Showing 21001 words to 24000 words out of 300844 words

Chapter 8 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2030

ya turo ka kawo musu kudin?" Salisu ya mike tsaye daga durkushen da yake a gaban jakar, fuskarsa dauke da yanayin tashin hankali da kuma tsantsar rashin gaskiya yace "am oga....ai wato oga.....oga me kake yi anan?" Ya fada cikin inda inda. Sai yanzu Hassan ya fahimci muryar da yake ji, sai yanzu yayi placing muryar, yaji zuciyarsa tayi sinking, yaji gwuiyoyinsa sunyi masa sanyi sun kasa daukan sa har sai daya durkushe a gurin yana jin zuciyarsa tana yi masa zafi.

"Salisu? Me yasa? Me yasa zaka yi mana haka ni da danuwana? Wannan wanne irin cin amana ne? Menene bamu yi maka ba? Menene bamu yiwa iyayenka ba? In kudi kake so mai yasa ba zaka tambaye ni ba? Me yasa ba zaka tambayi Hussain ba? Duk abinda kake so zai yi maka"

Salisu ya shafa kansa yana girgiza kansa yace "zaku bani kudi na sani amma ba irin wadannan kudin ba" ya fada yana zaro wrapper ta dollars ya jefa a gaban Hassan "irin wannan kudin na keso, irin kudin da zan ke chanja motar da naga dama a lokacin da naga dama kamar yadda oga Hussain yake yi" Hassan yana girgiza kansa shima yace "akan kuɗi? Akan kuɗi zaka ci amanar mu? Akan kudi zaka saka rayuwata acikin hatsari salisu? Menene kuɗi? Is the money really worth it? Is this money really worth haɗa rayuwarka data irin wadannan mutanen?"

Ya fada yana nuna sauran mutanen guda biyu, maganar ta makale a bakinsa sanda ya hada ido dasu, duk su biyun shi suke kallo kuma idanuwansu babu ko da digon imani a ciki sannan bakin bindigarsu yana saitin sa, zuciyar Hassan ta sake bugawa yana kara fahimtar situation din daya ke ciki. Yanzu ya tabbatar ba zasu barshi da rai ba, ya gan su yaga fuskokin su, asirin Salisu kuma ya tonu yasan yana da hannu a ciki, babu yadda za'a yi su barshi da rai.

Ya girgiza kansa da sauri yana daga hannayen sa sama "babu wanda zan gaya wa, ku dauki kudin ku kuyi tafiyar ku nima zanyi tafiya ta babu wanda zai ji komai daga bakina" Dayan yace "ai ba yau aka haife mu ba Malam, kana fita daga gurin nan zaka bawa duk wanda zai tsaya ya saurare ka labari a kanmu, zaka kwatantawa police kamannin mu da bayanin gidan nan. Niyyar mu mu sake drugging dinka mu mayar da kai har kusa da gidan ku inda za'a tsince ka a mayar da kai gidan ku, but you seems to be in a hurry, shine ka fito ka rusha pland din mu. Kai kayi asara, mu mun riga mun karbi kudin mu".

Salisu ya kalli Hassan sannan ya kalli sauran mutanen biyu, sai ya tsallaka ya shiga tsakani "ba zaiyi magana ba, bamuyi haka daku ba, kuɗi muka ce zamu karba kuma gashi mun karba bamuyi daku cewa zaku kashe shi ba, na gaya muku brother dinsa zai bada kuɗin kuma gashi ya bayar. Let him go".

Babban ya saka hannu ya ture shi yana cewa "bamuyi Yarjejeniyar cewa zai ga fuskar mu ba, yanzu yaga fuskokin mu kuma yaganka, the deal is off, dole ya mutu"

Nan take musu ya kaure a tsakanin su, shi Salisu baya son a kashe Hassan, so yake a barshi ya tafi in yaso sai su gudu su bar kasar, su kuma basa son taking that risk. A lokacin ne Hassan ya ga dama ta same shi, ya lura da yadda mutumin ya rike bindigar a sassauce dan haka yayi yunkuri ya doke bindigar ta fadi kasa can karshen dakin, cikin second daya duk su ukun suka kaiwa bindigar wawaso, shi kuma a second din ya kama window ya haura, ba tare daya jira komai ba ya doshi kofar shigowa gidan a guje duk da ciwon da kafarsa take yi masa.

