Showing 114001 words to 117000 words out of 300844 words

Chapter 39 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2666

iya fitowa daga ciki ba. And yau ta tabbatar da haka.

Ta mike itama ta fice daga dakin ta koma nata dakin, tasan dama dole watarana sai haka ta faru a tsakanin su amma bata dauka hakan zata faru da wuri ba, plan dinta shine ta haifa masa as many yaya as possible yadda babu yadda zai yi da ita. Ta tsaya tana kallon sticker din data lika a jikin mirror dinta

"Have you taken your pills today?"

Sai ta saka hannu ta cire ta ta yar. Ta jawo drawer din da birth control pills dinta suke ta kwashe su gabaki daya taje ta zuba a waste bin. In yasan wata ai bai san wata ba. Ta kashe fitilar dakin ta kwanta, tana jin haushin sa a ranta, har da gori ma yayi mata wai ya siya wa baban ta gida.

Tana jinsa ya shigo dakin, ya jera mata yayan ta a kan gado, yayi musu addu'a ya shafa musu sannan ya tashi ya fita. Ta juyo tana kallon yaran, sai kuma tayi murmushi, dolen sa yayan ta ne yaya kuma dole sai uwarsu.



And yes. Hussain da Fatima sunje sunga fertility doctor a Washington DC. Doctor din yana kallonsu yana murmushi yace "one year you said?" Hussain ya daga kafada yana kallon Fatima da take twisting hannunta yace "she insisted sai munzo" doctor din ya juya yana kallon ta yace "am sure babu wani abu madam, but zamuyi running some tests dan mu tabbatar babu komai din. Pregnancy takes longer to get in some couples than in others ba tare da wani dalili ba".

Daga nan aka fara yi musu tests, a dauki jini a dauki fitsari, vaginal swab, sperm samples da sauransu. Kwanan su biyu ana ta faman abu daya, Hussain dai yana zuwa ne saboda ya farantawa Fatima amma shi a ransa yasan babu mai bashi haihuwa sai Allah. A week after aka kira su karbar result, suka zauna kamar yadda suka zauna last week, Fatima looking very nervous while Hussain is relaxed yana ta tsokanar ta. Doctor din shima ya dan tsokane ta kadan sannan yace "results dinku gasu nan sun fito gabaki daya, amma babu wani problem da muka gani, gabaki dayan ku lafiya lau kuke kuma zaku iya samun haihuwa a kowanne lokaci. Abinda zamu iya yi muku na taimako kawai shine zamu baku magunguna da zasu yi boosting fertility dinku sannan zamu baku shawarwarin da zasu taimaka muku sosai da kuma diet din da shima zai taimaka wajen boosting fertility din. Most importantly kuma ke Madam dole kiyi relaxing ki kwantar da hankalin ki saboda anxiety, rashin kwanciyar hankali, yawan tunani da damuwa duk suna affecting fertility din mace" Hussain ya juya yana kallon Fatima tare da kama kunnensa daya yace "kina dai ji ko? To babu ruwa na" tayi murmushi.

Aka gama yi musu bayanin duk da za'a yi musu, aka basu drugs dinsu aka sallame su. A hanya Hussain ya tasa Fatima da tsokana. "Sai kin shirya fa, tunda dai kinji sunce yawan yin abin nan yana kara chances, to double za'a ke yi yanzu" ta harare shi "to ayi double din ma mana, kasan dai ai bana jin tsoro ko?" Yace "kar ki cika baki fa? Sai kuma anzo gurin kuma ki fara neman a tausaya miki. To babu tausayi yanzu yarinya in....." Ta rufe ido "ka daina dan Allah kunyar ka nake ji fa" yayi dariya "to zamu karasa maganar a turaka".

