Showing 291001 words to 294000 words out of 300844 words
da zagaye gurin da idonsa har idon ya sauka akan wata double door, ya tafi gurin da take ya saka hannu biyu ya murda handles din sannan ya tura su suka bude gabadaya yana jin fresh air tana wuce shi tana shiga palon. Ya lumshe idonsa ya bude yana dora hannun sa akan tudun diary din da aka bashi, his father's words written for him. Ya shiga cikin balcony din tare da zaro diary din ya bude, yana lura da yadda pages din suka manne da juna saboda dadewa, a page din farko yaga an rubuta
Dear baby.. .....
Sai yayi murmushi, wai shine baby din.
Motsiya ya hango daya dauki hankalin sa a waje, ya rufe diary din, this is not the time to read it sai ya samu nutsuwa tukunna. Ya mayar da shi cikin aljihun sa tare da kallon kasa dan ganin abinda yake faruwa. Sumayya ya gani tare da Hussain da Yusuf da Amatullah da Abdulrahim sun fito daga cikin gidan, Ruqayyah a rungume a kirjin Hussain yayi mata irin daukan jarirai. Yana kallo Yusuf ya tafi da sauri ya kunna mota sai suka bude baya suka saka ta sannan Hussain ya shiga gaba Sumayya kuma ta shiga baya kusa da Ruqayyah sannan wata mata mai kayan ma'aikatan asibiti ta shiga daya side din Ruqayyah suka tafi suka bar Amatullah da Abdulrahim.
Yayi shiru yana tunani, yasan dauke ta suka yi daga gidan zadu chanja mata wani gurin zaman, sai kawai yaji zuciyarsa tana jin babu dadi saboda su, saboda su Hussain, they didn't choose her as a mother Allah ne ya basu ita, kaddarar su ce. Sai ya mike straight yana realising wani abu, between yesterday and today yayi loosing kansa, yayi mamakin yadda akayi jiya har ya shigo gidan da niyyar kashe Ruqayyah bayan kuma shi din shine kullum mai yiwa mutane preaching akan yadda da kaddara, shine mai gayawa mutane cewa is either suyi accepting destiny dinsu a yadda yazo suyi murma ko kuma su yi living a miserable life, amma shi ga shi lokaci daya bacin rai ya saka ya manta cewa destiny dinsa ne rayuwa for 35 years ba tare da iyayensa ba. Kamar yadda yake destiny din su Hussain ne su zama yayan mutum kamar Ruqayyah.
Ya lunshe idonsa ya bude yana kallon su suna fita da ita daga gidan da tayi asarar komai saboda ta mallaka kuma mallakar tasa bata samar mata komai ba sai karin wasu asarorin masu yawa. Karar wayarsa ce ta katse masa tunanin sa, ya dauko ta yana ganin number din sultan ya dauka da sauri "ba dai har kun karaso ba" yace "yanzu dai zamu iso insha Allah, ka fito kan hanya sai ka tarye mu, matar nan taka ce ta bata mana lokaci tana ta hado maka kaya sai kace cewa akayi ba zaka dawo Abuja ba" Amir yayi murmushi, "kar ka takurawa sweetheart dina please, nasan haka zaka saka ta a gaba kayi ta tsokana har ku zo" yace "ba kula ni zata yi ba, tana ta faman dashe baki kamar gonar auduga" Amir yace "bata waya" Sultan yace "anki din, ai kana da number din ta kakira ta mana, ni mata basa karbar mim waya kar su goga fuskar su a inda na goga tawa. Kasan matata tana da kishi" Amir yayi tsaki. "Allah yasa dai nima ina da matar. Ballantana a yi min gori, kuma soon zan zo in wuce ka in ka tsaya wasa" ya kashe wayar yana dariyar mugunta sannan ya kira Aysha, yana sauraron yadda take ta murna, yana jin Maimoon tana tsokanar ta, suka yi sallama bayan ya gaya musu inda zasu tsaya in sun shigo gari.
