Showing 81001 words to 84000 words out of 300844 words

Chapter 28 - Tagwaye Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

2098

ya dan rissina ya gaishe da Hassan sannan ya mika masa key din motar. Sai kuma ya juyo yana kallon Ruqayyah yace "Madam barka da fitowa" ta nuna shi da hannu "kai! Me kake yi anan?" Hassan ya juyo yana kallon ta yace "kin san shi ne?" Bata amsa ba ta sake cewa "me yake yi a gidan nan?" Yace "Sumayya bata gaya miki ba? Let's go, zan gaya miki a hanya" ta sake juyawa tana kallon Adam sai ya daga mata kafada sannan ya juya yayi tafiyar sa hannayensa a cikin aljihun wandon sa.

Ta bude motar ta shiga shima ya zagaya ya shiga. Yana zama tun kafin ya tayar da motar tace "me Adam yake yi a gidan nan?" Yace "wai dama kin san shi ne? Da naga Sumayya tana biye miki shi na dauka baki san shi ba bata son ki sani" ta kara bata fuska tace "Sumayya? Wai kana nufin kasan shi tare da Sumayya?" Yace "a tare ma na gansu. Daga baya ba dauke shi aiki, yanzu driver ne shi a gidan nan. Yadda na fahimta kamar saurayin ta ne" ta sake cewa "Sumayyan? Lallai wannan yarinyar ta wuce duk inda nake tunani wallahi. Wato ashe Adam ne suke waya dashi, shine wanda ta karbi number dinsa a hannun ka kuka ce min wai abokin ka ne" yayi dariya, "I noticed bata son ki sani, I tot zata gaya miki kafin bikin mu shi yasa ban gaya miki ba" tace "ba zata gaya min ba ai. Ta san bata da gaskiya" ya dan bata rai yace "menene problem din? Ni a ganina kamar bashi da problem except that he was a christian sai ya musulunta, iyayensa har yanzu Christians ne. But character wise bana jin yana da aibu" Ruqayyah ta rike baki, tubabbe? Yanzu Sumayya a kan tubabbe zata kare? Amma ganin Hassan yana nuna hakan ba komai bane ba sai bata yi comment akan hakan ba. Amma sai tace "no you are wrong, yana pretending ne amma bana gari bane ba. A inda na sanshi, a inda muka fara haduwa dashi a motar sa ne taxi ya dauko mu daga school ni da Sumayya, and ge tried to touch me, a gaban Sumayyan. Shi yasa nayi mamaki da har zata kula shi har suke soyayya" Hassan yayi shiru maganar tana taba zuciyarsa, wato abinda ya dauko ya kawo musu gidan su kenan? Yace "tabbas biri yayi kama da mutum. Ranar dana fara ganin shi a kofar gidan ku ya faya min gaisawa yake so kuyi, amma sai yace da Sumayya zasu gaisa dan yasan in ya miki magana maba zaki kula shi ba. Wato wannan shine dalili" tace "tabbas. Yasan ni ba zan kuka mai dabi'a irin tasa ba". Kafin su je gidan Baba Hassan ya yanke hukuncin korar Adam. "Muna da yammata a gidan, he is a risk to them".

Sai da suka je aka yiwa Ruqayyah passport aka gama sannan suka biya ta bakery suka yiwa su Inna siyayyar kayan kwalama, suka kuma siya musu fruits da drinks da yawa sannan ya kaita gida, bai shiga ba yace zaije unguwa shima sai ya dawo zai shiga, ta turo Zunnur ya kwashi kayan ya shigar musu dashi.

Ita kanta sai data gansu sannan ta san tayi missing dinsu. Suma suna ta murnar ganinta kamar wadanda suka yi shekara basu ganta ba. Ta basu labarin tafiyar da zasuyi da Hassan da Hussain da Fatima, nan take su Zunnur suka fara jera mata list na kayan da zata siyo musu tsaraba. Anan suka ci abincin rana tare a palo, sai taji ta kasa cin abincin sosai duk kuwa da cewa babu laifi da kyansa duk da babu kaji amma akwai kifi da ganye a ciki. Amma kifin ne ma taji yana tayar mata da zuciya.

