Showing 237001 words to 240000 words out of 300844 words
da yake barinta tana zuwa duba Ruqayyah duk da shi baya shigowa, Baba ma kuma sai gashi ya sauko ya bar Inna ita take jinyar Ruqayyah. Anan ne ta kara fahimtar halin da yar tata take ciki, wannan firgicin yana nan har yanzu, ga wata uwar rama da tayi, hannunta kamar skeleton.
Lukman yaji labarin abinda ya faru, kuma ba bata lokaci ya garzaya asibiti gurin Ruqayyah, a zahiri ya nuna kamar ya damu be da halin da Ruqayyah take ciki, a badini kuma ta cikon kudin sa yake yi. Sunyi magana da police kuma sun tabbatar masa da cewa kai Ruqayyah mental institution shine kadai hanyar tseratar da rayuwar ta. Lukman ya danyi tunani akan hakan sai yaga shima wata kafar samun wasu kudin ne ta bude masa. Idan Ruqayyah ta tafi mental institution dole tana da bukatar mai kula mata da dukiyar ta, a matsayin sa na lawyer zai iya wannan aikin, zai ci rabon sa ya bar mata saura, in ta kwashi shekaru acan sai yayi kokari ya fito da ita, daga nan kuma zata biya shi kudin aikin sa, in yayi Sa'a ma kuma zata iya.........
Amma sanda ya samu Ruqayyah da maganar sai yaga kamar ba Ruqayyan daya sani bace ba. "Ina so zanje inyi confessing. Ina so ka shige min gaba inyi confessing" ya bude baki a ransa yana cewa "ji wannan sakartar yarinyar, in tayi confessing kuma da wanne kudin zata biya ni?" A zahiri kuma yace "no.... don't even try that... Kin san kuwa me hakan yake nufi? In kika yi confessing you will loose everything" ta juyo tana kallon sa, "I don't care" sai hawaye suka zubo mata. "I already lost everything long time ago". Ya gyara zama yana jera kalmomin da zaiyi mata amfani dasu yace "okay, tunda haka kike so haka za'a yi. Let's go over abubuwan da zasu faru if you confess" tace "na riga na sani, za'a kai ni gidan mahaukata kuma za'a karbe dukiyar da take hannu na a bawa masu ita" yace "no, that was before, lokacin da ba'a tabbatar ke kika yi laifin ba, amma in kika yi confessing shikenan an tabbatar beyond doubt, za'a hada miki dukkan laifuffukan ki kuma a kara miki da laifin wasa da hankalin Shari'a, you will be hanged. Amma wannan ba komai bane ba tunda naga kamar kin shirya tafiya lahirar, abinda nafi ji miki shine family dinki, kin ga duk wannan abin da ake yi har yanzu basu tabbatar da kinyi abinda ake zargin ki dashi ba, amma kina confessing shikenan sun tabbatar, and they will be so heart broken. Basu bama, ni nafi jin yayanki, those innocent cute babies, the fact that anyi hanging uwarsu zai bi su ne har karshen rayuwar su. Wannan shine abinda kike so musu? If that is your wish I will help you to get it granted".
*********************
A sanda ake ta wannan rikicin a Kaduna, a kano kuma shirye shiryen tafiyar su Fatima ake tayi, ya yarda zai biya Dubai kamar yadda ita da kanta ta bukaci hakan. Yayi settling down sosai a gidan Sarki, da yake he is social nan da nan yayi mingling. Ranar nan Umar ya kira shi a wayarsa ya gaya masa ya same shi a cikin gida a falon Hajiya Ummah kuma ya tafi da takardun sa, yana so zai fara processing neman admission dinsu shi da Fatima.
