Showing 69001 words to 72000 words out of 300844 words
bishiyoyin gurin ido tana kallon su tana lissafo rayuwar da take gabanta.
Bakin ciki dai kam tasan zata sha shi har sai ta godewa Allah. Abu daya ne zai saka ba zata fasa auren Hassan ba shine saboda tasan in ta rabu dashi ko a mafarki ba zata samu mijin da ya kai ko da rabin sa bane ba, ceo or not ceo tasan cewa Hassan ba sa'an aurenta bane ba kaddara ce kawai ta hada ta da shi har kuma ta kulla aure a tsakanin su, ta kuma san cewa yana son ta da gasken gaske, dan haka zata yi amfani son da yake yi mata gurin samun cikar burinta. Burinta na auren ceo, bata san yadda hakan zai faru ba bata san ta inda zata fara ba amma tasan abinda take so kenan, abinda ta hango wa kanta kenan. Wannan gidan, wannan valcony din na can sama shi take so. Title din matar ceo na H and H shi take so.
Su Hassan suna kai su Hussain gurin zamansu sai ya juyo ya dawo inda ya bar Ruqayyah, amma sai ya tarar bata nan sai Sumayya da bata ma san Ruqayyah ta tashi ba, ya zauna ya kira yawarta ta dauka ta gaya masa inda take, so take ya taso ya bar gurin bikin ya taho gurinta. Ai kuwa ko minti goma ba'a yi ba sai gashi a gabanta yana mata murmushi. "Shine kika gudu ko?" Tace "kida yayi kara da yawa, kaina kuma ciwo yake yi min" ya zauna a kusa da ita yana murmushi yace "wannan ciwon kai, ki gaya min yaya zanyi dashi ne" ta dafa kan tace "gajiya ce kawai, da ace ba'a taho dani ba kaga da yanzu ina can ina hutawa ta" ya gyada kai yana dada jin rashin dacewar tahowa da ita da Aunty ta dage sai anyi, sannan yace "kawo kan inyi miki addu'a" ta makale kafada yayi dariya "adduar ce ba kya so? Kin san dai adduar miji ga matarsa tana da saurin karbuwa inayi miki zaki ga kin warke" ita dai taki yadda, ta san wayon ya tabata ne babu wata addu'a da zai yi mata, wai ita zaiyi wa wayo bayan itama tana da wayon ta. Shi kuma yayi ta mata dariya, yasan abinda take gudu kuma abin yana kara masa sonta a zuciyarsa, yana kara nuna masa cewa she is pure, baya jin ta taba rike hannu da wani balagaggen namiji, dan haka tashi ce shi kadai babu wanda ya gutsira ya rage masa.
Ya saka hannu a aljihu ya zaro kudi, sababbin 200 notes bandir biyu ya ajiye a tsakiyar su, sannan yayi folding hannunsa yana kallonta yace "ga kudi nan, ban sani ba ko kina so ki shiga cikin gurin biki kiyi liƙi" ta kalli kudin sannan ya kalle shi, tana lura da yadda idanuwansa suke studying dinta tace "liƙi kuma? Dole ne sai anyi likin?" Ya girgiza kansa yace "ba dole bane ba, ra'ayi ne, ban sani ba ko kina da ra'ayin yi?" Ta dan yi murmushi tace "kai me yasa ba zaka je kayi musu likin ba" yace "ni bana yi" tace "saboda me?" Yace "saboda banga abinda hakan zai amfane ni dashi ba, a duniya da kuma a lahira. Banga amfanin in dauki kudin da zan iya yin wani abu dasu mai muhimmanci a duniya, ko kuma inyi sadakar su in samu ladan a lahira, sannan in ringa watsi dasu mutane suna rawa akai ba. I don't see the logic in that" ta harde hannayenta itama irin yadda yayi tace "kuma ni shine kake bani inje inyi?" Yayi murmushi bai ce komai ba, ta dauki kudin ta jujjuya su a hannun ta mentally tana calculating adadinsu, ba laifi, shima fa yana da kudin, ta mayar dasu ta ajiye tace "har na lissafo irin amfanin da za'a yi da wadannan kudin, ba zan zubar dasu a kasa ba" ya jima yana kallon ta, fuskarsa da sassanyan murmushi sannan yace "take it" tace "bazan yi likin ba fa" yace "na sani, ki saka su a jakarki ko zaku fita shopping dasu Nafisa, nasan babu abinda suke kauna irin shopping, maybe zaki ga abinda kike bukata kema" ta girgiza kai sai ya saka hannu ya dauki jakarta ya bude ya zuba mata kudin a ciki sannan ya rufe ya mika mata. Ta karba a hankali tace "Nagode" zuciyarta fal farin ciki, tabbas ta samo bakin zaren sa.