Yana fita daga gidan yaji karar harbin bindiga, bai waiga ba kuma bai tsaya ba sai ma kara mai da yayi yayi hannun dama ba wai dan yasan hanya ba sai dan neman Sa'a.

Kamar yadda yayi tsammani, gidan a cikin unguwa yake, duk da dai ya dan yi gefe kadan kuma kwangwaye ne a zagaye dashi kuma shi din ma kusan kwangon ne, inda ya hango gidaje sosai nan ya dosa duk kuwa da cewa duhun dare ya ratsa sosai dan ma dai akwai hasken farin wata wanda yake haska masa hanya, layikan babu kowa, duk gidajen mutane da shaguna a rurrufe, a lokacin yaji zafin wani abu kamar an saka karfe a wuta an goga masa a gefen wuyansa, zafin yazo tare da sake jin wata karar bindigar daga bayansa. Bashi dako tantama yasan cewa harbinsa akayi kuma bullet din ya wuce ta gefen wuyansa.

Kwanar daya gani a gabansa ita ya sha a guje, yana shan kwanar yaga wani gida a zagaje da langa langa sai ya samu kansa da bude gefen langa langar ya shige cikin gidan, yaji tsinin wani abu ya shige cikin kafarsa dako takalmi babu, azaba ta saka shi ya fadi kasa yana rike kafar tasa da hannu biyu yana tunanin cewa koya tsira daga wannan halin zai iya rasa kafarsa. Ya saka hannu ya shafa kafar yaji kusa ce ya taka ta shige cikin kafar, ya kama ta ya zare daga jikin kafar yana rintse idonsa cikin azabar zafi sannan kuma ya saka hannu daya ya rike gefen yuwansa da yake zubar da jini, daya hannun kuma ya rike kafar tasa itama da take zubar da jini. A hankali ya zame ya kwanta a gurin yana mayar da numfashi.

********************************************

Tun farkon dare Ruqayyah da Sumayya suka dauko littattafan su suna karatu saboda yanayin jarabawar da suke ciki. Babu wanda yake magana a cikin su sai dai lokaci zuwa lokaci sukan dan tambayi junan su abinda basu fahimta ba kuma suyi wa junan su bayani har su samu su fahimta din. Lokaci zuwa lokaci kuma Ruqayyah takan yi tsaki "yar wayar nan ma ta zama ni bamu da ita, ballantana mu ringa shiga yanar gizo muna duba abubuwan da bamu sani ba kamar yadda sauran ɗalibai suke yi" Sumayya tace "Rukee ki gode Allah. Ke ta waya kike yi, wani ta abincin da zaici yake yi, wani haka ya kwanta yau bai ci komai ba, wani ma kuma bama ya zuwa makarantar gabaki daya" Ruqayyah tace "kaina na sani Sumayya, abinda yake damuna nake fada ba abinda yake damun sauran mutane ba. Idan ba kyason ji ki to she kunnuwanki" daga nan Sumayya bata kara tanka mata ba suka cigaba da karatunsu har dare ya raba sosai sannan suka yi adduoin su suka kwanta. Bayan sun kwanta ne suka ji wata kara mai kama da harbin bindiga. Sumayya ta mike zaune da sauri "Ruqayyah? Kinji abinda naji kuwa? Kamar karar bindiga nake ji" Ruqayyah ta gyara kwanciyar ta "ke kika sani, karar bindiga kuma Allah na tuba a zamanin nan ai ba bakon abu bane ba" Sumayya ta jawo jiki tazo ta makalkale a jikin Ruqayyah "ni wallahi tsoro nake ji, kar fa ace yan fashi ne suka shigo unguwar nan" Ruqayyah ta ture hannunta, "dan Allah malama ki bar ni inyi bacci na, in yan fashin ne ma nan gidan zasu shigo? Me zasu dauka a nan gidan? Alluna ko ƙasa?" A lokacin suka sake jin karar wani harbin na biyu, Sumayya ta takure a guri daya tana adduoi, Ruqayyah kuma tayi tsaki tana gyara kwanciyar ta. Sai kuma ta mike zaune kamar wadda aka mintsina tana cewa "ni fitsari nake ji ma, toilet zanje" Sumayya ta rike ta "harbi fa ake yi Hassana, ke wacce irin zuciya ce dake?" Ruqayyah tace "to ni tunda bani ake harbi ba ina ruwana, ko so kike yi inyi fitsarin a kan katifa? Ki kwantar da hankalin ki ba anan kusa bane ba can layin bayan mune maybe ma police ne suke training" Daga nan ta fita ko fitila bata dauka ba saboda dakakkiyar zuciyarta.