Ganin Amatullah da Abdulrahim sun fito daga gidan da kaya a hannun su ya saka ya juya ya fita da sauri yana hada stairs a uku uku har ya fita waje sannan ya gansu sun dauki hanyar gate sai yace "psss" suka juyo a tare da alamar damuwa a fuskarsu sai kuma yaga sun fara kokarin yi masa murmushi, ya karaso inda suke da key din mota a hannunsa yace "ina zuwa haka?" Abdulrahim yace "gida, kaya ne zamu bayar a shiga dasu ciki" ya gyada kai kawai yana so ya tambaye su inda za'a kai Ruqayyah amma sai yayi shiru, Amatullah tace "kai kuma fa? Na ganka da key" yace "mutanen Abuja ne suka kusa karasowa shine zanje hanya in taho dasu, ko zaki rakani?" Ta danyi shiru kamar zata ce a'a sai kuma tayi tunanin shima bako ne ba lallai ya san hanya sosai ba sai tace "Okay bara in dan gyara sai mu tafi" ya kalle ta sama da kasa yace "you look fine, great even. Me zaki gyara? Common let's go" ta dan bata fuska, Abdulrahim yace "yar gayu ce fa, bata fita sai tayi kwalliya, bara inzo muje" sai Amir ya harare shi ba tare da Amatullah ta gani ba, Abdulrahim a danyi dariya kadan yace "ohh na manta ana jira na zamuje wani guri yanzu. Kuje kawai sai kun dawo. Ya karbi jakar hannun Amaty yayi gaba da sauri.
Bata motsa ba har Amir yaje ya dauko motarsa da tun daya gyara mata packing jiya bai kuma bi ta kanta ba, ya zo gaban Amaty ya tsaya sannan ya bude mata kofar kusa dashi ta zagaya ta shiga ta rufe suka tafi. Har yanzu yana ganin alamar damuwa a fuskarta sai ya tambaya "naga dazu an fita da........" Sai kuma ya kasa fadar sunan dan shi dai yaji a ransa ba zai iya ce mata aunty ba kuma ba zai iya kiranta da sunanta a gaban Amaty ba, sai ta hutacce shi tace "Aunty Ruqayyah. Eh an mayar da ita gidan yaya Yusuf zata cigaba da zama a can" ya danyi shiru yana jin sa lost, sannan yace "amma babu takura acan din? Ina nufin iyalin yaya Yusuf ba zasu gako an takura su ba?" Ta girgiza kai tace "babu, ai akwai maaikaciyar lafiyar da yaya Hussain ya dauka musamman saboda take kula da ita, to babu wani nauyi da za'a dora musu. Dama tun da aka sallamo ta daga asibiti yaya Aminu yace ta koma Abuja gurinsa mommy ce ta hana, sai yanxu kuma da kanta tace a mayar da ita gidan yaya Yusuf din tunda shi ba barin garin za'a yi ba. Ita bata so tayi nisa da ita ne kawai" ya gyada kai cikin fahimta, amma kuma bakinsa ya kasa furta komai.
Suka cigaba da tafiya zuwa inda zasu hadu dasu Sultan cikin shiru sai dan nuna masa hanya da take yi. Sai ta dauko sunglasses ta saka a idonta dan boye damuwar ta har suka je i da zasu je duka yi packing ya kira su suka ce sun kusa karasowa suma. Sai ya fara kokarin kawar da tension din tsakanin su ta hanyar bata labarin family din shi, Aysha da yaran su, ita kuma tunda mai son yara ce sai ta fara murmushi tana jin dadin hirar. A haka har bakin suka karaso sukayi packing motocin su suna facing juna, driver yana tukawa Sultan a gaba sai Aysha da Maimoon a baya tare da little Sultan da Afnan a hannun Aysha, sai yace mata "akwai kyauta ta musamman in kika gane wacece matata a cikin matan can guda biyu tun kafin inje gurin" ta danyi murmushi tace "okay" amma kafin ya bata amsa sai yaga Sultan ya bude mota ya fito sannan ya bude wa Maimoon kofa yana cewa "gwara dai in fito da matata in rike hannun abata, kar wani yazo wucewa ya dauka ta mai rabo ce".
