Showing 216001 words to 219000 words out of 300844 words
maganar mutuwar kawarta makes her guilty, idan bata da hannu a batan yaron mai yasa zata ce Fatima ta mutu? Me yasa zata yi karya? Sannan dagewarta akan dukiyar Hussain harda threatening bata masa suna duk dan saboda kudi makes her guiltier, saboda ya nuna irin tsabar son kudin datake dashi ya nuna cewa zata iya yin komai saboda kudi"
Sai kuma ya bada labarin irin yadda Ruqayyah ta yaudare shi har ya aure ta saboda kuɗin sa, da yadda tayi ta kokarin hada shi da Hussain da kuma Fatima duk dan saboda kudi, daga nan sai ya bawa Fatima hakuri akan sabanin da suka yi ta samu a lokacin zaman su tare, ta gyada kai kawai tana share hawaye, har a cikin bargon ta tana ji cewa Ruqayyah tasan inda dan ta yake.
Abubakar yace "then what are we waiting for? Aje a kama ta mana ayi ta dukanta har sai ta fadi gaskiya" Umar yace "that crazy crippled witch. Tabbas zata aikawa dan aikin da nake yi a yanzu a tare da ita na san irin masifar son kudinta, amma ba wai a kamata ayi ta dukan ta bane ba solution, mu masu hankali ne masu ilimi ne dan haka zamuyi aiki irin na masu hankali kuma masu ilimi, zamu shigar da karar ta court, a tsaya ayi Shari'a, hakkin Shari'a ne ta tuhume ta a matsanta mata har ta fadi gaskiya sannan a yanke mata hukunci dai dai da laifin ta. Wannan shine abinda za'a yi"
A haka aka tashi. Kowa ya yarda da shawarar da Umar din ya bayar, sannan mai martaba sarki ma bayan Umar din ya shiga gurin sa sai ya nuna masa amincewarsa akan hakan. A take kuma suka sake sabon zama tsakanin umar da Hassan suka nemi lauyoyin su suka yi hadin gwiwa gurin shigar da karar Ruqayyah a federal high court, Abuja.
A bangaren Sumayya, tunda suka zo gidan take jin babu dadi, take jin inama bata zo ba da ta sani tayi zamanta a gida amma kuma tana so tayi supporting mijinta, tana son duk sanda mijinta ya shiga wani hali ya kasance cewa tana kusa dashi yadda da ya juya zai ganta ya fahimci cewa he is not alone. Sai dai kuma jin ta take yi tamkar outsider a cikin su, musamman bayan an shiga taron an fito, bayan an gama maganganu akan abinda ake zargin Ruqayyah tayi, kuma duk kusan kowa a gurin yasan cewa Ruqayyah twin sister dinta ce, sai take jin tamkar Ruqayyah ta dauki wani mummunan tambari ta biga a goshinta. Taji stress din gayawa iyayensu ya kuma dawo mata, musamman yanzu data fahimci mugun abinda Ruqayyah ta aikata ba wai boye mutuwar Minal bane kadai, har ma da batan dan jaririn Fatima. Bata san ta yadda zata iya gaya musu ba, tana tsoron kar zuciyar wani daga cikin su ta buga su rasa shi.
Sannan ga Adam. Tunda suka shiga gurin taron ta ganshi, standing out a cikin duk mutanen gurin, tun daga kallon farko ta sunkuyar da kanta tana hana zuciyarta sake kallon inda yake, tana kara tunawa kanta cewa ita da Adam har abada, tana da mijin ta yanzu Hassan kuma yana sonta sosai itama kuma tana sonsa, yana kuma kyautata mata iyakacin kyautatawa. Bata kuma kallon sa ba, bata sani ba ko shi ya kalleta, bata sani ba ko yasan da zancen auren Hassan da yake kanta a yanzu?
