni ko kula ni ba zaiyi ba, kawai sai yake fushi dani duk da bansan laifin da nayi masa ba?" Bai ce komai ba ya fara shafa man sa, ta zo gabansa ta tsaya tana shagwabe fuska kamar zata yi kuka. Ya zauna a bakin gado sai ta bishi ta zauna akan cinyarsa tana leka fuskarsa. "To ni ka kalle ni mana? Ni ka gaya min laifin da nayi maka" ta fada tana kakalo kuka. Ya dakata da abinda yake yi yana kallon ta sai ya fara tunanin laifin menene tayi masa wai? Menene laifinta a cikin maganar? Ai kamar ma ita akayi wa laifi ko?

Sai ya kara hade fuska yace "shine kuma bayan kinga nayi fushi kika rabu dani ko?" Ta matso hawayenta "to ni ai bansan me zanyi maka ba, ka taho daga dakina ka dawo nan bayan tunda nazo a dakina muke kwana, ka saka ni na kasa bacci ina ta jin tsoro cikin dare" ta kara matse kwalla "kuma dazu ma da nayi maka murmushi baka rama min ba" ta turo baki.

Ya bi bakin da kallo yana jin murmushi yana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login