Showing 279001 words to 282000 words out of 300844 words
Ya fada cikin kara ji. Ta goge hawayen daya fito a gefen idonta tace "tace kaje ka karanta, in ka gama sai ka dawo kuyi magana" ya juya yana kallon kofar data fito yace
"Ki koma ki gaya mata cewa ni ba yaronta ba ne ba, she is not the boss of me da har zata ke bani directives, na zo ne kawai dan inyi mata tambaya daya kuma tana bani amsar tambaya ta zan koma inda na fito ba zata kara gani na ba. Tell her to come out and face me, tell her to come out and answer me. Menene dalilin da yasa ta yar da ni" ya fada da muryar daya tabbatar cewa ta cikin dakin ta jiyo shi
Hawayen fuskar tane ya karu, yana biyo kuncin ta yana sauka akan bangon littafin da yake rike a hannun ta. Tace "she can't" ya juyo da kallonsa kanta amma bai ce komai ba, fuskarta da hawayenta sun taba zuciyarsa. Shi mutum ne mai rauni abu kadan yakan ta ba shi.
Ta sake cewa "she can't come out and face you saboda bata iya tafiya. She can't answer you saboda bata iya magana".
Yaji zuciyarsa ta dunkule a guri daya, ya mayar da idonsa kan kofar dakin wata zuciyar tana gaya masa yaje ya bude ya shiga amma wata tana hana shi. Sai kuma ya saka hannu ya karbi littafin da ake miko masa. Shi a hankali yayi niyyar karba amma sai ya kasance tamkar warta yayi, wannan yasa Amatullah ta tafi kamar zata fadi sai ta dafe kujera. Then without a second glance ya juya da sauri ya bar parlon.
Blindly ya fita, har ya shiga motarsa ya jefa littafin a kan seat din kusa da driver sannan yayi wa motar key, sannan ya ja motar, faster than he intended ya bar harabar gidan. Yana ji a jikinsa cewa a yau din nan zai kuma dawowa.
Hotel ɗin daya sauka ya zarce, yayi packing ya fito da littafin a hannunsa ya shiga ba tare daya amsa gaisuwar da ma'aikatan hotel ɗin suke yi masa ba. Yana shiga dakin ya jefar da littafin akan gado sannan ya wuce toilet ya wanke fuskarsa, ya jima yana kallon fuskar a madubi yana tuno hoton tagwayen daya gani, sai kuma ya koma cikin dakin da sauri ya tsaya yana kallon littafin. Wato a cikin wannan littafin ne duk amsoshin tambayoyinsa suke, maybe a ciki zai samu amsar dalilinta na jefar da shi.
"She can't. She can't come out and face you saboda bata iya tafiya, she can't come out and answer you saboda bata iya magana"
Ya tuna maganganun yarinyar. Ya girgiza kansa da sauri. Shi yasan bayan duk wannan abin ya wuce sai yaje asibiti gurin Moon ta duba lafiyar kwakwalwar sa.
Ya zauna a bakin gado tare da ɗaukan littafin yana jujjuya shi. Babu wani rubuta a bangon sa. A hankali ya bude page din farko shima babu rubutun komai sai ya cigaba da flipping through pages din sannan ya ga ashe littafin a cike yake da handwritten rubutu, chapter by chapter. Ya danyi karamin tsaki. Shi bashi da wannan lokacin, bashi da lokacin karatun littafi shi amsa kawai yake so dan haka sai yayi deciding zai dudduba littafin ne kawai har ya nemo inda amsar sa take ya karanta shikenan ya gama dashi.
Da sauri ya ringa bubbuda pages din, noticing only the keywords. Yayi noticing Hassan sannan da Hussain, ya kuma ga Ruqayyah da Sumayya, daga nan yaga kalmar kidnapping amma bai karanta yaga wa akayi kidnapping din ba amma dai yaga an biya ransom. Sai yaga wedding, amma bai san auren waye ba, sai kuma yaga Fatima. Ya jima yana kallon sunan fatiman amma bai karanta labarin daya zagaye sunan nata ba sai ya wuce. A can gaba da nisa yaga kalmar accident, a kusa da ita akwai baby. Wannan ya ja hankalin sa ya karance wannan chapter din tsaf dan jikinsa ya bashi anan amsar sa take.