Dan haka suna komawa cikin gida sai ta ware kanta daga cikin mutane ta zauna ita da zuciyarta tana lissafin yadda rayuwa take tafiyar mata. Taji hukuncin da aka yanke akan Ruqayyah and her heart break for her sister. Me Ruqayyah ta mayar da rayuwar ta da tasu gabaki daya? Ba zata taba iya musa laifuffukan da ake tuhumar Ruqayyah akan su ba kamar yadda ba zata iya musa cewa Ruqayyah twin sister dinta ce ba, ko ma menene tayi, ko ma menene za'a yi mata she is still her sister.
Ta goge hawayen fuskarta a lokacin da kira ya shigo wayarta daga Hassan. Ta daga tana kokarin gyara muryar ta tare da yi masa sallama sai yace "are you crying?" Ta girgiza kanta kamar yana ganin ta amma kuma sai kukan ya kwace mata gabaki daya. Yayi shiru yana sauraron ta, sai data gama kukan ta sannan yace "ki zo ki same ni yanzu" sai yayi mata kwatancen inda yake.
A wani kebantaccen guri ta same shi shi kadai akan kujera. Ta zauna a gefensa tana kara goge idonta. Sai ya rike hannun da hannun sa daya ya kuma dago fuskar ta da daya hannun yana kallon cikin idonta yace "she doesn't deserve a single drop of your tears" ta gyada kanta amma sai wasu hawayen suka sake zubowa. Ya sake ta yana kallon ta "kinsan dai dole ne a kaita court ko?" Ta gyada kai "na sani, I just can't believe zata iya aikawa duk wadannan laifuffukan. The baby, the innocent baby, I can't believe Ruqayyah zata iya hurting baby".
Ya dafe kansa da hannunsa, tunda ake yin maganar yakasa barin kansa yayi tunanin possible abubuwan da Ruqayyah tayi da babyn. Ba zai iya tunanin abin ba, in yayi tunanin kuwa tabbas zai iya rasa hankalin sa baki daya.
Tace "ni yanzu ta yaya zan gaya wa su Baba, ni kaina yaya nake jin maganar nan ballantana su? Ina tsoron abinda zai iya samun su ta dalilin Ruqayyah" yace "babu abinda zai same su, ki barni ni zan san yadda zanyi in gaya musu, kamar yadda zan san yadda zanyi in gaya wa Alhaji Kabiru ta hanyar da za'a samu maslaha da fahimtar juna. Amma Ruqayyah kiyi hakuri, dole hukunci sai ya hau kanta, dole ta fadi abinda tayi da yaron nan kuma dole a hukunta ta da duk laifin da aka kamata da shi"
Sumayya ta gyada kai, tana so ta saka zuciyarta akan abinda yake cewa amma ta kasa.
Sun dan jima a haka sannan yace "Adam yana tambayarki. He wants to know if you are okay" ta dan dago kai tana kallonsa tace "ka gaya masa ai, kace masa am okay ko?" Ya gyada kai yace "na gaya masa, ina so inji ne ko kina son ganinsa, kina so kuyi magana dashi dan ku......" Tace "duk abinda zanji daga gare shi na riga naji dazu, ya fadi dukkan excuse din sa kuma na gamsu dashi. Na ganshi lafiya lau yake. Babu sauran Magana tsakanin mu kuma" yayi shiru yana studying dinta, ita kuma tana jin idinsa a kanta amma taki dago kanta, kuma har cikin ranta tana jin cewa babu wata magana da zasuyi da Adam kuma.
Sai yace "shikenan. Na gaya masa dama cewa kinyi aure, though ban gaya masa wanda kika aura din ba yet, sai dai nan gaba" ta gyada kai kawai, shi kuma a cigaba dayi mata bayanin yadda suka fara shirya shigar da karar Ruqayyah. Already har sunyi waya da police za'a kamata a yau kafin su koma Kaduna.