Da addu'a a bakinta ta shiga toilet din, ta tsugunna bakin rariya tayi fitsarin ta tayi tsarki sannan ta tashi tana gyara rigarta, anan ne taga abu kamar jini, tayi shiru tana kallon abin sannan idonta ya sauka akan langa langar da take a bude kamar an dube ta da karfi, tabbas an shigo gidan nasu kuma wanda ya shigo din yaji ciwo. Ta mike da sauri tana buɗe baki da niyyar yin ihu sai taji an saka hannu an toshe mata baki ta baya an saka wani hannun an jata baya zuwa cikin inuwar da take jikin katanga, ta jita a jikin mutum, ya hada ta kirjinsa, shi kuma ya jingina da jikin katangar.

Daga karfin hannun daya riketa ta fahimci namiji ne, daga warin da take ji yana tasowa daga jikinsa na datti tasan ba daga guri mai kyau yake ba, daga kuma bugun zuciyarsa da take ji tana bugawa da sauri sannan da kuma karfi a kirjinsa tana bugun bayanta tasan cewa a matukar tsorace yake.

A lokacin ne taji motsin wasu sun shigo kwanar gidan su a guje, daya yana tambayar dayan cikin hausa marar kyau "ka tabbatar nan kaga ya shigo?" Dayan yace "nan ya shigo, am very sure" suka wuce da sauri. Mutumin daya rike ta ya sassauta rikon da yayi mata, sannan ya kawo fuskarsa dai dai kunnen ta a hankali yace "help me, please. Ki taimakamin, dan Allah"

Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.


Episode Ten: Brave and Selfless

Last free Episode

"Please, help me. Dan Allah, ki taimaka min" Sai kuma ya cika ta a hankali ya bi jikin katangar ya fadi kasa.

Sai data ja numfashi sosai ta dawo cikin hayyacin ta sannan ta juyo tana kallonsa daga tsayen da take a kansa, sai kuma ta sunkuyo sosai tana kare masa kallo, he looked dirty and terrible. Ta kuma lura da ciwon da uake fitar da jini a wuyansa. But there is something about him, something da yake ta fincikar zuciyarta zuwa gare shi ta kuma kasa fahimtar menene, ta durkusa tana karewa fuskarsa kallo ko zata fahimci ko ta sanshi somewhere amma taga cewa bata taba ganin wannan fuskar ba. But something a zuciyarta keeps screaming "money" ta kuma rasa a ina money din yake.

Tayi analysing situation din. Ta tuno da sautukan da suka ji a daki masu kama dana harbin bindiga, ta kuma tuno da mutanen da taji sun wuce ta kusa da gidan su kuma da alama wani suke nema, ta kalli Hassan tana tabbatar wa da kanta cewa shi ne wanda suke nema, kuma sune suka ji masa ciwon jikinsa. Amma me yasa? Waye shi su kuma su waye? Zata iya yiwuwa shi mugu ne su kuma police, za kuma ta iya yiwuwa sune mugaye shi kuma victim dinsu. " A kidnapped victim" zuciyarta ta gaya mata. Ta kalli kayan jikinsa, duk da cukurkudewar su amma ta fahimci masu tsada ne, meaning shi din mai kudi ne.