Ai kuwa ya ga amsar. Amsar da ta saka shi yayi jifa da littafin ya mike tsaye idanunsa suna ganin duhu kansa yana juyawa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" yayi kokarin ambata amma sai wata zuciyar ta hana shi. Tabbas in ya kira Allah zai ji sassauci a abinda yake ji a zuciyarsa kuma hakan zai iya hana shi daukan hukuncin da tun kafin ya gama karantawa ya riga ya yanke a zuciyarsa. He is going to Kill her.
A yanzu ba wai yar da shi da akayi ne yafi masa ciwo ba, abinda yafi masa ciwo shine blaming mahaifiyar sa da ya shafe tsahon rayuwarsa yana yi. Ashe ba ita ta yar da shi ba, ashe dauke shi akayi daga jikinta batare da an barsu sunji dumin juna ba. Wannan a gurinsa shine babban laifin da tayi masa wanda a gurinsa yake sama da jefar dashi da tayi..
Da lalube ya dauki key din motarsa, sannan ya fita cikin sauri mai hade da gudu. Bai kula da ma'aikatan da suke masa magana ba ya tayar da mota ya fita cikin sauri fiye da na sanda ya shigo. Blindly yake tukin, zuciyarsa tana yi masa bitar abinda ya karanta. Duk da bai karanta farkon labarin ko karshen sa ba, amma gani yake kisan da zaiyi mata shine hukuncin daya dace da ita. Da hannunsa zai shake ta sai ta daina numfashi, a yau ba sai gobe ba.
A haka ya karasa bakin gate din gidan, ya tsaya yana jiran mai gadi ya bude masa kofa yayin da shi kuma ya sake komawa cikin gidan yana sanar da zuwansa. Tabbas da da bindiga a hannunsa da zai iya harbe mai gadin baki daya saboda lokacin da yake bata masa, ya akayi ya daina yawo da bindiga ne? He missed his gang bang days.
At last aka bude masa ya shiga, sai dai kallon da mai gadin ya bishi dashi ya saka shima ya kalli hannayensa da suke rike da stiring, karkarwa hannayen suke yi kamar mazari, sai a lokacin ya lura cewa jikinsa gabaki daya karkarwa yake yi. Sai a lokacin ya lura ashe kuka yake yi.
*The fire and the ice*
*Two days ago.......*
Tun ranar da Sumayya ta tura wa Amir e-mail din take jin rashin dadi a zuciyarta, tunanin ta shine Hassan zai dauki hukuncin nata, amma kuma sai take ganin ko yayi fadan zai fahimce ta tunda shima yana da Hussain, ya san kuma yadda yake jin sa a ransa, ya san abinda zai iya yi dan ya samar wa Hussain sassauci idan da ace zai kasance cikin kunci, ya san cewa babu abinda ba zaiyi ba indai yana da iko dan lahirar Hussain tayi kyau. Ita kanta shaida ce cewa yayi kuma yana kan yin komai saboda Hussain. Ita me yasa ba zata yi saboda Ruqayyah ba?
Bata yi karya ba a duk abinda ta rubuta wa Amir a littafin ta, duk abinda ta rubuta gaskiya ne based on her knowledge, ita kuma bata yi niyya kuma ko a ranta bata da burin tursasa Amir ta kowace hanya ce dan ganin ya yafewa Ruqayyah ba, burin ta shine ya samu labarin gaskiyar abinda Ruqayyah tayi masa sannan kuma ya samu labarin sakayyar da ubangiji ya riga yayi masa a kanta, sannan ya ganta da idonsa one on one, ya tabbatar da abinda ya karanta din kuma ya fahimci babu wani ai da yayi saura da zai iya dauka a gurinta wanda Allah bai riga ya dauka ba, babu wani abu daya rage mata sai numfashin ta, then maybe, zai iya jin tausayin ta, maybe imanin sa zai iya sakawa yaji a ransa cewa ya yafe mata.