Hirar su suka kama yi, mostly labarin drama din da ake yi a gurin abokan su yake bata, yadda aka sako su a gaba ana ta tsokanar su shida Hussain akan aure, har zaunar dasu masu auren ciki sukayi wai suna koya musu yadda zasu yi wa matan su. Tun Ruqayyah tana dan basarwa har ta fara murmushi, daga baya sai gata tana kyalkyala dariya duk wani ciwon kanta ta bacin ranta ya tafi. Anan suka yi tasu dinner din, yayi waya aka aiko musu da abinci nan aka jera musu suka ci suka sha, yaji dadin zamansu a gurin sosai duk da yasan Hussain yana can ya kumbura in ya lura baya cikin gurin.
Suna komawa masaukin su Aunty ta kama hannun Ruqayyah "Ruqayyah ina kika je? Ina ta nemanki ni da nake so in ganki a kusa dani?" Ruqayyah ta danyi murmushi tace "uhmm dama........" Sumayya tace "tare da yaya Hassan suka fita, nima bansan inda suka je ba" Aunty ta saki hannun Ruqayyah tana cewa " wannan yaro, zai zo ya same ni ne, wato shine shi bai zauna ba ita ma kuma ya hana ta zama? Menene amfanin tahowa da ita da nayi kenan?" Tayi ta fadan ta ita kadai su dai su Ruqayyah suka fara shirin kwanciya bacci.
Karfe goma na safe aka daura auren auren Hussain Aminu Abdullahi da Gimbiya Fatima. Daurin auren daya samu halarta manya manyan kusoshin kasarnan dan Hussain duk wanda yake fada aji sai daya gayyace shi daurin aurensa, kuma yawancin su sunzo wadanda basu samu zuwa ba kuma sun turo representatives dinsu. An dauta auren ne a masallacin juma'a na kofar kudu, duk girman masallacin sai da mutane suka cika shi taf wadansu ma a haraba suka tsatstsaya, daga nan aka tafi reception, cikin gida kuma aka fara shirye shiryen daukan amarya zuwa kaduna inda acan kuma za'a daura auren Hassana da karfe biyu na rana. Dan haka ba tare da bata lokaci ba duk aka gama shiri, sannan aka dunguma gabaki daya har gaban mai martaba sarkin Kano, yau sai ga Sumayya da Ruqayyah a gaban sarki. Inda yayi wa Fatima doguwar nasiha akan aure, sannan kuma ya danka amanar ta a hannun yan uwan mijinta ya kuma yi musu addu'ar samun zaman lafiya da kuma zuriya mai albarka, daga nan sai aka bi aka rarrabawa duk matan da suke gurin littafin da maimartaba da kansa ya rubutawa Fatima na nasihohi akan zaman aure wanda yayi wa tittle da "Nasiha gareki yata Fatima" saboda ta ringa karantawa a duk lokacin da taji ta shiga duhu a game da zaman aurenta. Aka bawa duk matan gurin suma su ringa karantawa albarkacin Fatima.
