Showing 180001 words to 183000 words out of 300844 words
gare ki ba ke zaki je gare shi ba".
Wannan maganar bata saka Sumayya ta hakura ba, ta cigaba da yiwa Inna Ade maganar Adam lokaci zuwa lokaci amma kuma ga mamakin Inna Ade ko sau daya Sumayya bata taba ambatar sunan Ruqayyah ba duk kuwa da yawan zancenta da Inna Aden take yi kullum. Ko ranar da Ruqayyah tazo gidan Baba yayi mata korar kare ma Sumayya bata fito daga daki ba balle taga ramammiyar fuskar Ruqayyah.
A hankali Sumayya ta cigaba da zuwa makaranta, ta cigaba da karatu duk da dai ba kamar da ba. Sukan hadu da Zulaihat lokaci zuwa lokaci kuma a hankali sai suka fara kawance, basu taba haduwa sunyi zancen Ruqayyah ba, sai dai sukan yi hirar Aminu da Yusuf da kuma little Hussain. Wani lokacin kuma Sumayyan ta kan je har gida taga yaran wani lokacin har ma ta tafi dasu gida su kwana biyu tare da ita kafin ta dawo dasu. Wannan ya saka basu manta da ita ba, suka saba da ita sosai. A haka shekara ta zagayo, Sumayya da Zulaihat suka shiga shekarar su ta karshe a jami'a. A lokacin ne akayi addu'ar shekarar Hussain da mutuwa, a lokacin ne kuma aka gabatar da walimar bude estate din farko da Hassan yayi, a lokacin ne kuma Zulaihat ta gayyaci Sumayya.
Tare suka tafi da Inna da Baba da Zunnur, saboda Hassan yazo har gida ya gayyace su suma. Anyi addu'a, anci ansha kuma an zagaya anga gida. Ita da Sumayya taga Inna tare da Aunty suna hira, sai ta basu guri ta tafi gurin su Zulaihat suna admiring flowers din gidan. Bata ankara ba sai waiga wa tayi ta nemi su Inna ta rasa, data nemi ba'asi sai aka ce mata ai sun tafi. Hankalin ta ya tashi dan bata da ko kwandala a jakarta, me yasa su inna zasu tafi su barta? Tana cikin tunanin Aunty ta kira ta, sai ta tarar dasu tare da Hassan suna magana sai taji tace masa "Hassan in ka gama sai ka sauke Sumayya a gida, su Sa'adatu sun tafi sun barta".
*The Fortune Teller*
Ya juyo yana kallonta, suna hada ido tayi sauri ta sauke kanta kasa tana kokarin barin gurin sai Aunty tace "Sumayya ki jira shi ya karasa dai ya kaiki gida" ta gyada kai, amma sai aunty tace "kinji?" A dole tace "eh naji aunty, zan jira shi" Aunty tace "good" sannan ta juya tana harhada kan yayanta da jikokinta. Sumayya tana kallon su suka shiga motocin su suka fara fita daga gurin, tana son tace su rage mata hanya amma babu dama dan haka ta ja bakinta tayi shiru ta bisu da kallo har suka fita sannan ta samu kujera can gefe ta zauna da waya a hannunta tana kallon tsofaffin pictures dinsu da Adam, in ta kai karshe sai ta dawo farko ta kuma maimaitawa sannan ta koma kan chats dinsu tana bi tana karantawa tana murmushi, ta karanta message dinsa na karshe "you know I love you, right?" sai taji hawaye yana diga akan wayar, tayi sauri ta dauke su a hankali tace "and I love you too" sai ta kife screen din wayar tana jin zuciyarta tana zafi. Me yasa ba zai zo ba? In dai har yana tare da iyayensa kuma yana cikin koshin lafiya ai ya kamata ya nemeta ko dan ya gaya mata cewa yana lafiya tunda yasan zata shiga damuwa saboda jin shiru daga gare shi. Sai taji tana jin haushin sa, To ko dai wani abun ya same shi ne?
Ta daga kai tana kallon mutanen da suke ta hada hada a gurin, kusan duk yan uwa sun tafi sai abokan Hassan suma da yake ta sallama dasu suna shiga motocin su suna fita, tasan da Adam yana nan maybe shima da yana gurin nan, da dashi za'a yi wannan hidimar, duk da babu Hussain tasan da Hassan zai cigaba da rikon sa in ma ba zai rike shi ba tasan Baba zai iya rike shi a gidan su. Da yanzu yana nan yana karatunsa, da yanzu sun shiga level four tare.