Sai da suka shiga daki da Sumayya zasuyi sallah sannan ta tayar mata da zancen Adam "yanzu dama Sumayya ashe Adam ne kuke wayar nan dashi? Duk wannan murmushin da kike yi ashe Adam kike yiwa? Yanzu ki rasa wanda zaki yi soyayya dashi Sumayya duk mazan garin nan sai inyamuri? Ina samarin hausawa? Ina fulani? Ina bare bari ina shuwa ina duk sauran kabila masu mutunci amma duk basu yi miki ba sai inyamuri? Kema kanki kinsan Inna Ade da Baba ba zasu taba karbar wannan maganar ba" Sumayya da take tsaye da hijab a hannun ta tace "kin gama? To bara in tuna miki, ni ce nake sonsa ba ke ba, in auren nema ni zan aure shi ba ke ba, ina ruwanki?" Tace "da ruwana mana, ke fa yaruwa tace, shi kuma drivern miji na ne, ba kya ganin alakar tsakanin ku kamar disgrace ne a guri na. Dama can ana min kallon wulakanci ballantana kin kara zubar min da mutunci" Sumayya tace "okay shine problem dinki? To ni babu ruwa na da kasancewar sa drivern mijin ki wannan problem dinki ne" Ruqayyah tace "amma dai ai na tabbatar kina da problem da kasancewarsa tubabbe ko?" Sumayya ta juyo tana yi mata wani irin kallo, Ruqayyah tayi dariya "ohhh kar dai kice min duk murmushin da kuke yiwa juna bai gaya miki ko shi waye ba" Sumayya ta ajiye hijab din hannunta tace "don't ever call him that again" Ruqayyah tace "in na sake kuma fa? Me zaki yi min?" Sumayya tace "zan tabbatar baki sake yiwa wani rashin kunya ba" Inna ta bude dakin ta tsaya tana kallon su "ohh ni Sa'adatu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yanzu yaran nan kwanan ku nawa baku hadu ba, amma daga haduwarku har zaku yi fadan naku da kuka saba? Yanzu kuma me ya hada ku?" A tare suka ce "babu komai Inna".


Not edited yau ma, sai an kara hakuri dani. Lol
Inna Ade ta bisu da kallo daya bayan daya, tana lura da tension din dake tsakanin su, da kuma bacin ran dake fuskar Sumayya, tasan cewa koma menene to tabbas babban abu ne tunda har ya bata wa Sumayya rai dan ko mai fadan da zasuyi Ruqayyah ce mai fushi amma Sumayya takan mayar da maganar kamar wasa. Amma bata so ta matsa musu akan lallai sai taji, ta fi son ta barsu suyi sulhu a tsakanin su kamar yadda suka saba. Tace "to ku fito ga baban ku nan ya shigo ku gaishe shi" tana fita Sumayya ta saka hijab din ta ba tare data kula Ruqayyah ba ta fita, ita ma Ruqayyah tayi kwafa ta bita a baya.