Tasan cewa indai ya shiga hannun Hassan, ko Fatima, the last thing da zasuyi masa magana a kai shine ya yafewa Ruqayyah, hatta yayan Ruqayyah bata jin zasu roki Amir ya yafe wa Ruqayyah nan kusa, in ma zasu roke shi din to sai an dauki lokaci, lokaci kuma shine abinda a yanzu Ruqayyah bata dashi. Ita kanta Sumayya tasan a yanzu Ruqayyah numfarfashin ta na karshe take ja a duniya dan kullum ta barta sai taji kamar ba zata dawo ta tarar da ita da rai ba. And it breaks her heart kullum in ta ganta. No matter how bad she was, no matter what she has done, twin sister dinta ce, that bond will never break no matter what.
Tana fatan Hassan zai fahimci haka.........
Tun da gari ya waye ta gaya wa Hassan cewa ta aika wa da Amir e-mail ta sanar dashi cewa yazo gurin su akwai labarin daya danganci iyayensa, ta gaya masa cewa ta aika masa da address amma bata gaya masa wanne address din ta bawa Amir ba, sai ta kwantar masa da hankali da cewa in dai ya gani tana da tabbacin zai zo, dan babu wanda zai tashi cikin rashin sanin su waye iyayensa sannan kuma ace masa ga labarin iyayensa amma yaki zuwa.
Ya yarda da haka, dan haka ya saka aka yi masa shimfida a harabar gidansa ya zauna yana facing gate tare da yayansa, anan suka yi breakfast anan suka yi lunch anan sukayi dinner. Daga an taba gate zasu juya gabaki dayansu, daga sunji horn zasu dakata daga maganganun da suke yi suna kasa kunne suji me ake cewa. Amma shiru babu Amir. Yaran gaba-daya anan suka wuni suna taya babansu hira da dauke masa hankali daga tunani, shima kuma sai yayi kokari sosai gurin tsayar da hankalin sa akan su yana basu labarin Hussain da irin yadda suke samun saɓanin ra'ayi akan abubuwa da yawa su kuma zauna suyi ta musu kowa yana ganin nasa shine dai dai. "Sai bayan daya fara rashin lafiya ne muka daina faɗa, in ma na neme shi da fada sai yace "ni ba zanyi fada da kai ba" ya fada yana murmushi, yana jin kamar yanzun be Hussain din yake gaya masa.
Sai daya tabbatar dare yayi Amir bai zo ba sannan ya fara damuwa. "Ko dai bai ga sakon ba? Ko kuma fushi yake yi damu? Dole yayi fushi, zai ga kamar muna sane muka rabu dashi a gidan marayu, muka barshi ya taso ya girma a matsayin marar asali marar gata, bayan shi din mai asali ne mai cikakken gata ne" Sumayya tace "ka kwantar da hankalin ka, dole yana bukatar lokacin da zaiyi tunani akan zuwan nasa, kasan ba abu ne mai sauki ba mutum ya tashi bai san iyayensa ba sannan rana daya ace masa yazo ga iyayensa, ka bar masa yau zuwa gobe insha Allah zaka ganshi a cikin gidan nan"
Sai ya hakura, ya kuma yi kokarin kwantar da hankalin satare da tursasawa kansa yin bacci duk da cewa baccin a tsitstsinke ya dunga yi, sai yake jin kamar ana knocking gate cikin barcin. Ita kuma Sumayya sai ta kwana bitar littafin ta tana tabbatar da ta rubuta duk abinda ya kamata ta rubuta, ta kuma yi duk bayanan da ya kamata tayi da irin yanayin da zai saka tausayi a zuciyar mutum.