Ta girgiza kanta tana son ta saita tunanin ta. "Uwar biyu an sace yaron nan, yaron da yayi mana interview wai ana tunanin masu garkuwa da mutane ne suka dauke shi" ta tuno da maganar Baba tun last week, dazu da yamma ma sai da taji yayi maganar "yaron nan har yanzu ba'a ganshi ba uwar biyu, dogo ne baki mai matsakaiciyar kiba da kyakkyawar fuska. Har yanzu ina ganinsa a idona. Allah ya bayyana shi"

Ta sake kallon Hassan, he fits the description. Akwai kyakkyawar fuska kam babu laifi. She might be wrong but she is going to help him, tasan in taci nasara zata samu reward mai kyau. Bata san ta yadda zata taimaka masa ita kadai ba kuma bata son taso mutanen gidan su saboda tana son ya san ita kadai ta taimaka masa saboda yafi ganin kokarin ta sosai dan tafi samun reward mai kyau. Abinda zata yi din yana da hatsari but she is going to do it. Ruqayyah ce fa, Ruqayyah kuma bata jin tsoro.

Ta tattaba fuskarsa, ya dan bude ido yana kallon fuskarta ta cikin hasken farin wata kamar yadda itama take kallon tasa fuskar tace "zan taimaka maka. Bansan ko waye kai ba za kuma ka iya cuta ta na sani amma na fahimci kana bukatar taimako dan haka zan taimaka maka dan Allah ba dan komai ba".

Ta cire dankwalin kanta ta yaga shi gida biyu ta ninke part daya ta dora a ciwon wuyansa sannan ta daure wuyan da dayan part din. Ta taba jikinsa taji ya dauki zafi alamar zazzaɓi ya fara saukar masa. Ta rafa lissafin abin yi. A lokacin taji maganganun mutanen sun kuma dawo wa farkon layin daya yana cewa "police might be on their way. Wani zai iya reporting harbin" dayan yace "not Nigerian police. Am not leaving unguwar nan sai na mayar dashi gawa. Gida gida zamu bi. Am sure na ganshi ya shigo layin nan na tabbatar he is hiding a cikin wani gidan. Ta nan farkon layin zamu fara" ya fada yana knocking kofar gidan da yake opposite nasu da karfi yace "open this door ko mu fasa ta".

Hassan ya kamo Ruqayyah jikinsa, idonsa yana kokarin juyewa, jini yana dibansa ya sake cewa "help me please. Ki kai ni gurin Hussain" dusu dusu yake ganin ta. Ta cire hannun sa daga jikinta tana jin wani iri, ita tun da take namiji bai taba taba ta ba, ko brothers dinsu basa irin wannan wasan saboda sun samu tarbiyya mai kyau a gurin Inna ade da Baba. Ta rada masa. "Ka kwanta anan, kar kaje ko'ina. Kar kayi motsi. Ina zuwa" sai ta mike zuciyarta tana yi mata plan na abinda zata yi. Ba tare da tsoro ko shayi ko kokwanto ko kuma tunanin komai ba ta zagaya ta daya side din toilet din ta taka bucket ta kama katanga ta haura, Hassan ya bi katangar da kallo sannan ya mayar da idonsa ya rufe yana jin tunanin sa yana barin kwakwalwar sa.

Ruqayyah ta dira a bayan gidan su, tana jin kafarta tana amsawa ta dan jima har taji kafar ta saki, tana jin maganganun mutanen a daya side din gidan daga dukkan alamu an bude musu kofar gidan sun shiga. Ta ja dogon numfashi sannan ta fita a guje tamkar yar tseren gudu, dogayen ƙafafuwan ta suna taimaka mata gurin covering distance mai yawa cikin lokaci kankani taje karshen layin bayansu sannan ta zagayo kan layin su gaban gidan dayake karshe, ta durkusa tana mayar da numfashi sannan ta mike tsaye tayi gyaran murya ta bude muryarta da dukkanin karfinta ta fara ihu "wayyo Allah jama'a ku taimaka min ga wani ya shigo min daki. Wayyo Allah gardi a dakina. Jama'a ku taimaka min jini ne a jikinsa"!