Tana zuwa ta tarar da baban a zaune da Sumayya a gaban sa tana bude ledar daya shigo da ita. "Baba naman kai ne wannan, ka ce gobe mu ci dadi kenan" yayi murmushi yace "sai ki dafa mana shi tun dare, da safe sai mu karya kumallo dashi. A zuba kayan kamshi da daddawa suji sosai" ta dauka ta fita dashi zuwa kitchen sannan Ruqayyah ta karaso ta durkusa ta gaishe da Baba. Da fara'a ya amsa mata. "Ya mutanen gidan naku? Kowa lafiya dai ko?" Tace "lafiya lau Baba. Kuma kuna lafiya ko?" Yace "alhamdulillah Hassana. Lafiya lau muke hankalin mu a kwance yake, banajin muna da wata matsala yanzu. Kinga abin hawan nan da kanin mijinki ya bani? Sulaiman ne yake jansa yanzu tunda suna hutu kuma kusan dashi muke cin abinci a gidan nan. Dan abinda zamu kara akai kadan ne, tunda mu ba yawa ne damu ba, kuma dama ba saba wa mukayi da kashe kudi masu yawa ba" Inna da take ajiye masa abinci tace "ni dai Baban biyu matsala ta daya ce a gidan nan" ya harde hannaye yace "matsalar me fa?" Sumayya ta shigo tana ajiye masa zobo mai sanyi a jug ta zuba masa a kofi. Inna Ade tace "duk jina nake yi babu dadi saboda rashin dalibai na da nake koyawa karatu. Na saba shekara da shekaru tun ina yarinya ta babu ranar da wani ba zai dauki karatu a gurina ba. Yanzu sai inji kamar ina asarar wani abu kullum" Baba yace "ai kuwa nima kadan ne banyi magana ba, musamman in yamma tayi sai inji gidan shiru babu dadi na saba da inji yara suna ta karatu" Ruqayyah tace "to ko a aika makota haka a gaya musu suke zuwa suna daukan karatun? Musamman in aka ce kyauta za'a ke yi musu zasu zo" Sumayya tace "anya kuwa? Bana jin zasu zo dan nan unguwar ba irin waccan bace ba, yaran su already suna da islamiyyar da suke zuwa, kunsan yanzu iyayen zamani sam sun daina kai yaran su makarantun allo sunfi gane wa da islamiyya" Inna tace "haka ne, acan na unguwar da muka taso ai duk daliban sun ragu, kuma abinda iyaye basa gane wa shine ba kowacce islamiyya ce ake iya baƙi sosai kamar yadda ake iya wa a makarantar allo ba, yaro zai iya baki, zai iya rubutu ta yadda karatunsa zai inganta sosai."

.Sumayya tace "amma Inna vda Baba, idan zaku yadda akwai wani dalibi da nake so in kawo muku ya koyi karatu a gidan nan. In kun amince" iyayen suka kalli juna sannan suka kalle ta, Ruqayyah ma ita take kallo, Baba yace "wanene dalibin? A unguwar nan yake? Yaro ne?" tana wasa da carpet tace "wani ne Baba, ba yaro bane ba kuma ba a unguwar nan yake ba. Amma duk inda yaje zai zo ya dauki ilimi a gurinku in dai gar kun amince zaku koyar dashi" Inna tace "mai zai hana mu koyar dashi? In dai yana so kice masa yazo ya karbi ilimi, mu kullum muna maraba da mai neman ilimi a gidan nan" Baba da yake ta studying Sumayya yace "a ina yake? Waye shi? Kuma shi yace miki yana neman ilimi?" Sumayya ta dago tana kallon Ruqayyah tace "a gidan su Ruqayyah yake, drivern mijinta ne" Ruqayyah ta bude baki tace "unbelievable! This is soooo not going to happen. Ina kokarin yakice shi daga can gidan ke kuma kina kokarin lika shi a gidan iyaye na? Ba zai yiwu ba, kar ma ki saka a ranki" iyayen suka juya suna kallon ta, Sumayya tace "iyayenki ko iyayen mu? Yadda kike ji dasu nima haka, yadda ba zaki kawo abinda zai cutar dasu ba nima haka ......"

Baba ya daga mata hannu "ya isa! Ya ishe ku! Menene wai? Waye kuke magana akansa?" Ruqayyah tayi saurin cewa "Baba wani inyamurin drivern taxi ne fa, wai dan abin kunya wai shi Sumayya take so, bayi kokarin hanata shine ta kakabawa Hassan shi ta matsa masa lallai sai daya dauke shi aiki kuma yanzu shine take so ta kawo shi gidan nan" Inna Ade ta bude ido tana salati "Sumayya? Me ya hada ki da inyamuri ni Sa'adatu?" Sumayya taji hawaye ya taru a idonta bata dauka inna zata yi reacting haka ba, Baba yace "dakata Sa'adatu. Hussaina gaya min menene hadin ki dashi"