Washegari da sassafe Hassan ya kuma sakawa aka sake masa shimfida irin ta jiya suka kuma zama tare da yayansa irin na jiya. Sumayya kuma ta tabbatar ta tana dar musu duk abinda zasu bukata sannan ta nemi izinin Hassan ta tafi gurin Ruqayyah, ya san yadda jikin Ruqayyah yake dan haka ya barta ta je din, saboda katanga daya ce tsakanin su in wani abu ya taso zasu neme ta ko kuma ita ta neme su.
Tana zuwa ta tarar mai kula da Ruqayyah ta gama shirya ta tana kokarin bata abinci. Sai ta karba ta na bata da kanta, sannan tana bata labari. "Yaran mu sun samo inda yaron Hussain yake, sunansa Amir, yana Abuja yanzu tare da iyalinsa" sai taga Ruqayyah ta juyo da idonta tana kallon ta, tayi kokarin yi mata murmushi "he is still alive Ruqayyah, watakila ma maganar nan da nake miki yana hanyar tahowa gidan nan dan an samu e-mail address din sa kuma na tura masa email" sai taga hawaye ya fara bin fuskar Ruqayyah, ta kama hannun ta a cikin nata tace "nayi wa Hassan laifi a kanki Ruqayyah, na ba wa Amir address din gidan nan ba gidan Hassan ba, ina so ya fara zuwa nan kafin yahe gurin Hassan" ta dauko littafin data rubuta tace "na rubuta masa duk labarin da nake ganin ya kamata ya sani anan, ina so in yazo nan din in bashi kuma in roke shi yaje ta karanta first kafin yaga kowa, ina fatan idan ya karanta kuma ya ganki zai yafe miki Ruqayyah, wannan shine fatana a yanzu, bana so ki mutu da hakkin yaron nan a kan ki Ruqayyah" ta fada tana taya Ruqayyah kuka
Kuka Ruqayyah take yi, da alama wani abu take so ta fada amma babu dama, so take ta gaya wa yaruwarta kar tayi haka, kar ta bata ran mijinta saboda ita dan ita din bata yi deserving wannan ba, bata yi deserving duk abinda suke yi mata ba, bayan duk abinda ta aikata musu bata yi tunanin zasu daga ido su kalleta ba ma ballantana har su kula da ita har kuma Sumayya take kokarin bata wa mijinta saboda ita. Saboda tana so ta nema mata yafiya a gurin wanda tasan ba zai taba yafe mata ba, idan kowa zai yafe mata a duniya tasan banda Fatima banda kuma wannan yaron, wannan mutumin da aka kira da suna Amir. Amma kuma taji dadin labarin cewa an ganshi, ko bai yafe mata ba to dawowarsa gurin iyayensa shima wani rage nauyi ne a gare ta.
Sai Sumayya ta dauko littafin tana karanta mata, tana jin ta kuma tana ta tuna yadda abubuwan da Sumayyan ta rubuta suka faru, amma kuma tana da gyararraki da yawa da zata iya yiwa Sumayya a littafin nata idan da tana da dama. Sai dai kash, damammakin ta sun kare a wannan duniyar, a lahira kuwa, bata jin za'a bata wata dama ko da kuwa guda daya ce.
Haka suka wuni a ranar shima kamar yadda su Hassan sukayi irin wunin da suka yi jiya. Amatullah tana dan shigowa gurinsu ta dan zauna taji labaran da Sumayya take bawa Ruqayyah sai kuma ta fita ta koma can gidan yaji labaran Hussain da Hassan yake bawa yanuwanta. Sai ta jinjina karfin bond din tagwaye, ta jinjina irin soyayyar da suke yiwa junansu.