Washegari da safe karar wayarsa ce ta tashe shi, ya daga cikin muryar bacci yana cewa "Hello. Who is on the line please?" Daga can aka yi masa bayanin cewa doctor din daya gansu ne yake son ya dawo shi kadai, akwai maganar da za'a yi masa. Ya ajiye wayar yana danyin tsaki, ya koma ya kwanta yana kara jawo Fatima jikinsa sai kuma ya mike, ya sake tsaki sannan ya shiga toilet. Mintuna kadan har ya fito, motsinsa ya tashe ta ta dago kai tana kallonsa "ina zaka je?" Yana daura agogo yace "zan dan fita, ki koma baccin ki yanzu zan dawo. Zan yi musu magana su kawo miki breakfast" ta tura baki "bayan ka hana ni bacci da dare ba dole in rama ba yanzu? Ba sai sun kawo ba dan ni banga ranar tashi na daga wannan baccin ba. In ka dawo ka taho mana da shi" yayi murmushi, "better eat something Madam, kar in dawo kuma kice ke ga zance ga magana. Cos da nayi niyyar mu koma Nigeria gobe but yesterday night ta saka na chanja shawara, sai next week zamu koma. Anan za'a yi making baby din" ta dauki pillow ta jefa masa, sannan ta rufe fuskarta da wani pillown.

Direct gurin doctor din ya koma, zuciyarsa tana ta yi masa sake sake iri iri. Doctor ya kalle shi da murmushi yace "kar ka damu da wannan kiran, I hope bamu tayar maka da hankali ba" Hussain yace "it is okay. What's up?" Doctor yace "result din da aka baku still stands, babu wani chanji. But a cikin gwaje gwajen da muka yi muku munga something da muke tunanin ya kamata ka sani kuma kayi taking action akai. It is just a suspicion Sir, we are not sure. Sai dai in ka yarda zamu tura ka gurin doctor din da zai sake maka wasu tests din for confirmation" Hussain ya gyara zaman sa yace "menene wai doctor, just say it" doctor ya gyara zama yace "we suspect that you have a column cancer"


Yana shiga hotel room din ya bude labulen da sauri, haske ya shigo ya haske dakin. Fatima ta daga kanta tana kifta ido tana adjusting to light din sannan tace cikin muryar bacci "har ka dawo? Ka taho da abincin?" Yace "tashi ki shirya, we are taking the next flight back to Nigeria" ta mike zaune tace "What? Why?" Yace "I said we are taking the next flight back to Nigeria" yanayin muryarsa ya sa ta san da gaske yake, ta san kuma something has happened.


Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani guri na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki ki yi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020



*The Brothers*

Cikin mintuna kadan suka gama hada kayansu, ita dai duk bata yarda da yanayin sa ba tace "wai me ya faru a Nigeria ne? Ko wani ne ya mutu aka gaya maka?" Ya kalle ta yana kokarin kirkirar murmushi yace "babu wanda ya mutu fa, kawai ji nayi ina missing Hassan" ta kalle shi kawai amma a ranta bata yarda da uzurinsa ba tace "Hassan din da kuna haduwa zaku fara rigima? A waya ma ina jin ku kuna yi" yace "mun daina daga yau, daga yau ba zan sake fada da Hassan ba ko ya neme ni da fadan ma cewa zanyi ni bana fada" tayi dariya, shima yayi, at least ta dan ji dadin ganin yayi dariya hakan yana nuna mata ba mutuwar akayi ba, but something is definitely up.

Sai da suka fito sannan suka samu abinci suka ci, har lokacin tana ta yi masa nacin sanin inda yaje da safe kuma me aka ce masa dan tasan abin yana da alaka da wannan tafiyar ta gaggawa amma sai yace mata abokin kasuwancin sa ne kawai ya gani, kuma kawai ji yayi yana son su koma gida. A hanyar airport ya kira Hassan ya gaya masa gasu nan zasu taho yanzu. A airport yaga wani bookshop, kawai sai ya shiga, a cikin jerin book yaga wani diary mai kyau mai girma kuma daga ganin sa zai yi kwari sai ya dauka tare da pen ya biya ya fita. Suna zama a cikin jirgi ya dauka dairy din ya bude front page ta fara rubutu.