"Bama son ta samu damar guduwa ko planning something"
*************. **************. *************
Jaririn ne a hannun ta yana ta tsalala kukan da take jinsa a cikin kwakwalwar ta ba a kunnuwan ta ba, kamar daga sama taga gate din gidan marayun a gabanta, cikin sauri taje ta ajiye shi a kofar gate din sannan ta juya da sauri zata bar gurin sai dai kafarta ta rike ta kasa tafiya, sai kuma kafafuwan duka fara kankancewa suna motsewa har suka koma kamar na jarirai sannan sai ya fadi a gurin da take, shi kuma jaririn data ajiye din sai yayi ta girma har ya koma katon cikakken mutum, ya taso zuwa inda take kwance sai taga kammannin sa sun zama irin na Hussain, sai ya daga kafa dai dai saitin fuskarta tamkar zai talitse ta.
Ta farka a firgice tana hada gumi, zuciyarta tana bugawa kamar zata fito daga kirjinta. Wannan ba shine karo na farko data yi irin wannan mafarkin ba amma kullum in tayi shi tana jin wani irin matsanancin tsoro da yake ratsa duk sassan jikinta, irin tsoron da bata taba jin irinsa ba a rayuwar ta. Ta share gurin fuskarta da bayan hannunta tana jin ana kiraye kirayen farko na sallar asuba.
Ta yaye abin da ta rufa dashi tana kallon motsatstsiyar kafarta, her heart breaking. Babu irin maganin da bata yi ba a cikin shekarun nan, na asibiti dana gargajiya dana islamic amma babu cigaba sai dai irin cigaban mai hakon rijiya. A halin yanzu ta fara tunanin duk son da take yiwa bene dole ta hakura ta koma dakunan kasa dan hawa benen ya fara gagarar ta. Ta kuma yi kokarin a saka mata lift a gidan amma likitan ta yayi advising dinta against it "the same pressure change da ake samu a jirgin sama irinta ake samu a lift" wannan yasa dole ta hakura dan bata shirya tafiya lahira ba.
Yanzu haka tayi order din wheel chair zata karaso next week...
Ta mike tana dogara sandan ta taje bakin taga sannan ta jingina da jikin bango ta daga labule tana kallon duhun garin, zuciyarta blank ita kanta bata san tunanin me take yi ba. A lokacin taga motsin mota ta fito daga gidan Hassan, tabi motar da kallo amma sai taga ta tsaya a kofar gate din aunty amma ba'a fito daga cikin motar ba. Jimawa kadan taga wata motar ta fito daga gidan Aunty, sai taga Hassan ya fito daga motarsa wani a shiga shi kuma ya koma seat din gaba, sannan taga Aunty da wata da bata gane sosai ba saboda duhu sun shiga motar Hassan sannan kuma ta lura akwai wasu a daya motar, sai taga sun tafi a tare.
Ta saki labulen kwakwalwar ta tana fara daukan chaji. Ina zasu je haka?
Har tayi sallah gari ya fara wayewa bata ji hankalin ta ya kwanta daga wannan tafiyar tasu ba. Ta lallaba da kyar ta sauka kasa inda tayi breakfast sannan ta zauna tana observing yaran ta suna ta kai kawon gyaran gida da sauran aiyuka. Sai ta kira lubabatu, daya daga cikin sababbin kuma amintattun yaranta. "Luba kije gidan Aunty, ki dan yi dabara ki tambayi mai gadi ko yasan inda suka tafi. Ki dan bugi cikinsa kadan in kinga ya fara tunanin wani abu sai ki rabi dashi ki tambayi na gidan Hassan".
Ta koma ta kwanta akan kujera tana jiran Luba ta dawo, tasan duk sanda mutum zai fita ya kan gayawa mai gadin gidan sa inda zashi. Maybe gurin da zasu je bashi da wani muhimmanci amma tana so ta sani, tana son ta san komai a harkokin su kar su shirya mata wata gadar zaren da bata san da ita ba.