Farko ya dan ji tsoron shiga cikin gidan amma sai yaga daya tafi ba'a hana shi ba, ya kira Fatima a wata ita tayi directing dinsa a waya har part din Hajiya Ummah kuma ya shiga har falon ta, anan ya tarar da Fatima already ta riga shi zuwa suna tare da Umar, ya dan rissina ya gaishe da Umar din shi kuma ya tsokane shi saboda yaji shi a waya yana gayawa Fatima tsoron shigowa yake kar dogarai su kama shi. Ya zauna yana mika wa Umar folder din hannunsa, ya karba ya hada data Fatima data bashi already, sai kuma yayi musu bayanin duk procedure din da za'a bi da kuma requirements din da makarantar suke bukata.
Sai ya fara going through takardun nasu dan ya tabbatar suna wa komai. A haka suka baje takardun suna ta dubawa Adam yana ta tattara nasa a guri daya wai baya son Fatima ta gani, tace "meye kake boyewa, ko baka yi kokari bane a makarantar ka" ya bata rai " kina magana da head boy ne fa" tace "in ma waye, if you have nothing to hide then why are you hiding?" Umar ya dauko birth certificate din Adam ya mika mata yace "kinga abinda yake boyewa" Adam a dafe kai sai kuma yayi dariya yace "ba boyewa nake ba fa, kawai dai bana son a raina ni ne" tayi dariya "boyewar kake yi kenan, let me see shekara nawa na baka dan in san Aunty zaka ke ce min ko yaya"
Ta bude takardar tana dubawa sai ta bude baki "wai kana nufin ka girme ni?" Adam ya gyara zama yana murmushi, "an gaya miki ni din na yau ne" ya dauki tata folder din yana neman tata birth certificate din, ya dauko yana dubawa yana murmushi yace "yaya Adam daga yau" tace "only in your dreams. Wata takwas kadai ka bani" yace "oho dai, am sure na fara tafiya sanda aka haife ki" tayi dariya, "sai dai rarrafe" yace "ko rarrafen ne dai na riga ki yi".
Umar yayi gyaran murya yace "zaku cigaba da musun shekaru ne ko kuma zaku zo muyi abinda yake gaban mu?" Sai suka matso either sides of him suna sauraron sa har ya gama, amma a ransa yana mamakin yadda yaga Fatima tana dariya, this is the first time da yaga dariyar ta tunda ta dawo gida.
Bayan sun gama sai ya basu labarin abinda yake faruwa a kaduna akan case din Ruqayyah, Fatima bata ce komai ba dan ita bama ta son jin maganar dan dai in ta tashi zata zama rude to her brother. Bayan ya gama yi musu bayani ne Adam yace "to! Allah yasa haka shi yafi alkhairi. Ni iyayenta nake tausayawa, mutanen kirki ne sosai, they help me alot a lokacin da nafi bukatar taimakon. Dama gobe nake saka ran zan je Kaduna in gaishe su in kuma yi musu bayanin tafiyar nan inyi musu sallama" Fatima ta dago kanta tace "in zaka je zan bika. Zan tambaya in an bar ni sai mu tafi, ina son inyi wa Aunty sallama nima"
Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020
*The Seventh Wave*
Washegari kamar yadda Adam ya fada sai ya shirya da niyyar zuwa gaishe da Baba da Inna Ade, ya gaya wa Takawa kuma ya barshi sannan ya saka Umar ya bashi kudi masu dan kauri a envelope yace ya kai wa Baba ya kuma gaishe shi saboda yaji dadin labarin da Adam ya bashi na yadda Baba da iyalinsa suka karbe shi ba tare da kyamatar inda ya fito ba, duk da kasancewar su iyayen Ruqayyah bai sa maimartaba ya ga aibun Baba da family dinsa ba saboda yasan Allah yana iya fitar da mummuna a cikin kyakykyawa kuma ya fitar da kyakykyawa a cikin mummuna.