Amatullah tayi dariya, Amir ya bita da kallo yana jin dadin ta saki jikinta tace "ta cikin motar wacee akayi abandoning ita ce matarka" ta mika masa hannu "a bani kyauta ta" yace "the bastard. Duk inda yake sai ya nuna halinsa, gashi nan ya tona min asiri. Bara nima inje gurin matata" ya fada yana bude kofa sannan ya leko yace "kina bina bashi".
Bai kula Sultan ba ballantana Maimoon matarsa sai ya tafi da sauri ya budewa Aisha kofa ta fito ya rungume abarsa, tana ta murna, su kuma su Sultan da Amatullah da take cikin mota suna ta murmushin taya su murna dan tabbas abin murna ne ya same su ba karami ba. Sai daya gama jin dumin matarsa sannan ya juya kan abokin sa shima ya rungume shi duna tasu murnar, kowa ya gansu sai ya lira da kauna da kuma shakuwar da take tsakanin su.
Amatullah ta fito cikin takunta mai kyau ta karaso inda suke tace "Assalamu alaikum. Sannunku da zuwa" suka juyo tare da amsa mata, ta dan rissina ta gaishe su, Maimoon tace "babu sauran tantama Amir, tabbas daga gida kake" ya nuna Amaty yace "she is my cousin" sai Sultan yace "babu bayani ma, she looks more like your sister ma ni a idona" Aysha kuma tana murmushi tace "ni kuma tafi yi min kama da little sultan ma" Amatullah ta kalli little sultan din da yake fitowa daga mota, daga alama sanda aka tsaya bacci yake yi sai yanzu ya tashi, ta mika masa hannu tana cewa "gaskiya ne Aunty Aysha munfi kama, musamman tunda bamu tara gashi a fuskar mu ba" duk suka yi dariya sun san tsokanar Amir take yi. Sai kuma Amir ya tambaye su yara, Maimoon tace "mun barsu gida saboda school. Suna gurin auntyn su Aisha" sai a lokacin ya kara godewa Allah da bai gaya wa Aysha yarinyar daya nema ba.
Ta dauki Sultan ta daga shi sama tana tayi kissing cheeks dinsa tace "bara in dauki rabona na kisses din da zaka samu dan in muka je gida Aunty sai ta lashe ka tas" yace "wacece aunty? Wacece ke?" Ta zaunar dashi a bonet din motar tace "ni sunana Amatullah, ni auntyn ka ce. Aunty kuma kakar Abban ka ce" Sultan yace "har da kaka ka samu Amir" Amatullah tace "har da kaka mai ran karfe, da kuma tarin iyaye lodi lodi"
Sai kuma Amatullah ta karasa kusa da Aysha tana cire sunglasses din idonta tare da saka su a jaka tace "kawo babyn, sai ki ji dadin rike mijin" duk suka yi dariya har Aysha data mika mata Afny da take bacci, sannan babu kunya ta kara rike mijin nata. Amaty tana kallon afnan tace "lah Yaya Amir, kasan babyn nan dawa take kama?" Ya juyo da sauri yana kallon ta yace "da wa?" Tace "aunty Fatimah wallahi. Ni dai da Aunty Fatimah naga tayi min kmaa" sai Amir yaji wani irin dadi a ransa..
Tun bayan da yayi aure ya kuma haifi Sultan, sai tunanin sa na problem din rashin Asalin sa ya tashi daga kan sa ya koma kan yayansa, wannan ne dalilin da yasa ya lallaba Aysha suka yi planning saboda yana tausayawa yaran dan yasan gorin ba a kansa kadai zai kare ba har sai ya dangana dasu da kuma yayansu. Amma ga yadda al'amurra suka juye masa, wai yau har yarsa ake cewa tayi kama da kakarta, mamansa.