Sai da aka daga Fatima za'a fita da ita sai ta saka kuka ta ruga gurin mahaifinta ta rungume shi, aka je da niyyar a dauko ta amma sai ya dakatar da mutanen ya mike da kansa ya kamata ya fita da ita ya saka ta a motar da zata kaita airport sannan ya shiga shima tare da kishiyar mamanta suka raka ta har gaban jirgi. Anan kowa ya kuma tabbatar da son da mai martaba sarki yake yiwa yarsa Fatima.
Ana sauka a Kaduna a ka cigaba da hidima, ana ƙoƙarin shiga da Fatima gidan ta kuma ana shirye shiryen daurin auren Hassana. Ruqayyah duk jinta take out of place, duk kuwa da cewa duk juyi sai Aunty ta kira sunan ta, sai ta lallaba ta ja Sumayya suka koma part dinta, Hassan ma ko duriyarsa bata ji ba bata sani ba mako ya dawo daga Kanon ko yana can, ta shiga daki kawai ta cire kwalliyar ta tayi wanka tayi kwanciyar ta, sama sama take jin guda da hayaniya daga gidan Hussain, ta san yanuwan amarya ne suke ta bidirin su a ciki, ta tashi ta jawo window ta rufe ta rufe curtain sannan ta kwanta, sai dai zafi take ji gashi dakin babu fanka ita kuma bata iya kunna ac ba, a haka tayi kwanciyar ta tana hada gumi.
Cikin ikon Allah sai ga yan gidan su nan sun zo, har da su Sulaiman da Zunnur da yan uwan inna Ade dana Baba, duk wadanda Inna ta bawa card din dinner sannan kuma ta turo su suje suyi wa Aunty Allah ya sanya alkhairi na daurin auren Hussain da Hassana. Yan uwan Hassan din da basu shigo ganin dakin amarya ba ranar da aka kawo ta suma duk suka shigo, wasu daga cikin yan uwan gimbiya suma suka leko, sai ya zamanto kamar wani bikin ake sakewa amma babu amarya, amaryar tana can ta kulle kanta a daki tana baccin wahala. Sai laasar ta tashi, shima gwoggo Habibah ce ta aiko Sumayya akan lallai ta tashe ta tayi wanka ta shirya ta fito. Dole ta tashi ta shirya din sannan ta nemi doguwar riga a cikin kayan lefenta ta saka tunda dinkunan nata sun kare sai wanda ta ware saboda dinner din yau. Ta kalli kanta a mudubi taga cewa tayi kyau sai dai idanunta da suka fada ciki suka yi baki. Ta danyi tsaki tana kara shafa hoda akan idon sannan ta fita.
Yadda taga gidan ya bata mamaki, ga abinciccika nan an kawo kala kala kowa yana serving kansa, ga kuma yan aiki nan an ajiye yadda daga an bata guri zasu gyara dan haka duk da yawan mutanen gidan fes fes yake yana kamshi. Ta gaggaishe da wadanda ya kamata ta gaisar su kuma wadanda ya kamata su gaishe ta suka gaishe ta.
Ana cikin haka sai ga jama'a nan suna ta shigowa, wai an kawo gimbiya gurinta za'a bata amanar ta a matsayin ta na yayar miji. A ranta tace "iyayi iya reto, wai matar da ta kusan haifa ta ita za'a bani amanar ta" aka zaunar da gimbiya a kasa, itama Ruqayyah aka zaunar da ita a kusa da gimbiyar sannan Aunty da sauran manyan iyaye suka zauna akan kujeru. Akayi ta jero musu nasiha akan su rike junansu amana. Aunty tace "to Ruqayyah da Fatima, ga amanar Hassan da Hussaini na na baku. Na san cewa kun sani marayu ne basu da uwa basu da uba dan haka basu da wanda yafi junan su kusanci da kansu. Dan Allah ku zamo sanadiyyar sake karfafa musu zumuncin su kar ku zamo sanadiyyar rushewar sa. Na san cewa Hassan da Hussain basa minti talatin a zaune tare ba tare da sunyi rigima ba amma hakan baya nufin cewa basa kaunar junan su dan ni ban taba ganin yan uwan da suke kaunar junan su ba kamar su. Dan Allah ku zamanto sanadiyyar karfafa wannan kauna a tsakanin su kar ku zama sanadiyyar haddasa gaba kiyayyar junan su a zukatan su". Daga nan sauran iyaye kowa ya kara da tasa. Duk sai da jikin kowa yayi sanyi a gurin harda Ruqayyah
Da zasu fita Aunty tace da Ruqayyah "in anyi magrib mai kwalliya zata zo tayi miki, sai ki fito da duk kayan da zaki bukata ki ajiye su a kusa sannan ki yi Sallah da wuri kar ta zo tana jira tunda ita zata yiwa Hassana ma. Fatima ta taho da nata" Ruqayyah ta gyada kai amma sai taji zuciyarta ta tabu, dan me aunty zata ce mata Fatima ta taho da nata? Ko tana tuna mata ne cewa ita bata taho da tata ba?