Ruqayyah tace "Baba saurayin ta ne, Hassan ma ya sani" ya daga mata hannu, "bake na tambaya ba Hassana. Ki barta ta gaya min ai tana da bakin ta itama" Sumayya tace "Baba Musulmi ne shi, iyayensa ba musulmai bane ba shine ya musulunta ya baro gidan su da kowa nasa a kano ya taho kaduna saboda kyamatarsa da ake yi da kuma iyayensa da suke so ya koma gurin su. Bai gayamin cikakken labarin ba amma na fahimci haka ne abinda ya faru. Bashi da ilimin addini sai wanda yake tsinta a titi, yana so ya koya amma yana gudun tsangwama da kyama daga mu musulmai, mu wadanda ya zabi addinin mu akan na iyayen sa. Ina so ne in taimaka masa ya samu a gurin mu. Muma kuma mu samu ladan ilmantar dashi. Kuma bani na hada shi da Hassan ba, a tare na gansu, Hassan kuma shi yayi niyyar daukansa aiki bani nace masa ya dauke shi ba"

Ruqayyah tace "amma dai saurayin ki ne ko?" Sumayya tace "wannan kuma ba abinda ya shafe ki bane ba" Ruqayyah tace "abinda ya shafe ni ne mana, saboda ke yar uwa ta ce ba zan so abinda zai cutar dake ba. Adam kuma ba alkhairi bane ba a tare dake" Sumayya tace "ta ya akayi kika sani? Ji nake Allah shine kadai masanin gaibu ba Ruqayyah ba. Ko kuma kin fara duba ne ban sani ba?" Ruqayyah tace "ai ba sai nayi duba ba, ko makaho da baya gani in ya shafa ki ya shafa Adamu yasan baku dace ba. Driver ne fa" Inna tace "ya isa haka, maganar ta ishe ku haka"

Baba yace "ai na dauka zasu tashi ne su rufe mu da duka, tunda mu bamu isa dan muna guri su kama kansu ba, bamu kai wannan matsayin ba. Ke Ruqayyah da kike cewa basu dace ba saboda shi driver ne ji nake ke naki uban dako yake yi sanda uwarki ta aure shi? Kuma gamu nan har yanzu muna zaune lafiya bamu taba fada ba bata taba yaji ba. Ko kin dauka kudi shine komai a rayuwa? Ko kin dauka dan kin auri Hassan mai kudi shikenan kin gama tsallake siradin rayuwa? Ko kin dauka in ta auri talaka shikenan rayuwarta ta tabe ta lalace? Bani da komai aka dauki uwarku aka bani auren ta dan haka nima ba zan taba hana wani auren yata ba saboda dalilin cewa shi talaka ne. In dai har yana da addini yana da asali yana da lafiya yana da kuma hanyar da zai ciyar da ita kuma yana sonta itama tana sonshi to kuwa zan ba shi auren ta"

Ya juya kan Sumayya "ke kuma ki kiyaye ni ki fita daga idona, kin fara jaye-jayen mutane kuma ko? Wato shine wanda ranar nan ya dawo dake gidan nan da daddare ko? To zan hana ki zuwa gidan Hassan din sai inga inda zaku ke haduwa dashi. Kuma ki turo min shi kice yazo ya same ni a tambayi izini na indai har yana so ya nemi auren yata. Idan kuwa ba haka ba duk sanda na sake ganin ku tare ko kuma na ganki ko naji labarin kin shiga motarsa sai ranki ya baci" ya mike yana tsallake abincin sa. Sumayya tace "Baba maganar karatun fa? Yake zuwa gurinka kana koya masa?" Yayi shiru amma bai juyo ba, sai kuma yace "a cikin ilimi aka haife mu a cikin sa kuma muka tashi, babu abinda yake saka mu farin ciki kamar bayar da ilimi ga wanda bashi dashi. Ki ce masa yazo, zan bashi ilimi da yardar Allah".