Sai kuma suka koma motocin su sannan suka karasa gidan. Tunda suka yi packing suka fito Sultan ya daga kai yana kallon gidan yace wow, sai Amir yace "hold your wow tukunna, zata yi maka amfani nan gaba". Gidan aunty aka fara shiga dasu, nan take Aunty ta rude ta rike Aysha ta rike little sultan ta ma rasa wanda zata tarya acikin su, ta kuma rasa da wanne baki zata yiwa Allah godiyar wannan kyauta da yayi mata. Wai yau ita ce ta ga ba ma dan Hussain kadai ba har ma da yayansa. Amatullah da take zaune akan hannun kujerar kusa da Aunty tace "aunty ki saki yaron nan Please, kar kije ki shafawa dan mu tsufa muzo mu rasa yadda zamuyi dashi in kin tafi, na sanki yanzu sai ki ce shima ya zama mijinki" Aunty ta harare ta "kinsan dai ni maxa har yawa suka yi min kullum sai na zaba na darje. Ke kuwa fa? Iyayi da kinibibi ya hana ki samun miji ko da guda daya ne. Ji wannan uban gilashi sai kace tsohuwar makauniya" Amatullah ta tura baki tare da mikewa. "Ni daya kwakwkwara zan samu ba irin mazajen ki ba taren yuyuyu"
Sun jima nan gurin Aunty sannan kuma suka tafi gidan Hassan, anan suka samu tarya mai kyau da abinci iri iri ga kuma shimfidar fuska. Sultan karami kuwa dama gidan Aunty aka baro shi ya samu yara saaninsa ya shige cikin su suna ta wasa sai da Sumayya tayi waya tace a rako shi suma su ganshi sannan sai gashi an kawo shi. Hassan kuwa ya dauka ya rungume ya hana Sumayya tabawa ita kuma ta karbi afnan tace shima ba zai dauka ba. Aysha kuwada Maimoon suna dakin Amatullah nan sukayi sallah harda kwanciya akan gado suka huta, ita kuma Amaty ta zauna tana tayi musu hira tana kuma amsa wa Aysha tambayoyin ta akan family kamar yadda ta ringa amsawa Amir. Amma bata bata labarin komai in details ba tunda tana ganin hurumin mijin ta ne ya bata wannan.
Sai bayan da Amir da Sultan suka ci abinci tare da Daddy da sauran mazan da suke gidan sannan Amir ya fita da Sultan zuwa gidan sa suka zauna acan su biyu kuma ya bashi labarin duk abinda ya sani game da yar da shi da akayi da kuma samo shi da akayi yanzu. Sultan ya taya shi murna sosai da sosai. Sai suka kira matan su suma suka zo suka ga gidan tare da rakiyar Amatullah. Suna nan har dare sannan suka koma gidan Daddy suka ci abincin dare shi kuma ya gama musu gobe gabaki daya zasu je Abuja suyi gaisuwa gurin mai martaba sarki kuma suyi godiya. "I can't wait to see his face idan yayi realising Amir dan abokin sa ne"
Da dare Sumayya tace su Aysha da Maimoon su kwana anan gidan gurin Amatullah tunda godan Amir din sai anyi gyara sosai a ciki, amma su kuma mazan zasu iya kwana a ciki. Amatullah tana ta murna tana tsokanar su "yau kowa ta zama gwaurowa, sai ku kwanta inyi ta muku tatsuniya" Maimoon tayi murmushi tace "rike tatsuniyar ki, in dai mazan mu ne basu san bakunta ba ballantana alkunya. Muna nan dake zaki ga abinda zai faru" ai kuwa ba'a jima ba Amir ya kira Aysha a waya wai su fito ita da Maimoon suji wata magana mai abin mamaki" suka dauki mayafan su da sauri kamar dama jira suke yi suka lallaba suka fice suka bar Amatullah da citson yatsa, bata kuma ganinsu ba sai data farka da assuba ta gansu suna bacci, bata san kuma ta yadda suka shigo ba.