Ta ringa fada tana maimaita wa, daga can ta hango mutanen sun fito da sauri daga gidan da suka shiga suna hasko inda take da fitila, sai kuma taga sun taho a guje zuwa wajenta. Daya da touchlight a hannun sa dayan kuma da bindiga.

Ta yi saurin shigewa cikin wani kango yadda ba zasu ganta ba sai dai suji sautin muryarta. Tana jin sun kusa zuwa tayi shiru, taji sunzo gidan karshe suna buga kofar da karfi, mai bindigar ya ture dayan ya saka bindiga ya harbi lock din gidan, karar bindigar yana amsa amo a cikin shirun daren.


Tun harbin farko inna ade ta bude idonta, ita dama bata fiya yin nauyin bacci ba. Ta jima kwance tana tunanin anya kuwa da gaske karar bindiga taji? A lokacin ta sake jin ta biyun. Ta mike zaune tana salati, abinda da uwa, yayan ta ne suka fara fado mata a rai, matan suna cikin gida kuma dakin da suke ciki na kasa ne, an ce kuma bullet baya iya wuce katangar kasa, samarin ne take jiwa tsoro, sune suke kwana a shagon gidan makotansu tate da samari da yawa kuma ginin siminti ne kar fa bullet ya same su.

Daga nan ne kuma taji ana bubbuga kofar gidan daya ke kallon nasu. "Open this door ko mu fasa ta" taji an fada da murya mai karfi. Ta fara jijjiga Baban biyu tana salati "baban biyu ka tashi barayi sun shigo unguwar nan, gasu can suna buga gidan Maman Minal" ya mike zaune yana salati shima yana mitstsika idonsa. A lokacin ne suka ji karar dirar mutum daga katanga. Kuma kamar katangar toilet dinsu ta baya, ko dai an hauro katangar an shigo gidan ko kuma an haura an fita. Inna ade ta mike "yan biyu na!" Ta fada cikin tashin hankali "baban biyu an shigo mana gida kar a shiga dakin yaran nan ayi musu wani abu na shiga uku" ta fada tana laluben hanyar fita daga dakin. Dama fitilar su daya a gidan kuma yaran suke bawa su su kwanta a haka.

Baban biyu ya rike ta "tsaya anan kar ki fita, bara ni inje gurinsu" ba tare daya jira abinda xata ce ba ya wuce ta ya bude kofar dakin ya fita. A bakin kofar dakin yaga Sumayya a tsaye, idanuwanta a waje, da touchlight a hannunta amma kuma a kashe. Cikin rawar murya da karkarwar jiki tace cikin rada "Baba naji an hauro gidan nan ta bandaki kuma Ruqayyah tana bandakin" bai jira karashen maganar tata ba ya karbi fitilar hannunta ya tafi bandakin cikin sauri. Inna ade itama da kunnuwanta suka jiyo mata kalaman Sumayya ta fito da sauri daga dakin tabi bayan mijinta zuciyarta kamar zata bar kirjinta. Sumayya, ganin an barta ita kadai yasa itama ta bisu da sassarfa.

Yana shiga toilet din ya kunna fitilar hannunsa, haske ya karade bandakin tare da bayyanar masa da jinin da yake malale a gurin, yayi kokarin kare Inna ade kar ta gani, a lokacin ne kuma ya ga Hassan a kwance a kasan katanga yana numfashi da kyar. Wannan ya tabbatar masa da cewa jinin bana Ruqayyah bane ba na wannan mutumin ne. Amma ina Ruqayyah?

A lokacin ne suka jiyo ihu

"wayyo Allah jama'a ku taimaka min ga wani ya shigo min daki. Wayyo Allah


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login