Kamar dag asama taji ance "in kina yawan zurfafa tunani.....kina zama ke kadai kiyi kuka.....zaki tsufa da wuri" ya fada da sigar tsokana. Ta dago kai tana kallon Hassan, fuskar sa babu yabo babu fallasa. Ta fahimci tsokanar ta yake yi but she is in no mood for wasa dan haka ta mike tana gyara hijab din jikinta tace "kun gama?" Yace "mun kusa dai, kar mosquitoes su cinye ki naga kin zauna kusa da flowers shi yasa nayi miki magana ko zaki koma daga can" ya fada yana nuna inda aka saka kujeru "saura few mutane mu gama" taji babu dadi, tana so tace masa zata yi tafiyar ta kawai in yaso in taje gida ta karbi kudi ta biya, amma kuma bata so yaga hakan a matsayin rashin kyautata wa. Sai ta tafi inda yace mata ta zauna tana cigaba da daddanna phone dinta har taga ya kuma tahowa shida wasu maza su biyu, suna ta hirar su sai ya dago mata hannu yace "let's go" ta mike tabi bayansu, amma ta bar dan space a tsakanin ta dasu. Suka je gurin mota sai taga ya zagaya ya bude mata kofar gefen driver, yayi mata alamar ta shiga da hannunsa. Zata shiga kenan taji wani a gurin yace "Madam babu magana? Ya gida ya yaran?" Ta juyo tana kallon sa, daga yadda yayi maganar ta fahimci ya dauka Ruqayyah ce, sau ta kalli Hassan sai taga ya bude baki ya rufe ya kasa yin magana, sai tayi sauri tace "lafiya lau. Yara sun bi Aunty" sai dayan yace "ohh anyi musu wayo an kora su dan asha soyayya a hanya ko? To ayi a hankali dai kar a soye" suka yi dariya su biyun. Da sauri Sumayya ta shiga ta rufe kofar, tana kallon suka yi sallama da Hassan sannan suka fara tafiya kafin shima yazo ya shiga kusa da ita ya zauna ya tayar da motar, sai taji a ranta ina ma a baya ta zauna ba'a gaba ba? Duk kuwa da cewa ba wai yau ne karo na farko da suka zauna kamar haka ba ita da Hassan amma da yana a matsayin mijin twin sister dinta ne amma yanzu babu wancan link din, sai taga kamar zaman nasu bai dace ba.
Bai ce mata komai ba har yayi magana da mai gadin gurin sannan suka fita. Sai da suka dauki hanya sannan yace "sorry about that. Da yawa daga friends dina basu san mun rabu da Ruqayyah ba, and you guys look alike, sun dauka ita ce" ta gyada kai tace "babu komai,na fahimta ai" suka sake yin shiru sannan ya kuma yin gyaran murya yace "to ya kikaga gurin? Yayi? Huh?" Tace "yayi kyau sosai, Allah ya sanya alkhairi" yace "ameen, yayi kyau fa, ko Hussain in da zai gani sai yace yayi kyau. Kinsan shi ba komai ne yake burge shi ba" ya danyi dariya, "but it took a lot out of me, sai da aikin nan yayi min tas, in nace tas ina nufin tas, account dina sai da yayi reading 0.00" yadda ya jera zeros din yasa ta danyi murmushi, tace "tunda an gama ai shikenan" yace "shikenan fa, sai da family suka saka min hannu sannan na samu na kammala, gashi already yanzu har an karbi wasu daga ciki" tace "Masha Allah. Allah yasa musu albarka baki daya".
Ji take yi a ranta kamar ta tura motar dan suyi sauri amma shi ta fahimci wani taking time dinsa yake yi. Ta dan kunna wayar ta tana kallon time, ya kalle ta yace "expecting a call?" Ta girgiza kai, ira waye zai kirata a wannan lokacin in ba Inna ba? Inna ce kawai zata iya kiranta tace ya akayi bata dawo gida ba har yanzu, ita ma kuma bata kira ba dan tana tunanin she is in safe hands.