A ranar haka Ruqayyah ta bar gidan su zuciyarta babu dadi, duk da dai taga alamar hankalin Inna Ade bai kwanta da cewa Adam inyamuri ne kuma iyayensa ba musulmai bane ba amma kuma bata jin hakan zai kawo wani babban nakasu a cikin lamarin, dan tasan yadda suke da soft heat for addini da zarar sun ga yana da rikon adfini kuma sun fahimci yana son Sumayya sosai to babu abinda zai hana su aura masa ita. Ita kuma bakin cikinta shine auren Sumayya da Adam zai kara rage mata kima a gidan mijinta, "ai kanwar Ruqayyah ce matar Adamu drivern. Ta runtse idonta already har ta fara jin ciwon abin a ranta, Hassan da yake ta bata labarin shirye shiryen da suke yi na tafiya shida Hussain yace "lafiya? Ko dai jikin ne? Naga kamar ranki babu dadi ko yauma kukan barin gidan zakiyi?" Ta tura baki "ka daina tsokana ta da kukan nan wallahi, nima zan nemi wani abun in ke tsokanar ka dashi" yayi dariya "haba yarinya, ai na gaba yayi gaba na baya sai labari, babu wani abu da zaki samu wanda har zaki ke tsokana ta dashi" tace "zan tambayi Aunty, na san sanda kana yaro ba zaka rasa wani abu da kayi ba wanda baka so a gaya maka" daga nan kuma sai hira, ya fara bata labarin yarintar su da irin yadda suke da Hussain, irin rigingimun Hussain shi kuma yana kare masa. Har ya bata labarin farkon fara kasuwancin Hussain da kason sa na gadon babansu. Tace "yanzu da ka yadda kun bashi kudin gabaki daya da maybe companies din sunfi na yanzu yawa, kuma da naku ne gabaki daya ba nasa bane shi kadai" Hassan yace "maybe. Maybe kuma da kudin sun lalace gabaki daya da yanzu mun koma Gombe gurin dangi da yanzu daya daga cikin mu ya fara shaye shaye, mayb. Haka rayuwa take komai bashi da tabbas" ya juya kansa yace "kullum abinda Hussain yake fada kenan. And now, I am beginning to believe him. Yanzu misali Adam bai yi min kama da zaiyi abinda yayi ba, tunda muka rabu dazu nake tunanin sa a raina. I so much wanted to help him especially saboda his religious issue, bana so ya koma ruwa duk dabanga alamar hakan ba amma an ce iyayensa har yanzu basu yi giving up ba. But tunda har zai kasance danger to my family dole I will have to let him go, amma zanyi kokarin ganin na taimaka masa ya samu kyakkyawar rayuwa outside my family" Ruqayyah tace "kana da kirki sosai mijina, in kayi haka ka kyauta sosai sai dai ince Allah ya vada lada. Kuma ina rokon wata alfarma, tunda kana maganar family ne dan Allah ka hada da Sumayya a ciki. Kayi wa Baba magana yayi mata iyaka dashi. Sumayya tana da rawar kai, ina tsoron kar ya jata zuwa wani abu wanda ba dai dai ba" ya gyada kai yace "insha Allah. Sumayya ai kanwa tace nima, zanyi wa Baba magana zan kuma yi masa bayani yadda zai fahimta" taji dadi a rata dan tasan yadda Baba yake girmama Hassan. Ta dora hannunta akan nasa tace "thank you mijina. Allah ya bar mu tare" yace "ameen my precious wife" suka yi wa juna murmushi.

Kwana biyu bayan nan Hassan ya gama yanke hukuncin abunda zaiyi akan maganar Adam. Sai ya dauko check yayi signing kudi masu kauri wadanda yasan zasu ishi adam ya kuma samun wani dakin na haya sannan kuma in ya chanchana su ishe shi ya kafa wani harkar samun kudin. Amma still baya jin dadi a ransa, sai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login