Fatima ma ta tambaya an kuma barta, amma sai aka hada ta da Asma'u dan tafi jin dadin tafiyar, har sun shirya kuma sai aka kira Abubakar aka ce ya bisu su tafi tare, ba'a fada masa dalili ba amma shima yasan dalilin, bai kuma musa ba sannan bai bata lokaci ba ya shirya suka tafi. Adam ne yake jan motar Abubakar yana gaba, Fatima da Asma'u suna baya. Fatima seems moody tun da ta tashi da safe, sun fara kokarin cheering din ta amma basu yi nasara ba sai duka rabu da ita suka cigaba da hirar su a tsakanin du suna dan saka ta kadan a ciki duk da dai bata amsa musu.
Kasancewar sun fita da wuri ya saka suka isa Kaduna da wuri, direct gidan Aunty suka tafi, Aunty wadda Hajiya Ummah ta gaya mata zuwansu ta tare su baki har kunne, amma ganin mood din Fatimah ya saka ita ma nata jikin yayi sanyi, Zulaihat ta fara hidimar saukar baki mata da suka shiga ciki, Asma'u tana ta tsokanar ta tana cewa ta zama in-law dinta, wai sai yanzu ta lura duk gidan ta fisu kyau. Hassan kuma a waje ya dauki Abubakar da Adam.
Dan refreshing kadai suka yi suka fita zuwa gidan Baba, sunyi Sa'a sun tarar dashi a gida, yayi murna sosai da ganin su. Gaisawa kawai suka yi sai Hassan da Abubakar suka koma gidan aunty suka bar Adam anan tare da Baba. Baba ya shigar dashi har cikin gida ya gaishe da Inna Ade tana ta murna "oh Adam, muna ta jajen ka sai Sumayya take bamu labarin abinda ya faru, munyi murna sosai. Allah yasa hakan shi yafi muku alkhairi" Adam yayi murmushi yace "ameen Inna, yasu Zunnur? Nayi kewar su sosai" Inna tace "suna lafiya lau, Zunnur fa har ya shiga jami'a, Sulaiman kuma ya gama sai cigaba da yake shirin tafiya, Hassan ne ya dauki nauyin sa" Adam ya bude baki yace "wow Inna, Masha Allah. Gaskiya nayi murna da jin wannan labarin. Alhamdulillah Allah abin godiya, zan so in gansu kafin in tafi" tace "au tafiya zaka yi? Na dauka zaka yi mana kwana biyu ne anan ai".
Adam ya dan sunkuyar da kai yana jin nauyin rashin kyautawar da yayi musu na kin zuwa da wuri duk da cewa sun damu dashi sosai, sai yayi saurin chanza shawara "ina nufin kafin in tafi gidan Aunty in dauko kayana dana bari a mota, kwana uku zanyi ai anan" Inna tayi murna, "yauwa, kaga sai inyi maka irin abincin da kake so". Sai ta dauko wayar ta tana kiran numbobin su Zunnur cikin doki tana gaya musu labarin zuwa Adam, sannan ne shi kuma Adam din suka kebe da Baba ya bashi labarin halin da yake ciki na komawar da yayi gidan sarki da zama da kuma maganar tafiya karatun sa.