Bata yi wanka ba tunda tayi dazu, dakunan kasa aka budewa yan uwanta suka yi ta shirin su a ciki, bata tuna da kawayenta ba sai data ji hayaniyar su sun shigo sannan suka hau sama gurinta. Suna ta hayaniyar su kuma mostly zancen basu akan waye mai gidan kusa dana Ruqayyah ne, ita Ruqayyah sai taji suna kara mata pressure ne , tayi nadamar ina ma bata yi hayar su ba? Kadan daga cikin su ta sani suma kuma Minal ce kawai wadda ta sani sosai, duk sauran hada ta akayi dasu. Anan suka shirya, tare da hargitsa wa Ruqayyah kayan kwalliyar ta, wasu suka debi rabon su a ciki. A karshe ma sai da Sumayya ta faki idonsu ta kwashe kayan ta saka a closet ta rufe sannan aka samu lafiya. Shima suka yi ta mata mita. Ruqayyah kuwa sai shiga toilet tayi ta rufe kanta saboda hayaniyar su tayi mata yawa. Sai da aka ce ga mai makeup din tazo sannan ta wanke jikinta tayi alwala ta fito. Sai data yi sallah sannan ta zauna suka fara kwalliyar, yarinyar ta kware sosai a aikinta dan haka nan da nan ta mayar da Ruqayyah zuwa irin matan da take ganin hotunan su a Instagram. Ta taimak mata ta sak kayanta, making some adjustments here and there, yadda rigar ta zauna sosai, sannan ta saka mata duk accessories din da suka dace, wanda taga baiyi ba kuma tace a chanja wani, har ta gama shirya ta tsaf yadda Ruqayyah tasan ko a Instagram din ne ma sai an duba kafin a samu amaryar da tayi kyawun ta.
Sumayya ta fito da ita palon sama ta zaunar da ita sannan itama ta tafi ta fara nata shiryawar. Itama irin ankon kawayen Ruqayyah ne ta saka sai dai nata dark pink nasu light pink. Ita kuma amarya peach. Sai a lokacin Ruqayyah ta kira Hassan. "Ka manta dani" ta fada da muryar shagwaba, yace "kin taba ganin inda mutum ya mance da rabin jikinsa a wani waje? Tace "gashi kuwa, tun safe fa baka ko bi ta kaina ba" yace "sake dubawa dai, ki lissfa missed calls nawa na ajiye miki a wayar ki" tace "ni ban gani ba" yace "kun shirya? Cos Gamu nan fitowa yanzu" tace "mun gama ai, ku kadai muke jira"
Abun ya matukar kayatar yadda angwaye Hassan da Hussain suka shigo su kadai a mota daya, Hussain da kansa ne yake driving Hassan yana gaba, suka fara zuwa kofar gidan Hassan Ruqayyah ta fito a bisa rakiyar kawayenta ta shiga sannan suka karasa kofar gidan Hussain Fatima ta fito itama ta shiga ita kadai, suka rufe mota suka ja suka yi tafiyar su. Sai bayan sun fita sannan aka fara rububin shiga motoci ana bin su a baya. Suna zuwa gurin taron suka yi packing a bakin kofar shiga gurin sannan suka yi zaman su a mota.