Luba bata dade ba ta dawo dan direct mai gadi ya gaya mata kano suka tafi, kuma ya tabbatar mata gabaki dayan su ne suka yi tafiyar yara kadai suka bari a gidan. Labarin daya rikita zuciyar Ruqayyah, Kano? Me zai saka su tafi kano irin wannan tafiyar? Gabaki dayan su?
Har yamma tana ta sakawa da warwarewa. Tayi tunanin tayi amfani da wannan damar ta shiga gidan taga ƴaƴan ta, dan kullum suna ranta amma bata da damar ganin su sai ta taga, kuma tana zargin Sumayya ce ta hana ake kawo mata su dan da kafin a aure ta ai ana kawo mata su. Amma kuma mood din ta ba zata iya fita ba, zata jira har sai ta yanke hukuncin me Hassan da family dinsa suka tafi yi Kano irin wannan tafiyar.
Amsa daya kanta yake bata, Fatima ta dawo, ta jima tana jiran dawowar Fatima gida dan yana daya daga cikin abubuwan da suke hanata bacci, idan kuwa hakane to sun tafi kano ne dan suyi deciding fate dinta. Na farko tasan by now sun fahimci gawar wa suka binne, meaning yan uwan Minal will soon be after her too. Tayi bitar yadda komai ya kasance, bata san daga ina Fatima take ba kuma bata san me tayi a lokacin da bata gida ba but tasan soon zata sani dan tasan soon police zasu shigo cikin gidan su kama ta.
Ta yanke hukuncin abinda ya kamata tayi a yanzu, sauran hukunci kuma sai taji sauran bayani.
Ta dauko wayarta ta ta kunna kamar yadda ta saba yi kullum ta shiga twitter neman labari. And there, ta tabbatar da zargin ta. "Yar maimartaba Sarkin Kano da ake zargin ta mutu a hadarin mota shekaru biyar da suka wuce ta dawo gida".
Ta rufe shafin ta nemo number din secretary dinta. "Hello Lukman. Ina so ka bincika min the best lawyer available a kasar nan, as soon as possible. And I also want you to hire bodyguards for me" ta katse wayar sannan ta kira Luba ta aika ta sama ta dauko mata kaya masu kyau complete set, sai kuma ta saka ta ta hada mata ruwan wanka anan kasa ta shiga tayi ta shirya shaf da ita kamar zata je gida biki sannan ta dawo ta zauna ta zubawa kofar shigowa palon ido
Bata jima ba kuwa aka turo kofa aka shigo, police, as she expected. "Madam you are under arrest" sai ta dago musu hannu ta miko musu. Suka saka mata handcuffs sannan wata macen police ta taimaka mata suka fita da ita suka saka a motar su, a lokacin da suke fita daga gidan a lokacin ne kuma motar su Hassan take kokarin shiga gidan sa. Ta side din idonta ta kalle su, suka hada ido da Sumayya, sai kuma da Hassan, and she smiles. A very wide smile.
*Shari'a, Saɓanin Hankali*
A ranar Ruqayyah a cell ta kwana bayan police sun karanto mata abinda ake tuhumar ta dashi, direct kuma tayi denying all accusations against her, sai dai police din sun gaza gurin amfani da karfi dan tuhumar ta saboda kasancewar ta nakasashshiya kuma mace. Sai dai basu tausaya mata gurin garkama ta a cell tare da barin ta ta kwana akan dandaryar siminti cikin sauro da zafi. Haka ta kwanta a kasa a kudundune a cikin hijab dinta. Zuciyarta blank.
Sai dai kamar yadda ta rigata sani, sam bata yi bacci ba dan ta raba ga ta gama zama addicted to sleeping pills dinta, in dai bata sha ba to kuwa tabbas ba zata ko rintse idonta ba kuma tana sane taki tahowa dasu daga gida kuma taki fadar cewa tana shan magani, kukan jaririn bai barta ba haka kuma hoton gawar Minal bata daina kallon taba kamar duk sauran darare, amma haka ta daure sai cikin dare sannan ta tashi daga kwanciyar ta ta fara kurma ihu tana cewa gasu nan sun biyo ta zasu kamata.