Baba ya taya shi murna sosai "ikon Allah, Lallai Adam kai din akwai tarin baiwa sosai a tare da kai, wannan abinda ka fara gani kenan, Allah ne kadai yasan abinda ya boye maka wanda zaka samu nan gaba." Adam ya gyada kai, dan shi kansa yana mamakin irin yadda rayuwa take juya masa, sai kuma Baba yace "ni ai na dauka ko kayi fushi ne shi yasa baka zo ba, na dauka kayi fushi akan maganar Sumayya" Adam yace "haba haba Baba, ba haka bane ba ai, Sumayya ba rabo na bace ba shi yasa ban aure ta ba, kuma ni na zabi hakura da ita dan nasan idan da ace na dawo da wuri da ba za'a hana ni ita ba. Na kuma yi murna da zabin da akayi mata na miji dan Hassan mutumin kirki ne. Allah ya basu zaman lafiya da zuriya mai albarka" Baba yaji dadi yace "ameen summa ameen Adam"
Sai kuma suka dora da labarin abubuwan da suke faruwa, Adam yana ta kwantar masa da hankali akan maganar Ruqayyah "kayi iyakacin kokarin ka Baba, mu mun sani, duniya duk ta sani" Baba yana juya kai yace "amma duk da haka nayi asarar yata" Adam yace "amma kuma ka samu Da, ni dan ka ne, a koda yaushe zaka kira ni da Da kuma karbi rile din dan a gurin ka insha Allah" Baba yayi murmushi yace "bayan an kwace min kai, mai martaba sarki yayi min fin karfi" Adam yace "duk ku biyun nawa ne Baba, duk iyaye na ne ku, nayi rashin uba sai gashi na samu iyaye har biyu" Baba yace "tabbas Adam kai aya ne ta ubangiji, cewa yana fitar da kyakykyawa daga cikin mummuna, kamar yadda Ruqayyah take aya kan cewa ubangiji yana fitar da mummuna daga cikin kyakykyawa".
A gidan Aunty, Fatimah ta rikice musu da kuka, musamman bayan taga hotunan Hussain da har yanzu suke rataye a falon Aunty. Gaba daya rayuwar ta a gidan ce take dawo mata, duk inda ta kalla akwai wani memory na Hussain a wajen, sai taji kamar har muryarsa take ji yana dariya tare dasu kamar yadda suke zama anan falon ayi ta wasa da dariya, duk inda ta kalla sai taga kamar zata ganshi a gurin yana yi mata murmushi. Aunty ta zauna lallashi sai itama ta fara kukan, Allah yaso Zulaihat ta fita gurin baki wajen Abubakar da itama da ita za'a yi kukan. Hassan sai ya zama ya saka su a gaba ya rasa wadda zai bawa hakuri a cikin su, a karshe sai ya tashi ya fita ya koma gidansa sa inda dana ya gaya wa Sumayya ta shirya yara zai kawo du su gaishe da Fatima, tunda baya jin Fatima zata shiga gidan sa, Sumayya ta gama shirya su ta kuma faya musu auntyn su ce tazo zasu he su gaishe ta dan duk cikin su babu wanda zai iya tunawa da ita.
Yana shiga ya tarar suna jiran sa, yana kallon Sumayya yace "are you sure ba zaki je ku gaisa ba?" Sumayya ta girgiza kai, "bana son fuskata ta kara mata more emotions dan what she already is in" sai ya kama hannun yaran suka fita tare Abdullahi kuma ya dauke shi. A hanya suna ta tambayar sa alakar su da wadda tazo, sai da suka shiga cikin falon sannan ya durkusa a gaban su yace "kun tuna uncle Hussain?" Hussain ya bude ido cikin murna "uncle Hussain da nake kama da shi ko? Wanda in na girma zanyi irin halinsa" Hassan yace "that's right sweety, to wannan matar sa ce lokacin da yana da rai, sunan ta Aunty Fatimah"
Sai ya jasu gaban Fatima, ta dago kanta daga kan kafadar Aunty inda take kukan ta, ta zuba wa yaran ido, lokaci daya ta gane Aminu da Yusuf, sai kuma ta sauke idonta akan little Hussain. Nan take ta bude ido tare da rufe bakin ta da hannayenta guda biyu, Hassan ya jawo shi zuwa gabanta yace "Fatima, this is Hussain, Hussain Hassan Aminu" Fatima ta zame ta durkusa akan guiwowinta, fuskar little Hussain irin ta Hussain dinta sak har dimples din. Ta rike fuskarsa a hannun ta cikin karyayyiyar murya tace "Hussain!" Sai yace "na'am" ta jawo shi ta rungume shi a jikinta tana sake wani sabon kukan.