Tun da Fatima ta shigo take ta yabon kyawun da Ruqayyah tayi, wannan yasa Ruqayyah ta kara kumbura tana ta faman fasa kai duk kuwa da cewa tun da Fatima ta shigo motar taji ta raina kanta, hatta kamshin da take yi na daban ne yanayin kwalliyar ta ma haka. Fatima irin cikakkun matan nan ne masu cikar kirji da hips, wannan yasa kayan jikinta suka yi mata matukar kyau suka fitar da kyakykyawan fasalinta duk da cewa ba kama mata jiki suka yi ba, ga kuma dogon trail din da aka dinka a jikin rigar kamar yanayin dinkin alkyabba daya taso tun daga kafadar ta ya rufe mata kurjinta sannan ya sauka har kasa yana jan kasa yana binta a baya, sai ya zamanto kamar yayi serving a matsayin mayafi kenan. Angwayen kuma anko suka yi, komai nasu iri daya ne hatta agogon hannayensu, sai a lokacin Ruqayyah ta kara tabbatar da kamannin su. Hira suke tayi, Hussain yana ta tsokanar kowa har Fatima bai bari ba ita ma kuma sai ta rama, yace wai kowa a cikin su ya kure adaka dan ace sunyi kyau shi kuma yasan duk ya fi su kyau, har da posing yake yi wai matso kyan sa yake yi, wai sai lallai sunce duk yafi su yin kyau. Ita Ruqayyah yadda taga Fatima tana magana da dariya sai abin ya bata mamaki, sai taga kamar ba wannan gimbiyar da bayi suke kwanciya a gabanta bace ba. Ita ta dauka ai da kyar take magana saboda mulki. Sunyi ta hotunan su a cikin motar, itama Ruqayyah ta dan ware tayi magana da taji Hussain ya saka ta a gaba wai in bata magana zata haifi kurma. Suna ganin mutane suna ta shiga hall din, sai da aka tabbatar kowa ya gama shiga sannan aka zo kiran su, a lokacin itama Hassana da angonta Saeed sun karaso. Sannan sai suka jera suka shiga. Kawayen sune suka fara shiga a layi, kawayen Ruqayyah a farko, sai na Fatima sannan na Hassana, kowanne sunyi anko. Daga sai masu gayya masu aiki, Hassan rike da hannun Ruqayyah a gaba, Hussain da Fatima a tsakiya, Hassana da Saeed a baya. Sai kuma abokan angwaye suka take musu baya. Abin gwanin burgewa.
Komai ya tafi bisa tsari, anci an sha an bar abinci, anyi programs masu kayatarwa yawancin su na barkwanci, sannan Aunty ta gabatar da jawabin godiya ga duk wanda ya samu halartar bikin. Daga nan kuma sai akayi ta daukan group pictures. Anyi kida nayi rawa, amma sai amaren duk kamar sun hada baki suka ƙi yin rawar. Angwaye kan sun cashe abinsu, abin mamaki sai ga Hassan ya biye wa Hussain suna ta rawa, ai kuwa nan take guri ya dauki ihu da tafi aka fito akayi ta musu ruwan kudi, kudi dai kam kamar ba'a talauci a Nigeria. Daga nan sai suka yanka cake akayi addu'a aka tashi.
Daga gurin taro aka wuce da Hassana gidan mijinta, wannan yasa duk yan gidan basu dawo gida ba can suka wuce, amaren ne kawai da kawayensu suka dawo. Kamar yadda aka dauke su haka aka dawo dasu, aka fara sauke Ruqayyah sannan aka karasa da Fatima.
A gajiye Ruqayyah ta shiga gida. Gidan ba kowa tunda su suka fara fita amma tas tas dashi yan aikin da aka kawo mata sun gyara mata shi kamar ba'a yi taro ba. Ta wuce sama ta cire tarkacen kayan jikinta dama duk sun bi sun ishe ta