Da safen kuwaaka shirya, iyaye da kuma manyan yaya, suka dauki hanyar Abuja bayan Sultan yayi waya ya sanar da zancen zuwansu da kuma abinda yake tafe dasu. Sanda suka sauka sai aka shigar da mazan gurin saukar baki na musamman da yake cikin gidan, matan kuma suka wuce cikin gida bisa jagorar Maimoon da Aysha, wadanda dama tare aka taho dasu. Suka wuce dasu direct gurin Ummee mahaifiyar Sultan, anan Sumayya taga balarabiyar da ake magana akanta. Sun samu sauka sosai a fadar Abuja abin dai sai san barka, Ummee da kanta take waya kowa da yasan Amir yazo yaga iyayensa gasu nan sunzo, haka aka yi ta zuwa ganin su kuma kowa yana ganinsu yake tabbatar wa cewa babu ja Amir dansu ne, sai kuma mutane suyi musu murna su kuma yiwa Aysha murna dan duk sun san sacrifice din da tayi ta auri Amir, sacrifice din da ba kowacce macece zata iya yin sa ba. Amma kuma yanzu gashi Allah yayi mata sakayya, dan ganin yanuwan Amir kadai ya isa ya nuna wa mutane cewa yan dangi ne kuma sun jiku da raina, da zarar an ambaci H and H kuwa sai abar mutane da sakakken baki. Mamakin kuma sai ya karu idan aka ambaci gidan sarautar kano a matsayin dangin sa na uwa.
"Lallai Amir din mu dan gata ne gaba da baya. Shi yasa aka ce duk inda kaga mutum kar ka wulakanta shi dan baka san ko shi waye ba"
A gurin maza ma haka ta kasance, hakiman gidan, yan'uwa da sauran bayi da barori kowa zancen yake yi "Amir dai wannan yaron abokin Sultan" "shine mai H and H din?" "Babansa ne, kuma uban ance ya mutu, kuma shi kadai ne dansa a duniya" "babarsa kuma yar marigayi sarkin kano ce, kanwa kuma ga sarkin kano na yanzu" "dan sarauta ne kenan?" "Sosai ma" "shi yasa ni tun farko naji ina son yaron nan, tun suna hatsabibancin su a gidan nan. Ashe babban mutum ne" Hmmmm
Mai martaba sarki yayi murna matuka, ya kuma yi mamakin tare da alajabin kasancewar Amir da a gurin abokin sa Hussain. "Hussain mutumin kirki ne, yana kuma daga cikin abokai na wadanda har yau ba zan taba mantawa dasu ba dan nasan da yana raye da har yanzu abotar mu tana nan. Labarin rasuwar sa data matarsa mai dauke da cikin tilon dansa ta taba zuciyata sosai a lokacin, har naji duniya duk ta fita daga kaina. Amma sam ni bani da labarin ma cewa Fatima ta dawo gida bata mutu ba, ba kuma ni da labarin har anyi Shari'a ana neman dansa. Amma hakan ba abin mamaki bane ba saboda akwai abubuwa da dama, abubuwan da suke da tsananin muhimmanci a gare ni da wadanda ban basu muhimmancin daya kamata ace na basu ba. Tabbas Amir muna yi maka murna, kuma wannan ya saka ka kuma zama da a gareni sosai fiye da yadda kake a da saboda dan Hussain tabbas da na ne. Amma kuma muna jimamin rabuwa da kai a gidan nan, dan munsan dole zaka koma gurin mahaifan ka, sai dai kuma munsan zumunci a tsakanin mu yanzu ne ma aka fara shi insha Allah".
Basu dawo Kaduna ba sai dare, kuma tun a hanya Hussain wanda shi Hassan ya dora wa bauyin shirye shiryen tafiya Dubai ya tabbatar musu da shirin yayi nisa tunda yasan wani a embassy wanda ya taimaka masa sosai gurin samar musu