Abu biyu ne suka saka ta kuka akan little Hussain, na farko shine kamannin sa da Amour dinta, na biyu kuma dan ta tuna cewa wata daya da yan kwanaki ne tsakanin sa da nata dan, da yana nan da yanzu shima ya kai haka a girma, da yanzu shima ya fara zuwa makaranta ta, da yanzu shima ya fara kiranta da mommy, da yanzu ta rungume shi kamar yadda ta rungume Hussain. Tabbas kuwa da duk duniya bata jin zata samu wani abu as valuable as him.
Ta dago daga jikin Hussain tana kallon fuskar sa sai yasa hannunsa yana goge mata hawayenta yace "ki daina kuka kar kiyi ciwon kai, mommy tace in mutum yayi kuka dayawa kansa zaiyi ciwo" ta gyada kai tace "na daina, na daina Hussain" Hassan ya zauna a kujerar kusa da ita yace "kina son sa in bar miki shi?" Tayi sauri ta juyo tana kallon sa, sai kuma ta sake juyawa ta kalli Hussain, Hassan yace "in dai kina sonsa, na baki shi ki tafi dashi" ta girgiza kai tace "I can't take him Hassan, kaima kana bukatar sa dan yake debe maka kewar dan uwanka" yace "haka ne, amma ke kewar mutum biyu zai debe miki. Ni ina da abubuwa da yawa da zasu debe min kewar Hussain"
Sai ya mike tsaye yace "let me show you something" ta mike itama duk da bata san me zai nuna mata ba, ta bishi a baya tana tafiya tana waiwayen little Hussain. Baya taga ya zagaya, tasan dai babu komai a bayan sai garden din da Aunty take shuke shuken ta, ta tambaye shi "menene a gurin?" Sai ya dakata da tafiyar da yake yi ya juyo yana kallonta yace "kabarin Hussain" sai ta dafe kirjinta ta fara tafiya da baya baya tana girgiza kai, hawayen daya tsaya yana dawo wa. Cikin in ina tace "you, you....burrrrry him here?" Ya gyada mata kai. "zaki iya zuwa kiyi masa addu'a? Ko kuma mu koma?" Ta kalli inda taga ya dosa da sauri, tana jin tamkar wani abu yana janta zuwa gurin, irin abinda yake jan ta ga Hussain a duk lokacin da yake kusa da ita.
Da sassarfa ta wuce Hassan ta doshi gurin, sai kuma da kabarin ya bayyana a gabanta sai ta durkushe akan guiwowinta ta rufe fuskarta da hannun ta tana kuka. Hassan ya tsugunna a kusa da ita tare da diban kasar kabarin a hannunsa yace "kar kiyi, kar kiyi masa kuka dan Allah. Kiyi masa addu'a ki nema masa rahamar ubangiji dan shine abinda yake bukata daga gare ki a yanzu, shine kuma abinda ya saka na kawo ki gurin sa" sai ta same ta zauna kan dandaryar kasar gurin tana kallon kabarin, a idonta tana tuno irin rayuwar da suka yi da Hussain sanda suna dating da kuma shekara biyun da suka yi a matsayin mata da miji, the love, the care, the life.........babu abinda Hussain bai bata ba. Those two years da tayi a tare dashi bata jin zata kuma yin masu dadin su anan gaba.
"Hussain" ta fada cikin rawar murya "my love". Sai Hassan ya mike ya juya zai bar gurin, ta juyo tana kallon sa tace "Hassan" ya dakata amma bai juyo ba, tace "naji labarin abinda kayi wa Hussain da dukiyar da ya bar maka da nufin daji dadi in baya duniya, sai kai kuma ka zabi ka yi masa sadaka danshi yaji dadi yanzu da baya duniya. Ban taba ganin dan'uwan da ya yiwa dan'uwan sa haka ba, ban taba ganin dan'uwan da yake son dan'uwan sa kamar yadda kake son Hussain ba. Ina son