Suka sake yin shiru sannan yace "ya labarin friend dinku kuwa? Any development? Da muna waya da mijinta kuma daga baya da abubuwa suka dan sha kaina sai na manta da maganar" tace "Minal? Har yanzu babu labari fa, har an fitar da rai kuma. Iyayenta sunyi kuka sun gama, yan uwanta ma haka. Ni har bana so in je gidan su wallahi saboda Maman su tausayi take bani sosai" yace "dole ta baki tausayi, batan mutum akwai tashin hankali ai ballantana a yanayin da take ciki" ta gyada kai da sauri hawaye yana cika idonta, ya lura da sanda ta goge hawayen sai yace "yana gidan su, kin sani" ta girgiza kanta "bamu tabbatar ba. We don't know for sure" yace "Ruqayyah ta aikawa iyayensa labarin inda yake, dama sun dade suna nemanshi, babansa yayi tafiya a dai dai lokacin da shi kuma ya bata, ko motar da yake ciki ba'a dauka ba, ko waya ta da take cikin motar ba'a dauka ba. It adds up to me. Yana tare da iyayensa" ta juyo tana kallon sa ta cikin hawayen ta tace "da zai kira ni ai, a zaiyi making effort na ganin ya dawo gare ni ai. Ba zai manta dani gaka lokaci daya ba, except...." Yace "except what?" Tace "ta gyara zamanta tace "except ko iyayen sunyi masa asiri ko something" ya danyi murmushi yace "mu kuma sai muyi masa addu'a. Duk a inda yake zata same shi am sure watarana zai zo gare ki da kansa"
Tace "ina so ya dawo gare ni tabbas, but ba wannan ne babban abinda nake bukata ba, I just want to know cewa he is fine. In na samu wannan assurance din hankali na zai kwanta sosai" ya gyada kai yace "na fahimce ki. Me kike so ayi?" Ta girgiza kai tace "abinda nake son yi ba zai yiwu ba, ba za'a barni ba" yace "menene kike so?" Tace "inje nemansa" ya danyi dariya yace "imo? Zaki tafi neman Adam? To in kinje ta ina zaki fara? Ta wanne local government din ta wanne unguwa?" Tayi shiru tana wasa da hannunta, itama bata sani ba, basu taba wannan maganar da Adam ba. Sai yace "Baba ba zai barki ba, nima ba zan barki ba" ta dago kai tana kallonsa tan mamakin yadda ya dauki responsibility din barinta ya dora a kansa.
Sai yace "abu daya zan iya barin ki kiyi, ko kuma ince zanyi miki, zamu saka rana mu koma Kano tare, mu sake gwada bribing mai gadin nan mu gani ko zai kara bamu wani info din. Daga nan zamu gani idan family din sun dawo gida sai mu gani ko suma zamu iya samun wani abu daga gare su" ta gyada kai da sauri. "Yaushe zamu tafi?" Yayi dariya yana jinjina soyayyar da Sumayya take yiwa adam yace "zan saka rana, sai in gaya miki. Sai dai ni yanzu kamar ma bani da phone number din ki" ya fada yana mika mata wayarsa, da sauri ta saka masa number din tayi saving ta mika masa. Ya karba yana packing a kofar gidan su, tayi masa godiya sannan ta fita, ya bita da kallo har ta bude kofar gidan su ta shiga sannan ya ja motar, a ransa yana tunawa da ranar daya fara zuwa zance gurin Ruqayyah, lokacin da Sumayya ta fara fitowa yayi tunanin Ruqayyah ce.
Da safe Hassan ya shiga gaishe da Aunty kamar yadda ya saba yi kullum kafin ya fita, ya tarar da ita a dakin ta bata fito ba, ya zauna a kasa yana gaisheta tayi hamma tace "har zaka fita Hassan? Ni kaga gajiya ta hana ni saukowa daga kan gado har yanzu" yayi murmushi, "nima akwai ciwon jikin fa, akwai wasu tenants ne da aka hada ni dasu jiya, to munyi dasu zamu hadu a can yu da karfe goma na safe zasu ga gidan. Bana so suje ni banje ba" Aunty ta gyada kai tace "hakan dai dai ne, Allah ya bada Sa'a. Ka sauka kasa kaci abinci amma kafin ka fita, kar kaje ka fadi a hanya" ya mike yana cewa "faduwa kuma Aunty sai kace wani tsoho? Da saura na fa" tace "to waye tsohon? Kasan dai in muka yi tsere dai sai na wuce ka" baice komai ba sai yayi kamar zai fita sai tace "yauwa Hassan? Jiya ya kukayi da Sumayya kuwa?" Ya dawo yana kallon agogon sa yace "ya muka yi kuwa Aunty? Kince in kaita gida kuma n kaita, and that is all" ta mike zaune tana kallonsa tace "jiya Sa'adatu take gaya min maganar da kuka yi da Yusuf a kan Sumayya, me yasa ni baka gaya min kunyi haka dashi ba?" Ya zauna akan side table yana kallon ta, ya marairaice murya "Aunty, magana ce yayi min wadda take close to impossible, to menene kuma amfanin ayi ta jan maganar" tace "gwara da kace "close to impossible" ba impossible ba. Kag hakan yana nufin it is possible kenan. Ni da ta gaya min maganar dadi naji wallahi, sai naji hankali na ya karkata a wannan bangaren. Ko ba dan komai ba ko dan yaran nan guda uku da Allah ya bamu" ya girgiza kai yace "Aunty don't get like that please, yara ko a hannun wa suke zasu rayu, kuma yanzu they got you and they are doing just fine. Kar azo ayi abu for the wrong reason kuma azo ana dana sani daga baya" tace "eh yara yanzu suna dani, amma daga ni har kai bamu san kwana nawa yarage min a duniya ba" ya sake mikewa kamar an mintsine shi yana cewa "mu bar maganar nan haka please, babu wanda yasan gawar fari sai Allah, maybe ma ita Sumayyan ta riga ki tafiya Allah ne kadai ya sani" bata bar maganar ba tace "haushin Ruqayyah suke so su huce maka da Sumayya, baka ganin kin karbar kamar watsa musu kasa ne a ido? Ina laifin wanda ya nuna ya damu da damuwarka?" Ya dafe kansa yace "Aunty, yarinyar nan bata sona, akwai wanda take so daban, kuma tasan nasan alakar ta da wancan din kusan nine ma na hada su, idan na karbi tayin Baba b akya ganin kamar na zubar da girmana a gurin su ita da saurayin nata?" Tace "bansan wannan ba, abinda nasani kawai shine matar mutum kamar kabarinsa take, in matarsa ce ba zaka taba auren ta ba" Yusuf ya bude kofar dakin ya shigo, sai ya dane kafafuwan babansa yana murna sannan ya je ya kama hannun Aunty yana janta, "Aunty ki tashi daga baccin nan ki zo muje muci abinci" Hassan ya hade rai yace "kai! Fita ka bamu guri" yaron yayi kamar zaiyi kuka amma sai ya juya zai fita, Aunty ta kira shi ta dauko wayarta ta nemo wani hoto da Sumayya suka dauka tare da Zulaihat da Nafisa ta nuna masa tace "Yusufa wacece wannan?" Ya karba ya gani sannan cikin murna yace "mommy!" Sai ya fita da gudu gurin yan'uwansa.