Police din gurin suka yi kanta cikin tsawa da hargagi amma bata kula su ba ta cigaba da ihun ta har sai da suka bude cell din suka fito da ita sannan ta kankame wata police tana kuka wai copses ne suke binta zasu kama ta. Sannan ta gaya musu cewa kullum haka suke zuwa mata tayi ta ganin su, tayi ta ganin abubuwa wanda mutane basa gani, ta gaya musu cewa a yanzu haka tana kan medication a gurin likitan ƙwaƙwalwa kuma tana ganin mental therapist duk sati.
Wannan yasa da sassafe yan sanda suka tafi da ita gurin doctor din da tace ya dora ta on medication, likitan data gani tun lokacin da tayi overdose na sleeping pills, kuma ya tabbatar musu da cewa tana da file a gurinsa sannan ya tabbatar musu da cewa tabbas tana abinda ta fada na gane gane da jiye jiyen abubuwan da sauran mutane basa gani ko ji hakane. Wannan yasa police din suka bar ta a gurin sa dan ya cigaba da bincike akan lafiyar kwakwalwar ta, a bisa tsaron dan sanda guda daya.
Wannan abin yayi mata dadi, at least komai ya tafi a yadda take so kuma bata damu da cigaba da zama a asibitin ba dan dama ita da asibiti kawayen juna ne. Abu guda daya da ta sani dai shine, ko sama da kasa zasu hadu ba zata taba karbar laifin da ake tuhumar ta dashi ba, saboda da zarar ta karbi laifinta to ta tashi daga aiki, she is definitely going to prison and zata rasa duk abinda ta mallaka saboda kudin da Hassan ya bar mata na gadon Hussain ne, in kuwa har dan Hussain yana da rai to Hassan bashi da gado ballantana har ya bar mata. Ko da ace an bar wa duk sauran da suka ci gadon Hussain saboda basu sani ba ita dole a karbi kudin hannunta saboda ta sani.
She will never, never plead guilty. Duk wata sharia da za'a yi lalube ne a cikin duhu dan basu da wata shaidar cewa tabbas ta aikata abinda uke zargi, zargi ne kawai, kuma babu alkalin da zai yanke mata hukunci based on zargi. Karkarinta ayi ta jan shari'ar har a gaji a kore ta batare da an yanke hukunci ba. Matsalar ta kawai shine case din Minal, anan ne kuma take buƙatar lawyer din da zai tsaya mata yadda maganar zata tafi kamar yadda already ta riga ta tsara.
Daga Hassan har Sumayya sunga murmushin fuskar Ruqayyah, and that made Hassan very frustrated. Wato murmushi ma take yi ko? Ta salwantar da rayuwar dan Hussain and she is smiling, tana ganin taci banza kenan ko me take nufi? Sai a lokacin yayi nadamar da ya yarda suka shigar da police ciki. "Ruqayyah shaidaniya ce, shaidan ma kansa ya sara mata wajen shaidan ci. She is planning something, I can feel it" Sumayya ce tayi ta rarrashin sa, da kyar ya nutsu sannan suka shirya da daddare suka tafi gidan Baba tare, Hassan kamar yadda yayi wa Sumayya alkawari shi ya zauna ya gaya wa Baba, Inna Ade, Sulaiman da Zunnur labarin halin da ake ciki, da duk kanin zargin da ake yiwa Ruqayyah. Sannan a karshe ya gaya musu cewa tana hannun police.
Ranar Sumayya taga tashin hankali. Bata taba ganin kukan Inna Ade irin na ranar nan ba, kuma bata taba ganin kukan Baba ta sai a wannan ranar,tsinuwa ce kawai bai yi wa Ruqayyah ba har sai da Hassan yayi ta basu hakuri dan