Dear Baby.......

Fatima ta leko tana cewa "me kake rubuta wa ne haka?" Ya rufe littafin yana zare mata ido "ke, sirri ne" tayi murmushi "fada min, love letter kake rubuta min?" Yace "in kalaman soyayya zan gaya miki Fatima ba zan rubuta su a takarda ba, zan kalli cikin idonki ne in gaya miki, ko kuma in rada miki a kunnuwan ki" ta bata fuska "to wa kake rubuta wa?" Ya bude littafin ya nuna mata inda ya fara rubutu yace "our baby" tayi dariya tana shafa rubutun tana jin son babyn da ko cikinsa babu. Sai ta gyara zaman ta ta kwantar da kanta a kafadar sa tace "me zaka rubuta masa?" Yace "a letter. Daga yau kullum zan dinga rubuta masa letter har sai ranar da aka haife shi. In ya girma ya iya karatu sai in bashi ya karanta" tace "kullum? Me zaka ke rubuta masa kullum?" Yace "duk abinda nayi a ranar zan bashi labari, maybe a ciki zai dauki wani darasi na rayuwa".

Ta lumshe idonta a lokacin da jirgin yake dagawa dasu zuwa sararin samaniya, ya bita da kallo har sai daya tabbatar bacci ya dauke ta sannan ya jawo diary din ya cigaba da rubutu.

Dear Baby.
Idan kana tare da littafin nan hakan yana nufin baka tare dani, dan in har ina raye ba zan baka littafi ba zan zauna ne in saka ka a gaba in yi ta baka labarin irin son da nake yi maka. Idan har bana tare da kai, Idan har ban samu naga fuskar ka a duniya ba, ina fatan ka zama yaro na gari kayi aiyukan alkhairi dan in samu damar ganin ka a lahira. A aljanna..............

Kiran wayar Hussain ce ta tashi Hassan daga bacci, yayi juyi yana kifta idonsa yana jin kansa yana yi masa ciwo saboda baccin da bai samu ya ishe shi ba. Ya dauki wayar "ya akayi?" Hussain yace "wai bacci kake yi? Karfe nawa ne a nan? Nan da 30 minutes zamu taso" Hassan yace "zaku taso kuma? I tot jiya kace min sai next week, what's up?" Hussain yace "nothing kawai na chanza shawara ne, kawai nayi missing dinka ne" Hassan yayi tsaki "neman magana dai kake yi. Ni ka katse min bacci ka sa kai na zai fara ciwo. Okay sai kun karaso" ya kashe wayar tun kafin Hussain ya bashi amsa, ya koma ya kwanta tare da dora pillow a kansa yana so ya koma bacci amma shi kansa yasan wasa yake yi.

Dama jiya da kyar bacci ya dauke shi saboda abubuwan da suka yi masa yawa akai. Ruqayyah. Ta bashi mamaki ba kadan ba kuma maganganun ta sun taba zuciyarsa ba kadan ba, gidan arziki, you have nothing, wadannan sunfi duk sauran kona masa zuciya. Bai taba tsammani ba in wani ne ma ya gaya masa cewa ida zata fada masa haka to kuwa tabbas ba zai yarda ba. Abu daya daya gano a gurinta shine ta bawa kudi wani babban matsayi a zuciyarta. Wannan wani abu ne da tayi matuƙar kokari gurin boye masa tun haduwar su sai jiya ya fahimta, bayan wannan kuma bai san what other things ta boye masa ba, bai san how many lies ta gaya masa ba.