Aunty ta kalli Hassan ta daga kafada tace "a gurin su mommy ce, ba step mom ba, duk matar da zaka aura will be their step mom not their mom. Kamar yadda nake a matsayin uwa a gare ku not a matsayin kushiyar uwa Sai kayi lissafin abinda zai iya faruwa da ku idan da ace iyayen mu basu yi tunanin hada aure na dana mahaifin ku ba. Maybe da bamu samu kan mu a matsayin da muke kai a yanzu ba. Wannan kadai ya ishe ka misali" ya sake cewa "aunty, this is a different case, na gaya miki yarinyar nan bata sona, in anyi abin nan zai zamanto kamar an tilasta mata ne" Aunty tace "nima sanda aka aura min babanku bana yi masa soyayyar aure, amma a yanzu da za'a dawo min da rayuwata baya ace in sake zabar miji da shi zan sake zaba over and over again"
Sai ya kama kofa ya bude zai fita ba tare da yace mata komai ba, tace "Hassan" ya juyo yanab kallon ta amma bai amsa ba sai tace "misali idan Sumayya ta yarda zata aure ka, zaka amince?" Yace "bata so na Aunty, ba zata yarda ta aure ni ba" ta sake cewa "misali nace ai, in ta yarda, zaka yarda kaima?" A rufe idonsa ya bude, sai kuma ya gyada kai yace "yes, zan yarda, but only in ta yarda, in ba tilasta mata akayi ba".
Wannan kenan.........
Bara mu leka muga yadda rayuwa ta kasancewa Ruqayyah a cikin wannan shekarar...........
A ranar data farka ta tarar ana katange gidan da take ciki, a ranar ne kuma yan aikin gidan kaf dinsu, wadanda suka yi aiki a karkashin fatima suka hada kayan su kaf suka zo yi mata sallama "zamu tafi, Allah ya sada mu da alkharinsa" Ruqayyah ta bude baki "ba gane zasu tafi ba, ni na sallame ku ne? Ni da iya kacin saninaba sallami kowa a cikin ku ba, ko akwai wata matsala ne wadda ban san daita ba?" Babbar cikinsu tace "babu wata matsala, kawai da bazamu iya cigaba da aiki a gidan nan ba alhalin masu gidan basa cikinsa" Ruqayyah tafara kufula, "ban gane masu gida basa ciki ba, ni nice mai gidan, wadanne masu gidan kumakuke magana akai?" Tace "gimbiya Fatima itace uwargidan mu, mutuniyar kirki da sanin ya kamata, tunda akayi auren ku ita muke yiwa aiki da haka yanzu lokaci daya ba zamu iya cigaba da aiki a cikin gidan nan sannan kuma ba a karkashin taba. Gwara mu tafi mu nemi wani aikin a wani gurin daban" Ruqayyah mamaki ya kamata, me suke nufi? Zasu iya yiwa Fatima aiki ammaita ba zasu iya yi mata ba? Dame Fatima ta fita?
Ta fara lallashin su da nuna musu cewa duk abinda Fatima take musu itama zata dora akai amma suka tubure suka ki zama. Har sun mike tace "zanyi muku doubling salaries dinku in kuka zauna" ita tana ganin wannan wani abu ne da ba zasu taba iya turning down ba amma sai taji daga daga cikin su tace "it is not about the money, it is about loyalty" daga nan suka fita suka barta a zaune.
Takaicin duniya ya ishe ta,