And then on the third day, Hassan yana tashi shiryawa ya fara yi "fita zaka yi kuma yau Habibi? Na dauka yauma zamu zauna ne ko Allah zai sa yazo, kar yazo kuma bama nan" ya juyo yana kallonta yace "binsa zanyi, idan shi ba zai zo gare ni bani zan tafi gare shi. Ba dai gidan sarki ba? Zanje in yi ta tambaya har in samu wanda ya sanshi sai ya bani address din gidan sa, ba zan cigaba da zama ina jiransa ba alhali nasan yana raye kuma nasan inda zan same shi. Tafiya zanyi in nemo shi da kaina, a yau ba sai gobe ba, dan bani da tabbas din zan kai gobe" tayi murmushin kwara masa kwarin gwiwa, amma kuma tana jin hakan ya rusa duk plans dinta amma ba zata yi delaying dinsa ba in dai har hakan yake so da gaske.
Tare suka fito suka tarar har Amatullah ta fara hada breakfast, ta samu ta lallaba shi ya dan ci kadan sannan ta aika Amatullah ta taso Hussain, wanda a gidan ya sauka duk da ya gina gidan sa da yake sauka in yazo da iyalinsa, sai kuma ta kira Abdulrahim shima ta gaya musu ga hukuncin da babansu ya yanke, suma basu musa masa ba sai suka yi gaggawa gurin shiryawa dan suyi masa rakiya. Ta jirgi suka tafi, Abdullahi ne ya kaisu airport daga nan shima ya wuce gurin aikinsa, Abdulrahman ma haka.
Suna tafiya Sumayya da Amatullah suka gama duk abinda zasu yi suka tafi gurin Ruqayyah, Sumayya tana ji a ranta cewa yau za'a gama komai, ko dai Amir yazo gida ya same ta ita da Ruqayyah ko kuma su Hassan suje su same shi a gida. A ranar kuma duk jikin Ruqayyah ya kara rikicewa dan ko dan kunun da ake dura mata ta yau dawowa yake yi, kamar ta fara loosing her ability to swallow, wanda doctor ya gaya musu shine last stage da zata je. Sumayya ta saka ta a gaba tana hawaye, sai Amatullah ta dauko musu Alqur'ani suka hadu su biyu suna karanta mata.
Can daga baya Amatullah suka yi waya da Abdulrahim ya gaya mata sun sauka a Abuja har sun dauki hanyar palace din ma, a lokacin ne kuma Lami, mai aikin gidan ta lokacin tazo tana sallama, ta bude kofar dakin ta fita sai Lami ta sanar musu da cewa mai gadi ya shigo yace anyi bako a waje. Amatullah ta katse wayar sannan ta amsa mata da cewa tace ya shigo, sai kuma ta fara tunanin waye wannan? Dan gidan kam ba baki ake yi ba, babu mai zuwa sai sulaiman da Zunnur wani lokacin, su kuma duk lami da mai gadi sun san su dan haka ba zasu tsaya tambaye tambaye ba. Ta juya tana kallon Sumayya "mommy? Wai bako akayi a waje ko waye kuma? Na dai ce ace ya shigo" Sumayya ta mike da sauri tana ajjiye Alqur'anin da yake hannun ta ganin haka yasa Amatullah tayi sauri tace "ko ince kar ya shigo?"
Sumayya ta girgiza kanta da sauri amma bakin ta ya kasa magana, idanuwan ta a waje, suka tsaya suna kallon kallo ita da Amatullah har suka ji motsin kofa alamar an shigo palo, Sumayya ta hadiye wani abu sannan a hankali tace "leƙa kiga waye", Amatullah ta bude kofa ta fita, Sumayya kuma ta cigaba da tsayuwa idanunta akan kofa kunnuwan ta kuma a bude tana so taji ko da muryar sa ne, ba jimawa kuwa taji muryar "where is she?!"
Taji gidan yayi amsa kuwwar muryar sa, idan ba dan tasan Hassan baya gari ba zata ce shine yayi maganar, murya mai amo murya mai sa tsoro a zuciyar wanda aka yiwa magana da ita. Ta juya da sauri ta kalli Ruqayyah, sai taga ta bude idonta