Ya mike ya shiga toilet ya hada wa kansa ruwa mai zafi yayi wanka wai ko zaiji ya watstsake, ya fito ya kalli dining yaga babu alamar an bude shima, ya kalli dakin Ruqayyah bai ji motsin kowa ba sai ya fito ya tafi gidan Aunty. A palo ya tarar dasu suna ta hayaniya suna ta cin abinci, ya gaishe da Aunty sannan ya ce Khadijah ta zuba masa abinci, Aunty tace "ina Ruqayyah kuma?" Yace "bata jin dadi, ta kwanta kuma bana so in tashe ta" Aunty tayi murmushi tace "ai ko wadannan guntayen yaran aka barta dasu sai sun saka mata ciwo" Safiyya tace "kai Aunty, salihan yara irin wadannan da ko kuka basa yi?" Aunty tace "basa kuka fa, amma duk wanda ya dauke su shine zai yi kuka dan sai sunyi masa duka" Nafisa tace "lafiyar kenan Aunty, duk yaran da kika ga ya zauna shiru to kuwa tabbas bashi da isashshiyar lafiya" Aunty tace "sai kuyi tayi ai, ku da ba'a taba muku yaya" Hassan dai yana jinsu bai tanka ba yana ta murmushi, duk wata magana data shafi gudan ransa yana sonta.

Ya jima a gurin Aunty suna shawarwari akan shirye shiryen bikin Safiyya da Jabir daya gaba to, ga kuma Hassana da tsohon ciki, sannan ga graduation din Khadijah tace sai an shirya mata party. Shi so yayi manemin Khadijah ya fito a hada bikin dana Safiyya a huta amma hakan ba zai samu ba saboda ya tafi karo karatu sai ya dawo za'ayi, kafin nan ta gama service dinta. Sosai yake jim dadin yadda rayuwar kannen nasa take tafiya duk da maraicin uba amma abinda suke samu ko da ace suna da uban ba lallai ne su samu kamar haka ba.

Sai da ya gama zai fita sannan ya fada wa Aunty zancen dawowar su Hussain yau. "daga nan zan dan leka gurin Jabir sannan sai in wuce dauko su" sai yaga jikin Aunty yayi sanyi tace "Allah dai yasa lafiya, Hussain bai taba cancelling trip dinsa ba sai dai in da babban dalili" Hassan ya mike yana cewa "rabu da shi Aunty, kin san halin Hussain, he can be dramatic sometimes, wai missing gida yake yi sai kace wani jariri" Aunty tace "to Allah ya kawo su lafiya. Ai gwara hankalin nasa yake dawowa gida, gwara ya zauna a gida muma mu samu mu ganshi sosai".

Sai daya biya gurin Jabir suka gama tsare tsaren su na shirin da suke yi zuwa Gombe gaisuwar iyaye, sannan yayi masa sallama ya tafi airport dan ya lokacin isowar su Hussain ya gabato. Bai jima da zuwa ba suka zo. Tun daga kallon farko da yayi wa fuskar Hussain ya fahimci akwai damuwa a tare da shi, kuma yaji gabansa ya fadi damuwar da take zuciyar Hussain ta wuce har zuwa tashi zuciyar ta kuma samar masa da damuwa. Ko menene yake damun Hussain to babba ne dan Hussain bashi da damuwar, da wahala kaji abinda zai bata masa rai balle har ya nuna a fuskarsa. Kuma duk da haka ma a yanzun in ba Hassan din ba da wahala wani yace akwai damuwa a fuskarsa, sai dai ko Aunty.

To ko an samu problem ne a fertility test din nasu?

Sai dai kallon fuskar Fatima ya saka ya fahimci ko ma menene problem din Hussain bai shafi Fatima ba kuma bata da masaniya akan sa. Hannunsu sarkafe dana juna suka karaso gaban Hussain "hello bro" sai kuma ya jawo Hassan ya rungume shi a jikinsa, d Hassan felt the tighness of his grief. Fatima tayi dariya, "Lallai Hassan da gaske anyi missing dinka" yayi murmushi yana cire Hussain daga jikinsa yace "iyayi, in yayi niyya kuma gobe ma ya ce wata tafiyar zai sake yi".

Har suka je gida Hassan yana lura da ya yanayin Hussain, yana kuma kara tabbatar wa da kansa da cewa akwai abinda yake damun Hussain din. Suna zuwa yayi packing, Hussain ya fito yana mika yace "home sweet home" sannan yabi kannensa da suka taho tarensa har Hassana ita kowa yayi hugging dinta sannan ya wuce har cikin gidan yayi hugging aunty itama. Duk suna tayi masa dariya, shima dariyar yake yi yace "baku san yadda nake son ku bane ba, you are all here, my life is all here" sai kuma ya tuno da twins yace "ina yaya na? Aje a dauko min yayana".

Ranar nan suka karasa wuni tare, sukayi lunch tare dinner ma haka sannan mijin Hassana yazo ya dauke ta, Fatima da Hussain ma suka tafi saboda sun dauki gajiya gashi basu huta ba. Hassan ma yayi wa Aunty sallama bayan ta bawa yaran ta su Yusuf sun mayar dasu gurin Ruqayyah, sai ta tsayar da hassan tace "menene yake damun Hussain?" Ya daga kafada yace "ban sani ba Aunty, tun da suka sauka na lura akwai abinda yake damunsa amma gobe zan tambaye shi" ta gyada kai tace "ka tambaye shi kaji, naga damuwa a fuskarsa. Sai da safe, ka duba Ruqayyah da jiki" ya gyada kai tare da ajjiyar zuciya, ambatar sunan Ruqayyah da tayi ya tayar masa da mikin da ke cikin zuciyarsa a kan Ruqayyan. Har baya son ya koma gida ma, amma babu yadda zaiyi dole ya koma.

A palo ya tarar da ita da plate din abinci a gabanta tana waya tana dariya, da alama hirar tayi mata dadi. Ta dan dauke wayar daga kunnenta tayi masa sannu da zuwa, ya amsa babu ya bo ba fallasa. Yaran suna kwance akan kujera Aminu yana bacci Yusuf kuma yana kokarin rigima. Ya saka hannu ya dauke shi yana mishi wasa ya wuce dashi dakin sa.

Ta bi bayansa da kallo sannan ta koma kan wayarta. "Na gaya miki Minal ba lallai bane ya barni inzo, ynazu ma kin ganshi ya shigo gidan ko kallo ban ishe shi ba duk uwar kwalliyar da naci" Minal tace "k kika so ai, na gaya miki ki zo mu koma gurin mutumin nan kin ki, bawan Allah jiya ma sai da ya tambaye ni ke yana cewa ya kike ciki. Ki je kawai a rufe miki bakin Hassan yadda ko Aunty kika zaga sai dai ya kalle ki ya dauke kai" Ruqayyah tace "hmmm. Ke dai bar ni kawai in tashi in je kar in kara wani laifin akan wani" ta katse wayar tana tauna shawarar minal a zuciyarta.

Ta tarar da shi a kwance da Yusuf akan cikin sa yana yi nasa wasa yaron yana bangala masa dariya, ta zauna a gefen gadon tace "ashe Hussain ya dawo, no sai ji nayi ance a kawo twins inji Hussain" " eh ya dawo" yace mata. Tace "amma ko ka gaya min? Ai da na shoga nayi masa sannu da zuwa ko?" Ya juyo yana kallon ta yace "da aka aiko ki vada Twins din ai kinsan ya zo din kenan, idan da kinyi niyya da zaki iya fita a lokacin kice masa sannu da zuwa" tace "to ai ban tambayeka ba ko? Ya zanyi in fita ba tare dana tambaye ka ba" yace "okay, sorry. Nayi tunanin kina da number waya ta ashe baki da ita" ta ji daci a ranta, tayi shiru tana kallon yadda ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login